Sashe 47
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ɓangaren undies suka nufa nan ma momy ta zaɓar mata masu kyau da tsada har da pad,bayan sun gama ne har sun juya za su tafi wajen biyan kuɗi ta tuna bata ɗaukar wa yusra chocolate da biscuits ba.
Juyowa halimatu ta yi ta kalli momy tare da cewa:
Momy bari naje na ɗakkowa yusra chocolate da biscuits"
Ta faɗa tare da saka hannu ta ɗauki ƙaramin basket.
"Toh ni dai bari na je ayi lissafin waɗan nan kayan,idan kin gama ki same ni a can"
Ta faɗa tare da tura basket ɗin ta ƙara gaba.
"Okay mommy"
Ɓangaren biscuits da su chocolate ta yi ta fara jida tana zubawa a basket,muryar wasu mata da miji ta ji a gefen ta in da mijin yake cewa matar:
"Amina ki yi sauri ki gama kwasar musu kayan zaƙin nan mu tafi bana son magriba ta yi mana a nan!"
Wani irin faɗuwar gaba ta ji a lokaci guda,domin ba zata taɓa mantawa da wannan muryar ba.
Ɗagowa ta yi ta dubi mutumin da yake tsaye a gefen ta da yaro ruƙe a hannun sa.
Sakin basket ɗin hannun ta ta yi ya faɗi ƙasa kayan ciki suka watse a gurin sakamakon arba da ta yi da fuskar mahaifin ta,duk da cewar ya canja sosai a kan yadda ta sanshi a baya, ga kuma alamu na jin daɗi da arziƙi da suka bayyana a tattare da shi amma hakan bai hana ta gane shi ba.
"Subhanallahi"
Baba ya furta lokacin da ya ji faɗuwar basket ɗin a ƙasa, ɗago kai ya yi domin ganin wacce ta yar da basket ɗin.
Karab idanun su suka sarƙe cikin na juna.✍🏻
Pls kuyi haƙuri da wannan.
Ina matuƙar godiya da addu'o'in ku a gare ni, ku ɗin na musamman a cikin zuciya ta, ina alfahari da ku ƙwarai da gaske, Allah ubangiji ya saka muku da mafificin alkhairin sa ya biya muku buƙatun ku na Alkhairi🙏🏻🙏🏻🥰
Daga alƙalamin FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)....✍🏻✍🏻
Game buƙatar wannan littafin tun daga farko zuwa inda aka tsaya ya tun tuɓeni ta wannan numbern wayar👇🏻👇🏻
08162055134.
Share fisabilillahi.
💝💞HALIMATU💝💞
(Love, sacrifices, destiny & betrayed)
💝💞💝💞💝💞💝💞
Story & Writing
By
FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)
Ƙarƙashin jagorancin
(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)
Golden pens..........✍🏻✍🏻
💝💞💝💞💝💞💝💞
A 2024 novel
💝💞💝💞💝💞💝💞
Pages____________59&60
___________A matuƙar razane ya ƙura mata idanun sa cikin ɗimuwa da fargaba,ita ɗin ma shi take kallo cike da al'ajabi haɗi da ban mamaki,ta rasa wanne irin abu take ji a cikin zuciyar ta,farin ciki zata yi game da ganin mahaifin na ta ko akasin haka.
Shekara kusan biyu kenan rabon da ta sanya shi a cikin idanun ta, babu irin neman da basu yi masa ba amma shiru basu samu labarin shi ba,har ƙauyen su momy ta tura drivern ta ya bin ciko musu labarin shi saboda HALIMATU ta ɗaga hankalin ta sosai a lokacin,amma dai amsar ɗaya ce tun da ya tafi babu labarin sa.
Haka suka yi haƙuri suka fawwala wa Allah lamarin su suka ci gaba da addu'a idan da rabon ganawar Allah ubangiji ya sada su da alkhairi.
Maganar da baba ya yi ne ya dawo da ita daga cikin duniyar tunanin da ta faɗa.
"Wa nake gani kamar HALIMATU.? ko dai idanu na ne suke yi min gizau..?"
