← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 80

Sashe 76

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna gamawa ya taya ta suka kwashe kayan suka kai kitchen suka juyewa su baba maigadi ragowar a cikin abincinsu sannan suka wanke kwanikan,ɗakko na su mai gadi ya yi suka fito daga cikin kitchen ɗin, kallonta ya yi tare da cewa,
"My love bari na kai musu na su yanzu zan dawo kin ji ?"
"Jin jina kai ta yi tare da cewa,
"Tom sai ka dawo"
Daga haka ya juya ya fita ita kuma ta zauna saman sofa.
Jim kaɗan ya dawo ya zauna a kusa da ita tare da ɗora kanta a kan cinyarta yana wasa da jelar gashin ta fuskarsa ɗauke da murmushi,sunan ta ya ya kirawo a hankali,
"My love!"
"Ummm"
"Iove you! I love everything about you!!"
Tashi ta yi zaune tare da zama a kan cinyarsa ta saƙalo hannayen ta bayan wuyansa tare da haɗa face ɗin su guri guda tsinin hancinsu yana gugan na juna ta kalle shi ido cikin ido ta ce,
"I love you too my habibi,my dearline,my soulmate,my partner,my sweetheart,my everything!!"
Ta ƙarasa maganar tana haɗe bakinsu waje ɗaya.

Cikin sauri ya cafke bakinta tare da saka hannu ya rungumo ta jikinsa sosai ya fara sha yana sauke ajiyar zuciya kamar wani mayunwaci,sai da ya yi mai isar sa sannan ya saki bakinta yana sauke numfashi kamar wanda ya yi gudu,ɗago da haɓarta ya yi tare da tsare ta da idanunsa masu kaifi ya ce,
"Dan Allah my love kar ki guje ni komai runtsi ki kasance a tare da ni,wlh idan babu ke a kusa da ni ban san ya zan yi da rai na ba,dan Allah ki taimaka kar ki guje ni wata rana"
Ya faɗa hawaye na taruwa a cikin idanunsa.
"Subhanallahi!! me ya yi zafi haka habibi! Ka kwantar da hankalin ka,in sha Allahu babu abinda zai raba mu sai mutuwa,ita ma mutuwar ina fata idan ta zo ta ɗauke my gaba ɗaya!!"
"Kana tunanin idan babu kai zan iya rayuwa ne.?? ina sam! sabo da haka ka sakawa kan ka cewa ni da kai mutuka raba,kar ka manta kai ne komai nawa,uwata,ubana,yayana,ɗan uwa na,uwa uba kuma mijina uban ƴaƴana,kai ne komai nawa, I really love you my supper hero!!"

Hannu ya sa ya kai mata wata wawar runguma tare da sauke gawurtacciyar ajiyar zuciya yana sakar mata kisses a duk in da bakinsa ya sauka daga ƙarshe ya ɗauke ta chak ya haye sama da ita......

®®®®®®®®®®®®®®©©©©©©©©©©©©®®

" RUFAIDA"

A ɓangaren rufaida kuwa Alhamdulillah sauƙi ya samu ba kamar da ba,tun da yanzu tana magana kuma tana zama,tafiyar ce dai bata iya yi sai dai jan gindi.sakamakon ƙafarta guda ɗaya da hannunta guda ɗaya da suka shanye,kullum sai ta zubar da hawayenta, sakamakon halin da ta tsinci kanta,uwa uba kuma ga rabuwa da nagartaccen miji da ta yi.ta san ko giyar wake Mukhtar yake sha ba zai taɓa mayar da ita gidansa ba,bugu da ƙari duk kyan da take taƙama da shi da izza da ji ji da kai yanzu duk sun gudu sun barta,fatarta ta yamushe ta yanƙwane ta koma kamar wata tsohuwa babu kyan gani.

