← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 80

Sashe 25

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Upstairs MOMY tahau tare da kiran HALIMATU,bin bayan MOMY tayi har bedroom ɗin ta,leda ta miƙa mata tare da cewa "wannan ki bawa MEENA,sannan idan kin sauka ƙasa ki shiga kitchen akwae snack da na shirya da dambun nama ki ɗauka ki kai masa" "to" tace tare da juyawa ta sakko ƙasa.

Daddy kawai ta samu har lokacin yana waya,direc kitchen ta nufa ta ɗakko wata kyakkyawar roba babba mai murfi da aka shirya snacks akayi sealing ɗinsa da foil paper, sannan ta ɗauki robar da aka zuba dambun nama a ciki ta fito daga cikin kitchen ɗin.wannan karan babu kowa a parlon,dirct waje ta fita zuwa parking space inda ta hango su tsai tsaya a bakin motar.yana ganin ta ya nufota a hankali tare da karɓan robobin hannunta suka nufi wajen motar,ita kuma MEENA tana can tsaye tare da Hafiz saboda lokacin da suka fito shima ya fito daga part ɗin su.

Seat ɗin baya ya buɗe tare da saka kayan a ciki,ledar hannun ta tamiƙa masa tare da cewa "wannan na MEENA ne" kallonta yayi tare da cewa "wannan kuma na cikin motar na waye??"ya faɗa yana tsare ta da idanunsa,a kunya ce tace masa "naka ne" murmushin jin daɗi yayi tare da cewa "lallai na zama ɗan gata" itama murmushin tayi.

MUKHTAR yace"HALEEMA bari mu tafi magariba tayi,akwai kuɗin suna nan akan kuje.......tun kafin ya ƙarasa maganar ta dakatar dashi ta hanyar cewa "a'a wallahi kabar kuɗinka mungode bari naje na ɗakko maka,ta faɗa tare da juyawa,hannun ta taji yayi saurin riƙewa,cikin sauri ta juyo ta kalleshi sakamakon wani irin shock da sukaji a tare.

Sakin hannun ta yayi tare da cewa "nifa bake na bawa ba na yusra ne kinji,idan kinje ki bata kice injini kinji" gyɗa kanta tayi badan taso ba"zantafi! Ki kulamin da kanki kinji" "to" tace masa, sallama sukayi tajuya tare da shigewa ciki.ganin haka ne yasa Hafiz ya rako MEENA tare da yin sallama da MUKHTAR suka shiga mota,horn yayi baba mai gadi ya wangale masa get ɗin shi kuma yaja motar tare da ficewa,baba mai gadi ne ya leƙo suka yi sallama, hannun sa ya saka a aljihu ya ɗakko kudin da bai san adadin suba ya miƙawa baba,jiki na rawa ya saka hannu ya karɓa yana mai addu'a da fatan alkhairi a gareshi, daga haka yaja motar suka tafi.

Wannan kenan..................✍🏻

Ina matuƙar godiya da addu'ar ku a gare ni tare da fatan alkhairin da kuke yimin a koda yaushe,wallahi kuɗin masoya ne na gari, Allah ubangiji ya saka muku da Alkhairin, Allah y haɗa mu a Aljannar firdausi gaba ɗayan mu.

Daga alƙalamin FATIMA BINTU ABDULLAHI (UMMU AYSHA).........✍🏻

Share fisabilillahi.

08162055134.

💝💞 HALIMATU💝💞

(Love, sacrifices, destiny & betrayed)

💝💞💝💞💝💞💝💞

Story & Writing

By

FATIMA BINTU ABDULLAHI (UMMU AYSHA)

Ƙarƙashin jagorancin

(MIKIYA WRITERS ASSOCIATION)

Golden pens..............✍🏻

💝💞💝💞💝💞💝💞

2024 novel

💝💞💝💞💝💞💝💞

Page_____________29&30

"HALIMATU"

A ɓangaren su HALIMATU kuwa,tana shigowa parlo direct upstairs ta nufa zuwa bedroom ɗinta,kayan jikinta ta cire ta shiga toilet tayi wanka tare da yin alwala sannan ta fito daga toilet ɗin. tsane jikinta da towel tayi tare da shafa lotion ɗinta sama sama, wata gown ta ɗakko pink colour mara nauyi ta saka tare da fesa turare kaɗan.dadduma ta shimfiɗa tare da ɗaukan hjijab ɗinta ta saka ta tada sallar magriba,bayan ta idar ta zauna yin addu'o'i da azkar har aka kirawo sallar isha'i.

