Sashe 79
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zaune take a kan sofa ta miƙawa momy ƙafarta tana daddana mata sakamakon kumburi da suka yi, ita kanta halimatun duk ta kumbura,ga wani irin girma da cikinta ya yi gwanin ban tausayi.wannan dalilin ne ya sa momy ta roƙi alfarma a dawo mata da ita kusa da ita ko hankalinta ya fi kwanciya tunda cikin nata ya shiga watan haihuwar ta.da ƙyar mukhtar ya yadda sai da daddynsa ya saka baki sannan ya yadda,amma shiru har yanzu bata haihuba watan har ya ƙare na goma ya shiga,ba ƙaramin tausayi take bawa momy ba.
Nishin da ta ji halimatu ta yi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da take yi,
"Me ya faru ne doughter.??"
"Marata ce ta ƙulle momy! fitsari nake ji!!"
Cikin sauri momy ta kamata a hankali ta miƙar da ita tsaye,domin idan ta zauna da ƙyar take iya tashi saboda nauyin cikin.
Kamata ta yi ta raka ta har banɗaki ta zaunar da ita a kan masai,domin ba zata iya tsugunawa ba.da
Da ƙyar da nishi ta samu fitsarin ya zubo kaɗan,jim kaɗan sai kuma ga jini ya biyo baya.
Cikin tashin hankali momy ta kamata ta ruƙe domin ta fara gala baits,a hankali ta miƙar da ita tsaye ta riƙe ta suka fito daga cikin toilet ɗin tana kwaɗawa baba ladi kira,da gudu baba ladi ta taho tana cewa,
"Hajiya ga ni"
"Dan Allah ki yi sauri ki ce a fito da mota yanzun nan zamu kai yarinyar nan asibiti"
Jikin baba ladi na rawa ta ruga a guje ko mayafi bata tsaya ɗauka ba.
Cikin sauri momy ta zaunar da ita a kan sofa sannan ta haye sama da gudu,hijab ta ɗakko musu sannan ta ɗakko wayarta,tana zuwa ta tarar da baba ladi ta dawo tana tsaye tana gyara zaman mayafinta.
"Hijab momy ta saka mata sannan suka kamata suka fito da ita, direct mota suka nufa aka buɗe musu suka shiga.kiran momyn Mukhtar ta yi ta sanar mata da abinda yake faruwa,daga ɗaya ɓangaren ta ce su same ta a asibitin Aminu Kano domin tana duty a lokacin.tun kafin su ƙaraso har ta tanadi lokitocin da zasu haɗu su dubata,suna zuwa babu ɓata lokaci aka shiga wani special ɗaki da ita.
Ba tare da ɓata lokaci ba suka fara duba ta cike da taka tsantsan, abinda ya ɗaga musu hankali shine bleeding ɗin da take ta yi ga shi kuma kan babyn yana sama!ga kuma labour da take yi sosai!
Ganin duk wata dabara sun yi mata amma abin ya ci tura ga shi kuma ƙarfinta ya fara ƙarewa ya sa suka yanke shawarar yi mata c,s nan da 30 minutes.
Fitowa momy ta yi daga ɗakin duk jikinta ya yi sanyi ta sanar da momy abin da yake faruwa,nan take hankalin momy ya tashi! Kwantar mata da hankali ta yi tare da cewa,
"Ki kirawo Alhaji ki gaya masa abin da yake faruwa,nima yanzu zan kurawo mukhtar da daddnsa na faɗa musu"
Girgiza kai kawai ta yi domin ta kasa magana,bugawa daddy ta yi ta gayamasa shi kuma ya kirawo baban halimatu ya sanar da shi abin da yake faruwa sannan ya ajiye wayar.
Kafin wani lokaci duk sun hallara a cikin asibitin kowa ka kalla hankalinsa tashe musamman momy da mukhtar,takarda momy ta bawa mukhtar ya saka hannu akai sannan ta ce su taya su da addu'a yanzu za su shiga da ita! addu'a aka dinga kwarara mata tare da fatan Allah ya sa ayi cikin nasara ya fito da ita lafiya.
