← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 80

Sashe 49

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"An gama masoyi na zan yi maka babban suprise"

Wani ɗan ƙaramin ihu ya yi tare da cewa:
"Can't wait to see this suprise my love,daga yanzu ki fara shirin tarba ta".

"As you wish my love".

"I love you too my love"
Ya faɗa yana kashe mata murya.

Murmushi ta yi mai sanyi har yana jiyo sautin sa.
"ya school ɗin.?"
"Hope dai babu wata matsala ko.?"

"School lafiya ƙalau my love,gaskiya babu wata matsala sai dai........ta yi shiru ta kasa ƙarasa maganar da ta yi niyyar yi sabo da bata san yadda zai ɗauki maganar ba.

Gaban sa ne ya faɗi ya yi shiru yana sauraren ta,ganin taƙi cewa komai ya sa ya ce mata:

"Faɗa min my love! kar ki ji komai ina Jin ki kinji faɗa min.?"
Sai da ta ɗan yi jim tana tunanin ta faɗa masa ko kar ta faɗa masa.

Shirun da yaji ne ya sa gaban sa ya ƙara faɗuwa yana fargabar ko wani abun ne.katse tunanin nata ya yi ta hanyar cewa:
"Ke nake jira ki faɗa min my love".
Cikin nutsuwa ta buɗe baki tare da cewa:

"Ni dai gaskiya habibi na hijabs ɗin da nake sawa sun yi min girma da nauyi sosai kuma kaga akwai zafi, sannan shima nikaf ɗin bana jin daɗin saka shi,kawai zan ci gaba da saka dogwayen riguna na".

Ta faɗa tana marairai cewa kamar zata yi kuka.wata irin wawiyar ajiyar zuciya ya sauke,nan take ya haɗe ran sa kamar bai taɓa dariya ba yace:
"A'a my love kar muyi haka dake in dai ba so kike yi mu ɓata yanzu yanzun nan ba,baki san ke ɗin babbar kadara bace ba! ta yaya zan bari mutane su dinga kalle min lu'u-lu'u na ina ji ina gani su shiga cikin hurumi na!! kina da matuƙar darajar da kuɗi ba zasu iya siyamin ita ba,
Dan haka maganar dena saka babban hijab da nikaf ma bai taso ba,in dai ba so kike yi zuciya ta ta buga in mutu ba kowa ya huta,sabo da ina da kishi sosai a kan ki,kuma ni idan ina son abu toh ba na yi masa ruƙon wasa kin ji ko.?"

"ina fatan dai kin fahimta"

Girgiza kanta ta yi kamar yana ganin ta tare da cewa:

"Toh habibi ka yi haƙuri bazan sake ba"
Ta faɗa murya cike da rauni.

Ajiyar zuciya ya sauke yana jin nutsuwa na ƙara shigar shi haɗe da wata iriyar madarar soyayyar ta mara algus tana ƙara shiga cikin jikin sa da zuciyar sa har cikin ɓargon sa,wani irin tausayin ta ya ji sabo da bata yi masa musu akan duk wani abu da ya umarce ta ta yi ko da bata son abin kuwa,shi yasa kullum yake ƙara jin ta a cikin ransa sosai.

Buɗe baki ya yi cikin sanyin muryar sa yace:

"I'm sorry my love,dan dai baki saba sawa bane shi yasa, amma da zarar kin saba zaki dena jin nauyin hijab ɗin da zafi kin ji.?"
"Toh habibi in sha Allah"

"Yauwwa my love, Allah ya yi miki Albarka"

Ta amsa da:
"Ameen"
Daga haka suka yi sallama ya ce mata zai je ya yi wani aiki.

-----------------------------------------------------------------
-----------------------------------------------------------------

A ɓangaren su RUFAIDA kuwa bayan da suka tashi da safe har an bata kunu ta karya sai ga malam salihu ya shigo domin ya ƙara duba jikin Alhaji USAMA da kuma yi masa ban gajyar su ta dawowa jiya, bayan sun gaisa ne yake yi masa magana akan rashin lafiyar rufaidan tare da gaya masa abin da likitoci suka ce game da ciwon nata.

