← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 80

Sashe 37

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin matsa nan cin farin ciki ne ya lulluɓesu,nan take suka hau ƙyalƙyala dariyar farin ciki da jin daɗi.

Sandar hannun sa ya ɗaga tare da doka ta a ƙasa,nan take ƙasar wajen ta tsage gida biyu wata iriyar kwalba ta bayyana a wajen.

Ɗakko kwalbar ya yi ya miƙa wa ALHAJI USAMA,cikin rawar jiki ya miƙa hannu ya karɓa tare da ƙurawa kwalbar ido, MUKHTAR ya gani zaune a cikin kwalbar yana kuka yana roƙon su.

Maganar da boka ya fara yi ne ta dawo da su cikin hayya cin su,in da yake cewa
"Ku kula da wannan kwalbar!! Kar ku bari ta fashe!! Domin fashewar ta ba zai yi muku daɗi ba!!"

Ya ci gaba da cewa
"Duk lokacin da kuke so ku juya shi kwalbar zaku ɗakko ku gaya masa abin da kuke so ya yi muku!!"

"An gama sarkin bokaye duniya"
ALHAJI Garba ya furta .

Kuɗi ALHAJI USAMA ya ciro kimanin dubu ɗari biyu ya ajiye wa boka a ƙasa,nuna su bokan ya yi da sandar hannun sa nan take suka ɓace ɓat daga cikin kogon dutsen.

Akan titi suka tsin ci kan su suna ta tafiya, mota suka tara ta mai da su makwan cin su,in da suka yanke shawarar koma wa a yau ɗin nan tun da sun sami abin da suke so.

Shiryawa suka yi tare da ɗaukan jakar kayan su suka kama hanyar zuwa tasha,ko da suka iso sun yi sa'ar samun ticket,in da aka ce musu mota za ta tashi ƙarfe biyar na yamma.

Ƙarfe biyar na yi mota ta tashi sai dai muce Allah ya kai lafiya .

Suna cikin tafiya ƙarfe biyu na dare ƴan fashi suka tare su a hanya,gaba ɗaya aka ce kowa da kowa ya sakko ƙasa,ɗaya bayan ɗaya suka din ga bi suna chaje mutane, idan sun sami kuɗi a gurin mutum a ware shi gefe,ya yin da waɗanda ba'a samu komai a gurin su ba suma ake ware su gefe daban .

Lokacin da aka zo kan ALHAJI Garba aka chaje shi tsaf ba'a sami wasu kuɗin kirki a gurin sa ba,sai aka tura shi layin waɗan da ba su da kuɗi a hannun su.

Shi kuwa ALHAJI USAMA da layi ya zo kansa chaje shi aka fara yi! In da aka yi aka yi da shi ya bayar da jakar hannun sa yaƙi, cikin hasala ɗaya daga cikin su ya harba masa bindiga a ƙafafun sa guda biyu,nan take ya saki wata iriyar ƙara tare da sakin jakar hannu sa ta faɗi a ƙasa ya kama shure shure..

Ɗaya daga cikin su ne ya zazzage jakar domin ganin abin da yake ciki,gurin zazzage war ne kwalbar da boka ya ba su tafaɗo ƙasa ta fashe rugu rugu.

Ko ta kan kwalbar ba su bi ba suka kwashe duk wani kuɗi da yake cikin jakar suka tsallake suka bar shi a gurin

Haka suka yi ta yiwa mutane,sai da suka kwashe kudin matafiya nan tasa suka harbi wasu daga cikin su,su kuma waɗan da basu da kuɗi a take a wajen suka saka bindiga suka harbesu har lahira,ciki kuwa har da ALHAJI Garba.

Wannan kenan .............

Ina matuƙar godiya da addu'o'in ku a gare ni tare da fatan alkhairi, kuɗin masoyan ƙwarai ne, ina alfahari da ku a koda yaushe....

Daga alƙalamin FATIMA BINTU(UMMU AYSHA)...........✍🏻

Share fisabilillahi

O8162055134...

