Sashe 35
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Flour ta ɗakko ta tankaɗe ta zuba ta a bowl ɗin standard mixer,sannan ta zuba butter da kwai da madarar gari da yeast da salt kaɗan da suger da vanilla extract ta zuba ruwa madai dai ci tare da kunna mixer ɗin ta kwaɓa mata na 20 minutes ko 15 minutes,idan baka da standard mixer sai ka yi amfani da hannun ka ka buga flour na 20 minutes ko 30 minutes.
Bayan tagama beating ɗin flour ta ciro daga cikin mixer ɗin ta ɗora akan marble ta bar baɗa flour tare da neading dinsa na 5 minutes.
Ragowar filling da MOMY ta yi meat pie ta ta ɗakko a cikin fridge ta ajiye a gefe,gwan gwanin gashin bread ta ɗakko guda uku tare da shafa butter a cikin su, yanko flour ta yi tare da murzawa ta yi tsawo da faɗi sannan ta zuba filling ɗin a tsakiya ta nannaɗe ta saka a cikin gwan gwanin.
Haka tayi tayi har ta gama gaba ɗaya,bayan ta gama ne ta ɗakko su gaba ɗaya ta jere su a cikin oven,dama ta kunna oven ɗin tun ɗazu yayi ɗumi sannan ta kashe sabo da yayi saurin ta shi.
Gyara kitchen ɗin ta hau yi domin baba ladi bata nan,sai da ta wanke komai tsaf ta kife sannan ta koma ta kunna oven ɗin ta, sabo da bread ɗin ta ya tashi kuma har yanzu oven ɗin yana da ɗumi.
Ci gaba ta yi da goge gogen ta,ba ita ta bar kitchen ɗin ba sai da bread ɗin ya gasu sannan ta ciro su ta saka kowane a cikin leda ta rufe.
Lokacin da ta gama yamma tayi,kuma damma tana da saurin aiki sosai,abin cin ta kwashe tare da kaiwa dinnig ta jere su, shi kuma na MUKHTAR ta kai parlon baƙi ta jere masa nasa a dining table ɗin parlon.
Up stairs ta haye domin zuwa ta yi wanka da alwala,sabo da ana gab da kiran sallar magrib.
Wannan kenan.......
Ina matuƙar godiya da addu'o'in ku a gare ni, ku ɗin na musamman ne a cikin zuciya ta,ina yi muku fatan Alkhairi a koda yaushe Allah ubangiji ya saka muku da mafificin alkhairin sa,ya biya muku buƙatun ku na Alkhairi..........
Daga alƙalamin
FATIMA BINTU ABDULLAHI (UMMU AYSHA)................✍🏻
Share fisabilillahi..
08162055134........
💝💞HALIMATU💝💞
(Love, sacrifices, destiny & betrayed)
💝💞💝💞💝💞💝💞
Story & Writing
By
FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)...........✍🏻
Ƙarƙashin jagorancin
(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)
Golden pens...........✍🏻
💝💞💝💞💝💞💝💞
A 2024 novel
💝💞💝💞💝💞💝💞
Pages_________43&44
"HALIMATU"
A ɓangaren HALIMATU kuwa, lokacin da ta haye up stairs domin ta yi wanka da alwala, direct toilet ta wuce ta yi wanka tare da yin alwala,kayan da ta cire ta jefa su a cikin washing machine sannan ta ɗaura towel a jikin ta ta fito daga cikin toilet ɗin.
Goge jikin ta ta yi tare da saka simple doguwar riga ta saka hijab tare da haye wa kan sallaya ta tada salla.
Bata tashi a kan daddumar ba sai da ta yi sallar isha'i.miƙewa ta yi ta ja kujerar jikin mirror ta zauna akai, sannan ta ɗakko haɗaɗɗen lotion ɗinta mai daɗin ƙamshi ta shafe jikin ta da shi.
Turarukan shafawa a jiki ta jawo ta mulke jikin ta da su, powder ta shafa a fuskar ta tare da eyeliner, sannan ta kawo red lipstick ta shafa a tattausan leɓen ta.
