Sashe 26
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushi MOMY tayi tare da karɓar ledar ta buɗe domin ganin abin da yake ciki.wasu irin turaruka ne namata designer's masu mugun ƙamshi tare da set ɗin mayukan gyaran gashi da kuma kayan make up.girgiza kai MOMY tayi tana mamakin wannan kyauta,domin gaskiya bazata yi ƙaryaba wallahi taji ɗin kyautar da aka yiwa autarta.
"Gaskiya mutanan akwai kirki da karamci" ta faɗa tare da kallon daddy, " ai kaɗan ma kika gani shi yasa nayi kwaɗayin haɗa zuri'a dasu" MOMY tace "haka ne Alhaji! Allah ubangiji ya tabbatar mana da Alkhairin sa" daddy yace "ameen".
Kallon MUKHTAR daddy yayi tare da cewa"surukar tawa batace a gaisheni ba!!" ya faɗa cike da zolaya, ai da sauri muktar ya sunnar da kanshi ƙasa.meena ce tayi caraf tare da cewa"tace tace tana gaisheku mana! gashi nan harda tsaraba tace a kawo muku!!" ta faɗa tana tashi tare da ɗakko robobin da sukazo da su ta ajiye a gaban su daddy.
"Da kyau ma sha Allah,muna godiya sosai Allah ubangiji yayi mata albarka" gaba ɗayan su suka amsa da ameen.momy bari na ɗakko abu na ɗibar mana inyaso sai a barwa yaya a ciki tunda shi tafiya zeyi" ta faɗa tare da miƙewa tsaye ta shige cikin kitchen.bata daɗe ba ta fito ɗauke da madai daicin try a hannun ta,ɗibar musu komai tayi tare da ajiyewa akan center table ɗin da yake gaban su.
Daddy ne yace"Alhmdllh,yau zanci kyautar da tafito daga hannun matar da ɗana zai aura,ko matarsa da ya aura tsawon shekaru bamu taɓa cin abincin taba,ya faɗa tare da yin bismillah ya kai cikin bakinsa.ita dai MOMY shiru tayi tana taci, amma a cikin zuciyarta wani irin daɗi takeji sosai .
MEENA ce tace "in sha Allah daddy abinda yafi wannan ma zakuci a wajen aunty halima,domin tana da kirki da hankali ga nutsuwa,kuma wallahi daddy yarinya ce koni na girme ta,saidai ta fini ƙirar jiki.kallonta daddy yayi tare da yin murmushin su na manya yace"ma sha Allah! kice nayi dacen suruka!!"
"Ae wallahi daddy gata muguwar kyakkyawa farasol ga gashi har nan kamar na yanka"ta faɗa tana nunawa daddy wajen ƙugunta.momy ta kalle ta tace"to parrot gashin matar yayan naki zaki yanka!!".gaba ɗayan su dariya suka yi banada MUKHTAR da ya kalleta ya girgiza kansa tare da yin murmushi.
Miƙewa MUKHTAR yayi tare da cewa"daddy MOMY ni zan wuce dare yana ƙarayi"daddy yace tom Allah ubangiji ya tsare,yakamata ma ka tattaro ka dawo gida kafin muga abinda Allah zaiyi" MOMY tace"nima gaskiya nayi tunanin hakan" sun kuyar da kanshi yayi tare da cewa ina sha Allahu nan da sati ɗaya zan dawo" "Allah ubangiji ya kaimu,zansa MEENA da mai aiki su gyara maka part ɗinka" girgiza kai yayi tare da yi musu sallama ya fita,bin bayansa MEENA tayi ɗauke da kayan.........
"INNA LAURE"
Tun bayan da altine tabi Inna laure gidan suka kwana tare,washe gari tunda suka tashi da safe zuciyoyin su suke cike da fargaba, Allah Allah suke yi baban kamilu ya siyar da tunkiyar wajen rahine ya kawo musu kuɗin ko sa samu salama a cikin rayuwar su....
Zaune suke sunyi jugum jugum kamar waƴanda aka aikomusu da saƙon mutuwa,kowanne daga cikin su da abin da yake saƙawa a cikin zuciyarsa.
Sunyi nisa a cikin tunanin da suke yi ne bazato ba tsammani sukaji ihu da hargowa na tashi a ƙofar gidan,cikin matsanancin tashin hankali suka miƙe tsaye a firgice,kafin sukai gayin wani yunƙuri sukaji an daddage an daki ganbun ƙofar gidan,nan take ya ɓalle tare da faɗuwa ƙasa.
