Sashe 13
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zaune ta taradda shi yana duba laptop ɗinsa, coffee ɗin ta ajiye masa akan center table ɗin d'akin, tana ajiye wa tayi ficewar ta.bayan fitar ta ya ɗauki coffee ɗin ya fara sha,kwata kwata babu daɗi kawai yana sha ne.yana gamawa ya shiga toilet yayi brush ya fito yayi addu'a ya kwanta...........
INNA LAURE
Lokacin da ta isa gidan wanta domin karb'o awakin ta,tana zuwa ta taradda shi zaune a bakin ƙofar gida yayi ta gumi.sau uku tana yin sallama amma baiji ta ba sai a na huɗu ne yaji ta, d'agowa yayi ya kalle ta yace "laure kece a tafe??" Inna laure tace "nice yaya,dafatan na same ku lafiya "yace hmmm kedai bari Laure!! Ina fa maganar lafiya!! aini na zata ma jaje kika zo kiyi mana!!"
Nan take gaban inna laure ya fad'i tace"jaje kuma yaya? dan Allah ka faɗa min mai ya faru da ku!!". cikin rawar murya yace"wallahi laure 'yan bindiga ne suka kawo mana hari!! gaba ɗaya kiwon da nake dashi duk sun kore sun tafi da su,kuma kuma har da naki gaba ɗaya ,sannan harda shanun ki guda biyu suma duka sun tafi dasu,yanzu haka zancen da nake miki bakida ko kaza a garin nan".bai kai ga ƙarasa maganar ba yaga inna laure ta yanke jiki ta faɗi.................✍🏻
Ina matuƙar godiya da addu'ar ku a gare ni tare da fatan alkhairi 🙏🏻🙏🏻
Kuma ina alfahari da ku a koda yaushe 🥰🥰
Daga al'kalamin
FATIMA BINTU ABDULLAHI (UMMU AYSHA)................✍🏻
08162055134
💝💞HALIMATU 💝💞
(Love, sacrifices, destiny & betrayed)
💝💞💝💞💝💞💝💞
Story & Writing
By
FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)
Ƙarƙashi jagorancin
(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)
Golden pens..............✍🏻
💝💞💝💞💝💞💝💞
2024 novel
💝💞💝💞💝💞💝💞
page_____________17&18
HALIMATU
Washe gari bayan sun yi sallar asuba HALIMATU bata koma bacci ba, kayan da suka yi shopping ta ɗakko ta zazzage tana warewa, ɗaya bayan ɗaya ta dinga ɗaukar su tana jerawa a cikin wardrop, ya ɗan ɗauke ta lokaci kafin ta gama jere su a cikin wardrop ɗin.d'ago da kanta ta yi ta kalli cikin wardrop ɗin "ma sha Allah"ta furta a fili, sabo da abin yayi matuƙar birgeta sosai, Ita fa abin ba ƙaramin mamaki yake bata ba,ace duk wannan tulin kayan masu kyau da tsada nata ne, a gaskiya babu abinda zata ce sai godiyar ubangiji,domin Allah yayi mata ni'imar da bata taɓa zaton zata samu ba.
Ganin lokaci na tafiya ne yasa ta fito daga d'akin ta sakko ƙasa domin shiga kitchen,koda ta sakko ta iske uwani tana ta aikin ta na share share da goge goge, tsaya wa ta yi suka gaisa da uwani, sannan ta nufi hanyar kitchen ɗin.koda ta shiga ta iske momy da baba uwani suna ta faman aiki,momy gwana ce sosai wajen iya tsara abinci kala kala.
Gaishe su tayi tare da kama musu aikin suka ci-gaba da yi,momy ce ta haɗa papper soup na kan saniya, sannan ta haɗa haɗad'iyar miyar taushe wadda taji naman rago da ganda da stock fish. Ita kuma inna laure tana ta faman suyar masa da sinasir, ita kuma HALIMATU kunun gyad'a take ƙoƙarin damawa.