Brush ɗin gyara gira ta ɗakko ta gyara girar ta,daga bisani ta ɗakko mascara ta shafe ta a mayalwatan gashin idanun ta.
Kumb ta ɗakko ta gyara gashin ta sosai tare da fesa masa hairs spray masu daɗin ƙamshi , sannan ta saka ribom ta ɗaure gashin daga ƙasa ta sake shi har ƙugun ta.
Ba ƙaramin kyau HALIMATU ta yi ba,gashin nan na gaban goshin ta ya kwanta lub lub gwanin ban sha'awa ,sai fuskar ta ƙara fitowa ɗas.
Royal blue ɗin abaya ta ɗakko ta saka, sannan ta ɗakko wasu ƴan kunne da sarƙa suma blue ta saka.rolling ɗin mayafin abayar ta yi,ta yi matuƙar yin kyau sosai,hakan ya bawa dogon gashin kanta damar fitowa yana reto.
Turaruka masu sanyin daɗi ta fesa a jikin ta, sannan ta ɗauki awarwaro da zobe da agogo ta saka a hannayen ta.
Ba ƙaramin haɗuwa ta yi ba,gaba ɗaya ɗakin wani irin ƙamshi ne yake tashi mai daɗi, takalmin ta ta ɗakko hills blue colour ta saka, ba ƙaramin kyau ya yi wa farar ƙafar ta ba.
Sallamar MOMY ta ji tare da shigowa cikin ɗakin tana ƙare mata kallo, rungume ta MOMY ta yi tare da cewa:
"Iyye ma sha Allah doughter kin yi kyau sosai! Maza kije yazo tun ɗazu yana jiran ki a parlon baƙi,ki kula da kan ki sosai kin ji doughter!!"
Cike da jin kunyar MOMY ta amsa da"to"
Juya wa MOMY ta yi tare da shigewa side ɗin ta,ita kuma HALIMATU ta fito tare da sauka ƙasa ta nufi parlon baƙin cike da nutsuwar da ta zame mata jiki.
Sallama ta yi cikin daddaɗar muryar ta tare da kutsa kai ciki parlon,amsa wa MUKHTAR ya yi tare da ɗago da kansa ya zuba mata mayun idanunsa.
Ƙarasowa ta yi a hankai kamar bata son taka ƙasa ta zo ta durƙusa a gaban sa ta gaishe shi cike da ladabi da biyayya.
Wani irin sanyi ya ji ya ratsa zuciyar sa tun daga kan Babban ɗanya tsan ƙafar sa zuwa cikin kwakwalwar kansa,bai san lokacin da ya sauke a jiyar zuciya ba kamar wanda ya sha kuka ya ƙoshi.
Wata iriyar nutsuwar da ya rasa shekara da shekaru ya ji tana sakko masa a hankali,sabo da duk lokacin da zai ga HALIMATU ko ya ji Muryar ta yana tsintar kansa a cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.
Shirun da taji ne yasa ta ɗago kanta a hankali domin taji shiru bai amsa mata gaisuwar ta ba,karaf suka haɗa idanu dashi nan take ya sakar mata wani irin lallausan Murmushi,wanda kana ganin sa ka san na musamman ne yake tafe daga cikin zuciyar masoyi.
Bata san lokacin da murmushi ya suɓuce wa fuskar ta ba,gaba ɗaya dimple ɗinta guda biyu sai da suka lotsa,hakan ba ƙaramin tafiya da imanin MUKHTAR yake yi ba,domin salon soyayyar da MUKHTAR yake nuna mata yana burgeta sosai da sosai.
"My love ya kike? ya gida? ya school...?
"Fatan na same ki lafiya..?
"Lafiya ƙalau yaya MUKHTAR"
"Ya su daddy da MOMY da MEENA..?
"Da fatan kowa yana lafiya..?"
MUKHTAR yace:
"Wallahi kowa yana nan ƙalau suna gaishe ku"
Cike da kunya tace "muna amsawa".
Miƙe wa ta yi ta nufi dining tare da ɗakko ruwa haɗe da cup tazo gaban sa ta durƙusa tare da tsiyaya masa ruwan,hannu ta sa ta ɗakko cup ɗin ruwan ta miƙa masa tare da cewa:
"Yaya MUKHTAR ga ruwa ka sha!"