Cikin hanzari BUBA da jama'arsa suka fara shigowa cikin gidan,baƙaramin yawa ne dasu ba duk girman tsakar gidan seda yayi musu kaɗan,dole wasu daga cikinsu suka tsaya a shigifar gidan .mutuwar tsaye inna laure da altine sukayi,gaba ɗaya jikinsu rawa yake yi kamar mazari.
Wata iriyar sheɗaniyar dariya BUBA ya kece da ita har da ƙyaƙyatawa,ganin haka yasa yaransa suka kurma wani irin uban ihu tare da hargowa,daga bisani suka tuntsure da wata iriyar dariya mai kama da kukan kare. zaro idanu Inna laure tayi daga bisani kuma ta fashe da kuka mai ban tausayi tare da durƙushewa a gurin.......
Itama altine kukan takeyi sabo da bata taɓa ganin tashin hankali ido da ido irin wannan ba,durƙusawa tayi a gaban buba tare da cewa "dan Allah ranka ya daɗe kayi haƙuri kayi mana rai,wallahi sabo da kai mukazo muka kwana a gidan nan domin munsan zakazo, shiyasa ma mijin ƙanwata yafita da tunkiyar ta kasuwa tunda safe domin ya siyar ya kawo a baka kuɗin.altine ta faɗa tane mai ƙara rushewa da kuka.
Wata iriyar tsawa BUBA ya daka mata tare da zaro sharɓeɓiyar adda tana sheƙi ya nunata da ita tare da cewa "rufemin baki! kinsan wanene Ni harda zata yaudare ni tayi min yawo da hankali??" to wallahi ba'a taɓani na ƙyale muddin mutum ya shiga gonata sai na hukun tashi" ya faɗa yana zare mata jajayen idanuwansa.
Ya cigaba da cewa "bayan na karɓi kuɗina dole ne ta karɓi hukuncin ta,dan wallahi bazan yafe mata ba,ya ƙarasa maganar tare da juyawa ya kalli inna laure da fuskatarta tayi kaca kaca da ruwan hawaye harda majina.
Wani daga cikin yaransa ne yayi kukan kura tare da ɗaga ƙatuwar gora ya daddage ya kwaɗawa inna laure a ƙafa jikake ruƙuƙus,wani irin gigitaccen ihu tayi tare da shemewa wanwar a ƙasa sumammiya.ganin haka yasa altine ta zaro idanunta tare da sakin wani irin marayan kuka ta duƙushe a gaban inna laure gwanin ban tausayi.
Ganin haka yasa BUBA sheƙewa da dariyar shakiyanci yaransa na tayashi, ana cikin wannan haline baban kamilu ya faɗo cikin gidan kamar an wurgoshi,suna ganinsa suka yi masa ƙawanya.kallonsa buba yayi tare da cewa "ina fatan kaine mai kawo saƙon" cike da dabur cewa baban kamilu yace"ae nine oga" hannu kawai BUBA ya miƙa masa,jiki na rawa ya saka hannu a aljihu ya zaro duka kuɗin gaba ɗaya ya miƙa masa,ba zato ba tsammani yaji an kafta masa adda a kafa!! nan take ya kurma ihu tare da zubewa a ƙasa ya fara shure shure, "wannan shine babban tukwicin ka" buba ya faɗa tare da ficewa daga cikin gidan yaransa na take masa baya.
"RUFAIDA"
Lokacin da mahaifiyar ta tafita daga gidan domin zuwa sama mata mafita,kai tsaye wajen wani malamin ta ta nufa wanda yake yawan yi mata aiki,bayan tayi masa bayanin dukkanin abinda yake faruwa ya girgiza kansa tare da buga ƙasa nan take ya ɗago ya kalleta da mamaki a fuskar sa.ƙara buga wata ƙasar yayi har sau biyu amma still dai abu ɗaya take nuna masa.
Sake kallonta yayi tare da share zufar da ta karyo masa a goshin sa yace"gaskiya akwai gagarumar matsala!!" cike da tashin hankali ta dubeshi tace "wacce irin matsala ce wannan harda zata firgita ka malam??" numfashi ya sauke tare da cewa"gaskiya yaron nan yaiwa yarinyar ki nisa sosai wanda na kasa ganin iyakarsa!!"
