Sashe 12
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jirgin yana sauka babu daɗewa aka buɗe shi mutane suka fara fitowa daga cikin sa,nan take ya mai da duban sa ga jerin masu fitowa ko zai hango dadyn sa.yana tsaka da duba passingers ɗin ne ya hango dadyn sa tare da wani mutumi suna sakkowa,nan da nan baiyi ƙasa a gwiwa ba ya nufa shi.
A ɓangaren su momy kuwa suna ganin jirgin ya sauka ƙasa suka fito daga cikin motar suka tsaitsaya a bakin motar,su hafiz kuwa suna hango dadyn su suka nufi inda yake da saurin su.kusan a tare suka nufi gurin da hafiz,suna zuwa basu yi wata wata ba suka rungume dadyn su tare da cewa "welcome dady"cike da farin ciki dady ya rungume su yana shafa kansu yace "yauwa my boys".
Shima hafiz a b'angaren sa rungume dadyn sa yayi yana masa sannu da zuwa,cike da farin ciki dadyn nasa shima ya rungume shi yana amsawa.Alhaji auwal mahaifin hafiz ya dubi Alhaji Ibrahim wato dadyn su hafiz yace"ma sha Allah waɗan nan duk yaran kane??" dady yace "ae yara na ne,akwai kuma autar su mace".ya faɗa yana murmushi.
Dady ya dubi su hafiz yace"ku gaisa da amini na,shine wanda nake yawan baku labarin sa, kusan tare muke tafiye-tafiye da shi".cike da ladabi suka gaishe shi, tare da yin musabaha da muktar.
Alhaji auwal ya dubi dady yace"wannan shine dana muktar da nake baka labari,yana da aure da yaran sa guda biyu,su uku Allah ya bani.shikad'ai ne namiji sai ƙannen sa mata guda biyu,mai bi masa tana aure a abuja, sai kuma auta ita tana nan gida" dady yace ma sha Allah, Allah ubangiji ya raya mana su ya albarkaci rayuwar su.gaba ɗaya suka amsa da ameen.
Farouq ya dubi dadyn su yace"dady mu tafi ga su momy can suna jiran ka".yace"okay to ku muje".gaba ɗayan su suka ɗun guma zuwa wajen da suka yi parking ɗin motocin su,tun kafin su ƙara so su momy suka hango ta howar su, da gudu auta ta nufesu ta yi gurin dady,tana zuwa ya buɗe mata hannu ta faɗa jikin sa ya rungume ta tare da ɗaukar ta cak suka ƙarasa gurin da su momy suke .
Momy ta du'ka tayiwa dady barka da zuwa tare da abokin sa,suka amsa fuskar su a sake, ita ma HALIMATU dur'kusawa tayi har ƙasa ta gaida dadyn, sannan ta juya a dur'kushen ta gaida mahaifin mukhtar.dady yace "yau wa my daughter,da fatan kinzo lafiya??"tace lafiya k'alau dady".
Jin muryar da yayi ne yasa ya d'ago da sauri daga latsa wayar da yake yi ya dubi in da yake jin muryar,gabansa ne ya fad'i sakamakon ganin HALIMATU !! Ido ya tsura mata yana tunanin inda yasan fuskar nan da kuma daddad'ar muryar nan.
Ganin kallon da yake mata ne yasa dady yace mata"daughter baki gaida yayanki mukhtar ba"cike da ladabi ta dur'kusa ta gaishe shi da daddad'ar muryar ta.amsawa yayi yana sake duban ta. acikin zuciyar sa mamaki yake yi, sabo da yasan yarin yar da ya sani mai kama da ita 'yar ƙauye ce mai tallan gyad'a,ita kuma wannan 'yar birni ce kuma gata 'yar gayu sosai.
Gaba-daya kansa ƙullewa yayi, ya rasa irin kalar tunanin da zai yi.yana tsaka da tunanin ne ya tsinkayi muryar dady yana cewa"ku shiga mota mutafi kar magariba tayi mana a nan".suka ce "to". nan su hafiz suka yiwa mukhtar sallama tare da dadyn sa suka shige cikin mota suna jiran dady,dama su momy tuni sun shige motar su.
