← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 80

Sashe 30

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nura yace "Allahu Akbar, gaskiya naji daɗin wannan labarin ƙwarai da gaske abokina, kuma ina tayaka murna sosai da sosai Allah ubangiji ya tabbatar mana da Alkhairin sa, Allah ubangiji ya haɗa kawunan ku yasa Albarka". "ameen ameen abokina,nagode ƙwarai da gaske Allah ubangiji ya bar ƙauna".

"Yanzu yaushe ne lokacin bikin??" Ajiyar zuciya MUKHTAR ya sauke tare da cewa "Nan da shekara ɗaya muke so ayi bikin, Amma kuma iyayen ta sun ce sai nan da shekara biyu, sabo da yarinya ce ƙarama duka duka ba tafi shekara sha shida zuwa sha bakwai ba.sannan kuma yanzu ne zata shiga jami'a!, amma daddy yace min yayi magana da babanta a rage shekara biyun abarshi nan da shekara ɗayan! Sunce masa za su duba su gani idan da yiwuwar yin hakan!!". Ya faɗa yana sauke ajiyar zuciya.

Nura yace "haka ne gaskiya,ya kamata su barshi nan da shekara ɗayan dan gaskiya shekara biyu yayi mana nisa, Maganar ƙanƙanta kuma ai waɗanda suke shekara sha biyar ma anyi musu aure sun zauna tsaf bare ita! karatu kuma ba matsala bane ba ko a ɗakinta ne zata cigaba!!". wannan haka yake! nima abin da na gani kenan! duk babu abinda zai ga gara in sha Allah, Allah ubangiji ya tabbatar mana da Alkhairin sa"

"Ameen abokina in sha Allahu ma kayi dacen mata,domin ni daga jin yadda ka bani labarin ta yarinyar ta kwanta min a raina sosai, in sha Allahu Allah ya karɓi addu'ar ka ya duba irin haƙurin da kayi shine ya saka maka da babban Alkhairi". MUKHTAR yace "Ameen abokina".

"To yanzu ya kamata mu fara shirye-shirye tun yanzu,domin biki nake so mu yi na kece raini!" To shikenan abokina na baka wuƙa da nama kayi duk yadda kaga dama!!" Murmushi Nura yayi tare da cewa "babu damuwa abokina Allah ubangiji ya nuna mana lokacin" MUKHTAR yace "ameen".

"Ya maganar tafiya??" "Tafiya tana nan in sha Allah nan da sati ɗaya ko biyu, sabo da daddy yace in tattaro gaba ɗaya in dawo gida cikin satin nan". Nura yace"haka ne gaskiya,gwara ka dawo ɗin kafi sakewa tun da kai kaɗai ne a can ɗin!!" hakama MOMY ma tace gwara na dawo ɗin".

"To amma ya maganar RUFAIDA ne?? naji baka ce min komai ba!!" haɗe fuska MUKHTAR yayi tare da cewa "haba abokina! Ya zaka ɓatamin farin ciki na! Wallahi na jingi ne maganar wata RUFAIDA a gefe na barwa Allah lamari na, kullum addu'a ta itace Allah ubangiji ya zaɓamin abinda yafi Zama Alkhairi,kuma in sha Allahu Allah ya zaɓamin, sannan maganar RUFAIDA sai abin da daddy yace!!".

Nura yace"Allah ubangiji ya shige mana gaba, bari naje office akwai ɗan aikin da nake so na ƙarasa" ya faɗa yana miƙewa tsaye tare da ficewa daga office ɗin.bayan fitar Nura ne MUKHTAR ya faɗa kogin tunanin HALIMATU,yana so yaji muryar ta amma ya rasa ta hanyar da zai bi ya samu sugaisa yaji muryar ta.

Hafiz ne ya faɗo masa a cikin ransa,nan take ya ɗauki wayar sa yayi dialling numbern sa, ringing ɗaya biyu ana ukun ya ɗaga tare da yin sallama.gaisawa suka yi tare da tambayar juna iyayen su, bayan sun gaisa ne MUKHTAR yayi shiru bai ƙara magana ba, daga ɗaya ɓangaren Hafiz yace "kayi shiru MUKHTAR!! ko akwai abinda kake so kace??".

Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "dama ina so mu gaisa da HALIMATU ne idan kana gida!!". murmushi Hafiz yayi tare da cewa"au dama wannan ne yasa kayi shiru kake jin nauyin faɗa!!, shiru MUKHTAR yayi ba tare da yace komai ba,daga ɗayan ɓangaren Hafiz ya cigaba da cewa "yanzu bana gidan ina office, amma zan tura maka da numbern MOMY sai ka kirawo ta,nasan yanzu dai ta dawo daga makaranta idan ka kirawo zaka sameta in sha Allahu".

"Okay tom shikenan na gode sosai!" Hafiz yace "babu komai" daga haka suka yi sallama tare da ajiye wayar hannun su.miƙewa yayi tsaye tare da har haɗa ƴan kayan sa ya zuba a cikin briefcase dinsa ya fito daga cikin office ɗin zuwa parking space,domin yana so ya koma gida da wuri saboda ya fara haɗa ƴan kayan sa ya dawo gida baki ɗaya.

"HALIMATU"

A ɓangaren HALIMATU kuwa lokacin da Farouk ya rakata makarantar direct office ɗin shugan makarantar suka nufa,da sallama suka shiga tare da gaishe da shugaban makarantar, amsawa yayi tare da cewa "ma sha Allah malama HALIMATU,yau in sha Allahu zaki fara shiga aji! Inaso ki mai da hankali sosai kiyi karatu,banda wasa! banda ƙawayen banza!! ki kula sosai,kinga ba wani nisa kika yi a karatun nan ba!! Shi yasa nake ƙara jadda da miki akan ki dage da karatun karkiyi wasa!! Yanzu za'a kaiki aji huɗu, saboda haka ki mai da hankali sosai.in sha Allah zaki fahimci duk abin da za'a koya miki!!.

HALIMATU tace "in sha Allahu zan mai da hankali sosai" ustaz yace"ma sha Allah,haka ake so,yanzu bari na baki litattafan ki" ya faɗa tare da miƙewa tsaye ya buɗe wata wardrove ya ɗakko wasu litattafai ya miƙa mata.tsugunawa tayi harƙasa sabo da girma mawa ta saka hannu biyu ta karɓa tare da sakawa a cikin jakar ta.

Kallon HALIMATU ustaz yayi tare da cewa "muje na raka ki ajin da zaki rinƙa zama" tace "to" tare da miƙewa,shima Farouk miƙawa yayi ustaz ya bashi hannu suka yi sallama yace masa "zaka iya tafiya! Idan an tashi ƙarfe shida sai kazo ka ɗauke ta, idan kuma tana iya tafiya a ƙasa to shikenan ba sai kazo ba"

Yace" tom shikenan ustaz sai anjima,daga haka ya juya ya fice daga office ɗin,ita kuma HALIMATU tabi bayan ustaz zuwa ajin su.sallama suka yi tare da shiga cikin ajin,malam aminu da yake koyar da ɗaliban sa hadisi ne ya amsa tare da tasowa ya miƙa hannu suka yi musa baha, bayan sun gaisa ne ustaz yayi masa bayani game da HALIMATU.

Malam aminu yace " babu komai zanyi ƙoƙari in sha Allah,ficewa ustaz yayi,ita kuma HALIMATU ya nuna mata guri kusa da amira yace "ameera ga ƙawa nan ta zauna a kusa da ke,duk abin da bata gane ba ki dinga nuna mata". "To malam in sha Allah " daga haka suka ci-gaba da gudanar da karatu har zuwa lokacin tashi daga makarantar.

Farouq ne yazo ɗaukan ta basu suka zo gida ba sai ƙarfe ɗaya na rana.wanka tayi tare da yin Sallah sannan ta sakko ƙasa ta tadda momy da yusra suna zaune akan sofa suna kallon Indian series a tashar zeey world,gaishe da MOMY tayi tare da yi mata barka da gida, amsawa tayi tare da cewa "doughter ya makaranta ya gajiya??" HALIMATU tace "Alhmdllhi MOMY" " to ma sha Allah,tashi kije ki zuba abinci kici!" to MOMY".

miƙewa tayi ta nufi dining table auta na biye da ita,abinci me rai da lafiya ta zuba musu suka ci ita da auta suka ƙoshi.bayan sun gama ne ta gyara dinnig ɗin suka dawo parlon ta zauna a kusa da mommy, kwantar da kanta tayi akan cinyar MOMY tare da cewa "wallahi MOMY na gaji sosai"

Kallon ta MOMY tayi tare da ɗora hannun ta akan HALIMATU tana shafa kanta a hankali tace "sannu my doughter kinji,dole ki gaji tun safe sai wajen azahar,amma da kin saba shikenan! Kinga ɗazu farouq yake gaya min jam ɗin ku ta fito,to nayi magana da daddyn ku yace min zai yiwa MUKHTAR magana in yaso sai ya duba miki yayi miki duk abinda ya kamata, Allah ubangiji yasa muji Alkhairi".

