← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 80

Sashe 14

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Direct ɗakin rufaida ya nufa, wannan karan a zaune ya same ta tana ta faman daddanna wayar hannu ta, ɗagowa ta yi ta kalleshi tare da cewa "lafiya dai ko!!"yace mata "ita ta kawo haka,maza maza ki tashi kije ki shirya yaran nan lokaci yana ƙurewa,kuma ki tabbatar kinyi musu wanka,domin nasan halinki sarai zaki iya shirya su ba tare da kin yimusu wanka ba" ya ƙarasa maganar yana duban ta babu wasa a fuskar sa.

Har ya juya zai fita ya daka ta domin jin tana cewa"wallahi babu wani shirya su da zanyi,domin iyaye na basu aura maka ni don in dinga yi maka bauta ba,meye amfanin arzi'kin da Allah yayi maka,kana da kuɗin da zaka ajiye 'yan aiki fiye da guda ɗari a gidan nan.saboda haka niba wahalalliya bace eheee"

Cike da mamaki yake kallonta ,sai yanzu ya ƙara tabbatar da cewa gidan su rufaida babu tarbiyya kwata kwata.nan take yaji wani ƙololon baƙin ciki ya mamaye ilahirin zuciyar sa,cike da b'acin rai ya dube ta yace "wallahil azimu muddin na fito naga baki shirya yaran nan ba zaki ga matakin da zan ɗauka a kan ki".,wani kallon raini ta watsa masa tare da cewa"ka daɗe baka ɗauki mataki ba mukhtar, wallahi bazan shirya su ba sai dai kayi abin da zakayi"

MUKHTAR yace mata"tom shikenan zaki gani kuwa"daga haka yasa kai ya fice daga ɗakin ya nufi ɗakinsa, ba tare da b'ata lokaci ba ya faɗa toilet yayi wanka a gurguje ya shirya cikin suit white colour, ba ƙaramin kyau kayau kayan suka yi masa ba,tsadadden turaren sa mai matuƙar ƙamshi ya fesa tare da ɗaukan wayoyin sa ya fito daga ɗakin ya sakko ƙasa.

Koda ya sakko yaran ya gani zaune a falo,suna ganin sa suka taho da gudu suka rungume shi,cike da mamaki yake kallon su,wato duk irin gargad'in da yayi mata akan tayi musu wanka ta shirya su a banza, lallai rufaida ta gama rainashi,wato bai isa da ita ba kenan, lallai zai nuna mata shi ne yake auren ta ba itace take auren sa ba.

Ya ƙarasa zancen zucin nasa tare da janye su daga jikin sa.jacket ɗin suit ɗinsa ya cire tare da kama hannun su suka haye sama zuwa ɗakin su,cikin sauri sauri yayi musu wanka ya shirya su cikin uniform ɗinsu,ya kamasu suka sakko ƙasa zuwa dining table ya zaunar dasu,ba wani break fast ɗin kuzo mu gani bane aka shirya akan dining ɗin.fried yam and egg ne kawai sai ruwan zafi da aka zuba a plask,sai indomie da aka dafa musu.

Zuba musu indomie ɗin yayi sannan ya haɗa musu tea,shima tea ɗin ya haɗa sannan ya zuba doya a plate yayi bismillah ya fara ci, suna gama yin break fast ɗin motar su na zuwa, kitchen ya shiga ya ɗakko musu lunch box's ɗin su tare da kama hannun su suka fita ya raka su suka shiga bus ɗin school ɗin su.

Sai da yaga tafiyarsu sannan ya dawo cikin gidan,direct sama ya hau zuwa ɗakin rufaida,yana shiga ya iske ta zaune a bakin gado ta ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya hannun ta riƙe da waya tana charting, sunan ta ya kirawo amma tayi banza da shi,ya ƙara kiran sunan ta a karo na biyu yace"kina jina ina magana kika ƙyaleni ko rufaida!!".

