← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 80

Sashe 67

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dan Allah ka rufa min asiri ka faɗi wani abun in yi maka amma ban da wannan wallahi ba zan iya ba!!"
Kallon ta ya yi tare da cewa,
"Ai kuwa dole ne ki koya domin wannan tsarina ne,daga yanzu komai tare zamu dinga yi da ke! sabo da haka ki shirya zama da mukhtar a yanda kika same shi!".
Ya faɗa tare da miƙewa ya fara cire kayan jikinsa a gaban ta babu abin da ya dame shi,domin yana so ta saba da shi sosai,ganin haka ne ya sa ta juya da sauri tare da rugawa a guje ta fita daga cikin ɗakin zuwa nata bedroom room ɗin ta kulle ƙofa domin gudun kar ya biyo ta, Sabo da maganar gaskiya mukhtar ya fara bata tsoro yanzu,ita ina zata iya yiwa garjejen ƙato kamar sa wanka! tab ɗi jam! wai dama haka auren yake! wallahi ni bazan iya ba!!".
Ta faɗa tana shigewa cikin toilet ɗin.

Lafiyayyen wanka ta yi ta fito ta yi kwalliya mai kyau,domin yanzu babu laifi ta iya kwalliya sosai,wasu riga da sket na wani purple ɗin less ta saka waɗan da suka bi shape ɗin ta sosai suka zauna a cikin jikin ta cif-cif gwanin ban sha'awa,taje gashin ta ta yi ta ɗaure da ƙaramin ribom purple ta sake shi har wajen ƙugun ta, sannan ta ɗakko ɗan kwalin less ɗin ta kafa ɗaurin ture kaga tsiya.
Ba ƙaramin kyau ta yi ba kamar ka sace ta ka gudu da ita,bakin nan nata ya sha red lipstick sai shinning yake yi.turare ta fesa kala kala sannan ta saka plate shoe kalar purple ta ɗakko mayafi da nufin ta yafa kenan ya yi nocking ɗin ƙofar,jin ana nocking ɗin ƙofar ne ya sa ta ƙarasa saka mayafin da sauri ta je ta buɗe ƙofar .

Shigowa ɗakin ya yi ya jawo ta jikinsa ya rungume ta tare da sauke a jiyar zuciya,hannu ya sa ya cire mata mayafin ya jefa a kan gadon tare da cewa,
"Bana buƙatar wannan a cikin gida na my love"
Daga haka ya kama hannun ta suka fita daga cikin ɗakin zuwa ƙasa,direct dining table suka nufa ya ja kujera ya zauna tare da jawo ta ya ɗorata a kan cinyar sa,jawo food wamers ɗin ya yi tare da serving ɗin su a cikin plate ɗaya, gashin kazar ma a plate ɗaya ya zuba musu sannan ya saka musu fork guda ɗaya,cup ya jawo ya haɗa musu tea mai kauri sannan ya ɗauki fork ya yi bismillah ya ɗebo irrish haɗe da source ya kai bakin ta.
Cike da kunya ta buɗe bakin ta a hankali ya zuzuba mata, miƙa mata fork ɗin ya yi tare da yi mata alama shima ta ba shi,cike da kunya ta ɗebi ta kai bakin sa yayi sauri ya karɓa.haka suka dinga ciyar da junan su cike da nishaɗi tun tana ɗari ɗari da shi har ta fara sakin jikin ta da shi.

Bayan sun gama ne ta kwashe kayan ta kai kitchen ta wanke sannan ta fito ta same shi zaune a kan sofa yana daddanna wayar hannunsa,giftashi ta yi zata wuce ya yi sauri ya ruƙota tare da ɗora ta akan cinyar sa,cikin wani irin salo ya matse ta a cikin ajikin sa tare da ɗora hannun sa akan cikin ta yana shafawa a hankali a hankali yana yin sama da hannun sa.
Nan take ta saki wani irin numfashi tana jin wani irin yanayi na saukar mata,a hankali ta ɗora hannun ta a kan nashi ta ruƙe gam domin wani irin abu take ji yana mata yawo a cikin jikinta.

