← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 80

Sashe 23

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ɓangaren su HALIMATU kuwa, lokacin da mai kwalliya ta fara tsatsara mata light make-up mai kyau sosai,sai taji abin kamar almara,wai yau itace ake yi mata wannan abun da ƴan makarantar su suke basu labarin anayi a birni!! bata san lokacin da murmushi ya suɓuce mata a kan kyakkyawar fuskarta ba.tana cikin tunanin ne taji mai kwalliyar tana taɓa mata gashi tare da ƙara gyara mata shi.

Bayan an gama yi mata make-up ɗin ne MOMY ta ɗakko mata wani less white colour da aka yimasa ado da orange ɗin flowers yayi matuƙar kyau ta miƙa mata tare da cewa "kiyi sauri ki shirya zata ɗaura miki ɗankwali"HALIMATU tace "to" tare da ɗaukar kayan ta shige toilet don ta shirya.cikin minti biyar ta saka kayan tare da kallon kanta a mirror ɗin toilet ɗin,woww ita kanta ta yaba da irin mugun kyawun da tayi sai kace wacce aka yiwa wankan inji!!

Ga ɗinkin less ɗin street gown ne ya bi shafe ɗin jikin ta ya zauna sosai abin sha'awa, cikin sauri ta fito daga cikin toilet ɗin sabo da tasan ana jiran ta.daga MOMY har mai kwalliyar sakin baki suka yi suna kallon kyan da tayi a cikin kayan"ma sha Allah doughter kinyi kyau sosai"MOMY ta faɗa tare da ɓuɗe clothes din HALIMATU ta ɗakko mata hill shoe orange colour da medium veil shima orange,ajiyewa tayi akan bed tare da cewa "bari naje na dawo"bata jirawo amsarsu ba ta fice daga cikin ɗakin.

Batare da ɓata lokaci ba mai kwalliyar ta tsan tsarawa HALIMATU ɗaurin ɗankwali mai matukar kyau, gashin gaban goshin ta ya kwanta lublub gwanin sha'awa,kalar ɗaurin da aka yi mata irin mai ɓuɗewar nan ne,hakan ne ya sanya jelar gashin nata fitowa har wajen ɗuwawun ta.ita kanta mai make-up ɗin kallon ta kawai take,tana mamakin irin baiwar kyan da Allah yayi wa wannan yarinya,ga diri kamar wata babbar mace!! nan gaba idan ta ƙara girma ai akwai kallo!!gaskiya wannan matar manya ce!!ta ƙarshe tunanin ta a cikin zuciyar ta.

Sallamar da suka ji ne yasa suka ɗago da kansu a lokaci guda, MOMY ce ɗauke da wani ɗan ƙaramin boxes a hannun ta.direct gaban HALIMATU ta nufa tare da buɗe box ɗin ta ciro wani set ɗin sarƙar gold ta sanyawa mata sarƙa da ɗan kunne da awarwaro tare da zoben su,dama ta tanade sune tun da daɗewa da suka je dubai ita da daddy ta siyo musu ita da yusra.

"Ma sha Allah doughter,kinyi kyau sosai wallahi! ai wani abin ma sai ranar auren ki" ta faɗa tana dariya HALIMATU tayi sauri ta rungume MOMY tare da ɓoye fuskar ta,ita kanta make up artist ɗin sai da suka yi mugun burgeta sosai.zaunar da ita MOMY ta yi abakin bed tare da ɗaukko turaruka masu daɗin ƙamshi ta feshe mata jikin ta dasu,nan take gaba ɗaya ɗakin ya ɗauki wani irin ni'imtaccen ƙamshi mai sanyaya zuciya.

