Sashe 40
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Umma ki ɗakko min mukullin motar RUFAIDA Mu tafi asibiti"
Juyawa ta yi da sauri ta koma ɗaki har tana yin tuntuɓe,ko minti biyu bata yi ba ta fito ɗauke da mukullin motar a hannun ta.miƙa masa tayi ya shiga cikin motar da sauri ya kunna, ita kuma ta shiga baya ta zauna tare da rungume RUFAIDA,motar ya ja suka fita daga gidan zuwa asibiti.
Suna isa aka karɓe ta cikin gaggawa likitoci suka rufa a kanta domin ceto rayuwar ta,kasan cewar asibitin da suke zuwa ne shi yasa basu wani sha wahala ba.
Kimanin two hours likitoci na kanta suna bincike,da ƙyar aka samu numfashin ta ya dawo da taimakon Allah, sannan aka saka mata oxygen sabo da numfashin ya daidaita,inda ko wacce gaɓa ta jikin ta bata motsi daga ido sai numfashin da take yi.
Lokacin da aka kiran sallar farko likitoci suka fito daga cikin emergency room ɗin,su umma da suke ta kaiwa da kawowa a ƙofar ɗakin ne suka bi bayan babban likitan da yake cikin su tare da cewa
"Doctor ya jikin nata?"
Juyowa ya yi ya kallesu tare da cewa
"Ku same ni a office yanzu nan!!"
Yana gama faɗi ya juya ya ci-gaba da tafiya.
Bin bayan sa suka yi har cikin office ɗin nasa suka samu guri suka zauna akan kujera,file doctor ya buɗe tare da yin ƴan rubuce rubuce daga bisani ya ɗago da kansa ya dube su tare da cewa
"HAJIYA patien ɗin ku da kuka kawo mun yi iya ƙoƙarin mu ganin mun gano abin da yake damun ta,domin dukkanin jikinta baya motsi daga idanunta sai numfashin da take yi ne kawai za'a gane cewa tana da rai, Babban abin da ya bamu mamaki shine duk wani gwaje gwaje mun yi mata shi amma komai normal yake nuna mana"
Shiru ya yi tare da sauke ajiyar zuciya ya ci gaba da cewa
"Yanzu akwai wasu manya manyan tests guda uku da zamu yi mata domin mu ƙara gano ainihin abin da yake damun ta,zaku biya dubu ɗari biyar da hamsin kuɗin tests ɗin!!"
Ya faɗa yana miƙo musu takardun tests ɗin.
Aminu ne ya yi ƙarfin halin muƙa hannun sa da yake rawa kamar mazari ya karɓi takardun,ya yin da umma ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro tana faɗin ta shiga uku.
Hannun ta Aminu ya ja suka nufi waje domin su kirawo ALHAJI USAMA su sanar da shi abin da yake faruwa, lokacin da Aminu ya kirawo numbern ALHAJI USAMA yaji wayar a kashe take ƙara kira ya yi domin ya tabbatar amma duk amsa ɗaya ce,sai da ya kirawo wajen sau goma sannan ya haƙura,a lokacin Hajiya Hauwa taci kuka ta ƙoshi abin duniya ya yi mata yawa,hannu ta guda biyu ta ɗauka ta rafka uban ta gumi da su,yayin da shi kuma Aminu yake ƙara trying ɗin numbern abban.
Suna cikin wannan halin ne kiran Hajiya RABI ya shigo wayar, ɗauka ta yi domin dama tana da niyyar kiranta domin ta tambaye ta ko tana samun numbern ALHAJI Garba.
Kukan da ta ji HUMAIRA tana yi ne yasa ta miƙe tsaye gaban ta ya yi wani irin faɗuwa dumm,bakin ta yana rawa tace
"HUMAIRA lafiya kike kuka haka? Ko wani abu ne kuma ya faru...?"
Sake fashewa da kuka ta yi domin ga dukkan alamu su hajiya Hauwa basu da labarin abin da yake faruwa.cikin kuka HUMAIRA ta zayyane mata dukkanin abin da yake faruwa.
