← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 80

Sashe 42

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kiran wayar aminu da aka yi ne ya dawo shi daga duniyar tunanin da ya afka,ɗakko wayar ya yi a cikin aljihun sa domin ganin mai kiran nasa, sunan umma ya gani ɓaro ɓaro akan fuskar wayar, bai san lokacin da gaban sa ya yanke ya faɗi ba.

Aro jarum ta ya yi tare da picking call ɗin,bayan sun gaisa ne ta fashe masa da kuka tare da tambayar sa shin da gaske ne abin da aka gaya musu cewa ya faru..?

Wasu hawaye masu ɗumi ne suka silalo akan fuskar sa,hannu ya sa tare da share hawayen sannan ya buɗe baki da ƙyar ya yi mata bayani tun daga zuwan su zuwa yanzu da suke waya.

Wani irin kuka ta fashe da shi mai tsuma zuciyar mai sauraro,babu abin da take furta wa sai na shiga uku!.

Cikin wannan yanayin Aminu yake gaya mata bayanin da Babban likitan ya yi musu da kuma kuɗin da ake buƙata.
Nan take ta fara faɗin maganganu marasa daɗin ji,inda take cewa:

"Wallahi tallahi baza'a yanke mata ƙafar miji ba! Sabo da haka a dawo mata da mijin ta gida!"

Ba ƙaramin tashin hankali Aminu ya shiga ba da jin kalaman ta,nan take ya fara rarrashin ta yana mata nasiha tare da kwantar mata da hankali.

Sai da KABIRU ya ƙara yi mata bayani tare da kwantar mata da hankali sannan da ƙyar da siɗin goshi ta amince da aikin da za'a yi masa,in da tace gobe da safe zata turo da kuɗin aikin da za'ayi masa.

Washe gari da safe ta tura masa da kuɗin aikin,ba tare da ɓata lokaci ba suka je shida KABIRU suka biya kuɗin dukkanin abinda ake buƙata.

Ƙarfe takwas na safe aka shiga da shi aikin,ya yin da shi kuma KABIRU da sauran matafiyan suka ɗauki gawar Alhaji Garba suka tafi da ita zuwa kano domin a yi masa suttura a kai shi gidan sa na gaskiya..

Allahu Akbar...

Rayuwa kenan....

"HALIMATU"

A ɓangaren HALIMATU kuwa, soyayyar su suke ta sha ita da MUKHTAR,ba ƙaramin shaƙuwa suka yi da junan su ba musanman ma shi MUKHTAR ɗin,ba ƙaramin jin ta yake yi a cikin zuciyar sa ba.

Duk wani shirye-shiryen fara zuwa makaranta babu abinda ba yi mata ba Sabo da tafiyar da zai yi, nan da ranar Monday zata fara shiga lecture,in da MUKHTAR ya zaɓa mata art & design.

Domin shi yake so ta karan ta,hakan ko aka yi,domin bata yi musu da zaɓin da ya yi mata ba,hakan ba ƙaramin faran ta ran MUKHTAR ya yi ba.

Tsaye take a cikin kitchen tana haɗa wa MUKHTAR dambun nama wanda zata bashi sabo da tafiyar da zai yi, domin gobe ne tafiyar ta shi,shi yasa take ƙoƙari ta haɗa masa ɗan abun da zai tafi dashi.

Domin ya shaida mata cewa zai zo anjima su yi sallama.
Dambun naman kaza ne ta haɗa masa mai ɗan yawa,sai kuma cookies da ta haɗa masa tare da haɗaɗɗen sponge cake,tana gama wa ta haɗa masa egg rice da pepper chicken da kuma cowslow,sai kuma haɗaɗɗen kunun aya da ta haɗa masa.

Ba ita ta gama aikin ba sai wajen ƙarfe biyar na maraice, in da ta yi packaging ɗin su a wasu haɗaɗɗun robobi masu kyau sosai, domin MOMY ta ce ba zata ƙara taya ta yin komai ba, a cewar ta tafi son ta dinga yin komai da kanta domin ta ƙware.

