← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 80

Sashe 77

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Numfashi inna Laure ta sauke ta kalli hansai ta ce,
"Toh yanzu ina kuka koma da zama.? ina kuma Safara'un take.?"
Gyara zama hansai ta yi ta fara bawa inna Laure labarin abin da ya faru da su tun daga tafiyarsu zuwa yanzu! sannan ta ci gaba da cewa,
"Ko yanzu ma zuwan nan da kika ga na yi batun auren Safara'u ne ya kawo ni! domin masu neman auren ta sunzo sati biyu da suka wuce an tsayarda lokacin ɗaurin aure,yanzu jibi ne ɗaurin auren,kuma a nan za a yi komai sannan a ɗauki amarya a wuce da ita gidan mijinta.shiya sa ma na zo na sanar da ke dan kar ki ji a gari domin ba nida aminiyar da ta wuce ki, sannan kuma shawarar da zan baki shine ki rungumi ƙaddara ki yi haƙuri ki barwa Allah lamarin ki ki tuba,kuma ki nemi yafiyar yarinyar nan domin kin cutar da ita"

Tana gama magana ta miƙe tare da gyara lulluɓinta ta kalli ina laure ta ce,
"Ni na tafi Laure,zan je na ƙarasa shirye shirye sai kin zo"
Daga haka ta juya ta yi tafiyar ta,da kallo inna Laure ta bita cike da mamakin chanjawar da tayi lokaci ɗaya kamar ba hansai ba,ajiyar zuciya ta sauke, sannan ta miƙa tsaye ta ɗauki buta ta wuce banɗaki.....

∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆

"BUBA"

Ƙura ce take tashi sama sosai har mutum baya iya ganin gabansa sosai,babu abinda kake ji sai ƙarar harbin bindiga da ifface ifface da suka cika cikin dajin sakamakon hari da sojoji suka kai musu maɓoyarsu, tsakanin ƴan ta'addan da sojojin babu sauƙi,domin kuwa kowanne ɓangare sun dage suna so su yi nasara,kasancewar su ƴan ta'addan sunfi sojojin mugwayen makamai masu matuƙar haɗari shi ya sa suka yi musu ɓarna sosai.

Amma kuma daga bisani Allah ya basu Sa'a suka kashe fiye da rabin ƴan ta'addan,ciki kuwa har da shi kansa shugaban na su wato BUBA, sauran kuma suka samu rauni sosai.
Suma sojojin an yi musu ɓarna sosai,domin an kashe musu mutane su da yawa.duk da cewa dama sun fi ƴan ta'addan yawa.
Gaba ɗaya labari ya bazu a social media,shi ya sa duk inda ka zaga labarin ake.lokacin da Labarin mutuwar BUBA ya riski mutanen garin haɗeja ba ƙaramin farin ciki suka yi ba da mutuwarsa,har da masu yin sadaka,wasu kuma masar gero suka dinga soyawa suna yin sadaka da ita.domin a cewarsu rana ce ta farin ciki ba za su taɓa mantawa da ita ba,sun ce Allah ne ya amshi addu'ar su,domin kullum cikin addu'a suke Allah ya kawo musu ƙarshen su buba da ire-iren azzalumai irinsu.
Wannan kenan.......

A gurguje....

After 3 months

Zaune take a katafaren parlon ta wanda ya ji kayan more rayuwa,ta yi kyau sosai ta ƙara fari bau kamar ka taɓa ta jini ya fito,ta ƙara ƙiba ƙirjinta da ƙugunta sun cika dam dam jikinta sai shinning yake yi ma sha Allah.wayace manne a kunnenta tana magana da momy tana zuba mata shagwaɓa wai ta yi missing ɗin ta.daga ɗaya ɓangaren momy ta ce,
"Haba doughter ,duka duka fa yau kwanan ki biyu da zuwa shine har kika yi missing ɗina"
Cike da shagwaɓa halimatu ta ce,
"Wallahi momy ni bana gajiya da ke kullum cikin missing ɗin ki nake yi!"
"Toh na ji shikenan ki yi haƙuri bayan kwana biyu sai ki tambaye shi ya kawo ki kin ji ?"
"Toh momy na,ina aura.?"
"Ga ta nan ta ce a gaishe ki"
"Tom ina amsawa yaushe za a kawo min ita.?"
"Ba yanzu ba sai sun yi hutu in sha Allah"
"Okay tom shikenan momy bye"
"Bye my doughter take care,ki gaishe min da su sahal"
"Okay tom za su ji idan sun dawo daga school"
Daga haka suka yi sallama,miƙewa ta yi a hankali domin bata jin daɗin jikinta dauriya kawai take yi.ko school ma da ƙyar take zuwa a ƴan kwanakin nan,dan ma dawowarsu sahal da amal ya yi mata daɗi sosai,domin suna ɗebe mata kewa idan mukhtar baya nan,ga yaran akwai shiga rai.

