← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 80

Sashe 36

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Turo bakin ta ta yi kamar zata yi kuka tace
"Sabo da kai fa na yi amma yanzu ka ce min cikin ka zai fashe!!". har bread na yi maka da kaina yaya MUKHTAR dan Allah kaci!!

Hannun sa ya sa da sauri ya rufe bakin sa gudun kar ya yi abin kunya, sabo da wani irin lhun daɗi da yake neman kuɓce masa, wannan irin tarairaya da shagwaɓa haka!! Ai sai ya zarce wallahi! domin shi mutum ne mai son shagwaɓa da kulawa.

"Cool down my love, please kar ki yi min asarar Waɗan nan tsadaddun hawayen naki,domin hawayen ki sun fi DIAMOND da GOLD tsada a guri na, ki kwantar da hankalin ki sarauniya ta!! tea da bread ɗin kuma da su zan tafi gida in sha Allah"

Ƙayataccen murmushi ta sake tare da cewa
"Thank you yaya MUKHTAR!! I proud of you".
Wata irin kibiyar son HALIMATU ce ta ƙara sukar shi,rasa in da zai saka kansa ya yi sabo da daɗi,yasan nan ba da daɗewa ba zata furta masa kalmar so.

Dawo wa ya yi daga duniyar tunanin da ya lula tare da kallon HALIMATU yace
"My love na gama shirya miki komai na fara zuwa makaran ta,sannan kuma na zaɓar miki cos ɗin da zaki yi,ina so ki karanci ARTISTS AND DESIGN sabo da ki yi aiki a company na,nima yana ɗaya daga cikin abubuwan da na karanta".

Cike da murna tace
"To yaya MUKHTAR, duk yadda kace haka za'a yi"

"Yauwa my love,than you so much"

Ya faɗa cike da jin daɗi.

Duban ta ya ƙara yi a karo na biyu ya ci gaba da cewa

"Akwai hijabai da niƙab da na ɗinka miki,ina son idan zaki fita zuwa makaranta ki dinga saka su!"

Ya faɗa tare da tsare ta da idanunsa masu kaifi.
Muryar ta na rawa tace
"To yaya MUKHTAR in sha Allahu zan dinga saka su"

"Good my princess,haka nake so idan na umarce ki da yin abu ki dinga yi kin ji ko..?

Kanta ta girgiza alamar to.

"HALIMATU"
Ɗagowa ta yi ta dube shi jin ya am baci sunan ta,shima ɗin kallon ta ya yi tare da cewa
"Jibi zan yi tafiya zuwa London! Ina so ki yi min addu'a da fatan alkhairi,zanje a kan business ɗina ne,domin akwai kayan da nake so na shigo da su"

Rau rau ta yi da idanun ta kamar zata yi kuka tace
"Allah ubangiji ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya, Allah ya haɗa ka da dukannin Alkhairin da yake cikin wannan tafiyar da zaka yi, Allah ya kare ka da dukkanin sharrin da yake cikin tafiyar nan, Allah ubangiji ya sa ka yi farar tafiya, Allah yasa tafiyar ta zamo maka ci-gaba da kuma babbar nassara a gare ka,ina yi maka fatan alkhairi a duk in da kake!!"

Ta ƙaras maganar cikin raunatacciyar Muryar ta.

Wani irin abu ya ji ya daki zuciyar sa da ruhin sa, domin tun da yake bayan iyayen sa babu wanda ya taɓa yi masa addu'a makamanciyar irin wannan,gaskiya idan har ya auri HALIMATU ya yi dacen mata mai nutsuwa da hankali,uwa uba ga haƙuri.

Kallon ta ya yi tare da cewa

"Ameen Ameen my love, Allah ubangiji ya yi miki Albarka, ki ci-gaba da yi min addu'a a duk lokacin da kika yi sallah kin ji my love! My wife to be in sha Allah!!"

