Sashe 24
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani irin ƙamshine ya ziyar ci hancin sa mai sanyaya zuciya da ruhi tare da saka nutsuwa, bai san lokacin da ya ɗago da manyan idanuwan sa ya zuba mata ido tun daga kan ƙafafuwan ta masu ɗauke da hill shoe gashi sun sha jan lalle ya fito raɗau gwanin ban sha'awa,nan take yaji gabansa yayi wani irin faɗuwa,ƙoƙarin saita kansa ya fara yi dan gudun kada yayi abin kunya.
Meena ce tayi sauri ta miƙe tare zuwa inda take zaune a ƙasa ta rungume ta tare da cewa "oyo yo aunty na dafan mun sameki lafiya"Murmushi HALIMATU tayi ba tare da ta ɗago fuskarta ba cikin ƙasa ƙasa da murya tace "lafiya ƙalau Alhmdllhi" miƙewa meena tayi tare da cewa bari muje na gaisa da MOMY" ta faɗa tare da miƙawa yusra hannu tace"zomuje gurin MOMY beauty"girgiza kai yusra tayi tare da cewa"a'a ni gurin uncle zanje"ta faɗa tana nuni da MUKHTAR.
Ajiye wayar hannu sa yayi tare da miƙa mata hannu yace"okay taho mugaisa"da sauri ta tafi wajen MUKTAR ta haye saman jikinsa ta zauna.murmushi MEENA tayi tare da cewa"okay tom shikenan tunda bazaki zo gurina ba na tafi"ta faɗa tare da juyawa ta fice daga parlorn.
"Ina wuni" ta faɗa kanta a sunkuyar,in a low voice ya amsa mata da lafiya lau,daga haka bata ƙara yi masa magana ba, shi kuma a nashi ɓangaren hira sukeyi shida auta.dabara ce ta faɗo masa ya dubi auta yace mata taje MOMY na kiranta,cikin sauri ta sakko daga saman jikin sa ta sheƙa a guje.
Gyaran murya yayi tare da cewa "HALIMATU" gabanta ne ya faɗi sakamakon kiran sunan ta yayi,da sauri ta ɗago da kanta ta kalleshi na second ɗaya ta kuma maida kanta ƙasa.sake kiran sunan ta yayi a karo na biyu tare da cewa "zonan" shiru tayi batare da ta tashi zuwa amsa kiran nashi ba "bana son gaddama fa"ya faɗi yana kallon ta.
Jikin ta na rawa ta tashi a hankali taje dai dai in da yake zaune a kan kujera ta durƙusa kanta a ƙasa."ɗago ki kalleni HALIMATU"ɗagowa tayi kamar mai jin tsoron haɗa idanu dashi ta kalleshi, shima kallon ta yake yi fuskarsa ɗauke da kwarjini,tunani takeyi a ina tasan wannan fuskar domin tabbas ta taɓa ganin mai irin wannan fuskar.
"Baki gane ni ba??" ya faɗa tare da tsare ta da idanun sa, tunawa tayi kamar mai zuwa yin sadaka a ƙauyen su har itama ya ke siye gyaɗar ta yayi sadaka,katse ta yayi tare da cewa "kin manta ni kenan!! girgiza masa kanta tayi batare da tace komai ba."baki zaki buɗe kiyi min magana fa"ya faɗa yana kallon ta.
Cikin sassanyar muryar ta mai daɗi tace"na gane" yace mata "kin gane me??" tace "na gane ka" MUKHTAR yace "a ina kika Sanni" tace"kamar kai ne me zuwa yin sadaka a ƙauyen mu tare da siyen gyaɗata gaba ɗaya" tattausan murmushi ya saki tare da cewa "good ba kama bace nine" cike da mamaki take kallon shi.
Kashe mata idanu yayi tare da cewa "haka ake tarɓar baƙo??" girgiza kanta tayi tare da cewa "kayi haƙuri" MUKHTAR ya dubeta yace "nayi amma nex time idan kika sake bazan haƙura ba!" kanta kawai ta girgiza ba tare da tace komai ba.