Shima a ɓangaren mukhtar motar sa ya shige yana jiran dadyn sa.akabar su dady tsaye agurin suna magana,Alhaji Auwal ya dubi dady yace"Alhaji ina kuka samu kyakkyawar yarinya nutsatsiya mai hankali haka??"murmushin manya dady yayi yace"ayya wai HALIMATU kake nufi!! ai ita ɗin 'yace a wajen mu,domin mahaifiyar ta yar matata ce,uwarsu ɗaya ubansu ɗaya.mahaifiyar ta tarasu tun tana ƙarama, gashi ta taso agurin matar uba tana muzguna mata, wannan dalilin ne ma yasa momyn yara taje ta ɗakko ta daga ƙauyen haɗeja dake Jigawa,da ƙyar mahaifin ta ya yadda ya bamu ita,yanzu haka zancen da nake yi maka ta dawo wajenmu da zama.
mahaifin ta ya dan'ka mana amanar ta,ya bamu ita halak malak.yanzu haka ta gama secondry school ɗin ta ,shine nake so na sama mata gurbin karatu a b.u.k" ya ƙarasa maganar yana mai kallon abokin nasa........
Alhaji Auwal yace" ikon Allah, Allah ubangiji ya jik'an mahaifiyar ta,mu kuma Allah ya taya mu ruƙo, sannan ina neman alfarma a gurin ku alhaji"ya faɗa yana ƙara duban dady.dady yace"to Allah yasa bata fi ƙarfi naba, faɗi muji"ajiyar zuciya ya sauke sannan yace "ina nemawa ɗana mukhtar auren HALIMATU!!".
Da sauri dady ya d'ago da kansa ya dubeshi yace "mukhtar kuma??,amma ai kace min yana da aure har da mata da yara biyu!!".sake d'ago da kansa yayi a karo na biyu ya kalli dady yace"ƙwarai kuwa mukhtar yana da mata,amma auren ne kwata kwata baya jin daɗin sa,wallahi matar nan tasa sai a hankali.bayajin daɗin zama da ita sam,mu kan mu da muke matsayin iyayen sa bata girmama mu.shiyasa nake so in nema masa auren HALIMATU, sabo da na yaba da hankalin ta da nutsuwar ta".
Ya cigaba da cewa"da naso na yi shiru da maganar har zuwa gaba,amma kuma sai nayi tunanin kada wani yazo ya rigamu,shiyasa kawai nace bari in gaya maka, Sabo da masu iya magana sun ce da zafi zafi ake bugun ƙarfe!!"
Dady yace "gakiya kazo da babban al'amari,amma in sha Allahu zanyi wa momyn su maganar,idan yaso duk yadda muka yi zan gaya maka.sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba"ya faɗa yana duban sa.
Alhaji auwal yace "wanne Irin hanzari ne kuma??"dady yace "mahaifiyar yarinyar nan tana da buri tayi karatu mai tsawo,shiyasa ma yanzu nake son ta zana jam domin samun gurbin karatu a jami'a"Alhaji Auwal yace "indai wannan ne babu matsala in sha Allah, tun da shima mukhtar ɗin yana lecturing a b.u.k, kaga koshi sai ya sama mata gurbin karatu a can ɗin"
Dady yace"Alhmdllhi,kaga fad'uwa ma tazo da zama shikenan,to Allah ubangiji ya tabbatar mana da Alkhairi,in sha Allahu zaka jini"ya ƙara sa maganar tarda miƙa masa hannu su kayi musa baha,daga haka kowa ya shiga mota suka tafi.
Suna shiga gida ana kiran sallar magrib, ba tare da b'ata lokaci ba kowa yayi alwala suka ɗun guma zuwa masallaci.su kuma matan suka yi abarsu a gida.basu suka dawo gidan ba sai da aka idar da sallar isha'i,suna shigowa gaba ɗayan su suka ɗun guma zuwa dining table,kowa ya ja kujera ya zauna.