Girgiza kansa malam salihu ya yi tare da cewa:

"Gaskiya wannan maganar abin dubawa ce sosai,musamman ma idan muka yi la'akari da yan da ciwon nan ya same ta dare ɗaya,nima gaskiya na yarda da maganar da likitocin nata suka faɗi,kuma in sha Allahu zamu yi amfani da shawar da suka bayar".

Ya ci gaba da cewa:

"Akwai wani abokina malami ne sosai a wannan fannin,kuma ya ƙware sosai game da irin wannan larurorin,in sha Allahu zan yi masa magana game da hakan,idan yaso duk yanda muka yi da shi zan gaya maka".

Godiya sosai Alhaji USAMA ya yi wa malam salihu, sannan ya sanar da shi shawar da ya yanke akan siyar da motocin rufaida.
Shima malam SALIHU ya yi na'am da zancen sosai in da yake cewa:

"Wannan shawara ce mai kyau sosai,toh amma mai zai hana a yiwa alhaji ma'aruf magana tun da naga shi yana harkar siyar da motoci".

"Haka ne gaskiya, wallahi na manta da shi shafi,dan Allah ka yi masa magana sai muji abin da zai ce,idan ya so sai yazo gida ya gansu".

Girgiza kai malam salihu ya yi tare da cewa:
"To shikenan babu damuwa bari naje na same shi tun kafin ya fita"
Ya faɗa yana ficewa daga cikin gidan.

Fitar sa babu daɗewa
Aminu ya yi sallama tare da shigowa cikin parlon ya nemi waje ya zauna a kan sofa,gaishe da daddyn ya yi tare da cewa:

"Daddy yanzu zan je kasuwa wajen siyar da ragowar sarƙar da ƴankunnen"

"Toh shikenan Allah ubangiji ya tsare,ka kula sosai kaji".
Murmushin ya yi tare da cewa:
"Toh daddy in sha Allah".
Har ya juya zai fita ya tsinkayo muryar daddy yana cewa:

"Mun yi magana da malam salihu akan maganar sai da motocin nan,sai ya bani shawarar a yiwa alhaji ma'aruf magana tun da shi yana yin harkar".

"To shikenan daddy hakan ma ya yi sosai kaga an huta,in ya so sai yazo ya gansu ko.?"

"Haka muma muka ce ni da malam salihu"
Daga haka suka yi sallama ya juya ya tafi.

Ɗakin RUFAIDA ya shiga domin ya duba ta,ko da yaje ya iske tana ta bacci, addu'a ya yi mata ya tofa mata sannan ya fito daga cikin ɗakin ya dawo parlo ya zauna.

Bai daɗe da zama ba umma ta shigo ɗakin ɗauke da madai dai cin try a hannun ta ta ajiye a kan center table ɗin da yake gaban sa,tsuguna wa ta yi ta ɗauki cup ta haɗa masa tea da bread ta tura masa gaban sa tare da cewa:

"Bismillah ga shayi nan na haɗa maka"
Murmushi ya yi tare da cewa:
"Na gode sosai"
Ya faɗa yana ɗaukar kofin shayin tare da kaiwa bakin sa ya yi bismillah ya fara sha.

Hira suke yi a tsakanin su jefi-jefi har ya gama shan tea ɗin.

Sallamar malam salihu suka jiyo tun daga can ƙofar gida,ta shi ya yi tare da ɗaukar sandar sa ya dogara yana tafiya a hankali har ya kai ƙofar gidan in da su alhaji ma'aruf da malam salihu suke tsaye.
Hannu ya basu suka gaisa sannan alhaji ma'aruf ya yi masa ya jiki,amsawa ya yi tare da ƙara yi wa Alhaji ma'aruf ɗin bayani a kan maganar siyar da motocin idan zai siya.
Amsawa ya yi tare da cewa:
"Maganar da ta kawo ni kenan alhaji domin nazo na gansu a yi ciniki"

"Haka ne! bismillah muje ka gansu"
Ya faɗa tare da yi musu jagora har cikin harabar gidan.
Bayan ya gansu yaga kuma manya ne kusan duk sababbi ne ya sa bai yi ƙasa a gwiwa ba ya siye su a kan farashi mai tsada.
Nan take suka amince da maganar sa domin farashin ya yi sosai babu cuta babu cutarwa,sallama suka yi ya karɓi account numbern su akan zai yi musu transfer in yaso sai yazo ya tafi da su.

