Sashe 52
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ina matuƙar godiya da addu'o'in ku a gare ni tare da fatan Alkhairi,ku ɗin na musamman ne a cikin zuciya ta, ina matuƙar alfahari da ku ƙwarai da gaske, Allah ubangiji ya saka muku da mafificin alkhairin sa ya biya muku buƙatun ku na Alkhairi..🙏🏻🙏🏻
Daga:
Alƙalamin FATIMA BINTU ABDULLAHI (UMMU AYSHA)...✍🏻✍🏻
Share fisabilillahi.
Ga me buƙatar littafin HALIMATU tun daga farko zuwa in da aka tsaya ya tun tuɓe ni ta wannan numbern wayar👇🏻👇🏻
08162055134..
💝💞HALIMATU💝💞
Love, sacrifices, destiny & betrayed)
💝💞💝💞💝💞💝💞
Story & Writing
FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)....✍🏻✍🏻
Ƙarƙashin jagorancin
(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)
Golden pens.......✍🏻✍🏻
💝💞💝💞💝💞💝💞
A 2024 novel
Pages____________65&66
_______________suna ƙarasowa gida su daddy da su sahal ne suka shiga cikin parlon,ya yin da mukhtar da meena suka kwaso duk boxes ɗin cakes ɗin da doughnut har da miet pie suka ajiye su akan center table ɗin dake gaban su daddy, kallon mamaki suke bin su da shi domin abin ya ɗaure musu kai ƙwarai da gaske.
Duk da cewa kuwa sun ga lokacin da meena take kwaso su a gidan su halimatu tana kai wa cikin mota hakan bai hana su ƙara shiga mamaki ba,lura da hakan da suka yi ya sa meena yin murmushi tare da cewa,
"Ku kwantar da hankalin ku daddy, birthday day ne aunty halimatu ta haɗawa yaya MUKHTAR na murnar dawowar sa gida lafiya"
Ta faɗa tana buɗe boxes ɗin da cakes ɗin suke ciki,sai da ta buɗe musu komai da ke gurin suka gani cike da ɗumbin mamaki da burgewa.
Daddy ne ya yi wani irin murmushi mai ƙayatar wa ya dubi mukhtar da yake zaune a kan sofa kan sa a duƙe yana murmushi ƙasa-ƙasa tare da sosa bayan ƙeyar sa,kan sa kawai ya girgiza tare da cewa,
"Wannan yarinya Allah ubangiji ya yi mata albarka ya mallaka maka ita,domin a yadda nake ganin ta idan ka aure ta zaka ji daɗin zama da ita sosai,ina ga Allah ne ya amsa addu'o'in da muke yi maka ya baka ita a matsayin matar da zaka aura"
"Ƙwarai kuwa Alhaji,ni kai na wallahi na yaba da kyawawan halayen yarinyar nan,ga ladabi da biyayya,kana ga fa har muka baro gidan nan kan ta a ƙasa yake bata ɗago ta kallemu ba sabo da tsananin kunyar ta,bugu da ƙari kuma ga ta yarinya ƙarama kyakkyawa"
Momy ta ƙarasa maganar tana murmushi.
"Gaskiya na ga alamar kin yaba da surukar nan taki sosai"
Daddy ya faɗa yana murmushi.
"Ai kaima ka yaba da ita,hakan ne ma ya sa kayi saurin kama masa ita kafin wani ya riga ku ya yi wuuf da ita"
Murmushi ya yi wannan karan mai sauti tare da cewa,
"Banda abin ki ina zan tsaya kallon ruwa kwaɗo ya yi mana ƙafa,shi yasa tun lokacin da na ɗora idanu na a kan ta ban yi ƙwauron baki ba na sanar tun a lokacin, sabo da kallon da na fara yi mata na ji hankali na ya kwanta da ita sosai da sosai,domin irin ta na daɗe ina addu'ar Allah ya musanya wa ɗana, sai gashi Allah ya amsa addu'a ta".
"Wannan haka yake, Allah ubangiji ya tabbatar mana da Alkhairin sa"
Gaba ɗayan su suka amsa da ameen.
Kallon muktar ya yi tare da cewa,
"Mun yi magana da Alhaji Auwal ya yi min bayani game da ganin mahaifin HALIMATU da aka yi,ashe wayar sa ce ta faɗi shi yasa ba'a samun sa kwata-kwata,amma yanzu Alhamdulillah ya dawo cikin garin Kano gaba ɗaya da zama,yanzu haka zancen da nake yi maka yana zaune a unguwar court road wajen gyaɗi-gyaɗi shi da matar sa da ya aura,in sha Allahu zuwa gobe idan muka dawo daga duba kakan yaran nan ni zan wuce gurin Alhaji Auwal domin muje mu gaisa da mahaifin nata,kai ma idan an kwana biyu sai kuje kai da nura ku gaishe shi ".
Cike da mamaki yake girgiza kai tare da cewa,
"Ma sha Allah, Alhmdllhi! gaskiya na ji daɗi sosai daddy, Allah ya kaimu goben da rai da lafiya"
"Ameen" daddy yace.
Meena ce ta hau sama zuwa bedroom ɗin ta ta ɗakko ring light ta ƙaraso in da su daddy suke zaune tace,
"Daddy momy yaya MUKHTAR kuzo mu yi pics pls"
Dungure mata kai momy ta yi tare da cewa,
"Haka kika iya ai,na san dama da ƙyar ne idan baki ce ayi hotuna ba"
Murmushi suka yi gaba ɗayan su,nan take suka haɗu aka fara ɗaukan pics na family gwanin ba sha'awa da burgewa, daddy ya yanko cake ya bawa momy a baki cike da farin ciki,ya yin da ita ta yanko cake ɗin ta bashi a baki meena na ta ɗaukan su hotu na.
