← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 80

Sashe 21

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana ƙarasowa tazo gaban daddy da MOMY ta durƙusa ta gaishe su, sannan ta gaida hafiz da Sadiq,amsawa sukayi fuskar su a sake.momy tace"ma sha Allahu doughter kinyi kyau sosai wallahi"murmushi tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa.duban ta daddy yayi da zolaya yace" ma sha Allahu ɗiya ta Irin wannan kwalliya haka kamar zakije gasar kyau" dariya suka kwashe da ita gaba ɗayan su banda farouq da haɗe fuska babu annuri.

Kallon ta farouq yayi tare a cewa"wato na fuskanci yarinyar nan duk faɗin gidan nan babu wanda ta raina kamar ni sabo da taga ina yi mata dariya ko??" ya ci-gaba da cewa "bama wannan ba,da kika ci wannan uwar kwalliyar an gaya miki gidan biki zaki je??" ya ƙarasa maganar yana jefa mata hara.momy ta dube shi tace"kaga malam ina ruwa ka da ita! ko so kake yi ta fita kamar korarriya babu ado babu kwalliya??,to ka kiyaye ni wallahi!!" ta ƙarasa maganar ranta a ɓace.

Kallon HALIMATU tayi tare da cewa "doughter tashi kije kiyi break fast ku tafi karku yi late"to tace tare da miƙewa ta wuce dining table ɗin.duban MOMY farouq yayi tare da cewa "gaskiya duk abin da yarinyar nan take yi kece kike ɗaure mata gindi" a fusa ce MOMY ta juyo ta kalli farouq tare da cewa "to ubana na ɗaure mata ɗin sai ka ɗauki bulala ka zane ni" ta ci-gaba da cewa "to wai ma ina ruwanka da ita ne?? to wallahi ka kiyaye ni,ka fita daga harkar yarinya ta na gaya maka"ta ƙarasa maganar tare da yi masa kashedi"

"Allah ya huci zuciyar ki first love ɗina,kiyi haƙuri in sha Allahu bazan sake ba"ya faɗa yana marairai ce fuska.a fusa ce tace" da ya fi maka hakan".duk wannan abin da ake yi daddy yana kallon dramar yana dariya irin tasu ta manya.miƙewa HALIMATU ta yi tana da goge bakin ta da tissue tazo kusa da daddy da MOMY ta durƙusa tace"momy daddy zamu tafi kuyi min addu'ar samun nassara"

Shafa kanta momy tayi tare da cewa"Allah ubangiji ya bada Sa'a doghter na, Allah yasa ki fito da sakamako mai kyau "ba ƙaramin daɗin addu'ar taji ba,nan take taji hawaye ya cika mata idanu, sakamakon tunawa da tayi da mahaifiyar ta.duk lokacin da take tare da momy sai taji kamar tana tare da mahaifiyar ta,koda yake ai jini ɗaya ba wasa bane ba .

Miƙewa tayi ta fada jikin MOMY tare da rungume ta.bayan ta MOMY ta bubbuga tare da cewa "kukan kuma na mene ne?? ba gani tare dake ba!! ko so kike yi nima nayi kukan ne??"nan take HALIMATU ta girgiza kanta tare da share hawayen ta,shiru daddy yayi yana kallon su,ba ƙaramin tausayi suka bashi ba, Sabo da ya daɗe baiga soyayya mara algus ba irin tasu.

Buɗe baki yayi tare da cewa "Allah ubangiji ya bada Sa'a doughter ya baki sakamako mai kyau,nasan kina da ƙoƙari to ina so ki dage ki nutsu ki zana jarabawar ki,muna miki fatan alkhairi" HALIMATU ta amsa da "ameen daddy thank you,im proud of you"ta faɗa tana miƙewa tsaye.kallon ta hafiz da Sadiq sukayi har suna haɗa baki wajen cewa "fatan nasara syster"kanta ta girgiza tare da yin murmushi tace "thank you"tana gama faɗi ta saka kai ta bi bayan farouq da har yayi ficewar sa.

