Sashe 41
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dama tun suna ƙana na mahaifin su ya rasu, ga shi kuma bai bar musu komai ba,hakan yasa suka taso cikin maraici da talaci,su uku iyayen su suka haifa maza biyu sai autar su mace.
Haka mahaifiyar su ta yi ta ɗawainiya da su cikin wahala,gashi ita ma ƴan uwan ta ba taimaka mata suke yi ba.
Lokacin da suka girma sai suka fara zuwa suna aiki a cikin gonakin mutane ana biyan su,da haka suke samun abin da zasu ci su sha su yi hidimar yau da gobe.
A haka shi ALHAJI USAMA ya fara bin masu motar kai kaya zuwa cikin garin Maiduguri suna saukewa,idan ya tafi yana sati ɗaya bai dawo ba,idan kuma ya tashi dawo wa sai ya yi musu siyayya ya kawo musu.
A cikin wannan yanayin ne wani zuwa da suka yi kai kaya ya haɗu da Hajiya Hauwa a unguwar da suke sauka gurin da suke zuwa siyan abin cin rana da na dare, mahaifiyar ta ita ce mai sai da abin cin.
Lokacin da Hajiya Hauwa ta ƙyallara idanun ta a kan Alhaji USAMA ta ji duk duniya babu namijin da take so sai shi,tun yana basarwa har ya zo ya amince mata suka fara soyayya.
Daga wannan lokaci duk abin da ya samu sai dai ya kashe wa Hajiya Hauwa ita da ƴan uwan ta da mahaifiyar ta,ya yin da mahaifiyar sa da ƴan uwan sa ya dena taimaka musu da komai,sai ya shafe wata uku bai zo ya duba su ba.
Lokacin da mahaifiyar Hajiya Hauwa ta fuskanci yana samu sosai sai ta umarce shi da ya turo iyayen sa a yi maganar auren su,a lokacin yana zuwa har cikin garin Kano kasuwanci,bai yi ƙasa a gwiwa ba yaje ya faɗawa mahaifiyar sa da yayen sa,domin a lokacin wansa sani har yayi aure da ɗansa guda ɗaya.
Ba su yi ƙasa a gwiwa ba suka tafi shi da ƙanin mahaifin su da usama ɗin,basu dawo ƙauyen ba sai da aka ɗaura auren Alhaji USAMA da Hauwa.
Watan su shida a Maiduguri ya samu aiki a cikin kasuwar garin Kano,daga nan kuma ya yi watsi da ƴan uwan sa da mahaifiyar sa,bai ƙara komawa ƙauyen su ba sai da mahaifiyar su ta rasu sannan yaje gaisuwa, daga nan kuma bai ƙara komawa ƙauyen nasu ba,sai ma watsi da ya yi da al'amarin ƴan uwan na sa.
Wannan kenan..
"KOGI LOKOJA"
"STATE"
Tun misalin ƙarfe takwas na safe suka ɗauki hanya,babu abin da yake tsayar da su sai sallah da kuma abin da zasu ci,duk da kasancewar ba kowa ne a cikin su yake iya cin abin cin ba,kowa ka kalla daga cikin su zaka hango damuwa ƙarara a kan fuskarsa,musamman ma waɗan da abin yafi shafar su sosai.
Ba su suka isa garin ba dai dare sabo da yana yin hanyar,direct Head Quater n ƴan sanda na garin suka nufa in da aka kwatan ta musu.
Suna zuwa suka kirawo numbern wayar wannan ɗan sandan da ya sanar musu da abin da yake faruwa,nan da nan ya fito daga office ɗin sa ya tare su, Allah ya sa aikin dare yake yi a lokacin,kuma ya san da zuwan su.
Ba tare da ɓata lokaci ba suka ɗunguma gaba ɗayan su zuwa asibitin bisa jagorancin wannan ɗan sandan,direct mutuary suka nufa gaba ɗayan su,basu sha wahalar bincike ba sabo da wannan ɗan sandan babbane kuma sananne ne.
Gurin da aka kai gawar wakin ya nufa da su tare da ma'aikatan mutuary ɗin.