Miƙewa tayi da nufin ta jawo bban center table ɗin da aka cikashi da kayan abinci kala kala kafin ta ƙarasa taji ƙamshin turaren sa ya daki hancin ta sosai, da sauri ta juya saboda taji alamar mutum a kusa da ita "bari na jawo miki shi yayi miki nauyi" jawowa yayi ya kawo shi gaban three seater sofa ɗin da yake zaune,ita dai shiru tayi tana kallon ikon Allah.
"Bismillah" ya faɗa yana tsare ta manyan idanuwan sa, ta kowa tayi a hankali tazo inda yake zaune ta tsuguna tare da cewa "me kake so na zuba maka??" tsura mata ido yayi yana kallon ɗan ƙaramin bakinta da yasha orange ɗin lipstick,ganin kallon da yake mata ne yasa tayi sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa.
"Duk abinda kika ga yayi miki ki zubamin"ɗago da kanta tayi ta kalleshi taga kamar ma ba shine wanda yayi maganar ba yana ta daddan na wayar dake hannun sa.
Buɗe warmers ɗin tayi ta ɗauki kyakkyawan plate ta zuba masa Chainees fried rice wadda taji zallan naman kaza da hanta da kuma vegetables,ta kawo coleslaw ta zuba masa a gefe.wani bowl ta ɗakko ta zuba masa gas meat a ciki, yoghurt fruit salad ta zuba masa tare da tura kayan zuwa gabansa.
Kallon ta yayi tare da cewa "duk wannan nawa ne nikaɗai??"murmushi tayi har dimple ɗinta guda biyu suna lotsawa tare da girgiza masa kanta, bismillah yayi tare da fara cin abincin.shiru ne ya ɗan gifta a tsakanin su,shi yana cin abincin yana ta lumshe idanun sa sabo da tsabar daɗin da yayi masa, a cikin zuciyar sa kuma yana tunanin irin chanjawar da HALIMATU tayi cikin ƙanƙanin lokaci,duk da yasan ko a adaɗin daya santa ita ɗin kyakkyawace sosai.
Kafin wani lokaci ya cinye abincin gaba ɗaya,dama shi mutum ne da baya wasa da cikin sa."Alhamdulillah" ya furta tare da kallon HALIMATU,lemo ta zuba masa a cup tare da ajiye masa tissue a gefe.bayan ya gama ne yayi gyaran murya tare da cewa "HALIMATU taso ki dawo nan kusa dani ki zauna zamu yi magana!!"
Ganin da tayi babu alamun wasa a fuskarsa ne yasa ta dawo gefensa da yake nuna mata ta zauna.shiru ne ya gifta a tsakanin su kafin yace mata"kinji bayanin da daddy da MOMY suka yi miki a game dani??" kai ta girgiza masa " baki fa zaki buɗe kiyimin magana!"cikin sassanyar muryar ta tace masa"ae sun gaya min" yace " Okey tom Alhmdllhi,menene matsayina a gurin ki!! ina so ki gayamin idan na samu karɓuwa a gurinki domin banaso a takuraki, sabo da shi zaman aure yafi daɗi musamman idan ana son juna"
Ya ƙara sa maganar yana tsareta da idanuwan sa masu mugun kwarjini,in banda abinka wacce mace ce zataƙi son ta auri haɗaɗɗen mutum irinka,ta faɗa acikin zuciyar ta.maganarsa ce ta dawo da ita daga zancen zucin da take yi "kinyi shiru baki ce komai ba hally fresh" da sauri ta ɗago kanta ta dubeshi jin sunan da ya kirawo ta dashi,kamar ba daga bakin sa maganar ta fito ba ya wani basar.
"Nasamu karɓuwa koban samuba??" ya ƙara tambayar ta a karo na uku "ga dukkan alamu dai ban samu karɓuwa ba a gurin HALIMATU!!" cikin sauri ta ɗago da kanta ta dubeshi"ae mana,shirun da kikayi shine ya tabbatar min da haka"kanta ta girgiza alamar a'a"Okey na samu karɓuwa kenan??" Sunkuyar da kanta tayi ta girgiza kanta a hankali cike da kunya.
