← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 80

Sashe 70

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikkn sanyin murya yace,
"To shikenan nan na gode momma bari na kirawo ta"
Daga haka suka yi sallama ya kashe wayar gaba ɗaya.buɗe motar ya yi ya fito tare da zagayawa ya buɗe mata motar ya kamo hannunta ya riƙe,runtse idanun ta tayi da ƙarfi saboda zafin da take ji,dama daurewa kawai take yi.
"Ko baza ki iya tafiya ba in ɗauke ki ne my love"
Girgiza kai ta yi tare da cewa,
"A'a zan iya tafiya ba sai ka ɗauke ni ba"
Kama hannunta ya yi suka fara tafiya a hankali a hankali har zuwa office ɗin momynsa, nocking ya yi tare da yin sallama,daga ciki ya ji muryar momy tace,
"Come in"
A hankali ya murɗa kofar office ɗin ya shiga yana ruƙe da hannun HALIMATU.guri suka samu suka zauna yayin da momy take bin su da kallon mamaki.ta shi halimatu ta yi ta durƙusa ƙasa da ƙyar ta gaida momy.
Tashi momy ta yi daga mazaunin ta tazo ta kama hannun halimatu ta miƙar da ita tare da bin ta da kallon nazari tana mamaki,zaunar da ita ta yi akan kujerar da take ganin patient ta mai da kallon ta kan mukhtar da ya sunkuyar da kansa tace,
"Me yake damun ta son!!"
Cikin inda-inda yace,
"Zazz... Zazzaɓi ne yake damun ta momy"

Juyo da kallon ta yi ta dubi halimatu da ta rufe fuskarta ruf jikinta yana ɗan rawa saboda wata iriyar kunya,shin yanzu momy ma tasan abin da suka yi kenan! wannan abin kunya ina zata kai shi!!
A hankali ta fashe da kuka,ganin haka ya sa momy ta ta shi tsaye tare da buɗe wata drawer ta ɗakko wata allura da sirin ji ta ja ruwan allurar sannan ta jiyo inda HALIMATU take zaune ta kamo hannunta ta miƙar da ita tsaye tare da tace,

"Doughter taho ki kwanta a nan kin ji.?"
Ta faɗa tana ƙaraso da ita bakin gadon.
A hankali HALIMATU ta ɗaga ƙafarta da ƙyar ta hau gadon ta kwanta ta juya musu baya.ganin ta haune ya sa momy ta matso sosai ta ɗaga rigar ta sama tayi mata allurar a hankali,wata iriyar siririyar ƙara ta saki tana sauke ajiyar zuciya.
Shafa bayan ta momy ta yi tana rarrashin ta har ta yi shiru tana sauke ajiyar zuciya akai-akai.komawa momy ta yi ta ci gaba da rubuce-rubecen ta ta yi banza da mukhtar da yake zaune kamar ruwa ya cinye shi.ko minti biyar ba a yi ba bacci mai nauyi ya ɗauke halimatu,dama allurar bacci momy ta yi mata,idan ba hakan ta yi ba HALIMATU ba zata bari ta duba ta ba.

Ta shi momy ta yi ta zo bakin gadon da halimatu take kwance ta janye rigar ta zuwa sama tare da cire pant ɗin jikin ta,wata ƙatuwar fitila mai haske sosai ta kunna da take maƙale a gefen gadon daga sama.buɗe ƙafafuwan ta tayi a hankali ta duba gurin sosai,cike da ɓacin rai ta juyo ta kalli mukhtar suka haɗa idanu ya yi sauri ya saukar da kansa ƙasa.
"Wannan wanne irin abu ne haka ka yi!! yarinyar nan kasan ƙarama ce amma ka kasa bi da ita a hankali!! yanzu gashi nan ai kaji mata ciwo hankalin ka ya kwanta ka ji daɗi ko.??"

