← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 80

Sashe 45

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina matuƙar godiya da addu'o'in ku a gare ni tare da fatan Alkhairi,ku ɗin masoya ne na ƙwarai da gaske, Allah ubangiji ya saka muku da mafificin alkhairin sa ya biya muku buƙatun ku na Alkhairi🙏🏻

Daga alƙalamin FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA).......✍🏻✍🏻

Ga masu neman book ɗin nan tun daga farko zuwa in da aka tsaya ya tun tuɓeni ta wannan numbern👇🏻👇🏻

08162055134

Share fisabilillahi.

💝💞HALIMATU💝💞

(Love, sacrifices, destiny & betrayed)

💝💞💝💞💝💞💝💞

Story & Writing

By

FATIMA BINTU ABDULLAHI (UMMU AYSHA)........✍🏻✍🏻

Ƙarƙashin jagorancin

(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)

Golden pens........✍🏻✍🏻

💝💞💝💞💝💞💝💞

A 2024 novel

💝💞💝💞💝💞💝💞

Pages ___________55&56

"HALIMATU"

_____________a ɓangaren HALIMATU kuwa abubuwa suna tafiya dai-dai yanda ya kamata,domin ta fara karatun ta cikin nasara da taimakon Ubangiji, sannan kuma da jajir cewa da kuma himma,ko kaɗan bata wasa da karatun ta kuma bata fashin zuwa makaranta da kuma latti.
Wannan dalilin ne ya sa ta taka muhimmiyar rawa wajen samun nasara a karatun ta.

Yanzu ma zaune take a bakin wata bishiyar darbejiya tana duba littafin ta,fitowar su daga lecture kenan kafin su shiga wata nan da two hours.
Ƙwala mata kira ta ji an yi daga nesa,sarai ta san me kiran nata amma ta yi burus kamar bata ji kiran ba har sai da mai kiran nata ta ƙaraso in da take zaune.

"Haba HALIMATU! tun daga nesa fa nake kiran ki amma kika share Ni kin bar ni na buɗe maƙoshi na ina ta ƙwala maki kira amma kin yi burus kamar bakya jina!"

"Hmm salma kenan,ke dai wallahi ba kya gajiya da ƙorafi! In banda abin ki tun daga nesa ki ke so na ɗaga murya ta na amsa miki.?"

"Toh meye idan kin amsa min ɗin! haba sai kace wata matar aure!"

"Ai ko ba matar aure ba haramun ne mace ta dinga ɗaga muryar ta,sabo da muryar mace al'aurace! Sannan kuma yana rage wa mace kima da daraja! kinga kuwa ɗaga muryar bashi da wani amfani".

"Hmm ke dai kika sani! Ai dama na san zancen bazai wuce haka ba,ace kullum mutum bashi da aiki sai dai wa'azi!!?"

Ta ƙarasa maganar tana zama kusa da halimatu.
Murmushin halimatu kawai ta yi tare da girgiza kan ta,hannu ta sa ta jawo jakar ta tare da buɗe wa ta ciro miet pie manya guda huɗu da lemo guda biyu ta a jiye musu a gaban su.
Ɗauka suka yi suka fara ci suna ɗan yin hira kaɗan- kaɗan a kan kara tun su.

Wayar halimatu da ke cikin jaka ce ta yi ƙara,hannu ta sa ta ciro domin tun daga jin ringing ɗin ta san me kiran nata.

Picking call ɗin ta yi tare da ɗora wayar a kunnen ta ta yi sallama cikin muryar ta mai san yi da nutsuwa.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa:

"Lafiya ƙalau my love,sai dai na yi missing ɗin ki sosai,ina fatan kema haka"
Murmushi ta yi har yana jiyo sautin shi tare da cewa:

"nima haka habibi ina fatan kana lafiya,ya aiki!"

