← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 80

Sashe 44

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba ƙaramin daɗin addu'ar daddy ya jiba,hannun sa ya saka a cikin aljihun sa ya ɗakko rafar sababbin kuɗi ƴan dubu dubu ya miƙa mata tare da cewa:

"Ungo karɓi wannan doughter ki ruƙe a hannun ki, sabo da ko da wani abu zai taso na siyan materials ɗin karatun ki bana nan,in ya so idan kuɗin suka ƙare sai ki gawa momyn ku zata fada min kin ji, sannan akwai drivern ki da na ajiye miki da zai dinga kai ki makaranta yana ɗakko ki,yanzu haka yana waje yana jiran ki "

Ya faɗa yana miƙa mata kudin.
Hanna yenta biyu ta saka ta karɓi kuɗin tare da yin godiya, miƙewa ta yi ta shiga cikin kitchen ta buɗe fridge ta ɗakko exotic da hollandia da cake ta saka a cikin jakar ta sannan ta fito daga cikin kitchen ɗin.

Tana fitowa taga farouq tsaye cikin shiri yana magana da Sadiq,da sauri ta nufi in da yake tare da cewa:

"Yaya farouq yau zaka tafi ka bar mu ashe! gaskiya zan yi missing ɗin ka sosai wallahi yaya na, Allah ubangiji ya kai ku lafiya ya baka dukkan nassara akan karatun da zaka je ka yi, Allah ya tsare mana kai daga sharrin maƙiya da mahassada! Ina yi maka fatan alkhairi ɗan uwana"

Ta ƙarasa maganar hawaye na zubo wa akan fuskar ta, hankachef ya ɗakko a cikin aljihun sa ya goge mata hawa yen tare da cewa:

"Haba ki dena kuka my lovely sister, addu'a zaki yi min kin ji.? Kuma ai zamu dinga yin waya ai ko.?"

Kan ta ta girgiza masa alamar eh.

"Yace yawwa good girl muje na raka ki driver na jiran ki karki yi latti kin ji"

Ya faɗa yana kama hannun ta suka fita daga cikin parlon,bin su suka yi da lallo suna murmushin dramer ɗin su.
Bayan ya rakata ne ya dawo parlon in da suma babu daɗewa suka ɗunguma gaba ɗayan su zuwa airport domin su yi musu rakiya.
Wannan kenan.

***********************************************************

"ALHAJI USAMA"

A ɓangaren ALHAJI USAMA kuwa Alhamdulillahi an yi masa aiki cikin nasara, domin ya farfaɗo ya dawo cikin hankalin sa kuma yana cin abinci sosai,domin duk surutan da yake yi yanzu duk ya dai na,sai dai yawan tunani da yake yi ne yasa jinin sa yake ɗan hawa wani lokacin.

Wannan dalilin ne yasa likitocin suka ce a dinga kwantar masa da hankali, sannan a dinga gujewa duk wani abu da aka san zai ɗaga masa hankali.

Wannan dalilin ne yasa Aminu yake tausar sa da daddaɗan kalamai masu kwantar da hankali ko kuma ya zauna ya yi ta jan sa da hira,amma duk da haka in dai ya tuna da mutuwar abokin sa kuma aminin sa ALHAJI Garba to ranar yuwni zai yi yana kuka.

Zuwa yanzu jikin nasa da sauƙi Alhmdllhi,shi yasa ma likitocin suke saka ran sallamar shi nan ba da jima wa ba.

"RUFAIDA"

A ɓangaren RUFAIDA kuwa sai dai mu ce lamarin dai sai godiya,domin jikin nata babu wani sauƙi da ci gaba da ake gani a kan al'amuran nata, dukkanin tests ɗin da aka yi mata da X-ray duk sun nuna lafiyar ta ƙalau babu wani ciwo a tattare da ita, gashi kuma sai kashe kuɗi suke yi.