Ta ƙarasa maganar ranta a matuƙar ɓace.
Tasowa ya yi ya durƙusa a gaban ta tare da cewa,
"Dan Allah momy ki yi haƙuri!"
"Ai dama dole ne ka bada haƙuri Tun da ka aikata abin da ranka yake so"
Ta faɗa tare da komawa gurin zamanta ta zauna.paper ta yago ta yi rubutu a jiki sannan ta miƙa masa tare da cewa,
"Idan kaga dama kaje ka shiga permacy ka biya kuɗi ka karɓo waɗannan magungunan"
A hankali ya miƙa hannu ya karɓa tare da fita daga cikin office ɗin.
Bai wani daɗe ba ya dawo da leda a hannunsa ya miƙa wa momy,karɓa ta yi tare da tashi ta zo gurin gadon ta tsaya tana haɗa allurai da abun da zata buƙata.
Safar hannu ta sa tare da kunna fitilar nan mai haske tafara yi mata stitches a wajen cikin ƙwarewa .tana gamawa ta saka mata drip ta zuba allurori a ciki sannan ta cire hand glove ɗin ta takarkata kayan da ta yi amfani da su tajefa a cikin dosbin.
Kallon mukhtar ta yi tare da cewa,
"Ka kula da ita sosai ni zan shiga thieater ana jirana,zan turo nurse ɗin da zata dinga zuwa tana duba ta time to time,zan sa a kawo muku take a way idan drip ɗin ya ƙare a bata abinci ta ci da magungunan ta,ta faɗa tana ficewa daga cikin ɗakin....✍🏻✍🏻

Ina matuƙar godiya da addu'o'in ku a gare ni tare da fatan Alkhairi,ku ɗin na musamman ne a cikin zuciya ta, ina matuƙar alfahari da ku ƙwarai da gaske.Allah ubangiji ya saka muku da mafificin Alkhairin sa,ya biya muku buƙatun ku na Alkhairi🙏🏻🙏🏻

Daga alƙalamin
FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)...✍🏻✍🏻

Share fisabilillahi🙏🏻

Ga me buƙatar littafin HALIMATU tun daga farko zuwa in da aka tsaya ya tun tuɓe ni ta wannan numbern wayar
👇🏻👇🏻

08162055134.

💝💞 HALIMATU 💝💞

(Love, sacrifices, destiny & betrayed)

💝💞💝💞💝💞💝💞

Story & Writing

By

FATIMA BINTU ABDALLAHI(UMMU AYSHA)....✍🏻✍🏻

Ƙarƙashin jagorancin

(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)