Bayan ta idar da sallar ne ta cire hijab ɗin tare da naɗe sallayar ta ajiye su a saman bedside,kwanciya tayi akan bed ɗinta domin ta gaji sosai tana son ta huta,domin yau tunda ta tashi da asuba bata zauna ta huta ba.kwanciyar ta babu daɗewa MOMY ta shigo cikin bedroom ɗin nata hannun ta ɗauke da madai dai cin faranti sakamakon rashin ganin sakkowar HALIMATU gurin yin dinner, ƙaramin center table ta jawo tare da ɗorawa akai.

Zama MOMY ta yi akan bed ɗin tare da kiran sunan HALIMATU,amsawa tayi tare da tashi zaune ta dubi MOMY tace "MOMY kece kika shigo??" kai ta girgiza mata tare da cewa "Nice na shigo HALIMATU sabo da naga baki sakko yin dinner ba shine na kawo miki domin nasan kin gaji sosai" ta ƙara sa maganar fuskarta ɗauke da murmushi.

Murmushi HALIMATU tayi tare da rungume MOMY ta baya tace"thank you my everything" ta faɗa tare da ɗora kanta a kafadar MOMY, Murmushin ta ƙara yi a karo na biyu tare da cewa "alright dear ya baƙon naki? ina fatan yayi miki ko??" shiru tayi tare da ƙara boye fuskarta tana murmushi. "ga dukkan alamu dai baƙo ya samu karɓuwa a wajen ɗiyata,to Allah ubangiji ya tabbatar da alkhairin sa"

"Ameen"ta furta a cikin zuciyarta,kiran sunan ta tayi tare da cewa"tashi zaune ina so zamu yi magana!" ganin babu alamun wasa akan fuskar MOMY yasa ta tashi ta saita nutsuwar ta."ina son ki gayamin dame dame yace Miki??" shiru tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa, "karkiji kunyata ni mahaifiyarki ce kuma aminiyarki ce sannan kuma abokiyar shawararki ce kinji" ta faɗa tana duban ta.

"Gayamin ina sauraron ki,cikin ƙasa ƙasa da murya ta zayyane mata duk yadda suka yi da MUKHTAR.murmushi ne ya bayyana akan fuskar MOMY, hannun ta saka ta ɗago da fuskar HALIMATU tare da cewa "duk abinda ya faɗa gaskiya ne doughter,domin haka akeson macen ƙwarar ta kasance,kuma in sha Allahu zaki kasan ce masa a duk yadda yake so ɗin.

Miƙewa tsaye MOMY tayi tare da cewa "idan kin gama cin abincin akwai kaya da suka kawo miki suna ƙasa kije ki ɗakko su,sannan dana kwaso kayan abincin falon baƙi naga kuɗi a ajiye akan kujera na menene??" ta faɗa tana tsare ta da idanuwan ta. Wani irin yawu maiɗaci ta haɗiye cike da tsoro muryarta na rawa tace "wallahi MOMY bansan ya ajiyesu ba sai da na rakashi yake faɗamin kuma nace ya barshi bana so,shine yake gayamin wai kuɗin na yusra ne".

Murmushi MOMY tayi tare da cewa"ikon Allah!! to shikenan yusra ta gode, sannan banaso roƙo domin yana zubar da kimar mutum,duk dadai nasan halinki sarai bakida wannan halin, sabo da haka ki ƙara kula da kimarki da kuma mutuncin kanki" "in sha Allahu MOMY zanyi amfani da abin da kikace min" MOMY tace "yawwa my doughter Allah ubangiji yayi miki albarka ki tashi kici abinci karya huce"ta faɗa tare da ficewa daga ɗakin nata.

Bayan fitar MOMY ta sakko daga gadon ta zauna akan sofa tare da buɗe food wamer ɗin dake kan center table ɗin,biryani rice ce da gas meat a gefe,sai ƙaramar food warmar ɗin datake ɗauke da papper soup,ga kuma fruit salad dake ɗauke a cikin wani ƙaramin bowl.

