← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 80

Sashe 62

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shafa kanta momy ta yi tana murmushi tare da cewa,
"To doughter a sha lafiya"
Murmushi ta yi tare da ci gaba da shan fruit salad ɗin ta.
Bayan ta gama sha ne ta je ta mayar da bowl ɗin kitchen sannan ta dawo parlon ta zauna kusa da momy.kallon ta momy ta yi tare da cewa,
"Doughter kinga yanzu bikin ku bai fi saura wata guda ya rage ba,toh ina so nan da sati ɗaya mai gyaran jiki zata zo daga maiduguri domin ta fara yi miki gyara,kullum da kin dawo daga makaranta za'a din ga yi miki har zuwa lokacin da za'a kai ki ɗakin mijin ki.
Mun yi waya da baban ki ya ce itama HANNE nan zata dawo gidan sa gaba ɗaya har a yi bikin tun da itama a nan garin mijin ta ya samu aiki,toh dan Allah ki bamu haɗin kai duk abin da kika ga an yi miki shine dai dai kin ji doughter.?"
Girgiza kai ta yi tare da cewa,
"Toh momy in sha Allah"
"Yauwa my doughter Allah ya yi miki Albarka ka kin ji.?daga yanzu ako da yaushe matar zata iya zuwa,shi ya sa ma na ce da baba ladi ta gyara ɗaya daga cikin bedrooms ɗin ƙasan nan domin a ciki za'a yi miki kin ji".
Cikin sanyin murya ta ce "toh momy"

Daga haka ta ta shi ta yiwa momy sallama ta haye sama domin ta ɗan kwanta ta ƙara huta wa.....✍🏻✍🏻

Ina matuƙar godiya da addu'o'in ku a gare ni tare da fatan Alkhairi, ku ɗin na musamman ne a cikin zuciya ta,ina matuƙar alfahari da ku ƙwarai da gaske, Allah ubangiji ya saka da mafificin Alkhairin sa ya biya muku buƙatun ku na Alkhairi.🙏🏻🙏🏻

Daga alƙalamin
FATIMA BINTU ABDALLAHI(UMMU AYSHA)....✍🏻✍🏻

Share fisabilillahi.

Ga masu buƙatar littafin HALIMATU tun daga farko zuwa in da aka tsaya ya tun tuɓe ni ta wannan numbern wayar👇🏻👇🏻

08162055134.

💝💞 HALIMATU💝💞

(Love, sacrifices, destiny & betrayed)

💝💞💝💞💝💞💝💞

Story & Writing

By

FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA).....✍🏻✍🏻

Ƙarƙashin jagorancin

(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)

💝💞💝💞💝💞💝💞

Golden pens....✍🏻✍🏻

A 2024 novel

💝💞💝💞💝💞💝💞

Pages__________79&80

___________Shirye-shiryen ga garumin biki ake yi babu kama hannun yaro ta kowanne ɓangaren,tuni mai gyaran jiki ta ƙaraso tun saura sati uku bikin,yau sati ɗaya kenan da fara yi wa halimatu gyaran jiki,ya yin da bikin ya rage saura sati biyu masu zuwa.wani irin sihirtaccen kyau halimatu ta yi ba na wasa ba,fatar ta ta ƙara laushi da sulɓi ga kuma sheƙin da take yi.
Wasu irin magunguna ingantattu momy take bata kullum safe da rana da daddare da zallar madarar shanu pure da zuma,ta ƙara cika sosai da sosai shape ɗin ta ya ƙara fitowa sosai gwanin ban sha'awa,ga kuma wani irin daddaɗan ƙamshin da yake tashi daga cikin jikin ta,ko fitsari ta yi sai ya yi ƙamshi,duk in da ta zauna sai ta bar ƙamshin ta a gurin.

