Sashe 15
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin haɗa baki suka ce"wa muke gani tafe kamar Hanne??" cikin sakin fuska hanne tace "wallahi ni ce tafe!! ina fatan na same ku lafiya??".uwale kishiyar laltine tace "wallahi k'alau muke,ya su inna!! da fatan kowa yana lafiya??"hanne tace"duk k'alau muke" tace "to madalla".daga haka hanne ta wuce su ta shiga ɗakin altine.
wucewar ta ba daɗewa altine ta biyo bayan ta,tana shigowa ta sameta zaune cikin ɗakin tayi shiru alamar ta faɗa duniyar tunani.cike da damuwa ta kirawo sunan ta"hanne lafiya na ganki kinyi shiru?? me ya faru??ko wani ne ya mutu??" Jin waɗan nan tambayoyi da altine take rattaba ne mata yasa ta fashewa da kuka,nan take altine ƙara rikicewa domin ta tabbatar ba lafiya ba.
"Dan Allah ki gaya min mai ya faru,wallahi duk kin ɗaga min hankali.cikin kuka hanne tace"yayan mu innar muce wallahi"altine tace"Innar mu kuma??ko dai wani abu ne ya faru da ita??"kan ta ta girgiza alamar a'a,tace to me ya faru"cikin kuka hanne ta bata labarin duk abin da ya faru.
Cike da tsanani mamaki take kallon ta tare da girgiza kanta tace"wato har yanzu innar mu bata bar mugun abin da take yiwa HALIMATU ba sai ma abinda ya ƙaru ko?? to wallahi zanje har gidan na sameta,shima baban namu bata ƙyaleshi ba sai da ta tozarta shi a idon mutane sannan hankalin ta ya kwanta ko?? ,yanzu ai gashi nan ya tafi ya barta!! to zanje gidan kawu musa na fad'o masa duk abin da yake faruwa tun da shi tana jin maganar sa!! ke kuma kiyi shiru ki bar kukan nan haka,kiyi zaman ki anan tukun na in yaso daga baya kya koma,bari naje na kawo miki ɗanwake" daga haka ta fice daga cikin ɗakin.
MUKHTAR
Tafe yake yana driving,amma kwata kwata ya rasa abin da yake yi masa daɗi sabo da tsabar baƙin cikin da rufaida ta ƙunsa masa.yana shiga cikin company ɗin direct office ɗin sa ya nufa, sakatariyar sa na gaishe shi hannu kawai ya ɗaga mata.jacket ɗin suit ɗinsa ya cire ya rataye ta ajikin hanger sannan ya nufi katafaren table ɗinsa ya jawo kujera ya zauna.
Laptop ɗin sa ya ciro ya fara duba ayyukan da aka turo masa,yana tsaka da aikin ne yaji an danna doorbell alamun wani yana so ya shigo,cikin ƙasa ƙasa da murya kamar baya son magana yace "come in"nan take aka buɗe ƙofar aka shigo, sakatariyar sa ce hannun ta riƙe fiels . ƙarasowa tayi gaban tale ɗin ta ɗora masa files ɗin tare da cewa "sire ga waɗan nan!! ana so ka duba ka saka hannu a cikin su" ba tare da ya ɗago ya kalleta ba yace mata "Okey". tsayawa tayi tare da zuba masa ido tana kallon sa ba tare da ta tafiba,still bai ɗago ba yace mata "what are you watting for".
Cike da kunya ta juya ta bar office ɗin.bayan ya gama duba files ɗin ne ya jawo telephone ɗin da ke kusa dashi ya daddana numbobi ya kara a kunnen sa,daga ɗaya bangaren aka ɗauka aka fara magana,yace okay "kasame ni a office ɗina".yana gama faɗi ya katse wayar, ba'a wani ɗauki lokaci ba ya ji ƙarar door bell,nan take ya bada izinin shigowa cikin office ɗin.