Bayan an ƙara gaisawa ne momy ta tashi ta yi saving ɗin dady, ta zuba nata itama, sannan tayi saving ɗin sauran suma,kowa abin da yake so dashi aka yi saving ɗinsa.bayan sun gama ne suka ɗan taɓa hira,dady yana tajan HALIMATU da hira dan ta sake da shi.
Mi'kewa dady yayi yace musu zai je yayi wanka ya kwanta ya huta,yana gama faɗi ya juya ya haye sama.itama momy tashi tayi ta bi bayan sa.bayan wucewar momy suma gaba ɗayan su suka mi'ke,mazan suka nufi part ɗin su,ita kuma HALIMATU ta kama hannun auta suka haye sama.d'akin auta suka nufa tayi mata wanka ta shirya ta cikin kayan bacci tayi mata addu'a ta kwantar da ita ta, glove ta kashe mata sannan ta jawo mata kofar d'akin ta fita
'Dakin ta ta nufa tayi wanka tare da yin brush, sannan ta fito ta shirya cikin kayan bacci ta fesa turare kaɗan ta haye gado ta yi addu'a ta kwanta . wannan kenan............
A ɓangaren su mukhtar kuwa suna isa gida suka samu kyakkyawar tarb'a a wajen mahaifiyar sa hajiya zainab,bayan sunyi sallar magriba sai da ya tsaya aka yi dinner da shi sannan ya tashi yace musu zai tafi, ƙanwar sa laila tace"yaya tun yanzu zaka tafi??"."yace auta yanzu zan wuce wallahi na gaji,ina so ne naje na huta".
Tace "tom shikenan yaya ka gaida gida Allah ubangiji ya hutar da gajiya,ka gaishe min dasu sahal".yace"amin auta zasuji in sha Allah".daga haka yayi wa su momy da dady sallama ya fice daga cikin gidan ya shiga motar sa ya kama hanyar gida.
Yana isowa gida yayi parking ɗin motar sa tare da fitowa ya nufi cikin parlon,yana shiga yaji parlon shiru ga yaran sa kwance a ƙasa sun yi bacci.a gefe guda kuma abinci ne aka ci aka zuzzubar a gurin,ga plates ɗin abinci nan da aka ci aka bari a wajen .wani ƙololon abu yaji ya tokare masa zuciya,ya rasa wacce irin mata Allah ya jarabce shi da ita.du'kawa yayi ya kwashe plates ɗin gaba ɗaya ya kai su kitchen, sannan ya dawo ya kashe wutar parlon da ta kitchen ɗin,ya ɗauki yaran sa ya haye sama da su.
'Dakinsu ya nufa da su ya canja musu kaya zuwa kayan bacci,sannan ya kwantar da su yayi musu addu'a ya kashe musu glove ya jawo musu ƙofa.d'akin sa ya nufa ya faɗa toilet yayi wanka, ba tare da b'ata lokaci ba ya shiya cikin pajmas milk colour.fitowa yayi ya nufi d'akin rufaida ya tura Kofar tare da yin sallama,cike da mamaki yake kallon ta,domin kwata kwata bai yi tunanin idon ta biyu ba.
Wayar hannu ta da take daddan nawa ta ajiye tare da juyowa ta zuba masa idanu tace"an dawo kenan"daga haka taja bakin ta tayi shiru bata ƙara ce masa komai ba.mukhtar ya ƙara duban ta a karo na biyu ya ga ta cigaba da danna wayar ta,ya dubi d'akin yagan shi gashi nan dai sai a hankali,domin babu wani gyara a tattare da shi, ita kanta ɗaurin ƙirji ne aka jikin ta.
Kansa kawai ya girgiza,tare da ce mata "ki kawo min coffee yanzun nan"daga haka yayi ficewar sa.ranta ba ƙara min ɓaci yayi ba,haka kawai tana cikin hutawar ta zai zo yakce ta kawo masa wani coffee.dolen ta ta mi'ke ta sauka ƙasa ta haɗa masa, ɗauka tayi ta kai masa har d'akin sa,sai da tayi sallama sannan ta shiga, sabo da ya hana mata shigo masa ɗaki ba tare da sallama ba.