Gawar wakin aka fara nuna musu suna gani,kowanne ka kalla daga cikin su zuciyar sa ta yi rauni sosai da sosai,wasun su ma har da hawayen su sakamakon ganin ƴan uwan su musulmai kwance cikin frizer babu rai a tattare da su,ana cikin haka ne aka gano gawar Alhaji Garba a cikin gawarwakin.
Lokacin da suka yi arba da gawar Alhaji Garba gaba ɗayan su sai da suka ruɗe suka kama surutai,kana ganin su kasan sun ga abin da ya ɗaga musu hankali musamman ma KABIRU da Aminu da suka durƙushe a wajen suna wani irin kuka mai ban tausayi da raunata zuciya.
Shi kan sa ALHAJI MUSTAPHA wan ALHAJI Garba kuka yake yi,malam SALIHU ne ya yi ƙarfin hali a cikin su,amma shi ɗin ma kana ganin sa kasan yana cikin tashin hankali.
Fito dasu aka yi waje aka bar Malam SALIHU shi kaɗai domin ci-gaba da duba gawar Alhaji USAMA,sai dai duk dubawar da aka yi Allah bai sa an ganshi a cikin su ba.
Wannan dalilin ne yasa wannan ɗan sandan ya bada shawarar su tafi asibiti domin a duba matasa lafiyar cikin su ko Allah zai sa yana ɗaya daga cikin su.
Hakan ko a ka yi,gaba dayan su suka ɗunguma zuwa asibitin,direct emergency suka nufa in da aka kwantar da marasa Lafiyan, ɗaya bayan ɗaya suka dinga bin gadajen su suna dubawa,duk wanda yake cikin ɗakin ya raunana sosai.
Suna cikin dubawa ne suka hango gadon wani mutum likitoci duk sun kewaye gadon,sai ƙugi da nishin mara lafiyar ne yake tashi a wajen,cikin sauri suka ƙarasa gadon domin duba mara lafiyan dake wannan ƙugi.
Suna ƙarasowa suka ji mara lafiyar na cewa
"Ku kirawo min mata ta da ƴaƴana Aminu da RUFAIDA,ina so na gansu kafin na mutu"
Turus suka tsaya! Ko wannen su ya yi cirko-cirko, ganin hakan da suka yi ne ɗan sandan yake tambayar su ko shine mutumin da suke nema,cike da ƙarfin hali Aminu ya gir-giza kai alamar eh.
Ƙarasawa ɗan sandan ya yi har gaban gadon ya yi wa likitocin bayani,hakanne yasa suka basu damar ƙarasowa gaban gadon domin su duba mara lafiyan da kyau su gani.
Lokacin da suka yi arba da Alhaji USAMA,gaba ɗayan su sai da suka fashe da kuka har malam SALIHU,gaba ɗaya kamannin sa sun chanja kamar ba shi ba,idan ka gan shi zaka ɗauka ya shekara biyu yana ciwo,ƙafar sa guda ta kumbura sun tum an nan naɗe ta da bandeji,ita kuma ɗaya ƙafar ta riga ta yi damage sakamakon bullets ɗin da suka dagargaza ƙashin ƙafar.
Babu abin da take sai zubar da wani irin ruwa mai wari da ƙarni,gashi duk jikin shi ya ɗashe Sabo da rashin jini.
Cikin shesh-sheƙar kuka Aminu ya ɗora hannun sa a saman kan Alhaji usama yace
"Baba! Kai ne ka koma haka cikin ƙanƙanin lokaci kamar ba kai ba!"
Ya faɗa yana ƙara fashewa da kuka.
Da sauri ya buɗe idon sa jin muryar ɗan na sa Aminu!,ya ƙura masa ido kamar bai taɓa ganin sa ba,daga bisani ya ɗago kansa ya dubi su malam SALIHU ɗaya bayan ɗaya sannan ya fashe da kuka mai ban tausayi,cikin kukan yake faɗin sunan su ɗaya bayan ɗaya tare da cewa
"Kunga yadda Allah ya yi damu ko! Agarin zalunci da san zuciya da rashin imani! gashi yadda ƙarshen mu ya kasan ce,shi ALHAJI Garba ya rasu! ni kuma ya nakasa! yanzu haka zancen da nake yi muku yanke min kafa ta za'a yi ta dama,ga azabar ciwo da take min ko bacci bana iya yi!!"