Cike da tsananin tashin hankali ta dubeshi tace"wacce irin magana ce wannan kake faɗa haka malam??" abinda kunnen ki ya jiye miki tabbas haka ne,kuma kinsan munyi shekaru tare ina yi muku aiki batare da wani shamaki ba!! sabo da haka duk inda zaki abin da za'a gayamiki kenan Hauwa!!".
Ya ci-gaba da cewa bama wannan ne abin damuwa ba, yaron nan aure zeyi nan bada jimawa ba!! Kuma duk bincike na yakasa nuna min wacce yarinya ce zai aura!! duk sanda na buga ƙasa duhu nake gani bana ganin komai!! tabbas yarinyar ta daban ce,kuma ita ɗin mai Sa'a ce,tabbas idan ya aure ta zai shahara sosai da sosai!! cikin tashin hankali ta zabura ta miƙe tsaye kamar wadda aka zubawa tafasashshen ruwan zafi.
Wannan kenan..................✍🏻
Ina matuƙar godiya a gareku masoya na masu tarin albarka, kuɗin masoyan ƙwarai ne,ina alfahari daku a koda yaushe...............
Daga alƙalamin FATIMA BINTU ABDULLAHI (UMMU AYSHA).........✍🏻
Share fisabilillahi .
08162056134.
💝💞HALIMATU💝💞
(Love, sacrifices, destiny & betrayed)
💝💞💝💞💝💞💝💞
Story & Writing
By
FATIMA BINTU ABDULLAHI (UMMU AYSHA)
Ƙarƙashin jagorancin
(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)
Golden pens..............✍🏻
💝💞💝💞💝💞💝💞
A 2024 novel
💝💞💝💞💝💞💝💞
Pages____________31&32
"UMMA"
A ɓangaren umma mahaifiyar RUFAIDA kuwa, lokacin da boka ya gama yi mata bayani take ta miƙe tsaye kamar an watsa mata ruwan zafi a jikin ta,ta dube shi da idanun ta da suka yi jajur sabo da ɓacin rai da tashin hankali tace "da kata malam!! Wannan wacce iriyar magana kake gaya min mara daɗin sauraro!! To bari kaji in gaya maka! Idan kai ɗin ba zaka iya yin wannan aikin ba ai sai ka gaya min! Amma bawai ka zauna kana tsara min ƙarya ba!!" Ta ƙara sa maganar tana masa wani irin mugun kallo.
Wani irin murmushin takaici malam ya saki sannan ya dube ta tare da cewa "Hajiya Hauwa kenan,haƙiƙa kin bani mamaki! Shekara ɗai ɗai har takwas ina yi miki aiki babu gajiya wa, kuma duk irin aikin da nayi miki yana tafiya dai dai kuma ana samun biyan buƙata sosai da sosai,amma shine yanzu sabo da ke ɗin butulu ce wadda kwata kwata bata san halacci ba zaki dubi tsabar idanu na ki gaya min wannan maganar!! Ai ko ba komai na haife ki!! Ko dan furfura ta ya kama ta ki girmama Ni!!"
Ajiyar zuciya ya sauke yana jin wani irin ɓacin rai na taso masa, cikin ƙunan rai ya ci-gaba da cewa "ina so ki buɗe kunnuwan ki ki saurari abin da zan faɗa miki!! Duk inda zaki je abin da na faɗa miki shi za'a ƙara faɗa miki! Idan kuma kin ji akasin haka to kuɗin ki kawai za'a ci!! Duk abin da kika ga na kasa lalubu shi to ba ƙaramin al'amari bane ba! Don haka ki fice min daga nan!! Kuma ina gargaɗin ki da kyau kar na ƙara ganin ƙafafuwan ki anan gurin!idan kuma ba haka ba kin san sauran!!".
Ya ƙara sa maganar cike da wata irin tsawa yana nuna mata hanyar fita.cike da tsoro jikin ta yana rawa ta juya cikin sauri ta fice daga ɗakin nasa,domin bata taɓa ganin ɓacin ran malam irin haka ba.ajiyar zuciya ta sauke tare da share gumin da ya tsatstsafo mata a goshin ta , sannan ta fita daga gidan ta miƙi hanya!tana tafe tana zancen zuci.