Shima muktar yan kowa ya yi ya bawa meena da su sahal a baki cike farin ciki, suma su sahal suka yanko suka saka masa a baki suna ta dariya,kowa ka kalli fuskar sa zaka gan ta cike da annuri,haka suka yi nasu birthday ɗin suma a wannan daren suna ta saka wa halimatu albarka,daga ƙarshe kowa ya yanki cake ɗin da doughnut da miet pie aka zauna ana ci ana hira.
"Gaskiya son baka kyauta ba kasa yarinyar nan kashin kuɗi da yawa!"
Daddy ya amshe da cewa,
"Nima abin da nake tunani kenan! ina fatan dai kayo mata tsarabar ta ta musamman ko.?"
Cike da ladabi ya ce,
"Ba siya ta yi ba,ita ta yi abin ta kanta wallahi daddy, nima ban sani ba wallahi, kawai ta ce min ta yi za ta yi suprise ɗina!sai da nazo kawai na gani,kuma na yi mata tsarabar ta idan na mutsu na ware zan kai mata"
Girgiza kai suka yi cike da mamakin yarin yar.
Bayan sun gama ciye-ciyen ne aka saka sauran a cikin freezer kowa ya wuce side ɗin sa domin ya kwanta.
Washe gari bayan sun yi break fast daddy da muktar suka fita zuwa office domin muktar yana so ya duba wasu ayyukan sa na musamman,ya yin da meena da su sahal suka wuce school aka bar momy ita kaɗai a gida.
Ƙarfe huɗu Alhaji Ibrahim ya samu daddy a office kamar yadda suka tsara za su je gurin baban halumatu,dama tun jiya ya karɓi numbern wayar sa a gurin momy ya kirawo shi ya sanar da shi maganar zuwan na su har ya tura masa da address ɗin gidan na sa.
Ba tare da ɓata lokaci ba suka fito suka shiga cikin motar Alhaji Ibrahim drivern sa ne ya jasu suka tafi.suna ƙaraso wa ƙofar get ɗin gidan daddy ya kirawo shi ya sanar da shi zuwan su, ba'a daɗe ba mai gadi ya buɗe musu get ɗin bisa umarnin baban.
Danna hancin motar drivern ya yi tare da shigewa cikin gidan ya yi parking motar a can gefe,tsaye suka hango baba a bakin babbar ƙofar da zata sada ka da babban parlon na su, fitowa suka yi daga cikin motar suka nufi in da yake tsaya fuskar shi ɗauke da murmushin jin daɗin ganin su.
Hannu ya miƙa musu suka yi musabaha tare da yi musu iso har cikin parlon,zama suka yi akan sofa suka ƙara gaisawa sosai sabo da an daɗe ba'a haɗu da juna ba, nan baba ya yi ta yiwa daddy godiya a kan irin ruƙo da ɗawainiyar da suka yi wa halumatun,abin har yaso ya bawa daddy kunya sai da ya ɗan nuna ɓacin ransa sannan baba ya dena yi masa godiyar. aunty ameena ce tazo suka gaisa tare da gabatar musu da abinci tare da abin sha.
Sun ɗan ci abincin ba laifi sannan suka shiga tattaunawa a kan abin da ya kawo su, gabatar da Alhaji Auwal daddy ya yi a gurin baba tare da yi masa bayani a kan ɗansa da yake nema wa auren halimatun,cikin gamsuwa da zancen na daddy baba ya kalle shi yace,
"Ai ni wannan maganar ba nida hurumi a cikin ta, HALIMATU dai ƴarka ce na damƙa muku ita halak malak bisa yarda da amincewar da na yi muku, sabo haka bani da wani hurumi a kan ta yanzu! na bar maka komai a hannun ka"
Daddy ba ƙaramin jin daɗin wannan karamcin da baba ya yi masa ya yi ba,nan take fuskar sa ta nuna alamar jin daɗin da ya yi sosai,fuskantar yana yin jin daɗin da daddyn ya yi ne ya sa ba ya ƙara kallon daddy tare da cewa,
"Karka damu Alhaji Ibrahim na yarda da kai ɗari bisa ɗari kuma na san zaka zaɓawa halimatu miji na gari wanda ya dace,don haka duk yadda kayi dai-dai ne hakan, sannan ina neman alfarmar a sanar da ni lokacin da aka saka na bakin nata domin in buga waya in sanar wa da ƴan uwan ta, sannan ga ƙanwarta HANNE itama an saka ranar bikin ta nan da wata biyu masu zuwa!".
Gyaran murya daddy ya yi tare da cewa,
"Eh to mun yanke shawarar cewa nan da shekara biyu za'a yi auren,kaga sannan ta ci kusan rabi a karatun ta idan ya so sai a saka lokacin bikin"
Jin jina kai baba ya yi tare da cewa,
"Eh to ban ƙi ta taka ba Alhaji,amma ina ga mai zai hana a yi auren kawai! Idan ya so ta ci gaba da karatun ta a ɗakin ta"
"Haka ne malam,sai dai momyn ta tace ta yi ƙan-ƙan ta da yawa,nan da shekara biyun idan Allah ya nuna mana ta ƙara yin ƙwari shi yasa take ganin a barshi a shekara biyun ya fi"
Ya faɗa yana murmushi,shi dai daddyn mukhtar Allah Allah yake yi baban halimatu kar ya amince da zancen shekara biyu nan,yana fatan a bar shi a ƴan watanni kawai.