"Alhamdulillah" ya furta tare da jin wani irin sanyi tun daga cikin ƙoƙon ransa,cikin ƙasa ƙasa da murya yace mata "ashe niɗin mai Sa'a ne" ita dai shiru tayi bata ce masa komai ba,cikin nutsuwar da ta zame masa jiki ya ciga da cewa "HALIMATU ina matuƙar farin ciki da kika karɓi soyayya ta kuma in sha Allahu bazaki taɓayin regretting ba, dama ni ta ɓangarena banida matsala,fatana shine Allah ubangiji ya mallakamin ke a matsayin matata ta sunnah, Allah ubangiji ya tabbatar mana da Alkhairin sa.
Ya cigaba da cewa "inaso na gaya miki ƙa'idodina, saboda ina son ki fahimce su a matsayin matar da zan aura nan bada daɗewa ba in sha Allah,inaso ki tsaya ki koyi girke girke kala kala,kuma bana ra'ayin cin abincin mai aiki,domin ni bana iya cin abincin waje,sannan inason matata ta kasance mai juriya da haƙuri,ni mutum ne mai son ado da kwalliya,tsaftar gida data jiki da dai sauran su".
Ya ci-gaba da cewa"bana son rawar kai,ina son mace mai nutsuwa da kamun kai,sannan inason matata ta girmama ni a matsayina na mijinta tare da bin umarni na da kuma girmama iyayena da ƴan uwana,kuma inason idan na yiwa matata kyauta ta nuna farin cikinta sosai,hakan yana sakani cikin farin ciki ƙwarai da gaske, idan kika kasance a haka zanji daɗin zama dake sosai da sosai,kuma zan kasance mai Sa'a a rayuwata".
Ya ƙarshe maganar yana kallon ta,cikin ƙasa ƙasa da murya tace"in sha Allahu zan kasan ce maka a duk yadda kake so na kasance" wani irin daɗi da farin ciki ne yaji ya tsarga masa a cikin zuciyar sa,babu abinda fuskarsa take fitarwa sai annuri,kana ganin sa kasan yana cikin farin ciki.
"Ma sha Allah haka nake son naji, Allah ubangiji yayi miki albarka" ya faɗa yana ƙara kallon kyakkyawar fuskarta, sannan ya ci-gaba da cewa " next time idan na dawo girkin ki zanci" girgiza masa kai tayi,kallon ƙunshin hannun ta yayi tare da cewa "wannan ƙunshin yayi min kyau sosai,dole ne na biya kuɗinsa tare da kwalliyar nan!!" murmushi HALIMATU tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa,hakan da tayi shi ya bashi damar ganin lallausan gashin kanta da ya sakko har gadon bayan ta.
A hankali ya saka hannun sa tare da kama gashin nata,nan take yaji wani irin laushi kamar ya taɓa auduga.cike da kokwanto yace" bana son wannan abinda aka sakamiki shi akanki,nex time karna ƙara ganin ansaka mikishi" cikin sauri ta ɗago da kanta domin ganin abinda yake magana a kansa, sabo da ita bata san ya taɓa mata gashi ba sai yanzu.
"Ba sakamin shi aka yi ba" cike da mamaki ya dubeta tare da cewa "kina nufin kice wannan gashin duk nakine??" gyaɗa masa kai tayi alamar ae, yace"ma sha Allah, Alhmdllh".ita dai shiru tayi bata ƙara cewa komai ba.daga haka ya miƙe domin ganin lokaci ya tafi,ya dubeta tare da cewa "ni zan wuce! muje ki rakani" "to" tace tare da yin gaba shi kuma ya biyota a baya.
Suna fitowa suka tarar da daddy yana sakkowa daga upstairs da waya a kunnen sa yana magana,ita kuma MOMY suna zaune a parlon ita da MEENA suna hira kamar sun daɗe da sanin junan su,yusra na kancinyar MEENA zaune.
Daddy yace "harka fito MUKHTAR"kansa ya sunkuyar tare da cewa "ae daddy na fito zamu wuce" "to Allah ubangiji ya kaiku lafiya,ina gaida mutanan gidan" yace "to daddy zasuji in sha Allah" durƙusawa yayi tare da yiwa MOMY sallama, cike da murmushi ta amsa tare da yi musu fatan sauka lafiya.