Cikin sauri ya janye hannun ta tare da ɗora bakinsa a kan kunnen ta ya ce,
"Kada ki haramta min abin da Allah ya halatta min my love,daga yau in dai ina cikin gidan nan haka nake so mudinga kasancewa kin ji.?? domin bana son abin da zai nisan ta ni da ke komai ƙanƙantar sa,sabo da haka dole na cire miki wannan tsoron nawa da yake cikin zuciyar ki!!"
Ya faɗa tare da haɗe bakin su waje ɗaya.

****************************************************************************************************

A ɓangaren su RUFAIDA kuwa,lokacin da suka samu labarin auren mukhtar ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba,domin daddy da kansa ya tura masa saƙo ya gaya masa domin kar su ji a gari suce ba a kyauta musu ba.cikin tsananin baƙin ciki hajiya Hauwa ta fashe da kuka kamar wadda aka yiwa wani mugun abun,ita kuwa RUFAIDA ƙin gaya mata aka yi domin gudun kar jikin ta ya burkice musu,tun da zuwa yanzu Alhmdllhi an samu ci gaba a kan ciwon nata.

Tun lokacin da malam jazuli ya kawo shekh ya fara yi mata ruƙiyya da addu'o'i jikin ta ya fara sauƙi, domin zuwa yanzu tana iya yin magana kaɗan -kaɗan ba mai yawa ba,amma har yanzu tana nan sedai a kwantar a tayar da ita.
Cike da lallashi alhaji usama ya dinga bata baki haɗe da yi mata nasiha,da ƙyar aka samu ta yi shiru, hawayen fuskar ta ta share tare da cewa,
"Shikenan mun yi asara babba wadda ba zamu taɓa maye gurbin ta ba, mun cuci kan mu mun cuci ƴar da muka haifa mun nakasta mata rayuwa,yanzu ga shinan daga ƙarshe ta tashi a tutar babu!! ta nakasa yadda babu namijin da zai iya rayuwa da ita,sai dai ta ƙare rayuwarta a haka!!"
Ta ƙarasa maganar tare fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai saurare.

Kallon ta alhaji usama ya yi yana goge hawayen fuskarsa ya ce,
"To ya zamu yi! dole mu yi haƙuri haka Allah ya ƙaddara mana babu yanda za mu yi!!.
Ta shi ta yi da gudu ta shige cikin ɗaki tana kuka,shima hawayen ya goge tare da girgiza kan sa yana jin wani irin ƙunci da ƙuna da zuciyar sa take yi,ta shi ya yi ya bi bayan hajiya Hauwa domin ya rarrashe ta,duk da cewar shima ɗin kukan yake yi.

A ɓangaren su HANSAI kuwa, suna tafiyar da al'amuran suhankalin su kwance yake ba suda wata damuwa,zuwa yanzu ta tsayarwa da Safara'u mijin da zata aura cikin jerin maneman auren ta,alhaji jamilu shine wanda ta zaɓa mata,kasancewar yanada rufin asiri dai dai gwargwado babu laifi.
Matan sa biyu da yara guda biyar, gidansa anan cikin gwammajar yake gaba da su kaɗan,kuma mutane sun san shi a unguwar sosai saboda mutumin kirki ne.wannan dalilin ne ya sa hansai tace ya fito idan da gaske yake yi,ba tare da ɓaya lokaci ba ya gayawa ƙannen baban sa yadda suka yi da hansai,in da tace masa zasu tafi ƙauyen haɗeja tare da su domin su gana da dangin mahaifin Safara'u.

Haka kuwa aka yi,sunje sun gana da su har an tsai da ranar biki wata biyu masu zuwa,zo kaga murna wajen hansai da Safara'u,domin a cewar su sun samu mai rufin asiri.