Shigewa ɗakin mukhtar ya yi ya tarar da wata nurse zata saka mata blue ɗin uniform na theater,da sauri ya karki kayan ya saka mata yana mai kwantar mata da hankali duk kuwa da cewar shima na shi hankalin a mutuƙar tashe yake, amma hakan ya ɓoye nasa yanayin da yake ciki.
Shigowa momy ta yi ta ce masa,
"Lokaci ya yi,ka fito za'a turo gadon a shiga da ita!"
"A'a momy ni zan turo ta da kaina"
Ya faɗa yana tura gadon nata waje.
Gaba momy ta yi ya bita a baya,suna fitowa kowa ya nufo inda suke yana yi mata addu'a da fatan alkhairi.har cikin ɗakin mukhtar ya shiga da ita inda ya tarar an gama shirya komai, momy ce da kanta ta yi mata allurar anthesia spinal cord tare da taimakon dr sagir da doctor Aisha.
Bayan batare da ɓata lokaci ba aka fara yi mata c,s ɗin, da ƙyar aka samu mukhtar ya fita.cikin 30 minutes aka ciro mata yaranta maza guda biyu kyawawa masu kama da mukhtar sak,hasken fatar ta kawai suka ɗebo da abinda ba za'a rasa ba,sai da aka gama shirya ta tsaf ita yaran nata sannan aka momy ta turo gadon ta fito da ita,yaran kuma doctor Aisha da doctor sagir suka fito ɗauke da su a hannunsu.
Habawa zo kaga murna da farin ciki a wajen wannan alhali ,domin kowa ya yi mamakin yara biyun da ta haifa, ko scaining bai nuna hakan ba, Allah ne ya ɓoye abinsa.da gudu mukhtar ya nufi gadon da momy ta turo halimatu ya ruƙe ya cigaba da turata har zuwa wani private room mai kyau,da kansa ya kwantar da ita a kan gadon ɗakin ya gyara mata kwaciya sannan ya zauna a kan gadon dai dai kusa da kanta ya ɗora hannusa guda a kanta ɗaya hannun nasa kuma ya kamo hannunta ya ruƙe gam yana tofa mata addu'a.
A haka sauran mutane suka shigo suka same su a ɗakin suna yi mata sannu,kanta kawai take ɗaga musu alamar amsawa.sai da mukhtar yaga jikin nata da sauƙi sosai har ta samu bacci sannan ya mai da hankalinsa gurin yaran ya karɓesu a wajen su mukhtar da sama'ila mijin hanne.ƙura musu idanu ya yi ƙwallar farin ciki na taruwa a cikin idanunsa.
A hankali ya bisu ɗaya bayan ɗaya yana sumbatarsu tare da shafa kansu.haƙiƙa yau rana ce ta biyu wadda ba zai taɓa mantawa da ita ba,wai yau shine Allah ya albarkace shi da yara maza guda biyu lokaci guda tare da matar da take mafi soyuwa a cikin zuciyarsa, wannan abin farin cikin har ina!.
Kunnesa ya kai dai dai saitin bakin Hassan ɗin ya yi masa kiran sallah tare da huɗuba ya raɗa masa sunan daddynsa,sannan yayiwa Hussaini huɗuba da sunan dadynsu hafiz.hannunsa ya sa a cikin aljihun rigarsa ya ɗakko dabino ya saka a cikin bakinsa ya tauna sannan ya buɗe cikin bakinsu ya lakata musu,cikin ƙanƙanin lokaci suka mamule abinsu.
Murmushi ya yi ya kuma taunawa ya basu, wannan karon ma shanyewa suka yi,sai da ya basu har sau uku sannan ya basu ruwan zamzam,murmushi malam ummaru ya yi tare da cewa,
"Alhaji Ibrahim waɗannan jikokin naku kwaɗayayyune gaskiya"
Kowa da yake zaune a gurin sai da ya yi dariya.