Gaba ɗaya kuɗin da aka sai da sarƙar gold ɗin ta sun ƙare har ma an kuma sai da wasu, wannan dalilin ne yasa likitocin suka ce mata su koma gida a jarraba yi mata na Hausa,domin a cewar su suna ganin kamar ciwon nata ba na asibiti bane ba.

Wannan dalilin ne yasa aka basu sallama suka dawo gida suka ci gaba da jin ya.
Yanzun ma zaune take ta yi tagumi ta faɗa duniyar tunani,ita yanzu ya zata yi da rayuwar ta..? yanzu idan abun da suke dashi ya ƙare ya zata yi..? shin wane ne zai ci gaba da taimakawa musu ne..?

Ga rashin lafiyar Alhaji USAMA ga kuma ta RUFAIDA, dare ɗaya Allah ya ai ko musu da wannan mummunar jarrabawar,gashi Aminu ba wani kasuwan ci yake yi ba illa koyarwa da yake yi a secondary school ana biyan shi albashi duk wata.

Dama can mijin RUFAIDA ne ya ɗauke musu larurorin komai na rayuwa babu abinda baya yi musu,duk abin da ya taso musu babu kunya suke tunkarar shi kai tsaye su roƙeshi kuɗi kuma hakan baya hana cewa yaƙi yi musu.

Duk da rashin kyautatawar da ƴarsu take yi masa haka yake ta faman ɗawainiya da su ko godiya basa yi masa,to gashi yanzu ya saki rufaidan ma basa tare gaba ɗaya,duk wani abu da yake yi musu shi a da yanzu duk ya dena yi musu,hatta da kiran wayar su da yake yi a kai a kai duk ya dena yi yanzu, shin yanzu ya zata yi..?.

Hawayen da ya zubo mata a kan fuskarta ta share, nan take ta ji wani irin ɗaci da maƙaƙi ya taso mata tun daga cikin zuciyar ta,ji take yi gaba ɗaya duniyar ta yi mata zafi tare da juya mata baya a cikin ƙanƙanin lokaci,kamar ba itace wacce ta yi rayuwa a cikin daula da jin daɗi ba.

Hawaye ne suka ƙara zubo mata a karo na biyu sakamakon tunawa da ta yi da yayan ta,dama su biyu kacal iyayen su suka haife su,tun lokacin da mahaifiyar su ta rasu ta dena kulawa da al'amarin sa,duk da cewa tasan bashi da shi kuma yana buƙatar taimakon ta.

Amma a haka ta yi watsi da al'amarin sa,yanzu haka yana can Maidugurin shida matan sa uku da yara guda ashirin da biyu,gashi duk yawan cin yaran mata sun fi yawa kuma sune manya a cikin gidan saɓanin yaran maza da suka kasan ce ƙanana.

Ɗago kanta ta yi ta lalli rufaida da ta ƙura mata idanu tana kallon ta,hakan ya nuna mata alamar cewa wani abin rufaidan take buƙata.
Miƙewa ta yi ta ƙaraso in da take kwance,babu wata gaɓa ta jikin ta da take motsawa illa fuskarta kawai,hannun ta ta kai kusa da ƙafafun ta da nufin ta gyara mata kwanciyar ta.

Danshin da ta ji a ƙarƙashin ƙafafun nata ne ya tabbatar mata da cewa rufaidan fitsari ta yi,nan take ta tuna cewa ta mance bata saka mata pampers ba,a hankali ta janye ta gefe tare da cire mata zanin jikin ta,ruwa ta ɗebo mai ɗan ɗumi ta zuba a ƴar madaidaiciyar roba ta saka towel a ciki.

Goge mata jikin ta ta yi tare da canja mata kaya sannan ta gyara gurin da ta yi fitsari, bayan ta gama gyara mata jikin ne ta ta zaunar da ita tare da saka mata pillow a bayan ta da gefe gefen ta, sannan ta ɗakko cup da cokali ta zuba kunu a cikin cup ɗin tasa cokali tana bata tana sha a hankali har ta shanye.