Gyare kitchen ɗin ta yi tsaf kamar ba a yi aiki a cikin sa ba, sannan ta jere kayan a kan dining table.
Bayan ta gama ne ta fito ta iske MOMY da daddy zaune kan sofa suna hira,tsugunawa ta yi a gaban su tare da sunkuyar da kanta ta gaishe su, ɗagowa daddy ya yi ya kalle ta tare da cewa:

"Doughter sannu da ƙoƙari kin ji, Allah ubangiji ya yi miki Albarka"

Ta ce :
"Ameen daddy"
Ya ci gaba da cewa :
"MUKHTAR ya gaya min ranar Monday zaki fara zuwa shool ko..?"

Kan ta ta ɗan girgiza alamar eh.

Ya ce:
"To Allah ubangiji ya kai mu,ki kula sosai ban da wasa,banda bin ƙawayen banza,duk da dai nasan in sha Allah bani da haufi a kan ki HALIMATU,ina so ki ƙara jajir cewa akan karatun ki,sannan ba da kowa zaki yi mu'amala ba kin ji ko..?"

Kai ta kuma girgizawa a karo na biyu.

Ya ci gaba da cewa:
"Shima MUKHTAR ɗin tafiya zai yi gobe goben nan idan Allah ya kai mu,duk da dai na san ya sanar da ke,ya kuma cemin zai zo anjima ku yi sallama,nima goben idan Allah ya kaimu zamu wuce uk nida farouq,zan je sabo da wani kasuwan ci da ya taso min,shi kuma farouq zai fara karatun sa ne a can ɗin".

Ya ƙarasa maganar yana kallon ta.

A hankali ta buɗe bakin ta cikin san yin murya da kuma nutsuwar da ya zame mata jiki ta ce:

"Allah ubangiji ya kai ku lafiya ya dawo da kai lafiya daddy, Allah ya baka nasara akan abin da zaka je nema, Allah ya tsare ka daga sharrin mahaddasa da tsau-tsayi da asara"

Babu abin da yake fitowa daga bakin su shi da MOMY sai
"Amin Amin Amin"
Wani irin nutsuwa ya ji ta saukar masa a cikin zuciyar sa,domin shakka babu ya ji daɗin addu'ar nan ta ta sosai.

Ɗagowa ya yi ya kalle ta tare da cewa:

"Allah ubangiji ya yi miki Albarka doughter,ina fatan dai babu wata matsala tsakanin ki da MUKHTAR ɗin dai ko.? Idan akwai karki ji kunyar komai ki gaya min kin ji..?"
Ya ƙarasa maganar yana kallon ta.

Sun kuyar da kanta ta ƙara yi tare da cewa:
"Ba komai wallahi daddy"

Cike da farin ciki daddy yace:
"To ma sha Allah, Alhmdllhi ai dama haka ake so a ji! Allah ubangiji ya ƙara haɗa mana kan ku baki ɗaya ya yi muku albarka".
Cike da kunya ta amsa da:
"Ameen".

Miƙewa ta yi ta haye up stairs zuwa ɗakin ta, direct toilet ta nufa ta yi lafiyayyan wanka da ruwan ɗumi ta yi brush tare da yin alwala, fitowa ta yi ɗaure da towel a ƙugun ta .

Kujerar gaban mirror ta jawo ta zauna tare da ɗaukan body lotion ɗin ta mai ɗan karan ƙamshi ta shafe jikin ta da shi.
Pant da brazier ta saka tare da ɗaura zani ta saka hijab, direct kan dadduma ta nufa ta tada sallar magriba,ba ita ta tashi daga gurin ba sai da ta yi sallar isha'i.

Bayan ta idar da sallar ne ta koma kan kujerar mirror ta tsara kwalliyar simple mai kyau,ba ƙara min kyau ta yi ba sosai.

Black a baya ta ɗakko ƙirar Dubai mai fararen duwatsu ta saka tare da yin rolling ɗin maya fin abayar a kan ta.