Jiya aka kai lefen Hafiz gidan su mukhtar,akwati set huɗu,kowacce daga cikin su cike take da kaya maƙil a cikin ta,an zuba kaya na gani na faɗa masu tsadar gaske har da set ɗin sarƙar gwal,nera ta yi kuka a wajen nan.
Ya yin da dangin su suka yaba da kayan sosai da sosai,ga kuma tarɓa da aka yi musu ta ban girma abin dai sai wanda ya gani,cike da murna suka dawo gida aka haɗo su da kayan ciye-ciye irin su snacks da kaji da kalolin lemuka tare da tukwici mai tsoka suna yaba mutunci da karamcin mutanen.tuni Hafiz ya ƙarasa gina tamfatsetsen gidan sa a nan gaba da su kaɗan,gidan ya yi kyau sosai da sosai nera ta yi kuka ba kaɗan ba.

Momy ta yi busy sosai da sosai kwata kwata bata samun hutu,sabo da auren ƴaƴa guda biyu kuma duk a lokaci ɗaya ba wasa ba.
Momy ce ta shigo bedroom ɗin halimatu don ta ji shiru bata ji ɗuriyar ta ba tun ɗazu da mai gyaran jiki ta gama yi mata shine tace za ta je ta kwanta ta huta,tsaye ta same ta a gaban wardrove ɗin ta tana gyara kayayyakin ta, waje ta samu a bakin gado ta zauna tare da kiran sunan halimatun.

"Doughter"
"Na'am momy na"
Ta ce tare da zama kusa da momyn.
Kallon ta momy ta yi tare da cewa,
"Kin san dai yau ɗin nan za a kawo kayan lefen ki ko.?"
A hankali ta jin jina kan ta.
"Okay good, ɗazu mun yi magana da baban ki ya ce min su rahine da altine da HANNE da sabuwa duk sun iso suna gidan sa, kuma baza su koma ba sai an gama bikin ku, dan kin ga ita ma HANNE na gaya miki a nan garin za ta zauna a sharaɗa phase 3,domin mijin ta ya samu aiki a waje jen nan,sabo da haka yanzu ki shirya drivern ki zai kai ki can gidan baban na ki sabo da bana son a kawo lefen nan kina cikin gidan nan kinji ko.?"
Girgiza kai halimatu ta yi ba tare da tace komai ba.

"Yauwa doughter na,idan drivern ya kai ki sai ya taho da altine da rahinatu da kuma matar malam Musa sabuwa da suntyn ku Amina,domin a karɓi kayan lefen da su kin ji,idan ya so gobe idan Allah ya kai mu sai ya je ya ɗakko min ke kin ji ko.?"

Jin jina kai ta kuma yi idanun ta suna ciko da ƙwalla.
"A'a me ye kuma na kuka doughter.?,maza share hawayen nan bana son ganin su kinji ko.?"
A hankali ta saka bayan hannun ta ta goge hawayen fuskar ta.
Miƙewa momy ta yi tare da cewa,
" Oya,maza maza ki shirya ki fito yana waje yana jiran ki kin ga mutane sun fara taruwa"
"To" ta ce tare da miƙewa ta zura black ɗin doguwar rigar ta mai kyau sosai ta yi rolling ɗin kan ta da maya fin rigar.duk da bata yi kwalliya ba amma ta yi kyau sosai ga wani irin ƙamshi da yake ta shi a jikin ta ba na wasa ba.
A hankali ta ke sakkowa daga up stairs ɗin da ka gan ta kaga amarya gan dariya,su kan su mutanen da ke zaune a parlon se da suka yi mamakin irin zallar kyawun halimatu da kuma ƙuruciyar ta,duk da dai wasu daga cikin su sun san ta, wasu kuma yau ɗin nan ne suka fara ganin ta, Musamman ma wasu daga cikin ƙawayen momy,amma bangaren dangin su daddy ya wanci duk sun san ta.

