Sashe 31
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Share fisabilillahi.
08162055134.
💝💞 HALIMATU💝💞
(Love, sacrifices, destiny & betrayed)
💝💞💝💞💝💞💝💞
Story & writing
By
FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)
Ƙarƙashin jagorancin
(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)
Golden pens.............✍🏻
A 2024 novel
Pages____________35&36
"MUKHTAR"
Cike da matsananciyar kunya MUKHTAR yace "MOMY MUKHTAR ne! dama ɗazu na karɓi numbern wayan ki a wajen Hafiz ne shine na kirawo mugaisa!!".
Gane da wanda take magana da shine yasa tace "ayya ka kyauta,ya mutanan gidan?? Ina fatan duk kowa yana lafiya??"
"Lafiya ƙalau suke MOMY, sunce suna gaishe ku"
"Masha Allah muna amsawa,bari na baka HALIMATU ku gaisa"
Cike da kunya yace "to MOMY".
Daga haka ta ƙwalawa HALIMATU kira domin bata wayar,dan ta gano shi sarai yana so ya gaisa ne da HALIMATU shi yasa ya karɓi numbern ta.
"MOMY gani!!"
Miƙa mata wayar tayi tare da cewa " ungo karɓi nan MUKTAR ne zaku gaisa!!" Shiru tayi cike da mamaki tana kallon wayar ta kasa sa hannu ta karɓa, kallon ta MOMY tayi tare da cewa "karɓi mana kuɗin shi na tafiya fa!!"
A hankali ta saka hannun ta karɓi wayar cike da kunya ta kara a kunnen ta tare da yin sallama,ganin haka yasa MOMY ta miƙe ta haye up stairs domin ta bata waje taji daɗin yin wayar,don ta san muddin tana kusa HALIMATU bazata taba sakewa suyi magana ba .
Daga ɗaya ɓangaren MUKHTAR ya amsa tare da sauke sassanyar ajiyar zuciya sakamakon jin daddaɗar muryar ta da ta ratsa cikin dodon kunnuwan sa da gangar jikin sa!..
Shiru ne ya ɗan biyo baya,daga bisani tace masa "ina wuni??"
MUKHTAR yace "lafiya lau"
"Ya gida,yasu MOMY daddy da MEENA??"
"Duk suna nan ƙalau! Sunce suna gaishe da surukar su!!".
Cike da kunya ta rufe fuskar ta kamar yana gaban ta,daga ɗaya ɓangaren MUKHTAR yace"kin yi shiru ko ba kya amsawa!!"
HALIMATU tace "ina amsawa mana!"
"Okey to zan gaya musu in ce surukar su tana gaishe da su ko??"
"A'a gaskiya ni kunya nake ji!!".
Dariya ce ta suɓuce masa yace "to meye abin kunya a gaisuwa??"
"Gaskiya ni dai ina jin kunya!" ta faɗa tare da marairai ce murya,
"Okey to shikenan tunda bakya so bazan faɗa musu ba".
Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa"ya kuka je gida??"
"Lafiya ƙalau Alhmdllhi"
"Ya aiki??"
MUKHTAR yace "Alhamdulillah mungode Allah,amma fa tunanin ki ya hana ni yin aikin,kwata kwata ya hana ni suku Ni a rayuwata!!.
Tace "Ni kuma??"
"Ya za'a yi tunani na ya hana ka suku Ni??"
MUKHTAR yace ...
"HALIMATU kenan! Baki san yanda nake jinki a cikin zuciya ta bane shi yasa kika ce haka!!"
"Amma da kinsan yanda nake jinki a cikin zuciya ta da baki ce min haka ba!!".
Ya ci gaba da cewa "wannan dalilin ne ma yasa na kasa haƙuri na karɓi numbern MOMY a wajen Hafiz domin naji daddaɗar muryar ki ko hankali na zai kwanta in samu suku ni a cikin raina da zuciya ta".
Ya ci gaba da cewa "kullum addu'a ta shi ne Allah ubangiji ya cika min burina,ya mallaka min ke a matsayin matar aure na!!". HALIMATU tace "aure kuma??"
"Ai ba yanzu ba! Sai na gama karatu na,kaga lokacin na girma"
Wani irin murmushin gefen baki yayi tare da cewa "au hakane fa,mantawa nayi sai kin girma sannan za mu yi aure ko??"