Bayan ta gama bata kunun ne ta wanke cup ɗin ta ajiye gefe, dawowa ta yi kusa da rufaidan ta rafka uban ta gumi ta faɗa duniyar tunani,domin yanzu tunani ya zame mata abokin rayuwa.

"MALAM UMMARU"

A ɓangaren su malam ummaru kuwa, lokacin da suka fito daga cikin gidan kai tsaye masallaci suka nufa domin su gaba tar da sallar la'asar,bayan an idar ne ya gaggaisa da jama'ar gari ya yi musu ɗan alkhari ciki kuwa har da malam musa,direct gidan malam musa suka nufa in da malam ummaru yace da malam musa ya shiga ya yi wa aunty AMINA magana ta fito su wuce kar su yi dare a hanya.

Da sallama malam musa ya shiga cikin gidan in da ya iske su Zazzau ne suna hira gwanin ban sha'awa,da yake aunty AMINA mutum ce mai kirki da fara'a wannan kuma ga saurin sabo da mutane, wannan dalilin ne yasa suka saki jikin su da ita tamkar sun daɗe da sanin junan su.
Sallamar suka amsa gaba ɗayan su tare da ƙara gaishe shi,amsawa ya yi tare da gaya wa aunty AMINA saƙon mijin ta,a tare suka miƙe gaba ɗayan su suka ɗunguma zuwa waje domin su yi musu rakiya.

Har bakin mota suka raka su tare da yin sallama da junan su,ba tare da ɓata lokaci ba driver ya ja motar suka tafi tare da ɗagawa junan su hannu kamar kar su rabu.

"HANSAI"

A ɓangaren su HANSAI kuwa ita da ƴarta Safara'u babu wata matsala a tattare da su,domin suna nan abin su hankali su kwance suna gudanar da al'amuran rayuwar su hankali kwance,domin Allah ya saka musu albarka a cikin sana'ar koko da ƙosan da suke yi,yanzu har abincin siyarwa suke yi da rana,da daddare kuma su soya dankali da awara.

Sosai mutane suka san su a unguwar ta gwammaja,kuma Alhamdulillahi suna ciniki sosai da sosai, wannan dalilin ne ma yasa suke cikin rufin asiri dai dai gwargwado,a gefe guda kuma Safara'u nata zuwa makarantar ta duka biyun, domin a cewar HANSAI baza ta yi mata aure ba sai ta sami ilimin addini dana boko,shi yasa duk wanda ya zo neman aurenta take cewa baza ta aurar da ita ba sai ta samu ilimin addini dana boko,domin a cewar ta shigowar su birni ta ga amfanin ilimi sosai.
Kwata kwata sun manta da damuwar BUBA,rayuwar su suke yi hankali kwance abin su.

"BUBA"

A ɓangaren BUBA da jama'arsa kuwa harƙalla ta ci gaba sosai da sosai,domin a halin yanzu gaba ɗaya ma bai cika zaman ƙauyen haɗeja sosai ba,yanzu gari gari suke shiga suna yin kidnapping ɗin mutane.

Ga shi jama'arsa sun ƙara yawa sosai da sosai,ta ko ina samun mugwayen makamai masu haɗarin gaske suke yi gurin iyayen gidan su,shi yasa yanzu jama'ar ƙauyen su suka samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Amma kuma duk ranar da BUBA ya ziyar ci ƙauyen to fa sai wani mugun abun ya faru,sun rasa yadda za su yi da BUBA domin ya zame musu bala'i da masifa,
Ko sun kai ƙara ba'a daukar mataki a kan al'amarin,ko mai gari da kan shi ya sha kai kukan su wajen manya manyan masu muƙami amma amsar dai ɗaya ce sai dai a ce masa ya je za'a ɗauki mataki a kai, amma kuma abin mamaki sai dai ka ji shiru wai malam ya ci shirwa.

Wannan kenan.✍🏻
Chapter 44 · 0% Book details