Cikin ƙan'kanin lokaci suka kammala komai, momy ta fita ta barsu suna gyara kitchen ɗin,suna gamawa suka jere komai a kan dining table.halimatu ta wuce sama zuwa d'akin auta domin ta shirya ta,bayan ta gama shirya ta tace taje ƙasa ta jirawo ta,ita kuma ta wuce da'kin taje tayi wanka, ta shirya cikin wata simple doguwar riga mara nauyi tare da rolling ɗin mayafin ta.
Koda ta sakko ƙasa ta taradda dukan su akan dining table suna break fast, ƙarasowa tayi ta tsuguna ta gaida dady da momy, dukkanin su suka amsa cike da fara'a, dady yace"come and join us my daughter" girgiza kai tayi alamar to tare da tashi ta jawo kujera kusa da yusra ta zauna.sai da ta fara gaishe da yayyin ta sannan ta jawo plate ta zuba masa da sinasir,miya ta zuba a gefe tare da ɗaukan bowl ta zuba pepper soup tayi bismillah ta fara ci.
Bayan sun gama ne hafiz ya kalli dady yace "dady akwai takaddu da files da ake so kasa hannu akan su"dady yace "okay tom shikenan son, anjima kaɗan zan shigo company ɗin,in yaso sai na dudduba abubuwan" hafiz yace "Okey tom shikenan daddy sai ka shigo ɗin".momy ta dubi sadiq tace"Kai kuma ya maganar jam ɗin HALIMATU" ya dube ta yace"momy nariga na kammala komai kawai lokaci muke jira" tace "tom shikenan Allah yayi muku albarka" ya amsa da ameen".
Mi'kewa suka yi suka yiwa momy da daddy sallama suka wuce office,suna fita shima farouq ya mi'ke domin kai auta school,daddy ne ya dubeshi yace "ina fatan dai kana ta shirye shirye ko??zan tura maka kuɗi ka siyi duk abin da kake so, saboda idan zan koma tare zamu wuce da kai"farouq yace"okay tom shikenan daddy zan ƙarasa shirye shiryen in sha Allah,Allah ubangiji ya kaimu lokacin" dady "yace ameen" daga haka ya kama hannun auta suka yi musu sallama suka fice daga gidan.
Bayan fitar su ne ya juyo ya kalli HALIMATU yace"daughter kema nan ba da daɗewa ba zaki zana jam,daga nan kuma sai University!! ina fatan dai daughter n tawa tana da ƙoƙari??" ya ƙarasa maganar yana duban ta fuskar sa ɗauke da murmushi,murmushin jin daɗi HALIMATU tayi tace"in sha Allah daddy zanyi ƙoƙari sosai", ya ce "yawwa my sweet daughter".daga haka ta mi'ke ta haye sama domin tana so ta ɗan kwanta kafin anjima.
Bayan HALIMATU ta tashi ne daddy ya kama hannun momy ya mi'kar da ita suka nufi kan kujera three seater suka zauna,daddy ya kirawo sunan momy tare da tsare ta da idanunsa,amsawa momy tayi tare da mai da hankalin ta gaba ɗaya kansa,domin tasan akwai maganar da yake so ya gaya mata.sake kiran sunan ta yayi a karo na biyu yace.
Maryam"ina so in faɗa miki wata muhimmiyar magana,amma kuma bansan yadda zaki ɗauki abun ba" ya faɗa tare da tsare ta da idanunsa.momy tace"haba my dear karka ji komai kawai ka gaya min kaji" numafashi daddy ya sauke tare da saka hannuwan sa guda biyu ya jawo ta jikinsa ya rungume ta sannan yace mata..........
"Dama akwai abokin nan nawa da muke tafiye-tafiye tare da shi wanda muka dawo tare,ina fatan dai kin gane shi??" ya faɗa yana duban fuskar ta, girgiza kanta tayi alamar ta gane shi.dady ya ci-gaba da cewa"to shine fa jiya a airport ya ga HALIMATU yace dan Allah yana so a bashi ita ya aurawa ɗansa hafiz" ai da sauri momy ta d'agowa ta kalleshi alamar tabbatar da abin da yake faɗa,nan taga babu alamun wasa a kan fuskarsa.