Cike da rashin wayo tace masa "eh"
Yace "to Allah ubangiji ya kaimu lokacin"
HALIMATU ta amsa da "Ameen".
MUKHTAR yace "gaya min kinyi missing ɗina kuwa??"
Sunkuyar da kanta ta yi kamar tana gaban sa tare da rufe fuskar ta tana murmushi ƙasa ƙasa.
"Kinyi shiru faɗa min inji!!"
Murya ƙasa ƙasa kamar tana jin tsoron wani ya jita tace "eh nayi".
Wani irin sanyi ne ya ratsa cikin ruhin sa da gangar jikin sa, nan take ya sauke ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya,cike da matsanancin farin ciki yace "ina sonki sosai HALIMATU!! Dan Allah kema ki soni koda kaɗan ne kinji!"
Cike da yarin ta tace masa "to". jin ana kiran sallar magriba ne yasa yace mata zaije masallaci, ita ma taje ta yi sallar zai kirawo ta anjima,daga haka suka yi sallama tare ajiye wayar.
"RUFAIDA"
Zaune suke a cikin parlon su su uku!.
RUFAIDA ce ita da yayan ta da baban su suna tattaunawa game da al'amarin ta da MUKHTAR, ɗagowa daddy yayi ya kalli RUFAIDA tare da cewa "kinga Wannan mijin naki idan bamu yi da gaske ba tabbas zai iya kuɓce mana!!"
"Domin ga dukkan alamu ayyukan da muka yi sun fara warware wa!!
Kwata kwata yanzu ya dena kiran waya ta, sannan ɗan Alkhairin da yake min shima yanzu ya dena!!"
Fashewa da kuka RUFAIDA tayi tare da cewa "nidai daddy kuyi duk yadda zaku yi na samu na koma ɗakin mijina,wallahi ina ƙaruwa da shi sosai, bazan taɓa samun mijin da yake sakar mun kuɗi sosai kamar sa ba!!".........
Ajiyar zuciya mai ƙarfi daddy ya sauke,ya ɗago ya dubeta a karo na biyu tare da cewa "yi shiru share hawayen ki,bari mu jirawo dawowar umman taki sai muga yadda zamu ɓullowa al'amarin kinji!!"
Kanta ta gyaɗa tare da cewa to dad..........bata kai ga ƙarasa maganar da takeyi ba suka jiyo muryar umma tana shigowa cikin parlon .
"Ƴar halak kinƙi ambato! Ya ake ciki??" Daddy ya faɗa yana kallon ta.
Sauke ajiyar zuciya ta yi tare da cewa "wallahi daddyn yara akwai matsala!! Abubuwa suna neman su lalace mana!!.
Nan take ta bawa daddyn su RUFAIDA labarin duk abin da yake faruwa,sannan ta ƙara da cewa
"Bayan na bar wajen malami na ban yi ƙasa a gwiwa ba sai da naje wajen malamai har uku amma abin da ya ƙara bani mamaki duk maganar tasu iri ɗaya ce!! Na rasa ma wanne irin tunani zanyi akan wannan lamarin!!"
Ta ƙarasa maganar hankalin ta a mutuƙar tashe.
Miƙewa tsaye daddyn RUFAIDA yayi ya kalli umma yace "zama bai gan mu ba,dole ne mu san abin yi!!"
"Bari na je gurin malam uzairu muyi magana dan akwai wani malamin sa da yake bani labarin sa ya iya aiki sosai!"
"In sha Allahu za'a dace"
Yana gama faɗin hakan yayi ficewar sa bai jirawo cewar su ba.
Yana fita RUFAIDA ta fashe da kuka tare da rungume umma tace "Na shiga uku umma!!"
"Yanzu yaya zan yi idan na rasa MUKHTAR!! Dan Allah ki taimaka min!! wallahi bana so na rasa shi, sabo da samun irin su wuya suke yi sai wanda yayi dace!!"
"Gashi Ni ɗin Na samu amma yana Neman ya kuɓce min!!".
Rufe mata baki umma tayi tare da cewa "yi shiru dena yi wa kan ki wannan mugun fatan! In sha Allahu yanzu kika fara zama da MUKHTAR!! Kuma wallahi muddin ya shigo hannun mu sai ya ɗan ɗana kuɗar sa!! Dan wannan karan baza mu yi masa ruƙon wasa ba!!".