Wani matashi ne yayi sallama ya shigo dogo fari wanda bazai wuce Sa'an mukhtar ba mubarak kenan!! shima a company ɗin yake aiki, shine mataimakin mukhtar sannan kuma aminin sa,yana ƙarasowa ya ja kujera ya zauna tare da duban mukhtar yace"ashe ka ƙaraso?? ɗazu nazo akace min baka zoba ,gaskiya yau kayi latti" mukhtar yace "wallahi mubarak abubuwa ne suka tsayar da ni shiyasa ban samu ƙarasowa da wuri ba"
Mubarak yace"okay,ya kake ya yara da madam!!" yace"yara suna nan ƙalau sun tafi makaranta,gwara da Allah yasa ka tuna min ma,bari na kirawo makarantar na sanar dasu idan an tashi kar a kawo su gida akaisu can gidan mu"ya ƙarasa maganar tarda ɗaukan wayar sa yayi dialling number su,bayan an yi picking call ɗin ne ya sanar dasu sannan ya katse kiran tare da ajiye wayar.
Kallon sa mubark yayi tare da cewa "naji kace kar a mayar da yara gida akaisu gidan dady!! ina fatan lafiya dai ko??"ya ƙarasa maganar yana kallon sa.ajiyar zuciya mukhtar ya sauke tare da bashi labarin duk abin da ya faru.cike da ɓacin rai mubarak ya dubeshi tare da cewa "wai me yake damun rufaida ne?? wacce irin rayuwa ta ɗaukarwa kanta ne??wallahi shiyasa kaga bana zuwa gidanka badan komai ba sabo da rashin mutun cin ta,duk irin ha'kurin ka sai da takai ka bango!! wallahi da nine tuntuni da na daɗe da ƙaro aure tun da ba ita kaɗai ce mace ba,ai gwara da kai mata hakan,yanzu sai taje gidan su a koya mata tarbiyya ai".ya ƙarasa maganar ransa a mutuƙar b'ace.
"MUKHTAR yace wallahi mubarak na rasa ya zanyi wa rufaida,kwata kwata nida gwauro bamu da maraba,bani da iko a cikin gidana ban isa in faɗa mata magana tajiba,magana duk wadda tazo bakin ta haka take yab'amin ita,gashi bata kula da yaran nan kwata kwata sai kace ba itace ta haife su ba, har ta ita kanta bata tsaya ta gyara jikin ta ba bare ta tsaftace shi , ga ƙazanta tayi mata yawa,uwa uba kuma ga shi bata son yin sallah, na rasa yadda zan yi mata.babu abinda na rage ta dashi duk abinda take so ina yi mata amma ni kullum cikin 'kuntatamin take yi, sannan idan na kai ƙarar ta gidan su iyayen ta su goya mata baya, gaskiya wallahi na gaji!! wannan karan aure nake so na ƙara,idan yaso sai taje ta cigaba da duk abin da take so"
Mubarak "yace gaskiya nima wannan karan na goyi bayan ka ƙara aure ko Allah zai sa a dace, ina fatan dai kana da wadda kake so ka aura ɗin??"ya ƙarasa maganar tare da kallon shi. mukhtar yace"wallahi banida wadda nakeso, saboda kasan ni ba kula mata nake yi ba".
Nasani ni shaida ne,amma ai kana da tarin masoya,ya kamata ka duba koda cikin ɗalibanka ne!!"mukhtar yace" ni wallahi yanzu tsoron mata nakeyi, sabo da kwata kwata baka gane halayyar su sai ka aure su ka kawo su cikin gidan ka!! ka ga dai yadda mukai da rufaida,kai ɗin nan shaida ne lokacin da ina neman auran ta,haka ta dinga yi min ladabi tana nuna min ita ɗin ta Allah ce,amma muna yin aure ta fito min da true colur ɗin ta".