Ya furta a matuƙar razane.
Wani irin sanyi ta ji ya taso mata daga cikin jikin ta yana hudo sassan fatar jikin ta guda bakwai da ubangiji ya halatta mata ita,cikin rauna nanniyar murya tace:
"Ni ce baba! wallahi nice!!".
Waro idanun sa ya yi cike da mamaki da ban al'ajabi yana ƙare mata kallo,tabbas itace! HALIMATU ce! ƴar sa ce!.
Duk da canjin rayuwar da ta samu hakan bai sa ya kasa gane ta ba.
Tsinkayo muryar ta ya yi tana cewa:
"Dama kana nan baba.? ina ka shiga.? babu irin neman da bamu yi maka ba amma bamu sameka ba,mun yi kiran wayar ka mun gaji,har can haɗeja momy ta aika amma ba'a samu labarin ka ba.
Ta faɗa tare da ƙarasawa in da yake ta rungume shi gam-gam kamar za'a ƙwace mata shi hawaye na zubowa a cikin idanun ta.
Miƙa wa aunty AMINA Ahmad ya yi tare da saka hannu ya rungume HALIMATU,wata iriyar ajiyar zuciya ya sauke hawaye na silalowa a cikin ƙwayar idanun sa,a hankali ya ji wani irin ƙulli yana warware wa a cikin zuciyar sa,abin da ya daɗe yana jin nauyin sa take ya ji lokaci guda kamar an sauke masa shi.
"Ina nan HALIMATU a cikin garin Kano,tun lokacin da muka rabu na rasa wayata ta faɗi,kuma da naje yin welcome back ɗin layin suka ce min bazai yi ba sakamakon ba ni ne na yi registern layin ba, shi ya sa idan kuka kirawo bakwa samu na,kuma nima babu irin neman da ban yi muku ba amma ban same ku ba,har gidan da momyn taki take sai da naje na tarar wasu ne suke zaune a ciki ba su ba,dana tambaya sai aka cemin ai sun tashi da daɗe wa".
"Haka na cigaba da cigiyar ku amma shiru,babu labarin ku,daga ƙarshe na bawa zuciya ta haƙuri jure rashin ku,na sakawa raina in dai kuna a cikin garin kano watarana zamu haɗu in sha Allah,gashi yanzu Allah ya amsa addu'a ta ya haɗa ni da ku".
Ya ƙarasa maganar yana shafa kanta.
Muryar auty amina suka jiyo tana cewa:
"Abban Ahmad da gaske halimatun mu ce wannan.?"
Cikin tsanani farin ciki baba yace:
"Itace wallahi Amina! yau gaki ga halimatun mu"
Ya faɗa fuskar sa ɗauke da yalwataccen farin ciki.
Ɗago kai HALIMATU ta yi ta kalle shi tare da cewa:
"Baba wannan wace ce.?"
Ta faɗa tana nuna aunty AMINA da ke sakar mata murmushi.
"Mamanki ce HALIMATU! mun yi aure shekara biyu da suka wuce, wannan kuma ƙaninku ne Ahmad da Allah ya albarka ce mu da shi".
Ya faɗa tare da janye ta a cikin jikin sa.
Jin jina kai ta yi fuskar ta ɗauke da murmushi tana kallon aunty amina.
Shirun da MOMY ta ji ne ya sa ta biyo bayan halimatu domin ganin abin da ya tsare ta,tana ƙaraso wa gurin ta yi turus ta tsaye tana ƙare musu kallo, da yake sun juya bayan su shi yasa basu ganta ba.
Cikin ran ta take mamakin wane ne wannan mutum da yake tare da halimatun.?,ganin babu mai bata amsa ya sa ta ƙarasa gaban su tare da cewa:
"Doughter ke da su waye kuke tsaye a nan gurin kin bar ni ni kaɗai ina ta jiran ki".
Juyowa suka yi gaba ɗayan su suka kalli momy a lokaci guda.
"Wa nake gani kamar MALAM UMMARU!!"
