← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 80

Sashe 46

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Miƙewa ya yi tare da ɗaukar sandar sa ya ya fara dogarawa a hankali,babu abinda jikin sa yake yi sai rawa kamar zai faɗi ƙasa, bedroom ɗin umma ya shiga domin ya san bazai wuce nan rufaidan take ba,yana shiga ya ja ya tsaya turus tare da ƙare mata kallo.

************************************

Zaune take a kan bed ɗin ta cikin shirin bacci tana duba litattafan ta na makaranta,ƙarar wayar ta ce ta katse mata karatun da take yi,miƙa hannu ta yi ta ɗakko wayar a kan bed side drower.

Ganin wanda yake kira ne ya sa ta mai da wayar in da ta ɗakko ta ta ci gaba da abin da take yi,ganin wayar ta dame ta da ringing ne ya sa ta ajiye littafin gefe guda tare da yin picking call ɗin ta kara a kunnen ta ta yi shiru.

Daga ɗaya ɓangaren MUKHTAR ya sauke wata irin ajiyar zuciya har tana jiyo sautin ta,da ƙyar ya iya buɗe baki yace mata:

"My love! so kike yi zuciya ta ta buga ne!! Me ya sa bakya tausayi na ne! kina ji ina kiran ki amma kika ƙi ɗaukar waya ta ko!!"

Shiru ta yi bata ce komai ba.
Ajiyar zuciya ya ƙara sauke wa a karo na biyu tare da cewa:

"My love kina jina kika yi shiru! gaskiya ina tunanin zan dawo gida ko ban kammala abin da nake yi ba,gwara na dawo na gayawa daddy a saka lokacin bikin mu ko hankali na ya kwanta,kar naje nayi sake wani ya yi min sakiyar da babu ruwa!!"

"Aure kuma habibi.?"
"Eh gwara a aura min ke gaskiya duk in da nasa ƙafa na cire kema ki saka taki!!"

"To ai ba yanzu ba na yi ƙarama sosai, kuma ma ai karatu nake yi"
Ta ƙarasa maganar cikin shagwaɓa.

Wani irin mayau darin murmushi ya yi wanda shi kaɗai ya san ma'anar sa.
"Ohh! ba kyaso mu yi aure yanzu amma shine idan na kirawo ki kike ƙin ɗaukar waya ta.?"
Cike da shagwaɓa tace:

"To ba kai ne muna waya ɗazu ka kashe ba"
"Ohh!! am sorry my love bazan sake ba kin ji "
Kan ta ta girgiza kamar tana gaban sa.

"Yaushe zaka dawo??"

"Kina so na dawo ne my love..?
"Kin yi missing ɗina..?
Cike da yarin ta tace masa:

"Eh"
"Very soon in sha Allah"
"Me kike so na taho miki da shi"
"Duk abin da ya yi maka ina son shi habibi na"
"Okay tom shikenan,yanzu bari na barki ki kwanta ki huta sabo da school ko..?"

"Okay habibi na goodnight"

"Good night my love muahhh".

Da sauri ta kashe wayar tare da runtse idanun ta, addu'a ta yi tare da kwanta wa cike da tunanin mukhtar ɗin ta.......✍🏻✍🏻

Ina matuƙar godiya da addu'o'in ku a gare ni, ku ɗin na musamman ne a cikin zuciya ta, ina yi muku fatan Alkhairi ƙwarai da gaske, Allah ubangiji ya saka muku da mafificin alkhairin sa ya biya muku buƙatun ku.

Daga alƙalamin FATIMA BINTU ABDULLAHI (UMMU AYSHA)....✍🏻✍🏻

Ga me buƙatar littafin tun da farko har zuwa in da aka tsaya ya tun tuɓe ni ta wannan numbern wayar👇🏻👇🏻

08162055134

Share fisabilillahi..