Balle kuma ga nakasar da ta sameta,ta tabbata da lokacin da take tare da mijinta ne rashin lafiyar nan ta same ta ba zai taɓa rabuwa da ita ba,domin shi ɗin mutum ne mai matuƙar kirki da tausayi.ya sota tsakani da Allah a lokacin da suke tare,amma bata saka masa da komai ba sai tsantsar sharri da mugunta da kuma cin zarafi,ta san cewa sarai ta zalunci mukhtar a zamantakewar auren su,hatta ƴaƴan da ta haifa a cikin cikinta bata bata ƙulla musu komai ba,bata kula da suba,bata jasu a cikin jikinta ba, tsakanin ta da su sai kyara da hanyar, wannan dalilin ne ya jawo babu soyayyarta a cikin zuciyar yaran nata ballantana kuma wata shaƙuwa.

Ko da aka kai mata su su yi sati biyu a gurin ta da ƙyar da siɗin goshi da rarrashi suka yi sati ɗaya ,da kukansu da komai a ka mai da su gurin kakaninsu wato iyayen mukhtar.

A hankali ta sauke a jiyar zuciya tare da share zazzafan hawayen da suka zubo mata a saman fuskarta,kallonta umma ta yi da take zaune tana ƙuƙƙulla kayan miya da su gawayi,dan yanzu sana'ar da take yi kenan,kuma Alhamdulillah ana samun ciniki sosai.tun zuwan da su muktar su ka yi duba abba yaga halin da suke ciki shine ya ɗauki ƙudurin taimaka musu,ya sakawa ran sa duk wata zai dinga aika musu da kayan abinci da kuɗin cefane da na kashewa albarkacin ƴaƴen da suka haifa da kuma zuciyar Muslunci,toh shine bayan sun koma gida ya aiko musu da kayan abinci da kuɗi.

Kallonta hajiya Hauwa ta yi tare da cewa,
"Yanzu RUFAIDA ba zaki dena yawan tunanin nan da kike yi ba! sai kin je wani ciwon ya ƙara kama ki.? dama ga shinan muna ta fama dan ma yanzu Alhmdllhi jikin da sauƙi! dan Allah ki rage yawan tunanin nan da kike yi kin ji.??"
Jin jina kai ta yi tare da jan gindi ta shige ɗaki,a hankali umma ta sauke a jiyar zuciya tare da ci gaba da ƙulla kayan miyan da take yi.

*************************

"Inna Laure"

Zaune take a tsakar gida a kan tabarma ta rafka uban tagumi ta faɗa Duniyar tunani,ta kasa cire tunanin malam ummaru a cikin zuciyar ta,duk lokacin da ta tuna cewa yanzu shi ɗin ba a matsayin mijinta yake ba mijin wata ne sai taji wani ƙaton ƙololo ya zo ya tokare mata zuciya.
Duk ƙibarta yanzu babu ita duk ta rame Sabo da tunani da ta sa a cikin ranta,duk da cewa ƴaƴanta suna iya bakin ƙoƙarin su wajen kwantar mata da hankali amma ta ƙi barin tunanin da take yi.

Ita damuwarta abu biyu ne,arziƙin da malam ummaru ya yi lokaci ɗaya,gashi kuma kullum arziƙin ƙara haɓaka yake,duk wata sai ya turowa yaranta kuɗaɗe masu tsoka domin su kula da kansu da ƴaƴansu.sannan kuma ga jari mai tsoka da ya ba su,zuwa yanzu Alhmdllhi babu abinda suka nema suka rasa.ta san a halin yanzu ko kallo bata ishi malam ba, domin ya wuce ajinta sosai,ga matarsa yarinya ƙarama sa'ar rajista,duk sanda ta tuna wannan abu hankalin ta na mutuƙar tashi.