"Ba kama bace Maryam! ni ne kika gani! mun shigo mu yi soyayya ni da mata ta ashe da rabon zamu haɗu da ku"
Ya ƙarasa maganar yana nuna aunty AMINA.
"Allah mai iko dama kana cikin garin nan mukai ta neman ka.? a wacce unguwa kuke.?"
"Ina nan a cikin garin kano Maryam,yanzu muna zaune a zooarod ne"
Jin jina kai momy ta yi tare da cewa:
"Allah mai iko! yanzu dai tun da Allah ya haɗa mu dole ne mu biku muga in da kuke zaune, idan yaso daga baya kwazo gidan mu kuma"
"Haka ne maryam! yanzu bari mu je mu biya kuɗin kayan sai mu wuce"
Ya faɗa tare da kamo hannun halimatu su kayi gaba momy da aunty AMINA suka biyo su a baya.
Bayan sun biya kuɗin ne suka fito ma'aikatan na biye da su da kaya niƙi niƙi a hannun su, musamman ma na su momy masu yawa ne sosai.
A cikin boot aka zuba kayan, su kuma suka shiga cikin motocin suka ɗauki hanyar zuwa gidan malam ummaru.
Ba ƙaramin mama ki suka yi ba lokacin da suka ƙarasa gidan malam ummaru,bayan mai gadi ya buɗe musu gate ɗin gidan sun shiga suka samu guri suka yi parking motar su.
Jagora ya yi musu har cikin parlon gidan wanda ya tsaru sosai,kana gani kasan akwai wada ta a tattare da su.
Zama suka yi akan sofa dukkan su banda aunty amina da ta shiga kitchen,jim kaɗan ta fito hannun ta ɗauke da madai dai cin try mai ɗauke da ruwa da lemo ta ajiye a kan center table ɗin dake gaban su.
Zama ta yi suka ƙara gaisawa sosai sannan malam ummaru ya basu labarin abin da ya faru tun bayan tafiyarsu har zuwa yanzu,momy bata yi mamakin jin haka ba,domin ta san abin da ya fi haka ma Inna laure zata iya ai katawa.
Sannan ya sanar musu da saka ranar bikin HANNE nan da wata biyu masu zuwa,yace idan Allah ya kaimu lokacin zai zo ya ɗauki HALIMATU su tafi tare da shi.
Momy tace:
Tom shikenan Allah ubangiji ya kai mu lokacin da rai da lafiya,kaga lokacin ma daddyn su ya dawo daga uk".
Gaba ɗaya suka amsa da ameen.
Momy ce ta kai duban ta gurin malam ummaru tare da cewa:
"Toh baban HALIMATU mudai zamu tafi sabo da magriba ta gaba to,in sha Allahu tun da munga guri zamu dinga zuwa sosai"
Ta ƙarasa maganar tana miƙewa tsaye.
Godiya sosai malam ummaru ya dinga yi wa momy har sai da ta ce ya isa haka,ai HALIMATU ƴarta ce halak malak babu abinda baza ta iya yi mata shi ba muddin tana da halin yin shi".
Jin jina kai baba ya yi domin ya ga tabbacin haka a jikin halimatun.exchanging numbers suka yi sannan suka yi musu sallama ,har bakin mota suka raka su cike da kewar su suna ɗaga musu hannu har suka fice daga gidan.
******************************************
"Alhaji USAMA"
Lokacin da ya jefa ƙafar sa cikin bedroom ɗin momy turus ya tsaya yana kallon RUFAIDA cike da tashin hankali da ɗimuwa,ita ɗin ma shi take kallo ta ƙure shi da idanun ta,gashi babu baki balle tace zata yi masa magana,daga bisani kuma sai hawaye suka dinga gangarowa daga gefen idanun ta suna shiga har cikin kunnen ta.
Wai yau itace kwance babu lafiya komai sai dai a yi mata,duk wulaƙancin da take yi wa mutane da jiji da kai da nuna cewa ita ɗin wata ce,yau gashi farat ɗaya Allah ya mayar da ita musaka ita da mahaifin ta gurin zalun ci da son zuciyar su.