💝💞HALIMATU💝💞

(Love, sacrifices, destiny & betrayed)

💝💞💝💞💝💞💝💞

Story & Writing

By

FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)

Ƙarƙashin jagorancin

(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)

Golden pens.........✍🏻✍🏻

💝💞💝💞💝💞💝💞

A 2024 novel

💝💞💝💞💝💞💝💞

Pages____________57&58

_________________washe gari tun da asuba ta tashi kamar yanda ta saba,bayan ta idar da sallah ne ta sakko ƙasa zuwa kitchen domin ta taya baba ladi aikin haɗa break fast,cikin ƙanƙanin lokaci suka kammala da yake ba wani abu mai wahala suka yi ba.

Kasancewar daddy baya gari shi ya sa,dama idan yana gari amfi yin girke-girke kala-kala.
Sakkowa ta ke yi daga saman bene a nutse cikin shirin makaranta,kamar koda yaushe shigar ta ta guda ɗaya ce dai doguwar riga da hijabi har ƙasa da kuma niƙaf,kan sofa ta zo ta zauna a gefen momy, hannayen ta ta saka guda biyu ta rungume momy tare da ɗora kan ta a kafaɗar momyn.

Ɗagowa momy ta yi ta ƙura mata ido tare da cewa:

"Me yake damun doughter na ne.?"

Ajiyar zuciya ta sauke sakamakon jin wani irin connection da yake fitowa daga cikin jikin momy yana shige wa cikin jikin ta.

"Kin yi shiru doughter na! me yake damun ki ne.?? tell me my baby.??"

Ƙara narke wa ta yi a cikin jikin momy cikin shagwaɓa tace:

"Momy wai yaya MUKHTAR ne ya ce zai dawo ya faɗa wa daddyn sa a saka ranar auren mu!"

Ta faɗa hawaye na zubo wa a saman kyakkyawar fuskar ta.
Cike da damuwa momy ta saka hannun ta ta share mata hawayen ta cikin sigar lallashi ta ce:

"A'a rabu da shi wasa yake yi miki kin ji doughter na,aure ba yanzu ba sai kin ƙara girma kin ji!!"

Murmushin farin ciki ta yi har dimple ɗin ta guda biyu suna lotsa wa.

"Ki kwantar da hankalin ki kin ji,babu mai yi miki aure yanzu"
Kan ta ta girgiza tare da ƙara rungume mommy,hannu momy ta ɗora a kan ta tana shafawa a hankali tare da cewa:

"Ta shi ki je doughter driver na jiran ki kar ki yi late kin ji.?,idan kin dawo daga school zamu je ki yi shopping kin ji..?"
Girgiza kai ta ƙarayl yi a karo na biyu ta miƙe tsaye cike da murna ta yiwa momy sallama tare da ficewa.

Ƙarfe 04:pm dai-dai ta dawo daga makaranta,ba ƙaramar gajiya da yunwa ta kwaso ba kasancewar bata iya cin abin ci a cikin mutane, direct sama ta nufa tare da shiga ɗakin momy,zaune ta tadda ita a kan sallaya tana sallah,yusra kuma na kan bed tana ta faman kwasar baccin gajiya,domin ita ma bata daɗe da dawowa daga school ba.

Juya wa ta yi zuwa ɗakin ta ganin bata idar da sallar ba, wanka ta faɗa tare da ɗauro alwala a cikin toilet ɗin,bayan ta fito ta samu simple doguwar riga mara nauyi ta saka ta tayar da sallah.
Tana idar wa ta sauka ƙasa domin bawa cikin ta haƙƙin sa,kai tsaye dining table ta nufa ta zauna tare da zuba abinci,tana cikin cin abin cin ne momy ta sakko cikin shirin ta na ƙasaitattun mata,kana ganin ta kaga babbar mace watayyi ya,kallo ɗaya zaka yi mata ka san nera ta zauna.

Wata irin maroon dubai abaya ce a jikin ta mai tsadar gaske,abin ka da farar mace sai ta haska ta sosai.
Zama ta yi akan sofa tare da mai da hankalin ta kan halimatu ganin ta cika bakin ta da naman kaza, dariya abin ya bata har bata san lokacin da ta dara ba.

