Sashe 8
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana cikin wannan halin ne ta samu cikin HALIMATU. a lokacin ƙanwarta maryam tana da yara biyu maza,a haka tayi ta rainon cikin ba yadda inna laure batayi ba don ganin cikin nan ya salwanta amma burin ta bai cika ba.da yake Allah ya ƙaddara sai an haifi cikin.
Kusan lokaci guda suka haihu da maryam,ita maryam ta haifi farouq ita kuma ta haifi HALIMATU.Bayan ta haihu ne ta kamu da rashin lafiya,yau da lafiya gobe babu lafiya har ciwon ya kwantar da ita..........
HALIMATU na da shekara shida a duniya mahaifiyarta ta rasu .maryam tayi kuka ba kaɗan ba.
Bayan anyi sadakar bakwai ne maryam taso ta tafi da HALIMATU amma malam ummaru ya hanata tafiya da ita.
Wannan
kenan...........
Cigaban labari
Zaune yake a katafaren ofice ɗinsa wanda yayi mutuƙar haɗuwa,yana ta faman tattare takardu yana sauri, sabo da yana son yaje gidan gonar sa ya duba shi ya gani dan ya kwana biyu bai jeba.
yana fitowa saka tariyar sa ta taso tana wani karai raya tana kashe murya tace"sir kana da baƙin da suke son ganin ka" ko kallon ta beyi ba yace"su jirawo zuwa gobe,dan yanzu ina da uzuri"
Daga haka yayi ficewar sa ya barta tsaye a gurin .yana fitowa ba tare da b'ata lokaci ba ya buɗe tsadaddiyar motar sa ƙirar jeep ya kunna ya ƙara gaba.sai da yayi tafiya mai nisa sannan ya shigo ƙauyen ya kama hanyar gidan gonar.
Lokacin da ya gama zagaye a cikin gidan gonar ya sallami ma'aikatan ya shiga motar sa ya fito daga gidan gonar.a hanyar sa ta komawa ne ya tsaya a inda ya saba tsayawa domin yin sadaka.
Mutane suna ganin ya faka motar sa suka zo suka lullub'e motar suna jiran ya fito.yana fitowa ya fara raba musu kuɗi suna ta saka masa albarka.
Lokacin da ya gama rabon sadakar ne yaje inda yake siyen gyad'a yayi sadaka sai ya tarar mai gyad'ar bata zoba.ya kasa hak'uri ya tambayi mutanen wajen suka ce masa ai ta kwana biyu bata zoba.
Yayi shiru ya rasa mai yake masa daɗi.da yaga tsayuwar bazata yi masa ba, gashi kuma yamma tayi kawai sai ya juya ya shiga mota ya kama hanya ya tafi.
Wannan kenan...............
Ina mu'kar godiya da addu'ar ku a gare ni tare da fatan alkhairi,ku ɗin na daban ne a gareni kuma masoyan ƙwarai,ina alfahari da ku na gode sosai........
A cigaba da yimin ruwan comments,nikuma shine zai bani ƙwarin gwiwar yi muku update a kai akai.
FATIMA BINTU ABDULLAHI( UMMU AYSHA)....................✍🏻
08162055134.
💝💞 HALIMATU 💝💞
(Love, sacrifices, destiny & betrayed)
💝💞💝💞💝💞💝💞
Story & Writing
By
FATIMA BINTU ABDULLAHI (UMMU AYSHA)
Ƙarƙashin jagorancin
(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)
Golden pens...............✍🏻
💝💞💝💞💝💞💝💞
2024 novel
💝💞💝💝💞💞💝💞
Page_____________11&12
A ɓangaren HALIMATU kuwa bayan sun idar da sallar la'asar ɗin sai suka sakko ƙasa.babu kowa a parlon, ta nemi waje ta zauna akan kujera,zaman ta ke da wuya ta jiyo motsi daga cikin kitchen ɗin su.