**********************

A hankali ya zame bakin sa daga cikin nata bayan minti takatin ɗin da ya ɗauka yana kissing ɗin ta,gaba ɗaya duk ya birkita mata lissafi da salon sa,jin jikin ta take yi kamar ba nata ba,gaba ɗaya ta lafe a cikin jikin sa kamar wata mage,ya yin da mukhtar ya ƙara gyara mata zama a jikin sa domin shi dama haka yake so.
Ƙarar door bell ce ta katse shirun na su,a hankali ya janye ta daga jikin sa tare da ɗaukar ɗankwalin ta ya yafa mata a kai tare da miƙewa tsaye ya nufi ƙofar parlon ya buɗe.

Su altine ne suka zo tare da aunty AMINA suka kawo gara,cike da girmamawa ya durƙusa har ƙasa ya gaishe da su tare da basu hanya suka wuce,har ya nufi matattakala zai hau sama aunty amina ta tsayar da shi tare da cewa,
"Kayan gara ne muka kawo,please kasamu waɗan da za su shigo muku da su!"
A hankali ya ɗago ya kalli aunty AMINA tare da cewa,
"Haba aunty!! Me ya sa baba zai min haka! Wallahi da na san da zancen da bazan bari a kawo ba!"
Ya faɗa muryar sa cike da damuwa.
Ka yi haƙuri mukhtar, wannan tsarin mahaifin ta ne,kuma ya riga da yayi niyya shi ya sa yayi musu ita da ƴar uwar ta.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa,
"Shikenan aunty na gode sosai! Allah ya ƙara girma".
Murmushi ta yi ta amsa da ameen.

Miƙewa ya yi ya haye sama zuwa bedroom ɗin sa ya ɗakko babbar rigar sa da hularsa ya saka ya ƙara feshe jikin sa da turare,mukullin mota ya ɗauka ya sakko ƙasa tare da kiran HALIMATU!
Tasowa ta yi a hankali tabi bayan sa har cikin ɗaya daga cikin bedrooms ɗin da ke parlon ƙasa.
Zaune ta same shi akan bed yana jiran ta,zuwa ta yi ta durƙusa a gaban sa tare da cewa,
"Ga ni"
Hannu ya sa a cikin aljihu ya ɗakko kuɗi rafers ɗin ƴan dubu-dubu sababbi guda biyu ya miƙa mata tare da cewa,
"Ki bawa su aunty wannan"
Daga haka ya miƙe ya fita daga cikin ɗakin ta bishi da addu'ar dawowa gida lafiya.sallama ya je ya yiwa su aunty Amina sannan ya fice daga cikin gidan.bayan ya fita megadi da mai bawa flowers ruwa suka shiga jido da kayan suna kaiwa store,ba laifi kayan suna da yawa,domin sai da aka ciko ƙaramar akori kura da su.

Anan suka wuni suka ƙara gyara mata gidan tare da ƙara yi mata nasiha da bata shawarwari,sai wajen la'asar suka bar gidan bayan aunty amina ta bata wasu magungunan mata masu kyau tare da wani irin turare mai shegen ƙamshi, da ƙyar suka rabu tana ta yi musu kuka.

Bayan tafiyarsu ne ta tashi ta shiga kitchen ta haɗa musu sakwara da miyar agushi wadda ta ji naman rago, sannan ta haɗa haɗaɗɗen chicken salad tare da fruits salad,sai kunun aya wanda ya ji kwakwa da dabino da condensce milk da madarar gari.
Kwashe kayan ta yi ta jere su a dining table, sannan ta saka kunun aya da fruits salad a cikin fridge,gyara kitchen ɗin ta yi tsaf sannan ta ƙara kunna turaren wuta a parlon ƙasa ta haye sama zuwa bedroom ɗin ta domin ta yi wanka.
Chapter 67 · 0% Book details