Daga haka ya juya ya tafi ya barsu shi da malam salihu a gurin,bayan tafiyar sa ne malam salihu ya dube shi tare da cewa:
"Gaskiya ciniki ya yi kyau sosai, Allah ubangiji ya sa albarka a cikin kasuwan cin da za'a fara"

"Ameen Ameen malam"
Kallon malam salihu ya yi tare da cewa:
"Ka samu malamin kuwa.?"

"Af wallahi kaga na sha'afa na manta shaf ban faɗa maka ba,na same shi harma mun yi magana da shi, yace min zai zo gobe idan Allah ya kaimu ya ganta domin yau yana da ayyukan da zai yi".

"To shikenan babu damuwa Allah ya kaimu goben,ai da yau da goben duk ɗaya ne a gurin ubangiji".

Daga haka malam salihu ya yi masa sallama ya tafi,ya yinda shi kuma ya dogara sandar sa ya koma cikin gida.
Wannan kenan....✍🏻✍🏻

Ina matuƙar godiya da addu'o'in ku a gare ni, ku ɗin na musamman ne a cikin zuciya ta, ina matuƙar alfahari da ku ƙwarai da gaske, Allah ubangiji ya saka muku da mafificin alkhairin sa,ya biya muku buƙatun ku na Alkhairi...🙏🏻🙏🏻

Daga alƙalamin FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)...✍🏻✍🏻

Share fisabilillahi.

Game buƙatar wannan littafin tun daga farko har zuwa in da aka tsaya ya tun tuɓe ni ta wannan numbern wayar👇🏻

08162055134.

💝💞HALIMATU💝💞

(Love, sacrifices, destiny & betrayed)

💝💞💝💞💝💞💝💞

Story & Writing

By

FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)....✍🏻✍🏻

Ƙarƙashin jagorancin

(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)

Golden pens.......✍🏻✍🏻

💝💞💝💞💝💞💝💞

A 2024 novel

💝💞💝💞💝💞💝💞

Pages____________63&64

________________bayan kwana biyu shirye-shiryen dawowar MUKHTAR halimatu take ta yi ba kama hannun yaro, ita ma momy a nata ɓangaren shirin dawowar daddy take yi,domin duk kusan lokaci guda za su dawo.
Yau jirgin su mukhtar ya sauka a Aminu Kano international airport,da yake da asuba jirgin nasu ya sauka shi yasa bai takurawa su momy ba, ya ce ba sai sun zo ɗaukar sa ba nura abokin sa zai zo ya ɗauke shi.
Hakan kuwa a kayi jirgin su yana yin landing ba da ɗewa bayan sun fito ya hangi nura jikin motar sa tsaye yana ta waige waigen in da zai ganshi,bai yi aune ba ya ji an rungumo shi ta baya har yana shirin faɗuwa,jujowar da zai yi suka yi ido biyu da mukhtar yana ƙyalƙyala masa dariya.

"Amma fa gaskiya ka shamma ce ni da yawa wallahi,ni ina nan ina ta faman duba ka ashe ka yimin wayo ka zagayo ta baya na"
Murmushi mukhtar ya yi tare da cewa:
"Suprise na yi maka ai"
Duka nura ya kai masa ya kauce yana dariya har da riƙe ciki tare da cewa:
"Kar ka yiwa mai sona asara wallahi"
"Oh! wato ni bani da mai sona kenan.?"
"A'a ni ban ce ba ka rufa min asiri gurin hafsa"
Ya faɗa yana kama bakin sa,dariya nura ya yi tare da cewa:
"Muje mu kwaso kayan"
Chapter 49 · 0% Book details