Nan take ta mi'ke tayi hanyar kitchen ɗin take ta kutsa kai ciki, tana shiga ta iske momy da baba ladi suna faman haɗa dinner .tace momy "sannu da aiki"tace yauwwa sannu daughter ai gwara ma da kika sakko dan da baki sakko bama yanzu nake da niyyar na kirawo ki.daga yanzu tare zamu dinga shiga kitchen da ke, sabo da ina so ki koyi girke girke kala-kala"
Cike da murmushi "tace to momy nima ina so na koyi abubuwa da yawa".kar ki damu daughter zaki kowa kinji"ta gyad'a mata kai tare da murmushi a fuskarta.halimatu ta ƙarasa India baba ladi take tsaye tana gyaran kayan miya tace "sannu baba"
"Tace yauwa HALIMATU na, an fito ko??"tace ae baba na fito nima ina so na tayaku aikin,yanzu dame zan fara!!"baba tace"to bari na baki ki ƙarasa gyaran kayan miyan ni kuma sai na yanka kayan lambu,amma ki rinƙa lura da abubuwan da muke yi kinji"tace to baba"
Nan suka cigaba da aikin su bayan sun gama HALIMATU da baba Laure suka kwashi food wamers ɗin suka jere su akan dining table.baba ta tafi d'akinsu bayan ta ɗauki nasu abin cin.
Ita kuma HALIMATU momy tace mata ta tafi taje tayi wanka tayi sallar magrib.daga haka suka hau sama kowa ya nufi d'akin sa.
***************************************
A ɓangaren su inna laure kuwa bayan sun gama jimami da koke koken abin da ya faru suka ajiye akan kowa yaje ya samo kuɗi domin zuwa inda za'a sama masu mafita.tunda zuciyar su ta riga da ta ƙe'kyashi sun yi nisa basa jin kira,sun manta Allah ubangiji shi ne mai kowa mai komai.shike tsara al'amarin sa duk yanda yaso.
Tana tafe tana ta sa'ke-sa'ke a cikin zuciyar ta, ganin duk irin abin da tayi sai da wannan muguwar matar tayi galaba a kaina.ai dole ne ma na sake sabon shiri dan wallahi ko zanyi yawo tsirara sai na kassara rayuwar su.
Yanzu gashi nan ɗauke HALIMATU da tayi bai ishe ta ba har sai da tayi sanadiyar da ta rabani da malam.wallahi maryam sai kinsan kinyi da laure,dan ba'a tab'ani a zauna lafiya.yanzu dole inje duk inda zanje na samo kuɗiin nan, sabo da ayyukan da za'ayi min.gashi yanzu aiki ya ƙaru saboda dole nasa a yiwa malam kiranye ya dawo gida.
duk wannan zancen a cikin zuciyar ta takeyin sa.tana tsaka da tunanin ne ta jiyo hargowa da zage-zage na tashi.nan da nan tayi duba da inda take jiyo hargowar,
gabanta ne yayi mummunan fad'uwa saka makon hango buba da jama'ar sa tafe.kuma ga dukkan alamu daga gidan ta suke tafe.
Ai batasan lokacin da ta runtuma a guje ba, tayi cikin duhun shukar gero ta boye a ciki ta,jikin ta sai rawa yake yi.bata ankara ba taji lema a jikin ta, zanin jikin ta ya ji'ke shar kaf ashe fitsari ta saki bata sani ba,saboda tsabar tashin hankalin da shiga.
Tana nan boye cikin gero taji sunzo zasu wasu ce buba na cewa"lallai matar nan wato ni zata rai nawa hankali har nazo neman ta bata nan.to wallahi duk ranar da na haɗu da ita muddin bata bani kuɗina ba sai na sassarata Allah wallahi.ya faɗa yana ciccije baki.
Tare da d'aga sharb'eb'iyar addar sa sama.ai inna laure na jin haka tayi sauri ta toshe bakin ta ta fashe da kuka.tana ta tsinewa hajiya maryam saboda duk itace ta jawo mata wannan bala'in da take ciki.
Tana jin wucewar su tayi sauri ta fito takama hanya cikin sauri ta ƙarasa gida. lokacin da ta shiga ciki ta iske an yiwa gidan kaca kaca duk an faffasa mata randunan ta,kwanukan ta duk anyi jifa dasu robobin ta suma duk an fasa mata su.