Sakin wayar ta yi a ƙasa tare da kurma wani uban ihu mai firgitarwa ta yi zaman ƴan bori tana shure shure da koke koke,da gudu Aminu ya yo kanta yana tambayar ta me yake faruwa.....✍🏻
Ayi haƙuri da jina kwana biyu shiru sakamakon wani uzuri da ya gifta min..
Ina matuƙar godiya a gareku masoya na masu Albarka abin alfharina, ku ɗin na musamman ne a cikin zuciya ta,ina yi muku fatan Alkhairi ƙwarai da gaske, Allah ubangiji ya saka muku da mafificin alkhairin sa ya biya muku buƙatun ku na Alkhairi..
Daga alƙalamin..
FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)........✍🏻✍🏻✍🏻
Share fisabilillahi....
08162055134
💝💞 HALIMATU💝💞
(Love, sacrifices, destiny & betrayed)
💝💞💝💞💝💞💝💞
Story & Writing
By
FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA).....✍🏻✍🏻
Ƙarƙashin jagorancin
(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)
Golden pens..........✍🏻✍🏻
💝💞💝💞💝💞💝💞
A 2024 novel
💝💞💝💞💝💞💝💞
Pages ___________49&50
__________________Gunjin kukan da take yi da shure-shure shine ya jawo hankalin mutanan da suke wajen kan su,kafin kace wani abu mutane sun taru a wajen ana tambayar su abin da yake faruwa,in banda kuka babu abinda take yi duk ta ɗagawa Aminu hankali.
Ganin cewa bata da niyyar yin shiru ga kuma mutane sun yi cirko-cirko a kansu yasa ya durƙusa a gaban ta,hannu sa yasa ya kamo hannayen ta guda biyu ya ruƙe su gam-gam ya kalle ta cikin sigar lallashi yace
"Haba umma,ki nutsu mana ki gayamin me yake faruwa! kinga yanzu kukan da kike yi gashi nan ya jawo hankalin mutane kanmu, dan Allah ki nutsu ki gayamin abin da yake damun ki"
Ɗagowa ta yi ta kalleshi idanun ta suna zubar da hawaye babu ƙaƙƙautawa, cikin shesheƙar kuka ta buɗe bakin ta da ƙyar tace masa
"Aminu ka ƙyale ni in yi kuka ko naji sanyi a cikin raina da zuciya ta,ya zanyi da wannan mummunar ƙafdarar da ta same ni! gashi yanzu kuma ƴar gidan Hajiya RABI ta kirawo tana kuka take gaya min cewa ALHAJI sun haɗu da tsau-tsayin ƴan fashi akan hanyar su ta dawowa daga ENUGU! yanzu haka zancen da nake yi maka sun kashe ALHAJI Garba har lahira! Shi kuma mahaifin ku ba'a san halin da yake ciki ba!!"
Ta ci gaba da cewa
"Domin jami'an tsaron sunce musu sun kashe wasu daga cikin su,yayin da suka har-harbi wasu daga cikin su, yanzu haka sunce mu shirya mu tafi mu gano halin da ake ciki!!"
Ta ƙarasa maganar cikin wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.
Cikin tashin hankali Aminu ya miƙe a gigice hankalin sa yayi ƙololuwa wajen tashi,kana ganin sa ka san yana cikin tashin hankali, babu abin da yake furta wa sai Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. duban sa ya kai zuwa in da mahaifiyar ta sa take zaune, cike da juriya Irin ta ɗa namiji yace mata
"Kiyi haƙuri umma ki dena kukan nan dan Allah,ki tashi kije ki zauna a gurin RUFAIDA ki kula da ita,ni zanje gidan Abba garban naji dukkanin abin da yake faruwa,idan yaso dukkan wani abu da ake buƙata sai ki biya a yi mata kafin na dawo,tunda naga akwai kuɗi a hannun ki, ki tabbata kin biya kuɗin X-ray ɗin da za'a yi mata,idan yaso duk abin da yake akwai sai ki yi min waya ki gayamin"
Ya ƙarasa maganar Muryar sa na rawa sosai.
Miƙewa ya yi da sauri ya juya ya fara tafiya sboda wasu hawaye masu zafi da suke shirin zubo masa,kuma baya so mahaifiyar sa ta gani sabo da baya so ya ƙara karya mata zuciya.