Tun da suna zuwa lokaci zuwa lokaci, sannan kuma su ɗin ma sukan je musu ziyara wani lokacin.
Tana ƙarasowa parlon ta durƙusa har ƙasa ta gaishe su kan ta a ƙasa cike da ladabi,amsawa suka yi cike da fara'a suna ƙare mata kallo,ganin kallon da suke mata ne ya sa momy ta ce,
"Doghter ta shi maza ku tafi kin bar shi yana ta faman jiran ki"
A hankali tace"to" tare da miƙewa tsaye ta yi wa momy sallama ta fice daga parlon, parking space ta nufa in da motocin gidan suke parke,tasowa habu driver da suke ta hira da baba maigadi ya yi tare da yiwa baba maigadin sallama.

Yana zuwa ya buɗe wa halimatu bayan motar ta shiga bayan sun gaisa,ba tare da ɓata lokaci ba ya kunna motar ya ja baba maigadi ya buɗe masa get suka bar gidan.sun ɗan yi tafiya mai ɗan nisa sannan suka ƙaraso get ɗin gidan,a bakin get habu driver ya yi parking ɗin motar tare da cewa halimatu,
"Dan Allah idan kin shiga ki cewa waɗan da za'a koma da su su fito mu tafi,sabo da hajiya na jirana zata ai ke ni"
"Toh"

Tace tare da ficewa daga cikin motar ta shige cikin gidan, parlon gidan ta shiga in da take jiyo hayaniya na tashi da shewa,da sallama a bakin ta ta shiga cikin parlon,gaba ɗaya mutanen da suke cikin parlon suka juyo tare da zuba mata ido,da fari ba su gane halimatu ba,sai da aunty AMINA ta ce,
"Halimatu har kun iso.?"
Ta faɗa fuskarta cike da murmushi.
"Eh mun iso aunty"
Ta faɗa tare da shigowa cikin parlon.

Ta shi HANNE ta yi da gudu tana ihun murna ta yi kan halimatu tare da faɗa wa jikin ta ta rungume ta sosai cike da murna da farin ciki,saura kaɗan su faɗi ƙasa Allah ya taimaka akwai kujera a kusa da halimatun ta yi sauri ta zauna a kan ta tare da cewa,
"Washh Allah na! HANNE zaki karya ni fa"
Gaba ɗaya dariya aka sanya mata,ɗagowa HANNE ta yi ta dube ta tare da cewa,
"Haba aunty halimatu! duk fa murnar ganin ki ce fa, wallahi kwata kwata ban gane ki ba gaba ɗaya kin koma kamar balarabiya wallahi".

Rahine ce ta cafe maganar tare da cewa,
"Alƙur'an nima ban gane ta ba wallahi sai da auntyn mu ta kirawo sunan ta".
Dariya aka kuma san yawa gaba ɗaya.
Ta shi halimatu ta yi tazo in da aunty AMINA da altine suke zaune ta durƙusa ta gashe su cike da ladabi, amsawa suka yi cike da fara'a,ya yin da yan uwanta suke mamakin chanjawar da ta yi kamar ba jinin su ba,gaba ɗaya parlon ya gauraye da ƙamshin jikin ta.
Jiyo wa ta yi ta gaishe da rahine da ta dawo kusa da ita ta zauna tana kallon ta tare da sakar mata murmushi,nan take hirar yau she gamo ta ɓarke a tsakanin su.

Suna cikin hirar ne wayar halimatu dake cikin jakar ta ta yi ƙara, gaba ɗaya ido suka zubo mata suna kallon kyakkyawar tsadaddiyar wayar da ta fito daga ita daga cikin jakar ta,sunan momy ne yake yawo a kan screen ɗin wayar, ba tare da ɓata lokaci ba ta yi sauri ta yi picking call ɗin tare da karawa a cikin kunnen ta.daga chan ɓangaren momy ta ce mata ya bata ga su altine sun ƙaraso ba,ga shi kuma masu kawo lefe sun kusa ƙarasowa,nan take ta tuna batun kawo lefen,domin murnar ganin ƴan uwan ta ya sa ta mance da batun sharf wallahi.

Cikin sassanyar muryarta ta ce,
"Ki yi haƙuri momy wallahi mantawa na yi,amma in sha Allahu yanzu yanzun nan za su taho"
Chapter 62 · 0% Book details