Ta faɗa tare da yin ƙwafa........
********************************
"INNA LAURE"
A ɓangaren su inna laure kuwa, gyaran da baba lado yayi musu yayi kyau sosai,shi yasa taji daɗin jikin ta sosai!
Gefe Guda kuma ga kyakkyawar kulawar da take samu gurin altine da Hanne.
Sannan Sama'ila saurayin hanne ya siyo mata magun gunan kashe raɗaɗi da kuma tsanewar ƙafar,kuma Alhamdulillah sauƙi yana samuwa sosai.
Zuwa yanzu ta yi nadamar abubuwa da yawa da ta aikata a rayuwar ta tare da neman gafarar ubangiji.
Sai dai har yanzu babu labarin baba sam sam, a kullum zuba ido take yi taga dawowar sa, amma shiru babu wani labari.
Hakan ne yasa ta sanya damuwa a cikin ranta,dan ma su altine na kwantar mata da hankali shi yasa ta samu sauƙin abin.
Wannan kenan............
"BUBA"
Zaune suke a cikin dokar daji shida yaran sa zuga guda, fuskar nan tasa babu alamar fara'a sabo da tsananin ɓacin ran da yake ciki.
Idanun nan nasa sun yi jawur da su kamar jan gauta,ajiyar zuciya kawai yake saukewa kamar wanda zai yi aman wuta.
Ba komai ne ya jawo hakan ba face rashin masoyiyar sa da yayi wato Safara'u!! babu inda bai sa yaran sa sun bin cika a cikin garin ba,amma babu su babu alamar su.
Wannan dalilin ne ya haifar masa da ɓacin ran da yake ciki.
Ɗagowa yayi ya kalli baban yaron sa tare da kiran sunan sa yace
"Sisa ina so ku shiga birni gaba ɗayan ku kuyi ɓadda kama ku zaga lungu da saƙo ku nemo min duk in da matata take ita da uwarta ku kawo min su!!"
"Na baku nan da kwana uku ku yi ƙoƙari ku kawo min su!! Domin ina so na koyawa uwarta hankali!! Wallahi zata san ta taɓani! Domin na fuskanci har yanzu bata san waye ni ba!!".
Ya ci gaba da cewa "ni zan je gurin iyayen gida na, sabo da akwai abubuwa masu muhimmanci da zamu tattauna akai!! Duk yan da ake ciki kuyi ƙoƙarin sanar da Ni!!"
Yana gama maganar ya muƙe tsaye ya shige wani kogon dutse mai duhu, ba tare da ya jirawo cewar su ba.
Bayan shigewar sa ne sisa ya jagoranci tawagar suka kasu kashi kashi tare da shiga cikin gari domin fara gudanar da aikin oga BUBA.............
Ina matuƙar godiya da addu'o'in ku a gare ni tare da fatan Alkhairi.....
Kuɗin masoya na ne kwarai da gaske, Allah ubangiji ya bar so da ƙauna.
Ina muku fatan Alkhairi ƙwarai da gaske.
Daga alƙalamin FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)..................✍🏻
Share fisabilillahi......
08162955134....
💝💞HALIMATU💝💞
(Love, sacrifices, destiny & betrayed)
💝💞💝💞💝💞💝💞
Story & writing
By
FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)
Ƙarƙashin jagorancin
(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)
Golden pens...............✍🏻
💝💞💝💞💝💞💝💞
A 2024 novel
Pages____________37&38
"HALIMATU"
A ɓangaren HALIMATU kuwa lokacin da suka yi sallama da MUKHTAR, miƙewa tayi tare da haye wa up stairs direct ɗakin MOMY ta nufa domin ta kai mata wayar ta.
Yusra ta tarar zaune akan sofa da tab a hannun ta tana daddana wa, tambayar ta tayi ina MOMY?
Ce Mata tayi tana toilet.
Daga haka ta ajiye wa MOMY wayar ta akan mirror ta fice daga ɗakin domin zuwa tayi salla.
Ɗakin ta ta nufa ta wuce toilet ta ɗauro alwala tazo ta tayar da sallar magriba,bata tashi a wurin ba sai da ta yi sallar isha'i tayi azkar ɗin da bata samu ta yi ba ɗazu.