Batare da ɓata lokaci ba MOMY ta dube ta tace "ki zauna a nan bari naje na dawo" kanta kawai ta girgiza.fita momy suka yi ita da mai make up ɗin dan zuwa ta sallame ta,suna sauka ƙasa ta bata kuɗi haɗe da turaruka ta sallame ta, godiya tayi tare da ficewa daga parlon.kitchen MOMY ta nufa ta taradda baba ladi tana ta faman gyare-gyaren wajen da suka ɓata"sannu da aiki baba,kinga na tafi na barki da aiki ko! wallahi ina can wajen shirya HALIMATU shiyasa kika jini shiru"

Baba ladi tace"wallahi babu komai hajiya! ai ba wani akine mai yawa ba,mudai fatan mu Allah ubangiji ya dai dai ta kansu" "ameen" MOMY tace tare da umar tar baba ladi da su kwaso girke girken da su kayi sukai parlon baƙin daddy,wasu kuma kan dining room aka jera su.bayan sun gama ne baba ladi ta ɗauki nasu ita da uwani ta wuce zuwa sashen su,ita kuma momy da dawo parlon ta zauna.

Zamnta keda wuya taji tsayuwar mota,har ta fara tunanin ko baƙon ne ya ƙaraso sai kuma taji sallamar su daddy shida hafiz,amsawa tayi tare da tashi tsaye tana yiwa daddy sannu da zuwa,amsawa yayi tare da nufar kan dining table ya zauna, shima hafiz ɗin zama yayi tare da cewa "MOMY barka da gida" tace "barka dai,ya naga daga shigowar ku kun nufi kan dinnig!!".

Daddy yace"to ba dole ba mun kwaso gajiya da yunwa,pls zo kiyi serving ɗin mu"batare da taƙara cewa komai ba ta ja kujera ta zauna ta fara serving ɗinsu.daddy ta fara zubawa funkaso da pepper soup na kan rago,sannan ta kawo wani plate daban ta zuba masa spring rolls da samosa tare da fruit salad a wani kyakkyawan bowl.kallon ta yayi yana mai jin wani sanyi a cikin zuciyar sa,shima hafiz serving ɗin shi tayi da chicken buryani rice ta zuba masa gas meat a gefe,sai spring rolls da samosa.tunda suka fara cin abincin babu wanda yayi magana har sai da suka gama sannan suka dawo cikin parlon suka zauna, shi Hafiz ficewa yayi ya nufi part ɗinsu, akabar MOMY da daddy suna hira.

"MUKHTAR"

A ɓangaren su MUKHTAR kuwa sai da suka biya super market suka yiwa HALIMATU shopping sannan suka nufo hanyar gidan,suna isowa suka tsaya a bakin get ɗin gidan tare da yin horn,mai gadi ne ya leƙo ta ƙaramar kafa yaga baƙuwar mota.cikin sauri ya fito ya nufi motar tare da tsayawa yana ƙarewa motar kallo,sauke glass ɗin motar MUKHTAR yayi tare da cewa "Assalamu alaikum"ya faɗa yana mai miƙowa baba hannu.

Cikin sauri baba ya miƙa masa hannu suka gaisa tare da cewa "gurin wa kuka zo??" MUKHTAR yayi shiru kamar bazeyi magana ba sai kuma can yace "gurin Alhaji mukazo! Allah yasa yana nan??" washe baki baba mai gadi yayi tare da cewa"wallahi bai daɗe da dawowa ba shida hafizu! ku shigo yana nan ciki"ya faɗa tare da juyawa ya shige ciki tare da ɓuɗe musu get ɗin.

Ba tare da ɓata lokaci ba MUKHTAR ya danna hancin motar sa cikin gidan tare da yin parking ɗinta a parking space.juyowa yayi tare da kallon meena yace mata "fito mu shiga ciki"to tace tare da fitowa daga cikin motar,shima fitowar yayi ya kalli meena yace"ki shiga daga ciki ki sanar musu zuwan mu,zansa mai gadi ya shigo da kayan" kanta ta girgiza alamar to tare da wucewa ta nufi babbar ƙofar da ta gani.

Tana zuwa bakin ƙofar tayi nocking tare da yin sallama,daga ciki taji an amsa mata tare da bata izinin shigowa.tura ƙofar tayi tare da ƙara yin sallama a karo na biyu ta shiga cikin Parlon, daddy da MOMY ta iske zaune akan kujera suna hira, durƙusawa tayi tare da gaishe su cike da ladabi,amsawa sukayi fuskarsu a sake suna mai ya bawa da irin tarbiyyar ta.