Kitchen ta shiga ts ta ɗora musu dinner ta yi musu lafiyayyen abinci,tana gamawa su sahal suka shigo cikin parlon,da gudu suka zo suka rungumeta cike da murnar ganinta.ita ma rungume su tayi tare da shafa kan su,miƙewa ta yi ta kama hannunsu suka haye sama zuwa bedroom ɗinsu,wanka ta yi musu ta shafa musu lotion da turare.sannan ta saka musu kaya marasa nauyi gwanin ban sha'awa.

Kamo hannunsu ta yi suka sakko parlon ƙasa suka zauna ta kunna musu cartoon, sannan ta shiga kitchen ta ɗakko musu doughnut da lemo.ajiyewa ta yi a gabansu tare da cewa,
"Oya kuzo yarana ku ci kafin daddyn ku ya dawo mu yi dinner ko.?"
Cike da murna har suna haɗa baki gurin faɗin,
"Toh momy"
Kiss ta yi musu a goshi sannan ta haye sama domin ta je ta yi wanka.
Tana hawa babu daɗewa mukhtar ya dawo gidan ya shigo parlo ya iske yaran zaune gwanin ban sha'awa suna kallo suna ciye ciyensu sike da nishaɗi.wani irin daɗin ne ya ratsa shi sosai ganin lokaci ɗaya yaran sun yi ɓulɓul gwanin ban sha'awa hankalinsu ya kwanta sosai.

Sahal ne ya fara ankara da daddyn na su,da gudu yaje ya rungume shi yana murna, ita ma amal zuwa ta yi ta rungume shi cike da murna ta ce,
"Welcome our daddy"
Murmushi ya yi tare da manna musu kiss a kumatu ya ce,
"Ina momyn ku.?"
"Ta tafi ta yi wanka"
"Okay tom ku ji rawo ni bari nima naje na yi wankan ko"
"Okay daddy"
Daga haka ya miƙe ya hau sama, direct ɗakin halimatu ya nufa bakinsa ɗauke da sallama.tsaye ya same ta fitowarta kenan daga wanka tana goge jikinta,bai yi wata wata ba ya ɗauke ta chak ya wuce ɗakinsa da ita, toilet ya buɗe ya shiga da ita,bai dire ta a ko ina ba sai cikin bathtube ɗin da ta haɗa masa ruwan wanka.kukan shagwaɓa da taɓara ta sakar masa tana shure ƙafafu tana yun ƙurin fitowa.

Cikin sauri ya ruƙeta da hannunsa guda ɗaya sannan ya cire kayan jikinsa ya shige cikin bathtube ɗin,hannu ya sa ya rungumota jikinsa ya ɗora kanta a saman ƙirjinsa sannan ya ɗora bakinsa a saman kunnenta cikin raɗa kamar wani na jin su ya ce,
"Wai duk wannan shagwaɓar tamece ce ne haka my love,na ga kwana biyun nan rigima kike ji me yake damun ki ne.??"
Ya faɗa fuskarsa cike da damuwa.
Numfashi ta sauke a hankali ta ce,
"Ni ma ban sani ba habibi,kawai dai bana jin daɗin jikina ne"
"Oh! I'm Sorry my love"
Ya faɗa yana kai hannunsa saman ƙirjinta ya matsa, siririyar ƙara ta saki sabo da jikin nata ya yi tsami,da sauri ya ce mene ne kuma.?"
"Ummm ummm nan ne yake yi min ciwo!"
Ta faɗa tana nuna ƙirjinta.
Ƙura mata ido yayi yana kallon yanda ƙirjinta suka ƙara cika dam dam har wani sheƙi da ƙyalli suke, hannunsa ya ƙara kaiwa a karo na biyu ya ɗan ƙara dannawa,nan take saki wani irin numfashi tare da cewa,
"Ni bana so kabari ciwo jikina yake yi min"
Ba tare da ya ce komai ba ya ɗora hannunsa a saman mararta ya ɗan danna,nan take ta saki wata irin ƙara tana yarfe hannuwanta jiki ta yana rawa alamar zafi.ganin hakan da ya yi ne ya sa ya rungumeta yana shafa bayanta a hankali har ta samu natsuwa sannan suka yi wanka suka ɗauro alwala domin anfara kiran sallar magrib.