Golden pens.....✍🏻✍🏻

💝💞💝💞💝💞💝💞

A 2024 novel

💝💞💝💞💝💞💝💞

Pages__________90&91

Note edited

_________Ƙarfe huɗu su momy suka fito daga cikin theater room ɗin, direct office ɗin ta ta nufa bakin ta ɗauke da sallama, daga ciki mukhtar ya amsa sallamar ta ta,kujera ta jawo ta zauna a gaban gadon da halimatu take zaune a kai.
A hankali halimatu ta sunkuyar da kanta ƙasa tace,
"Momy sannu da dawowa ya aiki.?"
Cike da fara'a momy tace,
Alhamdulillahi doughter na ya jikin baki.? i hope dai jikin da sauƙi sosai ko.??"
"Eh da sauƙi"
"Ina ne yake miki ciwo yanzu.??"
Sunkuyar da kanta ƙasa tayi tare da yin shiru kamar bazata yi magana ba,sai kuma can ta ce,
"Jiki na ne yake yi min ciwo, sannan kuma ina jin baki na yana yi min ɗaci"
"Kin ci abinci kin sha maganin.??"
"Nayi nayi da ita ta ci abincin amma taƙi,da ƙyar na samu tasha ruwan tea sannan aka bata magani"
Mukhtar ya faɗa.
"Jikin ne bata jin daɗin sa ne shi yasa,amma in sha Allahu tun da ta sha magungunan zata ji daɗin jikin nata"
Ta ƙarasa maganar tana miƙewa tsaye,kallon mukhtar ta yi tare da cewa,
"Ka haɗa mata magungunan waje ɗaya zamu wuce gida yanzu"
"To momy"
Daga haka ya miƙe ya tattara magungunan nata a guri ɗaya,hijab ɗin ta ya ɗakko zai saka mata ta yi sauri taja baya tana tura masa ɗan ƙaramin bakin ta cike da shagwaɓa tace,
"Ni bana so ka ƙyale ni zan sa abu na da kai na!"
Murmushi ya yi ya faki idan momy ya rungumo ta jikinsa tare da ziraro da harshen sa ya lashi lips ɗin ta na ƙasa.
Wata iriyar siririyar ƙara ta saki tare da ture shi ta fito daga cikin jikinsa.jiyowa momy ta yi da sauri ta ce,
"Subhanallahi! me ya faru doughter ko jikin ne.??"
Girgiza kanta ta yi da sauri tare da cewa,
"Na zo sakkowa daga kan gadon ne ƙafata ta gurɗe"
Kallon mukhtar ta yi wanda ya sunkuyar da kansa ƙasa kamar ruwa ya cinye shi alamar ba shida gaskiya, girgiza kai ta yi tare da cewa,
Ayya sorry doughter kin ji!! bari son ya kama ki sai ki sakko a hankali"
Ta ƙarasa maganar tana kallon mukhtar ɗin.
A hankali ya kamata ya sakko da ita daga kan gadon,hijabin ta da takalmin ta ta ɗauka ta saka ta fara tafiya a hankali ta ƙarasa gaban kan teble ɗin da momy take rubuce rubuce ta ɗauki jakar momy ta ruƙe a hannun ta,ɗagowa momy ta yi ta kalle ta tare da cewa,
"A'a doughter miƙomin jakar na riƙe! ke da baki da lafiya ya za'a yi ki ɗauki jaka ki riƙe"
Murmushi halimatu ta yi tare da cewa,
"Momy naji sauƙi zan iya riƙewa dan Allah ki barshi na riƙe Miki!"
Ta faɗa tana marai rai cewa.

"Allah ya yi miki Albarka doughter ya baku zaman lafiya kin ji!"
Sun kuyar da kanta ƙasa ta yi tana murmushi ba tare da tace komai ba.
Ƙarasowa momy ta yi kusa da ita ta kama hannun ta ta riƙe suka fita daga cikin office ɗin,ya yin da mukhtar ya ɗauki ledar maganin ya biyo bayan su tare da rufe office ɗin ya saka masa key.

Biyo bayan su yayi yana kallon yanda halimatu take tafiya a hankali, kana gani kasan dauriya kawai take yi,nan take yaji wani irin tausayin ta da ƙaunarta sun ƙara shiga cikin ruhinsa sosai.
A bakin motar momy suka tsaya, ƙarasowa ya yi da sauri ya buɗe musu motar ya taimaka wa halimatu ta shiga,ita kuma momy ta juya ta shiga ɗaya gefen na mazaunin driver ta zauna tare da yiwa motar key.
Sauke glass ɗin motar momy ta yi tare da cewa,
"Ka same mu a gida"
Daga haka taja motar ta yi reverse ta juya ta tafi.
Tsaye ya yi a gurin kamar wanda aka dasa yana makin momy! toh me momy take nufi da ta ɗauke masa mata ta tafi da ita! shifa wallahi ya ɗauka zata bashi matarsa ne su tafi gidansu, amma yanzu a gaban idanusa ta ɗauke masa mata ta tafi da ita! ai kuwa dole ya bi bayan momy ya karɓo matarsa.
Ya ƙarasa tunanin da yake yi tare da juyawa ya buɗe motar sa ya shige yaja tare da barin gurin.
Chapter 70 · 0% Book details