Duƙar da kanta tayi ƙasa tare da cewa "dama tare muke da yaya MUKHTAR shine yace na shigo na........bata kai ga ƙarasa maganar ba daddy ya katse ta hanyar cewa "dama tare da MUKHTAR ɗin kuke shine ya tsaya a waje kamar wani baƙo!! hala ke ƙanwarsa ce dan naga kuna kama"girgiza kai tayi alamar ae,yace"to maza kije ki gaya masa ya shigo inji ni" to tace tare da miƙawa ta fice daga Parlon.

Kallonsa ya mayar kan MOMY tare da cewa " tashi kije ki kirawo HALIMATU tun da yaron nan ya iso" "to" tace tare da miƙewa ta haye up stairs.

"MEENA"

A ɓangaren meena kuwa, lokacin da ta fito tsaye ta samu MUKHTAR a parking space gaban motarsa ya fito da manyan manyan ledodi guda uku yana magana da mai gadi,tana ƙarasowa wajen tace masa"yaya daddy yace ka shigo" "to" yace tare da cewa baba mai gadi "baba ka shigar da kayan ciki" "to" baba yace tare da kinkimar kayan yayi gaba.

Kallon sa MEENA tayi tare da cewa "muje yaya" batare da yayi magana ba tayi gaba ya bita a baya.kafin su ƙarasa suka haɗu da baba mai gadi ya fito tare da cewa MUKHTAR ya kai kayan, godiya yayi masa tare da wucewa sukayi sallama suka shiga cikin parlorn.

Dadddy suka tarar zaune akan kujera, durƙusawa MUKHTAR yayi ya gaishe shi,amsawa yayi tare da cewa "maimakon ka shigo daga ciki shine ka tsaya a waje kamar wani baƙo!!"sunkuyar da kai yayi tare da yin murmushi yace "ayi haƙuri daddy" yace tom shikenan ya mutanan gidan?? dafatan kowa yana lafiya ko??" MUKHTAR yace "lafiya ƙalau daddy,duk sunce a gaishe ku" "to masha Allah muna amsawa".

Juyawa yayi ya kalli kayan da mai gadi ya shigo dasu yace"haba MUKHTAR harda wata ɗawainiya kuma!! maimakon kazo kanka tsaye basai ka wahalar da kanka ba!!" yace "ba komai daddy" miƙewa yayi tare da cewa"to mungode Allah ubangiji ya ƙara buɗi" ya faɗa tare da buɗe wata babbar ƙofa yace da MUKHTAR bismillah"

Miƙewa MUKHTAR yayi tare da shiga cikin parlorn meena ta mara masa baya itama.juyawa daddy yayi tare da haye wa up stairs ya ƙwalawa MOMY kira,amsawa tayi tare da fitowa yusra na biye da ita "MUKHTAR na jiran HALIMATU" MOMY tace" Okey tom bari nayi mata magana".

Juyawa tayi tayi tare da shigewa cikin bedroom ɗin HALIMATU,ƙara fesa mata turare tayi tare da miƙa mata mayafi tace "oya tashi kije ku gaisa yana parlon baƙin daddyn ku shi da ƙanwarsa,ga auta nan ta raka ki"rau rau tayi da idanun ta kamar zata yi kuka ta kalli MOMY.

MOMY tace "kar kiyi kuka mana my beautiful daughter! zaki ɓata kwalliyar ai, sannan kar ki manta da abin da na faɗa miki kinji" girgiza kai tayi tare da muƙewa tsaye MOMY ta karɓi mayafin ta yafa mata sannan ta ce mata"muje" wucewa tayi suka biyo ta a baya ita da yusra.

Suna sakkowa MOMY ta samu waje a kan kujera ta zauna tana daddana wayar hannun ta,hannun auta ta kama tare da nufar ƙofar Parlon.dakatawa ta ɗanyi jimm tare da yin sallama,amsa mata taji anyi tare da bata izinin shigowa.
Chapter 23 · 0% Book details