Ganin dariyar da momy take yi ne ya sa halimatu marai-raice fuska kamar ƙaramar yarinya,cike da murmushi momy ta ce:

"Doughter ci a hankali mana kar ya shaƙe ki"

"Wallahi momy yunwa nake ji sosai kuma gashi ina sauri kar ki tafi ki bar ni".
"A'a ya za'a yi in tafi in bar ki douhter na!! ai kusan rabin tafiyar ma taki ce"

Murmushin jin daɗi ta yi tare da cewa:

"I love you my best mom in the world,and I proud of you momy na"

Miƙewa momy ta yi daga kan sofa ta nufi in da take zaune ta rungume ta sosai tare da cewa:

"Ilove you too my lovely daughter, Allah ya baki miji na gari wanda zai riƙe min ke amana"

"Gaskiya ni dai momy bana son na yi nesa da ke"
"Kar ki damu doughter na ai ko kin yi aure bamu rabu ba duk lokacin da kike son gani na zaki ganni kin ji.?"

Kai ta girgiza.

"Oya tashi ki je ki shirya mu tafi kar dare ya yi mana kin ji doughter"

Cike da murna ta tashi da gudu ta yi sama, murmushi momy ta yi tare da girgiza kan ta.

Koma wa ta yi kan sofa ta zauna ta yi shiru tare da faɗawa duniyar tunani,ita kan ta tana zulumin ranar da halimatu zata bar gidan nan ta koma rayuwa a gidan wani, ba ƙaramin missing ɗin ta zata yi ba sabo da sun yi masifar shaƙuwa.

In banda aure me zai raba ta da ita,shi kan sa auren wallahi dan ya zama dole ne amma da babu mai raba ta da halimatu sai mutuwa,amma yanzu dole ta rarrashi zuciyar ta sannan kuma ta san da cewa nan da wani ɗan lokaci halimatu za ta yi aure ta tafi ta bar ta.

Tuna nin ta ne ya katse lokacin da ta ji sautin ƙarar ta kalmin halimatu ƙwas ƙwas ƙwas tana sakkowa daga sama, ɗago kan ta ta yi tana ƙarewa shigar ta ta kallo.

Sanye take da purple dubai abaya mai shegen kyau,an yi wa rigar ado da wasu irin stones masu masifar ƙyalli da walwala,ƙafar ta sanye da purple ɗin hill shoe masu kyau sosai da suka dace da ƙafar ta ta, fuskar ta ɗauke da sumple make-up ta yi rolling ɗin mayafin abayar a kan ta,jikin ta sai tashin ƙamshin turare mai sanyi yake.

Ma sha Allah momy ta furta,ta yi kyau kamar ka sace ta ka gudu.
Ƙaraso wa ta yi ta rungume momy tare da cewa:

"Momy na shirya tashi mu tafi"

"Kin yi kyau sosai doughter na"

Ta faɗa fuskar ta ɗauke da murmushi tare da miƙewa ta ɗauki key ɗin mota ta saka a cikin ƴar ƙaramar hand bag ɗin ta suka fita daga cikin parlon.

Parking space suka nufa momy ta buɗe musu wata baƙar jeep suka shiga ciki,ba tare da ɓata lokaci ba ta ja motar baba mai gadi ya wangale musu get suka fita.

Sun yi ƴar tafiya mai ɗan nisa sannan suka ƙaraso sahad store dake nan zooarod suka yi parking ɗin motar su,da yake momy ta fi jin daɗin siyayya a nan.

Ba tare da ɓata lokaci ba halimatu ta ɗakko musu babban basket ɗin nan da ake turawa,kaya suka fara jida masu kyau irin na ƴan gayu,tun daga kan ƙana nan kaya dogwayen riguna,kayan bacci, takalma,turaruka,kayan cosmetic da sauran su.
Tun daga kan momy da halimatu da auta duk sai da aka yi wa kowa siyayya mai yawa.
Chapter 46 · 0% Book details