Abu na biyu kuma shine HALIMATU,duk irin abin da tayiwa HALIMATU yau Allah ya ɗaga darajarta ya azurta ta da managarcin miji mai rufin asiri,musamman ma da labari ya sameta gurin su altine suke bata labarin mutuncin mijin da kuma rufin asirin da Allah ya yi masa nan take ta saki kukan baƙin ciki ƙiri ƙiri.gashi tana son ta ga halimatun amma baba ya yi mata iyaka da ita,a cewarsa duk ranar da ya ji labarin ta taka ƙafafunta a gidan HALIMATU toh hukuma ce za ta raba su, wannan dalilin ne ya sa ta kasa zuwa domin tana mutuƙar tsoron hukuma.

Tana tsaka da tunanin da take yi ne ta jiyo sallama, nan take ta dawo daga duniyar tunanin da ta shilla,tana ɗago kanta suka haɗa idanu da HANSAI!
Wani irin salati hansai ta rafka tana riƙe baki tare da cewa,
"Ke kuwa laure wacce irin duniyar tunani kika lula haka ina ta faman rafka sallama bakya jina!!"
Ta ƙarasa maganar ta ƙarewa inna Laure kallo sama da ƙasa.
Gwauron numfashi inna Laure ta ja ta dire sannan ta buɗe baki da ƙyar ta ce,
"Wa nake gani kamar hansai!!"
"Ba kama ba ce ni ce nan laure ehe!"
"Taɓ ɗi jam!wlh da a hanya muka haɗu da ke ba zan gane ki ba hansai! ashe dama zan sake ganin ki.? ina kika shiga kika ɓoye.??"
Ta ƙarasa maganar cike da mamaki!.

Wata iriyar dariyar rainin wayo hansai ta kece da ita daga bisani kuma ta kalli inna Laure ta ce mata,
"Wai tukunna ma in tambaye ki laure.? me ya same ki haka duk kika lalace kika rame kuma kika wulaƙanta haka.? ina fatan dai ba wata muguwar cuta kika kwaso ba.? domin na san ita ce take yi wa mutum karaf ɗaya lokaci guda"
Kuka inna Laure ta fashe da shi har da shashsheƙa ta ce,
"Ke dai bari hansai! ai idan da cutar ce ma da sauƙi tunda zaka nemawa kanka magani,amma abin da yake damuna ba shida magani! domin na riga na yiwa kai na na cuci kai na!!"
Dawowa kusa da ita hansai ta yi ta zauna tare da cewa,
"Haba Laure! ni fa kuka nace ki yi min ba,kawai tambayar ki na yi,dan Allah ki faɗa min abin da yake damun ki!".

Goge hawayen fuskarta ta yi tare da sauke ajiyar zuciya,sannan ta numfasa ta fara bawa hansai labari tun daga lokacin da suka rabu har zuwa yanzu.

Riƙe haɓa hansai ta yi cike da mamaki ta na kallon ina laure tana girgiza kai ta ce,
"Lallai laure kin ga jalalar rayuwa ko in ce kina kan gani! dama an ce duk abin da ka shuka shine zaka girba,gashi duk wani mugun abin da kika ƙulla ya dawo kanki,dama ni ko a lokacin ina zaman zamana ki ka zo kika jani muka je wajen boka! daga ƙarshe kuma abin ya ƙare a kan ƴata,ni dama tun da naga take taken mugun yaron nan na san zai iya yin komai a kan ƙudurinsa, wannan yaro wannan yaro ba ƙaramin tantirin hatsabibi bane,uwarsa ta haifa mana muguwar annoba ta mutu ta bar mu da bala'i da masifa!!".

"Ya addabi kowa a garin nan bama iya ƙauyen nan namu ba,yanzu zancen da nake yi Miki neman su ake ruwa a jallo!! domin ɓarnar da suke yi shida yaransa ta yi yawa,ni dama tun da naga take takensa na ɗauki Safara'u muka gudu daga garin gaba ɗaya muka koma wata na hiyar da ban da zama,domin na san idan ba guduwa na yi ba tsaf zai iya kashe ni har lahira ya kashe banza domin babu Allah a cikin ransa, wannan dalilin ne ya sa kuka neme mu rana tsaka kuka rasa!!"
Chapter 76 · 0% Book details