Jallabiya ya zura a jikinsa ita kuma ya ɗakko mata doguwar riga da hijab ta saka,hannunta ya riƙe suka sakko ƙasa.da gudu yaran suka zo suka rungume su,hannun sahal ya ruƙe suka wuce masallaci,ita kuma amal ta je ta yi alwala domin su yi sallah da halimatu.

Basu dawo gidan ba sai da suka yi sallar isha'i, direct dining table suka nufa domin su yi dinner,bayan sun zauna halimatu ta yi serving ɗin kowa sannan ta ɗan zuba fruit salad kaɗan a cikin ɗan bowl.ɗagowa Mukhtar ya yi cike da mamaki ya kalleta tare da cewa,
"Haba my love,ki fara cin abincin mana,da safe ma baki ci komai ba sai fruit salad fa!"
Ya faɗa yana tsare ta da idanunsa.
"Ba zan iya cin abincin ba habibi! Wannan ɗin ma dan dai ina ɗan jin yunwa ne shi ya sa kawai zan sha!!"
"Toh ki ƙara mana wannan ya yi kaɗan ba zai ishe ki ba"
"Wallahi habibi wannan ɗin ma da ƙyar zan iya shanye wa"
Ba dan ya so ba ya ƙyaketa.

Suna gama cin abincin ya ce su tashi su tafi gidan su momy,cike da murna yaran suka miƙe suna ta tsalle....✍🏻✍🏻

Dan Allah ku yi haƙuri da ni, wallahi busy nake sosai ban samu zama ba.

Sauran mu one page mu gama🙏🏻🙏🏻🥰🥰

Daga alƙalamin FATIMA BINTU(UMMU AYSHA)....✍🏻✍🏻

💝💞HALIMATU💝💞

(Love, sacrifices, destiny & betrayed)

💝💞💝💞💝💞💝💞

Story & Writing

By

FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)...✍🏻✍🏻

Ƙarƙashin jagorancin...

(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)

Golden pen.....✍🏻✍🏻

💝💞💝💞💝💞💝💞

A 2024 novel

💝💞💝💞💝💞💝💞

Pages______94&95

Note edited.

____________ Motarsu tana yin parking a parking space sahal ya yi sauri ya buɗe murfin motar ya fito yana faɗuwa saboda murna,cikin sauri halimatu ta fito ta riƙe shi tare da cewa,
"Yi a hankali my son kar kaje kaji ciwo"
Murmushi ya yi ya ce,
"Momy so nake na riga amal zuwa wajensu grandfather"
Murmushi ta yi tare da kamo hannun sahal sannan ta kamo hannun amal suka wuce,biyo bayansu Mukhtar ya yi hannunsa ruƙe da wasu plastic ɗin robobi guda biyu ma su ɗan girma.ɗaya cike take da dambun kaza,ya yin da ɗayar take cike da samosa.

Sallama suka yi tare da shiga cikin parlon gaba ɗayansu,da gudu sahal ya je ya rugume momy cike da murnar ganinta,yayin da ita ma amal ta je ta rungume daddy tana murna.murmushi halimatu ta yi tare da girgiza kan ta tana kallonsu cike da sha'awa da burgewa.ta kowa ta yi a hankali ta ƙaraso cikin parlon ta durƙusa har ƙasa ta gaishe da surukan na ta kanta a sunkuye,cike da fara'a suka amsa suna masu matuƙar jin daɗin ganin ɗan na su da matarsa da yaransu.
Chapter 77 · 0% Book details