"Lafiya ƙalau,sai dai bana jin daɗin komai Sabo da rashin ganin sanyin idaniya ta"
"Murmushi ta yi tare da cewa:

"Toh baga shi yanzu muna waya ba habibi"
Ta faɗa cikin shagwaɓa.
Wani irin abu ya ji yana taso masa tun daga babban ɗan ya tsan ƙafar shi,nan take ya kashe wayar ba tare da ya yi mata sallama ba.

Ƙura mata ido salma ta yi tare da cewa:

"Dawa kike wannan maganar haka kina shagwaɓa.?"

Miƙewa halimatu ta yi tare da cewa:
"Idan kin gama surutun ki same ni a class"
Daga haka ta miƙe ta yi tafiyar ta ba tare da ta jirawo abin da salma zata ce ba.

Ganin ta yi tafiyar ta ne ya sa salma ita ma ta miƙe tare da bin bayan ta tana ta surfa mata masifa.

"ALHAJI USAMA"

A ɓangaren su alhaji usama kuwa jikin sa ya yi sauƙi sosai Alhamdulillah, domin kuwa yanzu har fita yake yana zagaya wa cikin a asibitin,ɗaya ƙafar tasa ta hagu ita ma ta yi sauƙi sosai,domin suna da ƙwararrun likitocin (authorpadic) wato ƙashi.
Wannan dalilin ne ya sa tun jiya da daddare da likitocin suka duba shi suka bashi sallama tare da rubuta masa magunguna.

Tun a daren suka fara har haɗa kayayyakin su domin tun da sassafe suke son su wuce.

Washe gari tun da sassafe suka ɗauki hanya bayan sun kirawo hajiya Hauwa sun sanar mata da tasowar ta su.
Sai wajen ƙarfe takwas suka iso sakamakon tsaye -tsayen da suka samu a hanya.

A dai -dai ƙofar gida mai taxi ya ajiye su,malam SALIHU da sauran maƙofta da suke zaune a ƙofar gidansa ne suka taso da sauri suka tsaya a bakin motar,da yake tun a mota Aminu ya sanarwa da malam SALIHU cewa suna nan tafe.
Hakanne ya sa malam SALIHU ya sanar da maƙofta zuwan na su,
buɗe motar malam SALIHU ya yi tare da kamo hannun Alhaji USAMA ya fito da shi daga cikin motar a hankali,yayin da Aminu ya miƙo masa sandar sa.

Karɓar sandar ya yi tare da zura ragowar ƙafar ta sa a cikin sannan ya dai -dai ta tsayuwar sa,ɗago da fuskar sa ya yi tare da kallon tarin mutanan da suka kewaye shi suna ta faman kallon sa,nan take ya fashe da wani irin kuka mai ban tausayi da tsuma zuciya.

Ganin hakan ne ya sa malam SALIHU da yake kusa da shi ya ɗora hannun sa a kan kafaɗar sa yana bubbuga wa alamar rarrashi tare da cewa:

"Haba ALHAJI! ai ba kuka ya kama ta kayi ba, gode wa Allah ya kamata ka yi da ya baka lafiya kuma ya dawo da kai cikin iyalin ka lafiya"

Cikin shesh-sheƙar kuka ya ɗago da kansa ya kalli malam salihu hawayen nadama na zuba a fuskar sa yace:

"Ƙyale ni in yi kuka malam salihu! domin kuka ya zama dole in yi shi, Sabo da duk abin da ya faru ni na jawo wa kai na gurin zalunci da son duniya haɗe da saɓawa ubangiji!! na daɗe ina saɓawa ubangiji na sabo da cikar burina!ga shi yanzu daga ƙarshe na afka ramin dana sani!!"

Hawayen da yake zubo masa ya share ya ci gaba da cewa:

"A gaban ido na ɓarayi suka kashe amini na har lahira!! hakan bai ishe su ba sai da suka bi takan wasu da motar su suka tattake su,ni kuma suka yi ta harbin ƙafafuwana da bindiga,wanda a sanadiyyar haka ne ina ji ina gani aka yanke min ƙafa guda ɗaya,gashi ita ma ɗayar ba wani ƙoshin lafiya ne da ita ba, daga ƙarshe ina ji ina gani na tafi da ƙafafuwa na guda biyu lafiya ƙalau amma yanzu na dawo da ƙafa guda ɗaya!!"

