Sashe 20
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lokacin da suka ƙarasa gidan sunga tashin hankali,domin sun iske malam musa da iyalin sa cikin wani irin hali gwanin ban tausayi,gaba ɗayan su kwance suke idan ka ɗauke salmanu da yake zaune.malam musa yana ta nishin wahala gaba ɗaya an nannad'e masa ƙafar da ya karye da bandeji,ita kuma lamunde gwiwar aka nannad'e mata abin ka da mai jiki duk ƙafar ta kumbure.
Malam musa na ganin su hanne ya fashe da kuka tare da cewa "altine kinga abin da laure ta jawo min ko?? ina zaman zamana banji ba ban gani ba ta jefani cikin bala'i ta gudu ta barmu!! Yanzu wanene zai yi jinyar mu??"ya faɗa yana share hawayen da suka zubo masa.lamunde ta buɗe baki da ƙyar tace"Allah ya isa tsakani na da laure!! wallahi bazan taɓa yafe mata ba duniya da lahira, wallahi laure ta zama muguwar azzaluma!! taje ta ciyo kuɗin ta'kadirin yaron nan yanzu gashi ta gudu ta barmu cikin bala'i" ta faɗa tana sheshe'kar kuka .altine ta buɗe baki zata yi magana kenan suka ji sallamar inna laure.
"MUKHTAR"
A ɓangaren su MUKHTAR kuwa lokacin da suka fita daga gidan basu nufi ko ina ba sai sahad store,nan take yayi parking a parking space tare da buɗe motar ya fito.zagayo wa yayi ya buɗewa sahal da amal,ita ma meena buɗewa tayi ta fito daga cikin motar,tare suka jera suka nufi cikin store ɗin.ba tare da b'ata lokaci ba suka nemi ƙaton basket suka fara jidar kaya.
Babu abin da basu ɗaukar wa yaran na amfani ba, Tun daga kan kayan sawa sheos nigh dress, teddy's, biscuits chocolate sweets da sauran su.mukhtar yace da meena ita ma ta zaɓi abin da take so,cikin murna ta ɗauki basket ta fara zab'an abubuwan da take da buƙata.bangaren kayan cosmetics ta koma nan ta rinƙa kwasar kaya tana lodawa, ɓangaren turaruka ta nufa tafara kwasar haɗad'd'un turaruka,bayan ta gama ne ta ɗakko kwando ni'ki ni'ki a hannun ta baza to ba tsammani taji an bangaje ta, gaba ɗaya ta kifa ta faɗi ƙasa wanwar kayan hannun duk suka watse a gurin,tana ɗagowa tayi arba da..............
Ina godiya ƙwarai da gaske da addu'o'in ku a gare ni tare da fatan alkhairi, kuɗin na daban ne kuma na musamman ne masu mutuƙar mahimmanci a gareni ,ina godiya sosai tare da fatan alkhairi.............🙏🏻🙏🏻
Daga al'kalamin FATIMA BINTU ABDULLAHI (UMMU AYSHA).........✍🏻
08162055134.
💝💞 HALIMATU 💝💞
(Love, sacrifices, destiny,& betrayed)
💝💞💝💞💝💞💝💞
Story & Writing
By
FATIMA BINTU ABDULLAHI (UMMU AYSHA)
Ƙarƙashin jagorancin
(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)
Golden pens...............✍🏻
💝💞💝💞💝💞💝💞
2024 novel
💝💞💝💞💝💞💝💞
Page_____________25&26
"MEENA"
Lokacin da tayi karo da mutum ta faɗi ƙasa wanwar a gurin,gaba ɗaya kayan da suke cikin basket ɗin suma duk suka watse a gurin,cikin sauri ta ɗago da kanta domin ganin mahalukin da ya ture ta ta faɗi ƙasa,karaf idanun su suka haɗu cikin na juna,nan take suka ji ƙirjin su ya buga sakamakon haɗa idanun da suka yi cikin na juna.
Hafiz ne yayi ƙarfin hali yace mata "ayya sorry dan Allah,wallahi ba'a son raina na ture kiba saurin da nake yi ne yajo hakan! dan Allah kiyi haƙuri".ya ƙarasa maganar yana duƙawa tare da tattare mata kayan da suka zube a ƙasa yana zuba mata su cikin basket ɗin.a ɓangaren mukhtar kuwa, lokacin da yaga faɗuwar meena,cikin sauri ya taho hannun sa riƙe da yaran sa ya ƙaraso in da take.