Ya ƙarasa maganar cikin raunin murya da karayar zuciya.
Gaba ɗayan su wani irin kuka suke yi,dukannin wani mutum mai imani idan ya ji kalaman Alhaji USAMA sai ya tausaya masa.
Nan wani babban likita daga cikin likitocin ya yi musu bayani akan larural Alhaji USAMA,in da yake cewa
"A gaskiya ƙafar nan tasa ta dama sai mun yanke ta,dan gaba ɗaya ta ta riga ta ruɓe,sabo da haka zakusa hannu a wannan takar dar.sannan zaku biya million ɗaya kuɗin aikin da za'ayi masa da kuma magungunan sa"
Ya ƙarasa maganar yana miƙo musu takardun.
Cike da karayar zuciya malam SALIHU ya miƙa hannu ya amshi takardun.
Bayani likitan ya ci-gaba da yi,in da yake cewa
"Sannan akwai jini da muke buƙata wanda za'a ƙara masa, dama leda huɗu muke buƙatar a saka masa,toh wasu bayin Allah sun bada leda biyu sadaka an saka masa,yanzu saura leda biyu muke buƙata mu saka masa, Sabo da aikin yanke ƙafar da za'a yi masa!"
Cikin kuka Aminu yace a gwada nasa idan ya yi dai-dai sai a ɗiba,shima KABIRU yace a gwada nasa.
Ba tare da ɓata lokaci ba aka gwada jinin su,cikin Sa'a jinin su ya yi dai- dai domin 0+ ne,nan take aka yi test aka ga babu wata cuta a cikin jinin,ba tare da ɓata lokaci ba suka kwanta aka ɗebi jinin su kowa leda ɗaya.
Nan likitan ya umarci suje su biya kuɗin aikin dan zuwa gobe da safe za'a shiga a yi masa surgery ɗin.
Wannan kenan....✍🏻
Pls ku yi haƙuri da rashin jina kwana biyu da baku yi ba,hakan ya faru ne sakamakon mijin yaya ta da Allah ya yi masa rasuwa.
Ina matuƙar godiya da addu'o'in ku a gare ni, ku ɗin na musamman ne a cikin zuciya ta, ina yi muku fatan Alkhairi ƙwarai da gaske, Allah ubangiji ya saka muku da mafificin alkhairin sa, ya biya muku buƙatun ku na Alkhairi 🙏🏻
Daga alƙalamin FATIMA BINTU ABDULLAHI (UMMU AYSHA)....✍🏻✍🏻
Share fisabilillahi..
Game buƙatar littafin tun daga farko ya tuntuɓe ni a wannan numbern wayan👇🏻👇🏻
08162055134.
💝💞HALIMATU 💝💞
(Love, sacrifices, destiny & betrayed)
💝💞💝💞💝💞💝💞
Story & Writing
By
FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)....✍🏻✍🏻
Ƙarƙashin jagorancin
(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)
Golden pens........✍🏻✍🏻
💝💞💝💞💝💞💝💞
A 2024 novel
💝💞💝💞💝💞💝💞
Page_____________51&52
______________masauki sauran suka je suka kama domin su huta su ci abinci sukuma yi sallah,ya yin da aka bar Aminu da KABIRU a wajen Alhaji USAMA za su kwana da shi.
Miƙewa Kabiru ya yi tare da cewa zai je ya yi sallah ya dawo,idan yaso sai aminu shima ya je ya yi sallar, Sabo da kar a tafi a barshi shi kaɗai.
Haka kuwa a kayi bayan Kabiru ya dawo aminu shima ya je ya yi tasa sallar,daga nan ya biyo musu da abincin da za suci.
Ba dan daɗi ba haka suka cuccusa Abin cin a cikin bakin su,in da suke ji kamar maɗaci suke taunawa a bakin su.
Bayan sun gama cin abincin ne suna zaune sun yi jugum da su gwanin ban tausayi,yayin ALHAJI USAMA yake bacci sakamakon allurar da aka yi masa ta bacci zugin da ƙafar ta dame shi da shi.