Bayan fitar sune suma suma su hafiz suka fice daga part ɗin zuwa nasu,kasan cewar yau babu office hutawa kawai suke yi.ya rage daga MOMY sai daddy a parlon,kallon juna su kayi tare da sakarwa junan su murmushi. Daddy ne ya katse shurun tare da cewa "my dear gobe ne fa zuwan MUKHTAR!! ina fatan kun fara shiri kafin goben!, sannan ya kamata ki sanar da yarin yar nan halin da ake ciki tun yau"ya ƙarasa maganar yana kallon MOMY.

Shiru MOMY tayi na ɗan wani lokaci sannan ta sauke ajiyar zuciya tare da cewa "wallahi noori ban gaya mata ba, saboda nauyi maganar nake ji,na rasa yanda zan yi na faɗa mata, sabo da bansan yadda zata ɗauki abun ba".ajiyar zuciya daddy ya sauke tare da cewa "kada ki damu sanyin idaniya ta,duk na fahim ce ki,ni zan gaya mata idan ta dawo anjima,nasan zata amince bazata bamu kunya ba, domin HALIMATU tana da kirki da nutsuwar,uwa uba ga hankali.in sha Allahu baza mu samu matsala da ita ba"ya ƙarasa maganar tare da tallabo fuskar MOMY a tafin hannun sa.da sauri ta shige jikinsa ya mai da hannun sa ya rungume ta, ƙasa ƙasa da murya tace "nagode abin alfahari na,ina mutuƙar farin ciki da samun ka a matsayin uban ƴaƴan"

Wani irin daɗi ne ya taso masa Tun daga ƙasan ruhina sa har zuwa cikin zuciyar sa .daga nan suka cigaba da hirar su cikin soyayya da ƙaunar junan su,wannan kenan ......

"MUKHTAR"

A ɓangaren MUKHTAR kuwa yana shigowa gida direct sama yayi ya faɗa toilet yayi wanka,bayan ya fito ne ya saka jallabiya tare da fesa turare kaɗan.wayar sa ya ɗauka ya fita daga cikin ɗakin ya sauka ƙasa ya zauna a kan two sweater.tv ya kunna tare da ɗakko remote ya fara controling ɗin tv ya kaita zuwa tashar Al-Jazeera .

Yana cikin kallon ne wayar sa tayi ƙara, ɗauka yayi tare da dubawa yaga daddyn sa ne yake kiran sa.cike da ladabi kamar yana gaban sa ya ɗaga wayar tare da karawa a cikin kunnen sa .daga ɗaya ɓangaren daddy ya kirawo sunan sa tare da labar ta masa yadda suka yi da daddyn su MUKHTAR,ya ƙara da cewa "gobe idan Allah ya kaimu zakaje gidan su HALIMATU ku gana! Ina fatan dai ka gane??". MUKHTAR yace "na gane daddy, Allah ubangiji y kaimu goben da rai da lafiya,in sha Allahu zan je bayan sallar la'asar.ɗazu ma mun haɗu da hafiz a super market,yace duk yana gaishe ku! daddy yace muna amsawa,daga haka suka yi sallama tare da ajiye wayar.

"INNA LAURE"

A ɓangaren su inna laure kuwa, lokacin da ta shigo cikin gidan taga halin da malam musa da iyalin sa suke ciki,nan take ta durƙushe a gurin ta fashe da kuka,tsoron Allah ne ya kamata sakamakon yana yin da ta gansu, sannan tasan duk abin da ya faru da su itace sila,domin da batazo gidansa ba da duk hakan bata faru ba.

Lamunde ce ta katse kukan nata tare da cewa "dakata baƙar muna fuka,algun guma,muguwa maci amana!! kinzo ne ki kuma jawo mana wani bala'in ne banda wanda muke ciki??,to wallahi tun kafin mutara miki jama'ar gari suyi miki tsinannen duka gwara ki tattara ki fice mana daga gida!!".ta faɗa tana sauke numfashin wahala.ta ci-gaba da cewa "wallahi laure kin cuce mu kuma baza mu taɓa yafe miki ba duniya da lahira, Allah ya isa tsakanin mu dake!!".