"Da gaskiyarsu,ai gwara su cika cikinsu su ƙoshi sosai kasan mu bama wasa da cikin mu"
Wannan karon ma dariya aka yi.
Sai kusan magriba halimatu ta tashi daga bacci,momyn Mukhtar ce da kanta ta ɗagata ta kaita toilet ta gasa mata jikinta da towel sannan ta kamata suka fito ta zaunar da ita a kan kujerar, tea momynta ta haɗa mata mai kauri ta miƙa mata.a hankali ta saka hannu ta karɓa ta yi bismillah tara kurɓa a hankali har ta shanye.
Magani momy ta bata tasha sannan ta miƙo mata abul hassan ta ce,
"Ungo bashi nono ya sha tun ɗazu ya dame mu da rigima wai shi yunwa yake ji"
Marairaice fuskarta ta yi tare da cewa,
"Momy a bari sai na warke sannan!!"
Cike da mamaki momy ta kalleta ta ce,
"To yaran kuma me za su sha idan baki basu ba.??"
"Abasu madara mana su sha"
To wannan sakalcin ba dani za'a yi shi ba"
Ta faɗa tare da ɗorawa halimatu yaran a kan cinyarta,hannu ta sa tq ta ɗaga rigarta ta fito da nonon ta sakawa yaran a baki.cikin sauri ya yi maza ya cafke ya fara sha,da sauri ta runtse idanunta saboda wani irin zafi da taji, amma haka ta daure saboda babu yadda zata momy ta kafa ta tsare.yana gama sha aka miƙo mata abul hussain shima ta bashi ya sha ya ƙoshi sannan momy ta ƙyaketa,cikin ƙanƙanin lokaci bacci ya ɗauke yaran.
Kwanansu huɗu aka sallame su a asibitin ganin jikin nata da sauƙi, wannan karon ma momy ce ta roƙi alfarma a bata ita.da ƙyar mukhtar ya yadda,haka aka cigaba da kula da ita sosai.ranar suna faɗan irin shagalin da aka yi da dukiyar da aka kashe ɓata baki ne,domin kuwa naira ta yi kuka sosai, yara sunzo da farin jininsu sun samu kyaututtuka na bam mamaki.
Me jego ta fito tayi ras da ita kamar ka sace ta ka gudu,ta ƙara cika ta yi ɓulɓul taƙara fari sosai gwanin ban sha'awa,duk kayan da tasa sai mukhtar ya saka colour ɗin su,duk inda tayi yana tare da ita har nura abokinsa yana yi masa tsiya.haka taro ya tashi aka raba kyaututtuka na alfarma
Haka halimatu ta cigaba da jegonta tana samun kulawa sosai ita da yaranta.
BAYAN KWANA ARBA'IN
Da ƙyar mukhtar ya bar halimatu ta yi ziyara har zuwa ƙauyen haɗeja, a gidansu ta sauka gurin inna Laure,ai kuwa ta sha gata da tarairaya gurin inna Lauren,abin ma har ya dinga bawa halimatu mamakin chanjawarta,ga kuma wani irin tausayi da take bata.bata gajiya da hidimar su abul hassan.hakan ne ya sa halimatu ta tambayi baba akan ya bari su tafi da inna Laure ta cigaba da taimaka mata wajen kula da su abul hussain ɗin.
Da ƙyar baba ya amince tare da yi mata babban gargaɗi, wannan shine dalilin tahowarta tare da halimatun kuma tana zaune da su lafiya ƙalau da zuciya ɗaya.yaran halimatu sun yi ɓulɓul sun yi ƙiba abinsu sun yi kyau sosai kamar ka ƙwace su,ta ko ina samun suke yi,gasu da farin jini da shiga rai,idan kuwa su sahal da amal suna gida kowa zuwa yake a bashi guda ya ruƙe,a cewarsu wai suma raino suke yi.