Ameen HALIMATU tace tare da miƙewa zaune, fuskarta cike da fargaba.kallon ta MOMY tayi tare da cewa "ki kwantar da hankalin ki in sha Allah kina cikin waɗanda jarabawar su ta yi kyau" murmushi ne ya suɓuce mata akan fuskar ta, ta saka hannun ta tarungume MOMY tace "ameen ameen MOMY".

Kiran sunan MOMY tayi tare da cewa "MOMY kayan da aka kawo suna da yawa sosai wallahi baki gani ba!" "Na gani doughter mun gode sosai,saura kusa su a gaba keda yusra kuyi ta zubawa cikin ku zaƙi,ga farouq a gefe shima ya taya ku" Murmushi HALIMATU tayi tare da cewa "ai MOMY kayan na yaya farouq ne sai yanda yayi dasu!!".

Murmushi MOMY tayi tare da cewa"kunfi kusa ai keda mutumin naki! Kuyi faɗa ku shirya!!".daga haka suka ci-gaba da hirar su ta uwa da ɗiyarta har aka kirawo sallar la'asar,tashi suka yi suka gabatar da sallah,bayan sun idar da sallar ne suka ɗunguma zuwa kitchen tare da baba ladi.

A ɓangaren mukhtar kuwa,bayan ya koma gida bai tsaya ɓata lokaci ba ya tattara kayansa da dukkanin wani abu mai mahimmanci ya zuba a mota ya nufi gidan su.mukulli ya karɓa gurin MOMY ya shigar da kayan sa cikin part ɗin sa, dama already meena da masu aiki sun gyara part ɗin tsaf sai tashin ƙamshin ddaɗan turarukan wuta da air freshener yake.

Da taimakon MEENA ya shirya kayan sa tsaf, sannan ya shiga toilet yayi wanka ya shirya cikin ƙana nan kaya,abinci MEENA ta kawo masa yaci ya ƙoshi dam.bayan ya gama cin abincin ne ya dawo parlo ya zauna akan sofa tare da kunna t.v. ya kamo tashar Al-Jazeera, rage volume ɗin t.v. ɗin yayi tare da ɗaukar wayar sa yayi dialling numbern MOMY.

Sau uku tana ringing ba'a ɗauka ba,ana huɗu ne HALIMATU ta jiyo ringing ɗin wayar a parlo ta fito daga cikin kitchen ɗin ta ɗakkowa MOMY wayar ta kawo mata, picking call ɗin MOMY tayi tare da kara wayar a kunnen ta,daga ɗaya ɓangaren MUKHTAR yayi sallama tare da gaishe da MOMY cike da ladabi,amsawa MOMY tayi.

Shiru MUKHTAR yayi tare da sunkuyar da kansa kamar yana gaban MOMY,shirun da MOMY ta ji ne yasa tace "bangane me magana ba!!" Cike da jin matsananciyar kunya MUKHTAR yace "MOMY MUKHTAR ne! dama ɗazu na karɓi numbern wayan ki a gurin Hafiz!!"................

Ina matuƙar godiya da addu'ar ku a gare ni tare da fatan alkhairi, kuɗin na daban ne a cikin rayuwa ta, ina yi muku fatan alkhairi ƙwari da gaske, Allah ubangiji yasa muku da Alkhairin sa.

"Kuyi haƙuri da rashin jina da kuka yi kwana biyu,hakan ya faru ne sakamakon rasuwa da aka yi min, wannan dalilin ne yasa tafiya ta sameni,in sha Allahu zamu ɗora daga inda muka tsaya!"

Daga Alƙalamin FATIMA BINTU(UMMU AYSHA)..............✍🏻
Chapter 30 · 0% Book details