Ba tare da ta ɗago ba tace masa"ai kunne ne yake ji!! ka faɗi maganar ka kawai ba sai na ɗagoba" yace "okay fine, dama abin da nake so na faɗa miki shine ki tattara duk wani abu da kika san nakine ki barmin gidana na sake ki saki ɗaya!!".

Cike da tashin hankali ta ɗago da sauri ta dubeshi har wayar hannun ta na fad'uwa ƙasa, domin bata taɓa tunanin zai iya sakin ta ba, sabo da tasan tana yi masa rashin kyautata wa kuma haka yake hak'uri ya ƙyaleta, amma shine yanzu zai ce ya sake ta.

Sake duban sa tayi a karo na biyu tace"na shiga!! mukhtar ni zaka saka?? saki fa,kodai mafarki nakeyi ne!!"mukhtar yace ba mafarki kike yi ba a zahiri ne,abin da kunnen ki ya jiye miki gaskiya ne, sabo da haka maza ki fice min daga gida zan kulle abina"yana gama faɗi ya juya ya fice daga ɗakin.

'Dakinsa ya shiga ya ɗakko briefcase ɗinsa ya fito,bai ga alamar ta fito ba, dan haka ya ƙara komawa ɗakin.wannan karan safa da marwa ya iske ta tana yi kamar wata taɓab'b'iya,ya dube ta yace"au dama kina nan baki tafi ba?? me kike jira ne wai!!" Cikin tashin hankali ta dubeshi tace "kayi hak'uri habibi,in sha Allahu bazan sake ba"

Cikin ɓacin rai ya jawo hannun ta tare da ɗakko mata hijabi ya wurga mata,ya kamata suka sauka ƙasa ya buɗe kofar parlon ya fito tare da ita,mukulli yasa ya kulle ƙofar ya bar rufaida a nan gurin tsaye,shikuma ya wuce parkin space ya buɗe mota ya shiga yaja ya bar gidan .

BUBA

A ɓangaren buba kuwa bayan wucewar su shida jama'ar sa bai zame ko ina ba sai gidan hansai,yana zuwa ko sallama babu ya faɗa cikin gidan, a tsakar gida ya taradda hansai ta gama dama kunun siyarwar da take yi kenan zata fara ƙullawa a cikin leda.tana ganin su tayi maza ta mi'ke tsaye jikin ta na rawa saura kaɗan ta faɗa cikin bahon kunun.

Wata irin dariya buba ya fashe da ita irin ta gogaggun 'yan duniya, ya kalli hansai yace mata"haba suruka ta meye haka!! daga gani na zaki wani mi'ke tsaye!! ko so kike kiyi mana asarar kunun da kika dama mana ne??".ya ƙarasa maganar yana kallon ta tare da ɗaga mata gira.

Wata irin dariya mara daɗin ji yaran sa suka fashe da ita,sai da suka yi mai isar su sannan buba yayi wani irin fito nan take gurin yayi tsit.d'ago da kansa yayi ya dubi hansai yace mata "ina amarya ta??" yafad'a yana tsare ta da jajayen idanunsa,hansai tace"na aike ta"wani irin mugun kallo buba ya watsawa hansai yace mata"bana son kina aiken ta ko ina ne sai da izini na!! Saboda haka ki kiyaye!! domin ina da kishi sosai"

Jikin hansai na rawa ta gyad'a masa kai alamar to,ya sake duban hansai a karo na biyu yace"dama abu biyu ne ya kawo ni,na farko shine duk inda laure take kije ki nemo min ita ,domin na san bakin ku daya!! na biyu kuma ina son a saka ranar bikin nan kusa kusa,saboda na gaji da tuzuran ci!!".

Ya ci-gaba da cewa"ina ƙara jadda da miki a karo na biyu duk inda laure ta shiga ki nemo min ita,idan ba haka ba duk abinda ya biyo baya kiyi kuka da kanki!!" ya ƙarasa maganar yana mi'kewa tsaye.juya wa yayi ya kalli yaran sa zuga guda ya kirawo banban yaron sa yace"duna ina son a ɗauki kunun nan gaba ɗaya mu tafi dashi!! Kaga yau kuɗin mu ya huta da siyan garau garau!!"

