Sashe 51
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duban shi momy ta yi ta sakar masa da harar wasa tare da cewa:
"Yanzu ka ji daɗi ai tun da ka kori yaran naka gaba ɗayan su".
Ƙasaitaccen murmushi ya saki tare da cewa:
"Ai gwara da suka bamu guri domin mu yi hirar yau she gamo sabo da nayi missing ɗin ki sosai"
Ya ƙarashe maganar tare da kamo hannun ta ya sumba ce shi, murmushi mai sanyi ta sakar masa sabo da ita ma ta yi missing ɗin sa sosai,miƙar da ita ya yi tsaye tare da kamo hannun ta suka nufi kan sofa suka zauna.
Jawo ta jikin sa ya yi ya rumgeta tsam a jikin sa tare da sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi,ita ma ajiyar zuciyar ta sauke domin ba ƙarya ta yi missing ɗin mijin ta sosai.
Ƙara lafewa ta yi a jikin sa har tana jin bugun zuciyar sa, ɗago kanta ta yi ta dube shi tare da cewa:
"Barka da zuwa hasken idaniya ta,da fatan ka dawo gida lafiya"
Ta faɗa tare da ɗora kan ta saman kafadar sa.
Kasa daure wa ya yi sai da ya ɗago ya sumbaci lips ɗin ta tare da cewa:.
"Lafiya ƙalau mar'atussalaha ta da fatan na same ku lafiya"
"Kowa yana lafiya sai dai mun yi kewar ka sosai"
"Ai ni na yi kewar ku da yawa,ko baki ga yanda na rame sabo da rashin ki a kusa da ni ba! ya kamata a kula da ni sosai ko na mai da jiki na!".
Ya faɗa tare da kai hannu ya shafa gefen fuskar ta.
Murmushi ta yi tare da cewa:
"Kada ka damu san yin idaniya ta,ai tun da Allah ya dawo min da kai lafiya zaka samu dukkan kulawar da ya kama ta daga gare ni fiye da yadda baka yi zato ba".
Rungume ta ya ƙara yi sosai tare da sauke wata iriyar ajiyar zuciya,ji yake duk wata damuwar sa ta kau,kwanciyar hankalin da ya rasa ya dawo tun da yana tare da sanyin idaniyar sa.
Kiran wayar sa da aka yi ne ya katse masa maganar zucin da yake yi,ciro wayar ya yi a cikin aljihun sa domin ganin mai kiran,abokin sa Alhaji Ibrahim ne mahaifin MUKHTAR.
Ɗaukar wayar ya yi tare da yin sallama ya kara a kunnen sa,daga ɗaya ɓangaren Alhaji Ibrahim ya amsa suka gaisa da junan su tare da yi masa barka da dawo wa,amsawa ya yi cike da nuna jin daɗin sa kamar yana gaban sa,daga ɗaya ɓangaren Alhaji Ibrahim yake sanar masa da cewa suna nan tafe idan an yi sallar magriba ko ishaa.
Jinjina kai ya yi kamar yana gaban sa tare da cewa:
"Allah ya kawo ku lafiya Alhaji"
Daga haka suka yi sallama da junan su tare da ajiye wayar,kamo hannun momy ya yi tare da miƙar da ita tsaye yace:
"Muje sama na ɗan huta kafin alhaji Ibrahim da iyalan sa su iso"
Ba tare da ta yi masa musu ba ta bishi zuwa saman.
Ƙarfe bakwai da rabi iyalan alhaji Ibrahim suka iso cikin gidan har da su MEENA da sahal da yasmin da hajiya zainab, basu zauna ba direct masallaci su mukhtar suka nufa shi da su daddy da su Hafiz,su kuma matan su ka yi sallar su a gida.
Ana idarwa suka nufo gida gaba ɗayan su aka zauna a parlo aka shiga gaggaisa wa,hajiya zainab tana kusa da momy zaune suna hirar su,ya yin da alhaji Ibrahim da daddy suke zaune guri ɗaya suna hira,su kuma su MUKHTAR suna daga can gefe gurin ɗaya set ɗin kujerun parlon suna zaune suna hira.
Su MEENA kuwa suna sama ɗakin halimatu suna hira suna cin abincin da halimatu ta kawo musu.
Jagora mummy ta yi musu zuwa dining table dan suci abinci,su kuma su Hafiz Sadiq ne ya shiga kitchen ya haɗo musu a bban try ya ajiye musu.
Kowa na cin abinci banda mukhtar da kunya ta hana shi cin komai,lura da hakan ne ya sa hafeez ɗaukar waya ya kirawo HALIMATU domin ta bawa mukhtar abin ci ko zai ci,toh tace tare da sauke yasmin da ke kan cinyar ta tana bata abin ci.
Kallon meena ta yi tare da cewa:
"Ku tashi muje ƙasa yaya hafeez na kiran mu"
"Babu wani nan kedai ki faɗi gaskiya kawai gurin yaya MUKHTAR za ki"
Murmushi ta yi kawai ba tare da tace komai ba,medium ɗin mayafin ta ta yafa tare da ƙara fesa turare kaɗan, MEENA ce a gaba ita da sahal,yayin da halimatu da yasmeen suka biyo bayan su.
Lokacin da suka sakko har su daddy sun gama cin abinci sun dawo kan sofers sun zauna, direct in da suke ta nufa kan ta na ƙasa ta durƙusa ta gashe su cike da ladabi da mutuntawa,amsawa suka yi cike da fara'a suna ƙara yaba zallar kyayu da ƙuruciyar halimatu.
Gaskiya za su yi farin ciki sosai idan ɗansu ya samu nasarar auren halumatu,domin daga ganin ta kaga yarinya mai cikakkiyar tarbiya da nutsuwa ko haɗa ido ta kasa yi da su.