Feshe jikin ta ta yi da turaruka masu daɗi da sanyin ƙamshi, sannan ta ɗakko fashion ɗin ɗankunne da sarƙa da abin hannu masu Black and white colour ɗin stones ta sanya.

Hill shoe ta ɗakko black colour ta sanya a kyakkyawar farar ƙafar ta, woww ba ƙaramin kyau ta yi ba sosai ma sha Allah.

Cupboard ta buɗe tana gyara ƴan kayan da suka zamo ƙasa,tana cikin gyarawar ne yusra ta yi sallama tare da cewa:

"Aunty wai ki zo uncle ya zo!"
Wani irin sanyi ta ji a cikin zuciyar ta bata san dalilin da yasa hakan ba,sai da ta ɗauki kusan 5 minutes sannan ta sakko ƙasa a hankali cike da nutsuwar nan ta ta.

Direct parlon baƙi ta nufa bakin ta ɗauke da sallama,zaune ta tadda MUKHTAR ya kafe ƙofar shigowa parlon da idanun sa.

Ajiyar zuciya ya sauke har tana iya jiyo sautin ta daga in da take tsaye,a hankali ta taka zuwa in da yake zaune ta durƙusa kanta a ƙasa tare da cewa:

"Barka da zuwa habibi na! da fatan kazo lafiya!"

Wata irin kibiyar sonta ce yaji ta soki zuciyar sa nan take yaji wata iriyar nutsuwa da kamala sun saukar masa tun daga cikin zuciyar sa.
Da ƙyar ya iya buɗe baki yace mata:

"Lafiya ƙalau my love,ina fatan kema kina lafiya!"

"Lafiya ƙalau,yasu daddy da MOMY da MEENA tare da yara na"

"Duk kowa yana lafiya my love,yaranki suna gaishe ki"

Ya ƙarasa maganar yana aika mata da wani irin shu'umin kallo mai narkar da zuciya.

Miƙewa ta yi tare da cewa:

Habibi taho muje in baka ruwa mai ɗan sanyi ka sha kaji..?

Ta ƙarasa maganar tare da nufar dining table ɗin.
Bin bayan ta ya yi zuwa dining ɗin ta jawa masa kujera ya zauna,zama ta yi a kujerar da take facing ɗin tashi kujerar tare da zuba masa ruwa a glass cup mai ɗan sanyi ta miƙa masa.

Karɓa ya yi tare da kafe ta da Mayun idanun sa kamar zai lashe ta sabo da tsananin son da yake mata.

Cikin wani irin salon da ita kanta bata san tana da shi ba ta buɗe baki cike da yanga tace:

"Habibi pls kasha ruwa mana ka tsaya kana kallona!!"

Ta ƙarasa maganar cikin shagwaɓa tare da turo masa ɗan ƙaramin bakinta.

Saura kaɗan MUKHTAR ya saki glass cup ɗin hannun sa sabo da rikirkita masa lissafi da take shirin yi,nan take ya aro nutsuwa da jarumta ya dai -dai yana yin sa tare da kai ruwan bakin sa ya ɗan kurɓi kaɗan ya ajiye ragowar.

Plate ta jawo ta zuba masa egg rice ɗin tare da pepper chicken da cowslow ta tura masa gaban sa tare da cewa:

"Habibi ga abinci na dafa maka da kaina nasan zaka ji daɗin sa!"

Ta ƙarasa maganar tana yi masa murmushin nan nata mai kashe zuciya.

"Na gode my love,ina matuƙar alfahari da samun ki a rayuwata,dan Allah karki guje ni komai runtsi komai wahala,ki kasan ce tare da ni,na yi miki alƙawarin zan baki farin ciki dai dai iyawa ta, Allah ubangiji ya mallaka min ke a matsayin matar aure na ta sunnah"

Ya ƙarasa maganar da wata iriyar murya mai rauni.

Ɗago idanun ta ta yi ta kalleshi cikin rauni tare da cewa:

"Habibi ka dena faɗin haka! In sha Allahu babu abin da zai raba mu kaji"

Tsare ta da idanun sa masu kaifi ya yi tare da cewa:
Chapter 42 · 0% Book details