Fashewa suka yi da wata 'yar iskar dariya irin ta ƙauraye tare da cewa "sai oga sai oga sai oga"daga haka suka kinkimi bahon kunu suka fice a gidan.suna fita hansai ta dur'kushe a gurin ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi,ita yanzu me zata ce da mai geron da ta karb'o bashi gunsa!! duk wannan bala'in laure ce ta jaza mata shi tana zaman zaman ta,yanzu gashi ta gudu ta barta cikin masifa!! ai wallahi duk inda take sai taje ta nemo ta.

INNA LAURE

A ɓangaren inna laure kuwa lokacin da ta yanke jiki ta fad'i,nan take malam musa yayan ta ya rikice da gudu ya shiga cikin gida ya kirawo matar sa lamunde,suna zuwa lamunde ta duba ta tace masa "malam ai suma tayi!! yi sauri maza ka d'ebo mana ruwa a yayyafa mata"cikin sauri malam musa ya ɗebo ruwa lamunde ta karb'a ta yayyafa inna laure.

Nan take ta sauke ajiyar zuciya, ɗago da kanta tayi ta kalleshi,nan take ta tuno da abinda ya faru,fashewa da kuka tayi kamar wata ƙaramar yarinya tace"na shiga uku yanzu ya zanyi da buba!! shike nan tawa ta ƙare,dan wallahi muddin ban biya shi kuɗin saba bazai taɓa ƙyaleni ba"ta ƙarasa maganar tana shesheshe'ka.

Malam Musa yace "keda waye ne Laure?? Kiyi min bayanin yadda zan fahimta!!"nan take inna laure ta bawa malam musa labarin,amma ta b'oye masa zuwa wajen boka da suka yi.cike da tsananin tashin hankali malam musa ya dubeta yace "lallai laure kin ɗebo ruwan dafa kanki!! ki rasa kuɗin wanda zaki ci sai na wannan hatsabibin yaron!! to wallahi babu ruwana nima ta kaina nake, yaran da ake zargin yana cikin ƙungiyar masu garkuwa da mutane!! tab ɗi jam,to wallahi gwara ma yanzu yanzun nan ki tashi ki barmin cikin gidan nan,domin bazaki jazamin masifa ba,muddin ya san kina gidan nan wallahi nima ba tsira zanyi ba!! Sabo da haka maza maza ki tashi ki fice ki barmin gidana!!"...…............

Ina mutukar godiya a gareku masoya na abin alfahari na, kuɗin na daban ne,kuma ina godiya da addu'ar ku a gare ni,na gode, Allah ubangiji ya bar ƙauna..................

Daga al'kalamin FATIMA BINTU ABDALLAHI (UMMU AYSHA)...................✍🏻

08162055134.

💝💞HALIMATU💝💞

(Love, sacrifices, destiny & betrayed)

💝💞💝💞💝💞💝💞

Story & Writing

By

FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)

Ƙarƙashin jagorancin

(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)

Golden pens...............✍🏻

💝💞💝💞💝💞💞💝

2024 novel

💝💞💝💞💝💞💝💞

Page_____________19&20

HANNE

Tun lokacin da ta tattara kayan ta tabar gidan bata nufi ko ina ba sai gidan babbar yayar su altine,kasan cewar basu da wani nisa tsakanin su shiyasa batayi wata tafiya mai nisa ba ta iso gidan. tana zuwa tayi sallama ta shiga cikin gidan,basu lura da ita ba Sabo da hayaniyar da take tashi a cikin gidan, domin gidane na jama'a sosai ko ina ka duba mutane ne,kowa da abinda yake yi.

Wasu daga cikin su sussukar gero suke yi,wasu kuma surfe sukeyi,yayin da wasu suke ke ta faman kirb'a fura.gurin kirb'a fura ta nufa sakamakon hango altine da tayi cikin jerin masu kirb'awa.da sallama ta ƙaraso wajen tare da cewa "ga faran ku dai"wai gowa dukkanin su suka yi sakamakon jin muryar hanne.
Chapter 14 · 0% Book details