Ya ƙarasa maganar yana wani irin gunjin kuka mai tsuma zuciya.
Duk wanda ka kalla a gurin kuka yake yi daga yaran har manyan, domin ba ƙaramin karya zuciyar mutane maganganun sa suka yi ba.
Gaba ɗayan su tsoron Allah ya ƙara shiga cikin zuciyoyin su.

Shi kanshi me taxi ɗin da ya kawo su sai da ya zubar da hawaye sabo da jin wannan mummunan labarin,kayan su ya sauke musu haɗi da yi musu sallama da fatan samun sauƙi ya juya ya tafi.
Da taimakon malam salihu ya shiga cikin gidan har cikin parlon ya raka shi tare da yi masa nasiha mai ratsa jiki.

Zaune take a cikin bedroom ɗinta tana ta faman sharɓar kuka kamar ranta zai fita,tun lokacin da mai taxi ya sauke su a bakin get take a gurin tana hangen duk abin da yake faruwa.
Lokacin da taga malam salihu ya ruƙoshi sun nufo cikin gidan sai tayi sauri ta koma Cikin gidan tare da shige wa cikin bedroom ɗin ta ta zauna take ta faman kuka.

Shirun da ya ji ne ya sa yake mamakin ina sauran mutanan gidan suka shiga ne,domin yana so ya gansu ko ya ji sanyi a cikin zuciyar sa.
Sallamar aminu ce ta katse masa tunani da yake yi in da ya ji Aminu yana cewa:

"A'a ya nagan ka zaune kai kaɗai a nan daddy.? Ina momyn take ne kuma ta barka kai kaɗai anan zaune.?"

Har ya buɗe baki da nufin yin magana sai ga hajiya Hauwa ta fito daga cikin bedroom ɗin idanuwan ta sun yi luhu luhu kana ganin ta kasan taci kuka ta ƙoshi.
Kusa da shi ta zauna tare da yi masa sannu da zuwa,kamo hannun ta yayi ya rungumo ta zuwa jikin sa,wata iriyar ajiyar zuciya suka sauke gaba ɗayan su.

Shiru tayi tare da yin lamo a cikin jikin sa tana sauke ajiyar zuciya akai-akai,ɗago kansa ya yi a hankali ya dube ta tare da cewa:

"Ina RUFAIDA ne! Tun da na shigo banji ɗuriyar ta ba! ko dai bata gidan ne!!"

Fashe wa da wani irin kuka ta yi mai cin rai har da shesh-sheƙa bakin ta yana rawa tana so ta yi magana amma kuma ta kasa, ba ƙaramin tashin hankali Alhaji USAMA ya shiga ba,cikin wani irin yanayi ya ɗago ya dubi Aminu tare da cewa:

"Me ya faru da RUFAIDA ne!! Me ya same ta!! ka gaya min me yake faruwa!!"

Shi kan sa Aminu duk dauriyar sa sai da ya zubar da hawaye,domin Alhaji USAMA bai san abin da yake faruwa da rufaida ba,sabo da ba'a faɗa masa ba gudun kar ya ɗaga hankalin sa,duk lokacin da yace a bata waya su gaisa sai hajiya Hauwa tace in taji maganar sa kuka take yi Sabo da tausa yin da da take yi.

Shirun da yaji ne ya sa ya daka wa Aminu wata iriyar gigitacciyar tsawa tare da cewa:

"Wai me kuke ɓoye min ne!! bazaka buɗe baki ka yi min bayani ba.?"
Hannu ya sa ya share hawayen sa tare da buɗe baki da ƙyar ya labar ta masa abun da yake faruwa da rufaidan.

Wani irin abu ne ya taso masa tun daga cikin cikin sa ya tokare masa zuciya,ya rasa ma ya zai yi da rayuwar sa,daga wannan sai wannan.
Chapter 45 · 0% Book details