Yace"subhanallahi auta,muna daga can na hango faɗuwar ki! sannu! Ina fatan bakaji ciwo ba ko??" tace"banji ciwo ba yaya, wannan mutumin ne ya bugeni na faɗi" ta ƙarasa maganar tare da nuna masa mukhtar.kusan tare suka jiyo suka kalli juna cike da mamaki akan fuskokin su,cikin sauri hafiz yace"kamar mukhtar nake gani!" MUKHTAR yace "ba kama bace nine Hafiz,ashe kai ne ka buge min ƙanwata"ya faɗa fuskar sa ɗauke da murmushi.
Hannu Hafiz ya miƙa masa suka yi musabaha tare da cewa "hmmm kedai bari! wallahi ina sauri na ƙarasa gida sabo da na gaji sosai,ban kula da ita ba na buge ta,ashe ma ƙanwata ce na buge" ya faɗa yana kafe ta da fararen idanun sa.bakinta ta zunɓuro tare da miƙewa tsaye ta ƙetare su ta wuce ta barsu tsaye a nan gurin tayi ficewar ta daga gurin gaba ɗaya.
Bayan wucewar tane hafiz ya duƙa tare da ɗaukan baaket ɗin nata yace"lallai na yiwa ƙanwata babban laifi,dole in san yadda zanyi na wanke kaina" ya faɗa yana murmushi. shima MUKHTAR ɗin murmushin yake yi,kallon hafiz yayi tare da cewa"ya gida, yasu daddy da MOMY,ya kukaje gida rannan!! dafatan kowa yana nan lafiya dai ko"
"Wallahi kowa yana nan lafiya k'alau,yasu momy da daddy" MUKHTAR yace suna nan lafiya ƙalau" yace "to ma sha Allah"hafiz ya kalli sahal da amal yace"waɗan nan yaran ka ne??" kai ya girgiza tare da cewa "ae sahal da amal ba"ma sha Allah, Allah ubangiji ya raya mana su" MUKHTAR ya amsa da ameen.
Ba tare da ɓata lokaci ba suka jero suka fara tafiya,hannun hafiz riƙe da basket ɗin meena,yana tafe yana ƙara zuba mata wasu kayan,duk abin da yaga ya burgeshi ɗauka yake yi ya saka mata,a haka har suka ƙarasa wajen paymen ɗin kuɗin.ba tare da ɓata lokaci ba hafiz ya miƙa musu basket ɗin,bayan an gama lissafa wa ne ya ciro a t m ɗinsa tare da miƙawa yace a cire kuɗin, dama shi MUKHTAR ya riga da ya biya na yaran nata ne yake jira ta gama ya biya su tafi.
Buɗe baki MUKHTAR yayi da nufin yin magana Hafiz ya ɗaga masa hannu tare da dakatar da shi yace"karka ce komai! ai nima ƙanwata ce! dan na biya mata kuɗi ai ba laifi nayi ba!!"shiru MUKHTAR yayi ba tare da ya ƙara cewa komai ba.bayan an gama ne ɗaya daga cikin ma'aikatan ya ɗakko musu kayan ya kawo musu har bakin mota.
MUKHTAR ya buɗe boot aka saka masa kayan a ciki.sallama suka yi da junan su tare da exchanging numbers.meena da ke tsaye tana ta satar kallon mukhtar cikin rashin Sa'a ya ɗago karaf suka haɗa idanu dashi,kamar ta nutse a gurin ta ji sabo da kunya.buɗe baki yayi tare da cewa "to ƙanwata ni zan tafi tunda kinƙi kiyimin magana sabo da haka ki kulamin da kanki" daga haka ya juya ya bar gurin ya nufi motar sa ya shiga yaja ya bar gurin.bayan tafiyarsa ne MUKHTAR yace mata "shiga mota mutafi" nan suma suka shiga suka ya ja motar tare da barin wajen lokacin da suka ƙarasa gida a bakin get ya ajiye su, shi kuma juyawa yayi ya tafi gida . da taimakon su ba mai gadi aka shigar musu da kayan cikin gidan.