Ba tare da ɓata lokaci ba ta ɗauki plate tayi serving tare da yin bismillah ta fara cin abincinta, sai da taji ta ƙoshi tayi nack sosai sannan tayi hamdala tare da yago tissue ta goge bakinta,gaskiya tana yabawa da abincin MOMY hundred percent,domin MOMY is the best cooker.

Miƙewa tayi tare da ɗaukan farantin ta fice daga bedroom ɗin zuwa down stairs,direct kitchen ta nufa ta zube sauran abincin da ya rage a cikin container ta saka a cikin freezer sannan ta wanke food wamers ɗin,kashe glove ɗin tayi tare da ficewa daga cikin kitchen ɗin zuwa parlon.manyan ledodi ta gani guda uku zube akan carpet, duƙawa tayi tarda ɗaukan guda biyu ta haye up stairs dasu,bata wani ɗauki lokaci ba ta dawo ta ɗauki sauran guda ɗayar sannan ta kashe glove ɗin parlorn ta wuce da ita upstairs itama, ajiye ta tayi a gurin da ta ajiye sauran, toilet ta nufa tare da yin brush da alwala sannan ta fito ta kashe glove ɗin ɗakin, bismillah tayi tare da hayewa lallausan bed ɗinta tayi addu'a ta kwanta,cikin ƙanƙanin lokaci bacci mai nauyi ya ɗauke ta.

"MUKHTAR"

A ɓangaren su MUKHTAR kuwa, lokacin da suka ƙarasa gida shida MEENA a bakin get yayi parking ɗin motarsa, buɗe motar suka yi tare da fitowa .back seat ɗin motar MEENA ta buɗe tare da ɗakko ƴan manyan robobin da aka basu tare da farar ledar da aka bawa MEENA,mai gadi ya kirawo tare da bashi umarnin shiga da kayan ciki,ba tare da ɓata lokaci ba ya kinkimi robobin tare da yin gaba dasu zuwa cikin parlorn.

Fitowa yayi tare da sanar musu da cewa yakai, hannu MUKHTAR ya saka a aljihu ya ɗakko kuɗi ya miƙa masa ,cike da farin ciki yasa hannu ya karɓe yana zabga godiya.idan da sabo ya saba duk lokacin da MUKHTAR yazo gidan sai ya bashi kuɗi,shiyasa kullum yake addu'a Allah ya kawo shi gidan domin yasan muddin yaxo tofa kakarsa ta yanke saƙa .

Farar ledar MUKHTAR ya miƙawa MEENA tare da cewa "wannan naki ne inji HALIMATU tace nabaki" cike da murna ta saka hannu ta karɓa tare da cewa"nagode sosai yaya, wallahi bakaji yanda naji daɗi ba, ina tayaka samun kyakkyawar yarinya nutsatsiya mai hankali,gaskiya yaya ta burgeni gata bata da rawar kai.ta ci-gaba da cewa "Ina tabbatar maka idan ka aureta kayi dacen mata wallahi"

Murmushi yayi kawai ba tare da yace mata komai ba,wucewa suka yi tare da yin sallama suka shiga cikin parlorn.da gudu sahal da amal suka taho tare da rungume mahaifinsu suna yimasa oyoyo,shima hannu yasa ya rungume su yana shafa kansu tare da sakarwa kowanne su kiss a goshi,sakinsa sukayi tare da rungume MEENA,itama rungume su tayi fuskarta ɗauke da murnar ganin su.

Daddy ne yayi gyaran murya tare da cewa "ƴan tafiya har an dawo??"murmushi MUKTAR yayi tare da sosa kansa,zuwa yayi ya duƙusa a gaban su daddy tare da cewa "ae daddy mundawo sunce suna gaisheku ku"wannan karan MOMY ce tayi magana tare da cewa "muna amsawa wallahi dafatan suma suna lafiya" MEENA ce tace"suma duk suna nan ƙalau MOMY,gaskiya mutanan nan akwaisu da kirki da karanci, baki ga yadda aka karrama muba,abinci kala kala da snacks da drinks,sannan da zamu tafi aunty HALIMATU tabani wannan!!" ta faɗa tana miƙewa tsaye tare da miƙawa MOMY ledar.
Chapter 25 · 0% Book details