Sashe 61
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A mugun gajiye ta miƙe ta shiga toilet ɗin ita kuma momy ta shimfida dadduma ta tada salla,bayan ta idar ne ta janyo telephone ta kirawo ma'aikatan hotel ɗin ta basu odar kalar abin cin da take so a kawo musu.ba a wani ɗauki lokaci ba aka yi musu nocking,ta shi momy ta yi ta buɗe musu ƙofar suka shigo tare da jera abinci akan wani haɗaɗen dinnig table suka juya suka fita.
Fitar su babu daɗewa halimatu ta fito daga cikin toilet ɗin ta buɗe trolly ɗin ta ta ɗauki wata gown mara nauyi ta saka tare da hajabi ta tayar da sallah,bayan ta rama sallolin da ake binta ne ta fito parllon ta zauna kusa da momy ta ɗora kanta a kafaɗar momyn ta ce,
"Wash! momy yunwa nake ji"
Shafa kanta ta yi tare da cewa,
"Sorry doughter,ta shi muje mu yi dinner ga abinci can a kan dining na yi mana order ɗin sa"
Ta faɗa tana nuna mata dinning ɗin.
Tashi suka yi a tare ita da momy suka wuce dinning table ɗin suka jawo kujera suka zauna tare da yin bismillah suka fara cin abincin,suna gamawa suka shige cikin bedroom ɗin suka haye gado suka kwanta cike da gajiya,nan take cikin ƙanƙanin lokaci baccin gajiya ya yi awon gaba da su.sai da suka yi kwana biyu suna hutawa kafin su fito su zaga gari,kasancewar momy ta san garin ba baƙon ta bane ba shiya sa basu sha wahala ba.
Nan take suka fara ai watar da abin da ya kawo su garin ba tare da ɓata lokaci ba,sai da suka yi soyayyar duk wani abu da suka san za su siya sannan suka auna kayan zuwa Nigeria,hatta lefen hafiz sai da momy ta haɗa naji da gani na alfarma abin dai ba'a cewa komai sai san barka.
Satin su uku a garin sannan suka wuce zuwa China suka ƙarasa siyayyar da za su yi nan ma suka yi sati uku sannan suka wuce zuwa saudia domin yin umara,sai da suka yi wata guda a saudia sannan suka yi haramar dawowa gida bayan sun yi siyayya mai ɗumbin yawa.
Ranar da za su dawo nigeria ba ƙaramin shiriye shirye a ke yi ba domin tarɓar su,lokacin da jirgin su ya yi ya sauka a Aminu Kano international airport da ke garin kano ba ƙaramin daɗi halimatu ta jiba,domin ba ƙarya ta yi kewar ƙasar haihuwar ta sosai da sosai,a gefe guda kuma ga kewar masoyin ta abin ƙaunar ta mukhtar.
Lokacin da suke sakkowa daga matattakalar jirgin akan idon su daddy da su mukhtar,sanye take da tsadaddiyar dubai abaya maroon colour wacce ta yi mata mugun kyau kamar ka sace ta ka gudu,ta yi rolling ɗin kan ta da mayafin abayar da wani irin style,hannun ta riƙe da tsadaddiyar madai dai ciyar jakar ta ta Company ɗin Gucci.
Ƙafafun ta sanye suke da wani irin hill shoe mai shegen kyau,ta saka wani brown sun glasses a idanun ta da ya wani irin ƙarawa fuskar ta kyau sosai,ta ƙara ƙiba da fari skin ɗin ta sai wani irin glowing ta ke yi, ga wani irin mugun ƙamshi da yake fita daga cikin jikin ta.
Tafiya suke yi a nutse ita da momy duk in da suka wuce sai an kalle su an ƙara kallon su,suna cikin tafiya sadiq ya tawo da saurin sa ya rungume mommy,ya yin da wani haɗaɗɗen guy ya tawo ya tsaya a gefen halumatu tare da yin sallama yana sakar mata wani irin Murmushi.
Juyo da kanta ta yi ta kalle shi up and down ba tare da ta amsa sallamar ta sa ba tabi bayan momy da Sadiq domin basu san abin da yake faruwa ba,gab da za su ƙaraso wajen da su daddy suke jiran su ya kuma shan gaban ta tare da cewa,
"Ya kamata a tsaya a saurare ni beauty,domin da ƙarfin gwiwa ta na zo banzo da wasa ba!"
Zagaye wa ta yi ta gefen sa zata ta wuce ba tare da ta tanka masa ba ya ƙara shan gaban ta da sauri.
"Kin kuwa san ko ni ɗin wanene nake tsaye a gaban ki ina yi miki magana kina ƙyale ni.?"
Ya faɗa a zuciya.
Wata murya ce ya ji daga gefen shi a na cewa,
"Koma wane ne kai ɗin ba zata kula ka ba sabo da ita ɗin mallaki na ce"
Da sauri halimatu ta juyo ta sauke idon ta akan masoyin ta mukhtar da ya tsuke fuskar sa babu alamar annuri a cikin ta,domin duk abin da yake faruwa a kan idanun su ne gaba ɗaya har da su daddy,wani irin murmushi ta sakar masa mai ƙayatarwa tare da cewa,
"Habibi kai ma kazo tarɓan mu.?"
Nan take ya saki fuskar sa tare da cewa,
"Ai dole ne na zo tarɓar sarauniya ta kuma gimbiya ta"
Dariya ta yi har da rufe fuskar ta da kyawawan hannayen ta.