Direct gidan ALHAJI Garba ya nufa, a ƙasa yake ta tafiya yana ta sauri kamar zai tashi sama,duk da kasancewar akwai ɗan tazara a tsakanin su.
Lokacin da ya ƙaraso ƙofar gidan ya iske mota sharon fake a ƙofar gidan,cikin sauri ya yi sallama tare da kutsa kai a cikin gidan sakamakon koke-koken da yake jiyowa daga cikin gidan.
A tsakar gidan ya same su a tsai-tsaye gaba ɗayan su,yayin da Hajiya RABI da HUMAIRA suke ta kuka maƙofta na ta rarrashin su.
Kai tsaye gurin Babban ɗan ALHAJI Garba ya nufa Kabiru, da yake Sa'anni ne kuma abokai ne suɗin,cike da dauriya da ƙwarin gwiwa yake ƙara tambayar sa game da abin da yake faruwa.
Cikin ƙarfin hali KABIRU ya yi masa bayanin dukkanin abinda yake faruwa,ya ƙara da cewa
"Yanzun nan muke so zamu tafi,mun ɗan tsaya jiran wan baban mu ne shi yasa ma ka same mu,ya kamata kai ɗin ma ka kirawo ƴan uwan mahaifin ku ka sanar da su,duk da dai nasan suna can Maiduguri babu wani ɗan uwan ku a nan kusa sai dai maƙofta,sabo da haka ya kamata ka kirawo Malam SALIHU maƙof cin ku ka sanar da shi abin da yake faruwa!"
Ya ƙarasa maganar yana goge hawayen da suka zubo masa.
Girgiza kansa yayi tare da zura hannu a cikin aljihun sa ya ɗakko wayar sa,sai da ya fara kiran wan baban su na Maiduguri ya faɗa masa, sannan ya kirawo malam SALIHU ya shaida masa abin da yake faruwa,sannan ya ƙara da cewa yanzu suke shirin tafiya gurin ɗakko su.
Babu abin da malam SALIHU yake sai nana ta kalmar innalillahi lillahi wa'inna ilaihi raji'un, hasbunallahu wanii mal wakeel.
Cikin raunin murya yace da Aminu su jira shi gashi nan zai shirya ya taho a tafi da shi, Aminu yace "to" tare da kashe wayar ya yi shiru ya faɗa duniyar tunani.
Lallai malam SALIHU ya cika mutumin ƙwarai,duk da kasancewar irin rashin mutunci da wulaƙancin da tozarcin da mahaifin su yake masa,amma duk da haka yanzu yace da shi za'a tafi,babu zumuntar komai sai haƙƙin maƙoftaka.
Wata irin ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ya sauke mai zafi tare da share hawayen da ya zubo masa akan kuncin sa.
Yana cikin wannan tunanin ne ya ji sallamar malam SALIHU a ƙofar gidan,kamar haɗin baki yana ƙarasowa babu daɗewa sai ga wan ALHAJI Garba shima ya ƙaraso, ba tare da ɓata lokaci ba suka ɗun guma gaba ɗayan su suka shiga motar suka tafi.
A ɓangaren ALHAJI Garba mutum uku ne,da KABIRU da Alhaji Mustapha wan ALHAJI Garba sai kuma ƙanin sa,duk da cewa ba wani mutun tasu Alhaji Garba yake yi ba, hasali ma baya bari su zo masa gidansa, sabo da a cewar sa Allah ya yi masa arziƙi ƴarsa na auren mai kuɗi shi yasa suke zuwa su ci banza, wannan dalilin ne ma yasa basu fiya zuwa gidan nasa ba.
A ɓangaren ALHAJI USAMA kuwa,daga Aminu sai maƙofcin su malam SALIHU limamin unguwar su,duk da shima ƴan uwan na sa ya banzatar da su baya kula dasu kwata-kwata,duk lokacin da suka ce zasu zo daga ƙauyen Maiduguri sai yace musu kar wanda ya sake ya zo masa gidansa,baya taimaka musu da komai na rayuwa,duk da cewa ya san halin da suke ciki na rashi da matsa-tsin rayuwa.