💝💞HALIMATU 💝💞

(Love, sacrifices, destiny & betrayed)

💝💞💝💞💝💞💝💞

Story & Writing

By

FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)......✍🏻✍🏻

Ƙarƙashin jagorancin

(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)

Golden pens...............✍🏻

💝💞💝💞💝💞💝💞

A 2024 novel

💝💞💝💞💝💞💝💞

Pages ___________45&46

A nan kan titin suka bar gawarwakin mutanan da suka kashe tare da waɗan da suka raunata sannan suka gudu daga wajen.

Suna tafiya babu daɗewa sai ga ƴan sanda sun zo wajen,motar asibiti suka kirawo cikin gaggawa domin su kwashe waɗan da aka kashe da kuma waɗan da aka harba.

Bin cike suka fara yi game da yadda fashin ya kasan ce,ƙarar ambulance ce ta katse bin ciken da suke yi,ba tare da ɓata lokaci ba suka kwashi marasa lafiyar tare da gawarwakin suka saka su a cikin motar suka tafi da su asibiti cikin gaggawa.

Drivern motar kuwa da sauran passingers ɗin da suka rage aka saka su a cikin motar polisawan aka tafi da su police station domin ci gaba da gudanar da bin ciken da suka fara.

Lokacin da ambulance ɗin ta ƙaraso cikin asibitin direct emergency ta nufa cikin gaggawa,ba tare da ɓata lokaci ba aka jawo gadaje aka sa kowanne su daga ciki a ka shigar da su ciki.

Gaba ɗaya ma'aikatan suka rufu a kan su domin ceto rayuwar su, in da suka ƙara dudduba gawarwakin suka tabbatar da cewa babu rai a jikin su,mutuary aka wuce da su kafin a samu labarin ƴan uwan su da dangin su .

Su kuwa waɗan da aka harba aka shiga da su theater aka fara aikin cire musu bullets ɗin.

Duk da cewa wasu daga cikin su sun farfaɗo suna ta surutai barkatai,wasun su kuma har yanzu basu farfaɗo ba ciki kuwa har da ALHAJI USAMA.

Domin shi ALHAJI USAMA ya samu mummunan rauni a ƙafar sa ta dama, sakamakon harbin da suka yi masa har guda huɗu a ƙafa ɗaya ne ya hadda sa ƙashin gwiwar ta sa dagargajewa,hatta jijiyoyin ƙafar ta sa wasu daga cikin su duk sun tsitstsin ke.yayin da ɗaya ƙafar ta sa ta hagu suka harbeshi a cinyar sa.

Hakan ne ya haddasa masa zubar jini a ƙafafun nasa babu ƙaƙƙautawa,musamman ma ƙafar daman tasa, wannan dalilin ne yasa likitocin suke tunanin da ƙyar ne idan baza'a yanke ƙafar hagun ta sa ba,gashi kuma sun yi masa gwaje-gwaje in da suka gano yana ɗauke da ciwon suger wato (Diebeties).

Ya zubar da jini da yawa sosai,wannan dalilin ne ya sa suke neman jini cikin gaggawa domin a samu a ƙara masa,domin rashin ƙara masa jinin zai iya jawo wa a rasa shi gaba ɗaya.

Wani bawan Allah ne ya kwanta yace a ɗebi jinin sa leda biyu sadaka a ƙarawa ALHAJI USAMA,sai da aka yi test aka tabbatar baya ɗauke da cututtuka sannan aka ɗebi jinin aka fara saka masa kafin a samu ƴan uwan sa,domin suna buƙatar ganin ƴan uwan sa cikin gaggawa.

Duk da cewa wasu daga cikin su an samu nasarar waya da ƴan uwan su,sakamakon aljihun su da ƴan sandan suka laluba,cikin Sa'a kuwa aka sassamu ƙana nan wayoyi wato (key pad) a cikin aljihun wasu, sabo da ƴan fashin basu an kare da su ba,amma duk sun karɓe musu manyan wayoyin su.

Marigayi ALHAJI Garba yana ɗaya daga cikin waɗan da aka samu ƙaramar waya a cikin aljihun su,yayin da shi kuma ALHAJI USAMA wayoyin nasa duk a cikin jakar sa ya saka su,kuma ƴan fashin sun haɗa da wayoyin da kuɗin duk sun kwashe sun tafi dasu.