Tana buɗe d'akinta tarar shima anyi masa d'ai-d'ai, gadon ta ma ba'a ƙyaleshi ba sai da aka yi masa filla filla.nan take ta dur'kushe a gurin ta kuma fashewa da kuka a karo na biyu,take taji wani mugun abu ya taso mata tun daga cikin cikin ta ya tokare mata zuciyar ta sabo da tsabar baƙin ciki.ta san ko tantama babu aikin buba ne wannan,kuma bata ga komai ba muddin bata biya shi kuɗin saba.
Sai yanzu ne ta tuna da hanne,dan ɗazu da ta fita a gida ta barta.lokacin da hanne ta ga kowa ya tafi an barta ita kaɗai a gidan,kawai itama sai ta haɗa kayan ta tafi gurin babbar yayar su altine.wannan kenan.
KANO............
Tafe yake yana sauri sabo da magariba ta sameshi a kan hanya, sakamakon go slow ɗin da ya tare shi a hanya,yana shigowa katafaren gidan sa da ke unguwar lamid'o cresent.yayi horn nan take mai gadi ya wangale 'katon get ɗin gaba ɗaya.
Ba tare da b'ata lokaci ba ya danna hancin motar sa cikin get ɗin gidan yaje yayi parking ɗin motar a parking space ɗin gidan,wanda yake ɗauke da tsadaddun motoci guda shida.gidan ya tsaru iya tsaruwa, saboda ginine wanda aka yi shi irin na turawa yayi matuƙar ɗaukan hankali.
Bayan yayi parking ya fito daga cikin motar hannun sa riƙe da briefcase ya ratayo jacket ɗin suit ɗinsa a kafad'ar sa, muktar kenan cikakken matashi kuma magidanci mai shekaru talatin da huɗu a duniya .tafiya yake a mutuƙar gajiye ga yunwa, sabo da shi mutum ne da baya son cin abin cin waje kwata kwata.ya fison wanda za'a girka masa a cikin gida yaci.
Yana ƙarasowa ƙofar da zata sada shi da ainihin babban parlon gidan ya danna wasu numbobi a jikin ƙofar glass ɗin, nan take Kofar ta zuge kanta .da sallama ya kutsa kai cikin hamsha'kin parlon wanda aka kashe masa dukiya ba kaɗan ba.
Ƙamshi ne yake tashi a parlon gauraye da sanyin a'c.muryar yaran sa ya jiyo sun taho wajen sa da gudu suna "Oyoyo dady". cikin sauri ya tsuguna ya kama su ya rungume su a jikin sa yana sauke ajiyar zuciya, sabo da shi mutum ne mai mutuƙar san yaran sa.
Yayi wa kowannen su kiss a goshi , ya kalli babban yace "sahal ina momyn ku??" yace tana d'akin ta, tun da ta dawo tace mana mu fita bacci zatayi karmu dameta muje baraka tayi mana wanka ta bamu abinci".yace "to yanzu kunci abincin??"
Sahal yace "ae munci dady amal ce bata ci abincin da yawa ba".da sauri ya juyo ya kalli Amal ɗin yace mata"princess me yasa ba kyason cin abinci sosai ne??"tace dady na ƙoshi". yace "are u sure"kai ta girgiza masa "yace okay".daga haka bai ƙara magana ba ya barsu nan suka cigaba da wasan su shi kuma ya haye sama.
Yana hawa ya nufi d'akin maman su,yayi sallama ya tura Kofar d'akin.koda ya shiga ya iske ta kwance a katafaren royal bed d'inta waya manne a kunnen ta,da alama waya take yi murmushi shimfid'e a saman fuskar ta.
Tana ganin ya shigo ta juyo ta kalle shi ta ce"ina zuwa zan kirawo ki anjima"ta karasa maganar tana kashe wayar tare da tashi zaune ta dubeshi tace"habibi barka da isowa,har ka dawo kenan kenan!!" yace na "dawo" tare da ƙarewa d'akin kallo,ko ina ka duba kaya ne a ƙasa zube ga plates ɗin abinci da aka ci aka bari a wajen.daga haka bai ƙara magana ba ya fice daga d'akin.