Cikin kuka ta ɗago da kanta suka haɗa ido da malam musa nan take ta hango tsan tsar tsanar ta a cikin ƙwayar idanun sa!!.nan take ta ruɗe tare da ƙara fashewa da kuka a karo na biyu tace "dan Allah yaya kayi haƙuri wallahi bansan haka zata faru ba,da nasan da hakan da bazan zo wajen kuba!!" cike da hasala malam musa ya buɗe baki yace"zaki tashi ki tattara tarkacen ki kubar gidan nan ko kuwa sai nasa an illatamin ku!!"

Ya ci-gaba da cewa"kuma kije Allah ya isa tsakani na dake ban yafe miki ba!!"ya ƙara sa maganar yana aika mata da wani irin mugun kallo idanun sa jawur.wannan karan ba ita ba har yaran sai da suka fashe da kukan baƙin ciki suna roƙon malam musa da ya yafewa innarsu tayi na dama.........

Wani kalan mugun ashar malam musa ya ƙunduma musu gaba ɗayan su,tare da ɗaukan ƙaton dutsen da aka kange masa ƙafar sa yaje fi inna laure dashi,cikin Sa'a kuwa ya same ta a goshi! nan take goshin ya fashe ya fara zubar da jini.ganin haka ne yasa gaba ɗayan su suka yi kanta tare da kama ta suka fice da ita daga cikin gidan suna kuka abin tausayi .note, Shi mahaifi duk yadda yake haka ake haƙuri dashi a zauna dashi, sabo da bazaka taɓa canja shi ba,ko da shi ɗin mahaukaci ne, ko kuma wani abu maka mancin haka .

Bayan fitar sune altine ta kalli rahinatu da hanne tace musu"ni zan bi innar mu gida mu gida in kwana tare da ita, sabo da na fuskan ci kowa gudun ta yake yi,idan yaso ke rahinatu ki tafi gida gurin yaran ki,ita kuma hanne sai ta koma gurin yara na su kwana tare, in yaso sai tayi wa baban su harisu bayani.haka kuwa a kayi kowa ya kama hanyar sa,su kuma suka nufi gidan ita da inna laure.

"HALIMATU"

Sai wajen yamma suka dawo gida,ba ƙaramar gajiya suka kwaso ba, farouq yana ta mita yana cewa shi an takura masa.tana shigowa parlon direct sama tayi ta nufi ɗakin MOMY sabo da bata ganta a ƙasa ba.sallama tayi auta ta amsa mata, tambayar ta tayi ina MOMY take?? Ce mata tayi tana ɗakin daddyn!! tace mata "to idan MOMY tazo ki gaya mata mun dawo" bata jira mai auta zata ce ba kawai ta juya ta nufi ɗakin ta.

Tana shiga kayanta ta fara cirewa tare da ɗaura towel ta shige toilet,bata wani ɗauki lokaci ba ta fito.lotion ta shafa sama sama tare da fesa turare kaɗan,riga ta ɗauka mara nauyi ta saka tare da saka ƙaton hijabi ta shimfiɗa dadduma ta tada sallah, dama already ta riga tayi alwalar ta a toilet.bayan ta idar da sallar ne ta cire hijab ɗin ta ninke tare da yin bismillah ta haye gadon ta ta kwanta sabo da tayi mutuƙar gajiya,bata daɗe da kwanciya ba bacci ya ɗauke ta .sai da aka kirawo sallar magriba sannan MOMY ta tashe ta.

Bayan ta idar da sallar ne ta zauna tana addu'a har aka kirawo sallar isha'i, bata tashi daga gurin ba sai da ta gabatar da sallar isha'i.addu'a tayi kafin ta tashi ta ninke sallayar,tana cikin ninke wa ne auta ta shigo tace mata tazo suyi dinner ita kaɗai ake kira.tana gama faɗa mata ta juya ta tafi a guje.ƙaramin hijabi ta ɗakko ta saka, fitowa tayi daga cikin ɗakin ta sauka zuwa ƙasa
Chapter 21 · 0% Book details