Ya ci gaba da cewa
"Kar ki yi kuka kinga zaki karya min zuciya, in sha Allahu ba zan wuce one month ba zan dawo,kuma kinga ga wayar MOMY zamu rinƙa gaisawa kafin in tawo miki da taki kinji....?"

Girgiza kai ta yi alamar to.

"Gud girl"

"Me zan tawo miki da shi...?"

Sun kuyar da kanta ta yi alamar Kunya, Murmushi ya yi tare da cewa
"Ko kin ba ni zaɓi ne??"

Cike da kunya tace "eh"

"Okey tom shikenan zan yi miki tsaraba mai kyau kinji...?" girgiza kai ta yi alamar to.

Miƙe wa ya yi tare da cewa
"Ni zan tafi my love,ki kula min da kanki! Sai mun yi waya ko??
"Allah ya tsare ya Kai ka gida lafiya"

Ta faɗa tare da juyawa ta yi kan dining ta ɗauki kyakkyawan flacks ɗin tea tare da ledar bread.

Gashin ta da yake reto ya ƙurawa ido kamar ya saka hannu ya taɓa.

Takowa ta yi tazo gaban sa ta tsaya tare da cewa
"Muje in raka ka mota"

Hannu sa ya sa ya karɓi flacks da ledar bread ɗin dake ruƙe a hannun ta,ya juya ya fita daga parlon ita kuma ta mara masa baya.

Lokacin da suka fito basu tadda kowa a parlon ba,hakan ya yi wa HALIMATU daɗi sosai, ficewa suka yi direct suka nufi parking space, seat ɗin baya na motar sa ya buɗe tare da saka kayan da yake hannun sa.

Boot ɗin motar sa ya buɗe tare da ɗakko manyan ledodi guda biyu ya miƙa mata tare da cewa

"Ga kayan naki"

Duƙusawa ta yi ta saka hannu ta karɓa tare da cewa

"An gode! Allah ubangiji ya saka da mafificin alkhairi ya ƙara buɗi"

Cike da jin daɗin addu'ar yace
"Ameen my lovely princess"

Sallama suka yi kamar kar su rabu,haka ya buɗe mota ya shiga ya tafi yana ɗaga mata hannu.

Ledodin ta ɗauka da ƙyar Sabo da suna da nauyi sosai tare da wucewa ta buɗe ƙofar parlon ta shige ciki.
Wannan kenan....

"ALHAJI USAMA"

A ɓangaren su ALHAJI USAMA kuwa, tafiya suke yi babu kama hannun yaro,sai da suka kwana suka wuni sannan suka shiga cikin garin ENUGU.

A tasha mota ta sauke su, taxi suka tare in da suka cewa mai taxi ɗin ya kai su hotel mai sauƙin kudi.

Haka kuwa a kayi,in da ya kaisu wani hotel na dai dai talaka, ɗaki guda suka kama in da suka yada zango domin huta gajiyar da suka kwaso.

Bayan sun huta ne ALHAJI Garba ya fita yaje ya siyo musu abincin da za su ci, amala ya sayo musu da miyar ganye,haka suka zauna suka ci suka ƙoshi abin su, suna gama wa suka rama sallolin da ake bin su.

Suna idarwa suka baje akan gadon tuni bacci ya ɗauke su sakamakon gajiyar da suka kwaso.

Washe gari bayan sun yi sallar asuba suka fito suka sayi abin karin kumallo suka karya. bayan sun karya ne suka fito titi in da suka suka tari wani mai taxi,kwatan ce in da za'a kai su ALHAJI Garba ya yi wa mai taxi ɗin in da ya buƙaci su bashi dubu biyar,domin hanyar ba wani kyau ne da ita ba.
Ba tare da musu ba suka amin ce kuwa, in da ya ɗauke su kama hanya suka tafi.

Sun yi tafiyar awa biyu sannan suka iso wani mugun daji.