Gaba ɗaya ji ya yi duniyar tana juya masa yana shawagi a sararin samaniya,wai yau shi ne aka durƙusa har ƙasa ake bashi ruwa cike da ladabi,lallai an ce mahaƙurci mawadaci,gashi ko auren ma ba'a yi ba amma ya fara ganin canji sosai, toh ina ga kuma an yi auren!!.
Karɓar ruwan yayi tare da kai wa bakin sa ya yi bismillah ya kurɓi kaɗan sannan ya ajiye sauran.kallon ta ya yi tare da cewa:
"Thank you my love,ni yunwa nake ji ba ƙishirwa ba! Ina fatan kin haɗa min dinner da kan ki ko..?"
Cike da murmushi tace:
"Na haɗa maka dinner yaya MUKHTAR,kuma nice na haɗa maka da kai na! Taso muje na yi serving ɗin ka".ta ƙarasa maganar tana miƙe wa tsaye.
Tashi ya yi shima tare da bin bayan ta suka nufi dining table ɗin,cike da girmama wa ta ja masa kujera ya zauna kamar yadda ta ga MOMY tana yi wa daddy,kujerar da take facing ɗin tashi ta ja ita ma ta zauna.
Ɗagowa ta yi karaf suka haɗa ido! Murmushi ta sakar masa tare da cewa:
"Faɗa min me kake so na zuba maka..?
"Na baki zaɓi my love,ki zuba min duk abin da kika ga ya dace! domin duk abin da ya fito daga hannun ki na san special ne my love,so go a head".
Murmushi kawai ta yi tare da buɗe food wamers ɗin,wani irin daddaɗan ƙamshin abinci ne ya bugi hancin MUKHTAR,nan take yawun sa ya tsinke tun ma kafin yaci abincin.
Shinkafa ta zuba masa a kyakkyawan plate,tare da zuba masa cows low a gefe,bowl ta ɗauka ta zuba masa haɗaɗɗiyar stew ɗin da ta ji naman kaza.
Bowl ta ɗakko mai kyau ta zuba masa yoghurt fruit salad tare da saka masa spoon a kai.tura masa ta yi gaban sa tare da cewa "bismillah yaya!!".
Wani irin girma da faɗi ya ji kansa ya yi,yana mamakin wai shi ne yau ake gatan ta shi.
"Please yaya MUKHTAR kaci abinci kar yayi sanyi!"
HALIMATU ta faɗa tare da turo ɗan ƙaramin bakin ta.
Murmushi kawai ya yi ba tare da yace komai ba,domin idan ya daka ta HALIMATU zaucewa kawai ze yi.
Bismillah ya yi tare da fara cin abincin,wani irin lumshe idanun sa yayi sakamakon daɗin abincin da ya ratsa har cikin kwakwalwar sa, gaskiya idan ya auri HALIMATU ya more sosai da sosai,shi yasa a kullum dare da rana yake addu'ar Allah ubangiji ya mallaka masa ita .
Zage wa ya yi yaci abincin sa sosai,bayan ya gama ya jawo fruit salad ɗin sa ya fara sha, spoon ɗin farko da ya yi sai da kunnuwan sa suka motsa tsabar daɗi,ƙura mata ido kawai yayi tare da ci gaba da shan fruit salad ɗin. Sai
Kasa magana ya yi sakamakon garɗin madara da garɗin yoghurt ga kuma ƙamshin vanilla flavour da kuma sanyin da ya ratsa cikin zuciyar sa.
Bayan ya gama ne ya ɗan kurɓi ruwa kaɗan tare da yin hamdala ga Ubangiji,tissue ta ya go ta miƙa masa ya karɓa ya goge bakin sa.
Kallon sa ta yi tare da cewa:
"In zuba maka tea ɗin..?"
Zaro idanun sa ya yi tare da cewa:
"Haba my love,so kike yi cikina ya fashe..?
Ya faɗa yana jifan ta da wani irin kallon da ta kasa fassara na mene ne.