Lambar Hajiya RABI matar ALHAJI Garba ita aka kirawo,domin itace mutum na ƙarshe da marigayin ya yi waya da ita a cikin daren, cikin Sa'a kuwa wayar tana fara ringin ta ɗauka tare da cewa

"Barka da safiya ALHAJI? ya hanya? ai na san yanzu kun yi nisa sosai kun kusa ƙarasowa ko...?"

Shirun da ta ji ne yasa ta ƙara cewa

"Hello ALHAJI! Kana jina kuwa....?"

Daga ɗaya ɓangaren taji wata muryara tana magana wadda ba ta ALHAJI Garba ba,in da mai maganar yake cewa

"Yi haƙuri madam! wannan ba mai wayar bane police ne!!".

Cike da tsananin tashin hankali ta miƙe zaune daga saman in da take zaune a kan kujera ta ɗora hannun ta akan ƙirjin ta ta dafe muryar ta na rawa tace

"Na shiga uku!! Police kuma..? me ya haɗa ALHAJI da police shi da yake tafe cikin mota!!".
Ta ƙarasa maganar tana ɗora hannun ta ɗaya akan ta.

"Ki yi haƙuri madam! me wayar ne Allah ya yi masa cikawa! Yanzu haka gawar sa tana nan a teaching hospital dake garin kogi state,sakamakon tare su da ƴan fashi da makami suka yi a cikin dajin kogi state,in da suka rauna ta wasu daga cikin su,wasu kuma suka karkashe su,ciki kuwa har da mijin ki!!"

Ya ci-gaba da cewa

"Sabo da haka muna buƙatar wasu daga cikin shaƙiƙan sa!! Idan kun zo sai ku kirawo wannan numbern wayar nashi!!".

Ya ƙarasa maganar muryar sa cike da rauni.

Wani irin mugun ashar Hajiya RABI ta lailayo ta maka wa mutumin,cikin sauri ya kashe wayar ba tare da yaji ƙarshen zagin ba.

A ɓangaren Hajiya RABI kuwa lokacin da ta ji ya kashe wayar,nan take ta yi wurgi da wayar hannu ta akan sofa,hannayen ta duka biyun ta ɗaga tare da ɗora su a kanta,ta ƙarƙare wa ta yi ta kurma uban ihu tare da cewa

"Na shiga uku ni RABI me nake ji haka ne..? ALHAJI ya rasu..!! me kuma yake shirin faruwa da Ni?? Na shiga uku!"

Ta faɗa tare da fashewa da matsanancin kuka.
Ihun ta ne ya jawo hankalin ƴarta HUMAIRA da take kwan ce a cikin ɗakin ta, koda ta shigo parlon taga halin da mahaifiyar ta take ciki ne ya ɗaga mata hankali.

Durƙusawa ta yi a gaban mahaifiyar ta ta ta miƙa hannu tana ƙoƙarin sauke mata hannayen ta da ta ɗora a kanta tare da cewa

"Subhanallahi! me ya sameki MOMY..? Dan Allah ki yi min magana ko hankali na ya kwanta!!"
Ta faɗa cike da ruɗani akan fuskar ta.

Cikin matsanan cin kuka har tana shiɗewa ta ɗago da fuskar ta ta kalli ƴartata tace

"Mun shiga uku mun lalace HUMAIRA ya zamu yi da ran mu!!"

"MOMY ki gaya min me yake faruwa ko baki da lafiya na..??"

HUMAIRA ta faɗa fuskar ta cike da tashin hankali.

"Ai idan rashin lafiya ne da sauƙi HUMAIRA!"

"Toh ki gayamin me yake faruwa MOMY!! baki ji yadda gaba na yake faɗuwa ba!!"

Ta ƙarasa maganar ƙwalla na taruwa a cikin idanun ta.

Cikin shashsheƙar kuka Hajiya RABI tace

"HUMAIRA ALHAJI! ALHAJI! Wallahi ALHAJI ne!!

Cike da fargaba HUMAIRA tace

"MOMY me ya faru da Abba...??"

"Yanzun nan wani mutum ya kirawo ni da numbern wayar sa yake cemin wai ya rasu!! ƴan fashi da makami sun harbe shi tare da wasu daga cikin abokan tafiyar su,wasu kuma an raunata su.
Chapter 37 · 0% Book details