Momy ce ta ce ta je su gaisa da mukhtar yana parlon baƙi,cike da kunya ta miƙe hannu ta riƙe da yasmin tun lokacin da suka zo yarinyar ta liƙe mata,da sallama ta shiga ta iske mukhtar zaune yana jiran ta tun lokacin da hafeez ya kirawo ta shima ya yi masa iso har cikin parlon.
Durƙusawa ta yi ta gaida shi tare da yi masa barka da dawowa,kallon ta yake yi kamar wadda aka chanja masa ita,domin gani ya yi ta ƙara kyau sosai kamar wadda a ka yiwa wankan inji, nuna mata gefen sa ya yi alamar ta zauna.
Babu musu ta dawo ta zauna tare da ɗora yasmin akan cinyar ta ta rungume ta da kyau,kallon su ya yi cike da jin dadi da kuma ban sha'awa ya ce da yasmin:
"Zo mu gaisa mana!"
Kafaɗar ta ta maƙe tare da cewa:
"A'a ni a wajen momy na zan zauna"
Mamaki ne ya kama shi sosai har sai da ya nuna a kan fuskarsa, har yaushe ta san halimatun da zata ƙi zuwa wajen shi, karantar yana yin da yake ciki ya sa halimatu yin murmushi tare da ƙara rungume yasmin akan cinyar ta, murmushi shima ya yi tare da cewa:
"Oh! zan rama nima"
Dariya suka yi gaba ɗayan su,da ƙyar halimatu ta yi mata wayo ta tafi ta basu waje,abin ci mai rai da lafiya ta zuba masa haɗe da coconut jus mai daɗin gaske,yana ci yana kallon ta kamar bai taɓa ganin ta ba.
Ta shi ta yi ta nufi dining table ɗin tare da buɗe fridge ɗin gurin ta ɗakko ƙaton cake ɗin da kuma ƙana na guda biyu,kunna candle ɗin cake ɗin ta yi tare da ɗakko fill doughnuts wanda ta zuba su a cikin manyan noxes guda uku ta yi musu a do da whip cream,wasu kuma ta yi musu glazen da condense milk da madarar gari ta saka lotus biscuit da orio akai, ta kawo dry coconut da zuma ta yar yaɗa a kai.
Koma wa ta yi inda yak zaune ta ce ya rufe idon sa, rufe wa ya yi ita kuma ta kamo hannun sa cike da kunya ta ƙarasa dining ɗin da shi ta ja kujera ta zaunar da shi a gaban ƙaton cake ɗin.
Umarni ta ba shi a kan ya buɗe idon sa,yana buɗe wa ya yi arba da ƙaton cake a gaban sa an rubuta welcome back home Habibi a jiki,zaro manyan idanun sa ya yi tare da kai duban sa in da take tsaye tana sakar masa da kyakkyawan murmushin nan nata mai kashe zuciya.
Mukhtar ya rasa wanne irin farin ciki zai yi,gaba ɗaya bakin sa ya mutu ya kasa furta kowacce irin kalma,fahimtar hakan da ta yi ne ya sa ta matso kusa da shi tare da cewa:
"All this is for you habibi! congratulations nd well come back home!!"
Wani irin tsananin farin ciki ne ya ziyar ce shi wanda rabon da ya ji irin sa an daɗe sosai, gaskiya yarinyar nan ta riga ta gama sace zuciyar sa gaba ɗaya,ya rasa wanne irin mugun so yake yiwa yarinyar nan.a hankali ya furta:
"Na gode my love, Allah ubangiji ya albarkaci rayuwar ki ya kuma mallaka min ke a matsayin matar aure na".
Rufe fuskar ta ta yi da tafin hannun ta cike da kunya tana murmushi,cikin wannan yanayin MEENA ta shigo ta same su,zaro idanun ta ta yi tare da ƙarasowa in da suke ta fara ɗaukar su pictures,ganin haka ne ya sa yace mata taje ta kirawo su yasmin su yi hotuna.
Ba tare da ɓata lokaci ba ta kirawo su suka haɗu gaba ɗayan su suna masa murnar dawo wa gida, ƙarshe da zasu yanka cake meena ce ta yi musu pictures,bayan sun yanka ya ɗakko ya saka mata a baki da ƙyar ta karɓa, yayin da itama ta yanko ta saka masa a bakin sa cike da kunya,babu abinda meena take yi sai ɗaukar pics cike da farin ciki.
Suma yaran a baki halimatu ta basu,shima MUKHTAR ya basu a baki cike da farin ciki,rungume su suka yi akai ta yi musu pictures cike da farin ciki da burgewa.bayan sun gama celebration ɗin ne MEENA tace masa daddy yace ya fito su tafi,ƙaton box halimatu ta ɗakko ta saka cake ɗin a ciki,suma ƙana nan ta saka su a cikin boxes ɗin su.
MEENA ya umar ta da ta kwashe cakes ɗin da doughnut ɗin ta kai su cikin mota, kashewa ta din ga yi ɗaya bayan ɗaya tana kai wa cikin mota,bayan ta gama ne suka fito gaba ɗayan su ta yi wa su daddy sallama ta haye sama, ya yin da daddy da MOMY suka raka su har bakin mota.
Sallama suka yi Alhaji Ibrahim yana ƙara jadda dawa daddy maganar da suka yi ta zuwa gurin mahaifin halumatu,amsawa ya yi da "toh".
Daga haka driver ya jasu suka tafi, shima MUKHTAR ya ja su meena suka bi bayan su.
Wannan kenan.....✍🏻✍🏻