Kusan suman tsaye guy ɗin nan ya yi sabo da wani irin sihirtaccen kyau da ta yi masa haɗi da jin daddaɗar muryar halimatu,nan take ya juyo a zuciye ya yi wa mukhtar wani mugun kallo tare da cewa,
"Waye kai da zaka shiga tsakani na da abar ƙauna ta!!"
Cike da mamaki mukhtar yake kallon shi tare da cewa,
"Mijin ta ne ni ɗin! kaga kuwa dole na shiga tsakanin ka da ita".
Yana gama faɗa ya kama hannun halimatu suka wuce gurin su daddy abin su,ganin guy ɗin ya biyo bayan a fusa ce su ne ya sa daddy ya tare shi ya bashi haƙuri tare da yi masa bayani cikin lallashi,da ƙyar ya yadda ya tafi ba don zuciyar sa ta so ba,domin maganar gaskiya ya ƙwallafa rai a kan halimatun.
Juyowa daddy ya yi tare da komawa in da suke aka fara gaishe gaishe,daga bisani kuma aka ɗunguma zuwa gida gaba ɗaya,nan ma sun samu tarɓa sosai gurin baba ladi da aunty AMINA,domin tun da sassafe aunty Amina ta zo ta taya baba ladi suka girka musu abinci kala-kala da abin sha.
Gaba ɗaya a kan dining table aka sauka domin akwai yunwa a tattare da su, halimatu kuma ta samu babban try ta haɗa kalolin abinci a ciki ta kaiwa mukhtar da ke parlon baƙi zaune,har ta juya zata tafi ya tsare ta tare da cewa,
"Ina kuma za ki ga abinci kin ajiye baki ci ba.?"
Murmushi ta yi tare da cewa,
"Ai duka na ka ne abin cin habibi na,ka cinye kafin na dawo yanzu nan!"
Ta faɗa fuskar ta ɗauke da murmushi.
"A'a ban yarda ba dawo ki zauna ki ci idan ba so kike yi rai na ya ɓaci ba!
Ganin ya ɓata rai ya sa ta zauna ta shiga zuba masa abin cin,sai da ta gama sannan shima ya jawo plate ya zuba mata,ganin wanda ya zuba mata yana da yawa ko rabin sa ba zata iya cin yewa ba ya sa ta ce,
"Habibi wallahi abin cin nan ya yi min yawa ba zan iya cinye ko rabin sa ba"
Ganin ba shida alamun ragewa ne ya sa ta marai rai ce masa fuska fuska kamar za ta yi kuka ta ce,
"Wallahi ya yi mun yawa habibi please ka rage!"
Hannu ya sa ya jawo plate ɗin tare da rage abin cin,nan take ya umarce ta da ta ci abin cin, bismillah ta yi ta saka cokali ta fara cin abincin a hankali cike da nutsuwa da jan hankali,cikin wani irin shauƙi ya ke kallon yanda take cin abinci cike da nutsuwa da burgewa,gaba ɗaya komai nata cikin nutsuwa take yin sa gwanin ban sha'awa.
Suna gama cin abincin ya miƙe tare da cewa,
"My love bari na tafi na barki ki huta ko.? ki tabbatar kin kwanta kin huta sosai domin naga akwai alamun gajiya a tattare da ke!!"
Miƙewa ta yi tare da cewa,
"Toh shikenan habibi na gode ka gaida su momy"
Amsawa ya yi yana binta da wani irin kallo kamar ya haɗiye ta,wani irin kyau ta ƙara da cika kamar wadda a ka yiwa wankan inji, ji yake kamar kar su rabu wallahi Sabo da kallon ta ba ƙaramin farin ciki da nishaɗi yake saka shi ba.
Fitowa ya yi daga parlon ya zo ya yiwa su daddy da momy sallama ya tafi,kayan da suka ci abin cin ta kwashe tare da kaiwa cikin kitchen ɗin ta ajiye,direct up stairs ta nufa zuwa bedroom ɗin ta ta shige toilet ta yi wanka da ruwa mai zafi tare da ɗauro alwala ta fitowa ta gabatar da sallar azahar da la'asar da ake bin ta,bayan ta gama ne ta yi addu'a tare da hayewa kan bed ɗin ta ta yi addu'a ta kwanta.
Ba ita ta tashi daga bacci ba sai gaban nin sallar magriba,alwala ta yi tare da gabatar da sallar magriba tare da yin azkar kamar ko yaushe,bata ta shi a gurin ba sai da ta gabatar da sallar isha'i.
Sauka ta yi ƙasa domin ta samu ta ɗan sha ko fruit ne domin bata so taci abu mai nauyi,su momy ta tarar Zazzau ne kan sofa suna hira,zuwa ta yi ta gaishe da su tare da wucewa cikin kitchen ɗin domin ta haɗa fruit salad ɗin da zata sha.
Tana gamawa ta ɗakko bowl ɗin a hannun ta tare da fitowa daga cikin kitchen ɗin ta zauna kusa da momy,kallon ta momy ta yi tare da cewa,
"Sannu doughter har kin ta shi.?"
Ɗagowa ta yi ta kalli momy tare da cewa,
"Eh wallahi momy tun ɗazu na tashi na yi sallar magriba da isha'i shine na sakko naɗan haɗa fruit salad domin shi nake son sha"