Ya ci-gaba da cewa "yace yana neman alfarma a gurin mu a taimaka a basu, Sabo da ya yaba da hankalin ta da tarbiyyar ta, shiyasa yake yiwa ɗan nasa sha'awar auren ta a matsayin matar sa ta sunnah,ko ya samu nutsuwa da kwanciyar hankalin da rasa a gurin matarsa.ya ƙarasa maganar yana kallon momy.shiru momy tayi bata ce komai ba,jin tayi shiru ne yasa ya ƙara kiran sunan ta yace"kinyi shiru Maryam baki ce min komai ba!!" ajiyar zuciya momy ta sauke ta d'agowa da kanta ta kalleshi tace
"Wallahi ni kaina ne ya ƙulle gaba ɗaya shiyasa ma kaji na kasa magana,yanzu duka duka HALIMATU guda nawa take da ake maganar aurenta,kuma gashi ma yaron yana da mata,gashi HALIMATU tana da sanyin hali bata da hayaniya kwata kwata, ni wallahi ina tsoron kada aje a cutar min da ita!!" ta sake kallon shi a karo na biyu ta ci-gaba da cewa "kaga yanzu ga maganar karatun ta, sannan kuma uwa uba shekarun ta sunyi ƙanƙanta, sannan shi yaron nan bafa shine da bakinsa yace yana sonta ba!!" ta ƙarasa maganar tare da yin shiru.
Ajiyar zuciya daddy ya ƙara saukewa, sannan ya ƙara duban ta yace mata"to yanzu maryam ya kike so na cewa bawan Allahn nan wallahi yana da mutunci da kima a idanuna,kinga ba daɗi ya nemi abu a gurina na hana masa muddin ina da iko akan abin!! Sannan nayi masa maganar karatun ta yace min babu damuwa ko shi hafiz ɗin zai iya samar mata gurbin karatu a b.u.k ɗin,tun da yana yin lecturing a can ɗin,kuma kinga yana da company mai zaman kansa wanda ake sarrafa fashions designer ɗin sar'ko'ki,ɗan kunnaye, zubuna,awarwaro da kuma gwala-gwalai,idan kuma maganar kishiya ne bari kema na ƙaro miki guda biyu kinga shikenan" ya ƙarasa maganar yana kallon ta yana dariya.
Nan take momy ta haɗe rai babu alamar annuri a fuskar ta,yace"a'a mai da wu'kar madam wallahi da wasa nake,wane ni!!" ya faɗa yana kama kunnuwan sa.fillow momy ta ɗauka ta jefa masa,ya cafe yana dariya tare da sa hannun sa ya jawo ta ya rungume ta ajikin sa, kiran sunan shi momy ta yi tare da cewa"na baka wu'ka da nama duk abinda ka zartar yayi, sabo da kai ɗin mahaifi ne agurin HALIMATU kana da ikon bada ita ga duk wanda kaji hankalin ka ya kwanta da shi".
Ta ci-gaba da cewa"sai dai ina neman alfarma a gurin ka!! ina so a ɗaga mata ƙafa ta ƙara ƙwari in yaso daga baya a yi maganar auren".daddy yace "maryam kenan banda abin ki lokacin da muka yi aure ai baki kai shekarun HALIMATU ba, shekarar ki sha huɗu a lokacin fa"ya faɗa fuskar sa ɗauke da murmushi yana sha fa gefen fuskar ta ,tace masa "haka ne,amma abin da nake so ka duba shine da da yanzu ba ɗaya bane ba, sannan ina so na koyawa wa HALIMATU abubuwa da dama,yanda zata iya kula da kanta da mijinta,girke girke kala-kala da kuma yadda zata zauna da abokiyar zaman ta".
Daddy yace"hakan ma shawara ce mai kyau,in sha Allahu zanyi masa bayani yadda zai fahim ta.daga haka ya kama hannun momy suka haye sama suka shige d'akin su.wannan kenan................
MUKHTAR
A ɓangaren mukhtar kuwa bashi ya tashi daga bacci ba sai ƙarfe huɗu na asuba,bayan yayi alwala direct ɗakin rufaida ya shiga ya tashe ta domin tayi nafila,yana tashin ta ya fito ya sauka ƙasa ya fita daga gidan zuwa masallaci,bashi ya dawo gidan ba sai da gari yayi haske sosai sannan ya dawo.