Ya ci-gaba da cewa"shiya sa wallahi nake tsoron matan, sabo da bakasan irin wadda zaka kuma ɗakko wa ka kawo cikin gidan ka ba,amma in sha Allahu zan yi magana da daddy" ya ƙarasa maganar tare da kallon mubarak,jinjina kai mubarak yayi tare da cewa"haka ne abokina,karka damu in sha Allahu wannan karan za'a dace da izinin ubangiji " yace"to Allah yasa".ya amsa da"ameen"
Mi'kewa yayi tare da duban mukhtar yace "ya maganar tafiyar da zaka yi?? sabo da kaga dilolin mu suna buƙatar kaya Masu yawa sosai,ya kamata mu fara shirye-shiryen tsara sababbin design" tafiya tana nan In sha Allahu nan bada daɗewa ba"yace"tom shikenan Allah ubangiji ya kamu".daga haka suka yi sallama.
Bayan fitar mubarak ne ya faɗa duniyar tunani,shi yanzu ta ina zai fara nemo matar da ta dace dashi ya aura,gashi yarin yar nan da yake gani a hanyar zuwa gidan gonar sa itama ranar nan da yaje bai ganta ba,yarasa me yasa yake jin tausayin ta!! ita kuma wannan da yagani a airport sunyi kama sosai da sosai,to kodai suna da alaƙa ne?? gaskiya dole naje na binka na gani.daga haka ya miƙe ya ɗauki mukullin motar sa ya fita,ko sallama bai yi wa mubarak ba ya bar company.
INNA LAURE
Cike da tsanani tashin hankali ta dubi malam musa tace" haba yaya ka rufamin asiri dan Allah,idan ka koreni daga nan ɗin ina kake so naje?? kasan bani da kowa sai Allah sai kai,mukad'ai fa iyayen mu suka haifa fa,dan Allah dan Annabi ka rufa min asiri "ta ƙarasa maganar tare da fashewa da kuka.
Wani bazan kallo malam musa yayi mata tare da cewa "ke kalle ni nan da kyau, maganar tsira da raina nake yi miki ba maganar 'yan uwan taka ba,yaron nan hatsabibin yaro ne,ya addabi kowa a garin nan babu mai iya taka masa burki sabo da yana da goyon baya sosai da sosai,kamar yanda na faɗa miki ana zargin sa yana cikin ƙungiyar masu garkuwa da mutane,yanzu haka harin da aka kawo mana ana rad'e rad'in yana da sa hannu a ciki, Allah ne ya tsare mu basu tafi damu ba sai dabbobin mu da suka kwashe mana tass suka tafi da su,yanzu zancen da nake yi miki wasu duk an tafi dasu tare da dabbobin na su, saboda haka wallahi maza maza ki tattara ki bar min gidana,domin bazaki zo ki jazamin wata masifar ba"
Inna laure ta sake fashewa da kuka a karo na biyu tace"wallahi yaya babu inda zan tafi anan zan zauna domin bani da inda yafi gidan ka, Sabo da haka duk abinda zakayi sai dai kayi" baki buɗe cike da mamaki malam musa yake kallon inna laure,har ya buɗe baki da nufin zai yi mata magana kenan yaji muryar matarsa lamun de na cewa "tabdijam wallahi laure sai kin bar gidan nan dan bazaki goga mana kashin kaji ba, idan kuma kince bazaki tafi ba to wallahi tattara kayana zanyi na barmuku gidan!! dan bazai yiwu na zauna da ke ba cikin dare a zo a yi min yankan rago ba!!" lamunde ta ƙarasa maganar tana huci.
Cike da hasala malam musa ya miƙe tare da duban Inna laure yace" zaki fita ko sai nayi maganin ki!! dan wallahi babu inda lamunde zataje sai dai ke kifi ta kibar mata gida ta,ai dama ba tun yanzu nake gargad'in ki akan ɗiban albarkar da kike yiwa mijin ki ba,shine yanzu da mugun halinki ya koreshi ni kuma zaki zo kiraba ni da tawa matar ko??to wallahi baki isa ba kinyi kaɗan"