Gaba ɗaya dajin duhu wa ce ta lulluɓe shi,duk in da ka duba bishiyoyi ne tare da manya manyan duwatsu masu ban al'ajabi da ban tsoro,ga wata iriyar guguwa da take tashi kamar ta ɗauke mutum ta gudu da shi.

A bakin dajin mai taxi ɗin ya sauke su domin ya ce ba zai shiga cikin dajin ba.

Badan sun so ba suka sauka tare da bashi haƙƙin sa,kama hanya suka yi tare da nausa wa cikin dajin.

Gaba ɗayan su a tsora ce suke, musamman ma ALHAJI USAMA da bai taɓa zuwa wajen ba.

Suna cikin tafiya kwatsam suka haɗu da ƙungiyar wasu irin halittu masu kama da mutane,rabin su mutane rabin su wasu irin halittu ne masu munin gaske.

ko da ALHAJI USAMA ya yi tozali da waɗannan halittu gaba ɗaya ya ruɗe jikin sa ya kama rawa kamar mazari, har ya buɗe baki da nufin kurma ihu da sauri ALHAJI Garba ya rufe masa baki,domin idan suka ji ihun sa to fa babu makawa sunan sa gawa.

Haka suka ci-gaba da tafiya suna haɗuwa da abubuwan al'ajabi kala kala har suka kawo wajen wata ƙatuwar bishiyar kuka mai ƙaton kogo.

Nan take wata irin guguwa ta kwashe su tare da yin hajujuwa da su sannan ɗauke su ta watsar da su a gefe kan su ya bugu da dutse,nan take suka sume gaba ɗayan su.

Ko da suka farka sun samu kan su a wani irin guri mara kyawun gani,gaba ɗaya ƙwaran gwal ɗin mutane ne a gurin,a gefe guda kuma ga tarin ƙo ƙunan kan mutane da yawa a wajen .

Wata iriyar dariya suka ji an kece da ita mai kama da kukan al'adu,a tsora ce suka ɗaga kan su domin ganin abin da yake dariyar.

Wani irin jibgegen mutum ne baƙiƙƙirin mai kama da samudawa,gaba ɗaya jikin shi layu ne da guraye,yana zaune a wata iriyar kujerar tsafi wadda ita ba'a sama ba ita ba'a ƙasa ba.

Kasancewar baya jin HAUSA sosai! Sabo da inyamuri ne ɗan ƙabilar Igbo shiya sa ya yi musu magana da gurɓatacciyar Hausar sa,in da yake sanar musu cewa yasan abin da yake tafe da su.

Sandar hannun sa ya yi nuni da ita akan wani jan ƙyalle,nan take wani irin madubin tsafi ya bayyana,sake ɗaga sandar sa ya yi a karo na biyu ya yi nuni da mudubin tsafin,nan take sai ga hoton MUKTAR ya bayyana a cikin mudubin tsafin.
Wasu irin ɗalasimai na tsafi ya ambata da ƙarfi tare da sake nuna madubin tsafin da sandar sa a karo na uku,nan take mudubin ya tarwatsa gaba ɗayan sa.

Zare ƙwala ƙwala idanun sa boka ya yi tare da juya wa ya kalli su ALHAJI USAMA ya fara magana cikin gurɓatacciyar Hausar sa
"Akwai wani abu da yake tattare da yarinyar nan da take tare da yaron nan,duk binciken da na yi ya kasa nuna min komai! Hatta hoton ta ma ya ƙi ya nuna min, wannan ya nuna min cewa yarinyar akwai babban al'amari a tattare da ita,kuma muddin yana tare da ita ba za'a taɓa yin galaba akan sa ba"

Ya cigaba da cewa
"Hanya ɗaya ce kawai nake gani zamu iya raba su shine, dole ne mukar katar da hankalin sa akan yarinyar! ta haka ne zamu iya raba su har a bada! Sannan zamu mallakewa ƴarka shi sai yadda kuka juya shi, dukkanin wani umarnin ku shi za bi,shi da iyayen sa sai dai kallo daga nesa!!".
Chapter 36 · 0% Book details