Suna shiga suka iske momy zaune ita kaɗai a falo,da gudu yaran suka je suka rungume ta suna murna,ita ma cikin murnar ganin su tare da soyayyar su ta kamo su zuwa jikinta ta rungume su tana yi musu oyoyo.ta kai duban ta gurin da meena take zaune rashe rashe tace mata"auta har kun dawo??" tace wallahi MOMY mun dawo baki ji gajiyar da nayi ba" ta cigaba da cewa"kinsan dama jikin nawa bana jin daɗin sa shi yasa" ta ƙarasa maganar tana lumshe idanun ta.
MOMY tace"sannu auta, Allah ubangiji ya sawawaƙe.yanzu ku tashi muje sama muyi salla sai kici abinci kisha magani" tace "to" tare da miƙewa tsaye,juyowa tayi ta kalli MOMY tare da cewa"MOMY kinga kayan da yaya ya siyo mana!" Juyawa MOMY tayi tare da kallon kayan tace "na gani auta, Allah ubangiji ya saka masa da alkhairi,ku wuce muje sama zansa baraka ta kai kayan sama,ta ƙarasa maganar tare da kama hannun yaran suka wuce saman.
"RUFAIDA"
A ɓangaren mahaifin RUFAIDA kuwa,lokacin da Alhaji Auwal mahaifin MUKHTAR ya katse wayar sa ya barsa da waya a hannu baki sake, tsayawa yayi sakato kamar an dasa shi agurin,gaba ɗaya jikin sa ya mutu.tunani yake yi a cikin zuciyar sa "wai shin me yake shirin faruwa ne??,ni Alhaji Auwal zai yiwa haka??,ni zai gayawa cewa ɗansa ba zai mai da ƴata ba??, lallai dole na tashi tsaye, idan ba haka ba komai ma zamu iya rasa shi".
Ya ci-gaba da cewa "yanzu yau kusan kwana uku rabon da MUKHTAR ya bugo min waya ya gaishe ni fa, tabɗi jam!! ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ci-gaba da cewa "ni bama wannan ba, ɗan kuɗin da yake turo mn akai a kai suma yanzu ya dena tun da yarinyar nan ta dawo gida,to wallahi ba zai yiwu ba dole ne nasan yanda zan yi yaron nan ya maida ita,idan ba haka ba akwai matsala"ya ƙarasa maganar tare da juyowa ya koma gida.
Lokacin da ya ƙarasa gida ya zayyane wa hauwa mahaifiyar rufaida abin da ya faru tsakanin sa da Alhaji Auwal mahaifin MUKHTAR,nan take ta ƙundumo wani mugun ashar tare da cewa "au haka yace shi auwalun,to wallahi zai san yayi damu dan sai mun koya musu hankali dukkan su,ya kamata kaje ka samu malam awaisu kayi masa bayanin duk abin da yake faruwa,ni ɗin ma ba zama zanyi ba, dole na tashi na nemo mana mafita idan ba haka ba yaron nan nema yake ya suɓuce mana!!" taƙarasa maganar tare da shigewa cikin ɗakin ta ta ɗakko mayafi ta yafa ta kama hanya ta fice daga gidan.
"HALIMATU"
A ɓangaren su HALIMATU kuwa, washe gari tunda asuba da ta tashi bata koma ba, bayan sun gama girka break fast taje tayi wanka ta shirya cikin black abaya mai white ɗin stone,ta feshe jikin da turaruka masu daɗin ƙamshi.ba ƙarsmin kyau tayi ba,fatar ta har wani shinning da glowing takeyi ,idan ka ganta sai ka ƙara kallon ta,bazaka taɓa tunanin cewa itace HALIMATUn nan ta ƙauye ba.
Jaka ta ɗakko mai kyau madai dai ciya ta ruƙe a hannun ta, sannan ta ɗakko wani hill shoe ta sanya a kyawawan ƙafafun ta sannan ta ƙara gyara rolling ɗin mayafin ta ya zauna sosai.ficewa tayi daga cikin ɗakin tare da sakkowa ƙasa cike da nutsuwar da ta zame mata jiki.gaba ɗaya ɗagowa suka yi suna kallon ta,ƙasa ƙasa hafiz yake kallon ta yanda babu wanda zai gane kallon ta yake yi.