Sashe 32
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana kammala wa ta miƙe ba tare da ta cire hijab ɗin da yake jikin ta ba.
Ƙasa ta sakko inda ta iske mutanan gidan zau ne a dinnig suna yin dinner.
Durƙusa wa tayi ta gaishe da daddy tare da yi masa sannu da dawowa, amsawa yayi cikin sakin fuska tare da tambayar ta "ya makaranta?"
Tace "Alhmdllh daddy"
"To ma sha Allah, Allah ubangiji ya taimaka"
Tace "ameen daddy! Thank you"
Har zata miƙe ta ji daddy yana cewa "Jam ɗin ku ta fito doughter,ki fara shiri nan ba da daɗewa ba zaki fara zuwa makaranta, already mun riga da mun yi magana da Alhaji Auwal yace a bar komai a hannun MUKHTAR".
Ya cigaba da cewa "ina so kafin naga komai ya kammala duk da cewa yayyin ki na nan,to naga suma ɗin ayyuka sun yi musu yawa basu cika zama ba shiyasa".
"Sabo da haka ki fara shiri tun daga yanzu!"
"To daddy in sha Allahu"
"Yauwa doughter na, Allah ubangiji ya yi miki Albarka".
"Tashi ki zuba abinci kici"
Miƙewa HALIMATU tayi tare da cewa "to".
Dining table ta nufa ta jawo kujera ta zauna,gaishe da yayyin ta tayi tare da tambayar su aiki suka amsa mata da "Alhmdllh".
Egge rice ta zuba kaɗan tare da zuba cowslow a gefe,sannan ta saka pepper chicken a gefe tayi bismillah ta fara ci.
Tana gamawa ta jawo wani bowl mai ɗauke da fruit salad ta ɗiba a cikin wani ƙaramin bowl.
Madarar gari ta zuba tare da Syrup,sannan ta kawo ice cube ta zuba a ciki.
Miƙewa tayi ta haye up stairs sabo da momy da daddy suna nan zaune akan sofa suna hira.
Direct bedroom ɗinta ta nufa ta samu waje ta sauna a kan sofa ta fara shan fruit salad ɗin.
Lokacin da ta kai spoon ɗin bakin ta ta wani lumshe idanun ta sanyi da garɗin madara ga kuma ƙamshin plavour da zaƙin Syrup ɗin da ya ratsa ilahirin jikin ta da zuciyar ta,nan take taji wata irin nutsuwa ta saukar mata.
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana jin kanta cikin wani irin yana yi mai ɗauke da farin ciki tare da kwanciyar hankali.
Tana cikin wannan halin ne taji sallamar yusra ta shigo cikin ɗakin hannun ta ɗauke da wayar MOMY.
Miƙa mata wayar tayi tare da cewa
"Aunty gashi MOMY tace in kawo miki an kirawo ki!"
Karɓar wayar ta yi tare da cewa "to".
Juyawa yusra ta yi tare da ficewa daga ɗakin.
Fitar ta babu daɗewa wayar MOMY ta fara ringin,sai da ta yi ringin kusan sau uku sannan ta yi picking call ɗin tare da yin sallama.
Daga ɗaya ɓangaren MUKHTAR ya sauke ajiyar zuciya tare da amsa sallamar, gaishe shi ta yi cike da ladabi.
Cike da nutsuwar da ya samu sakamakon jin muryar ta ya amsa mata,domin in dai zai ji muryar ta yana tsintar kansa cikin kwanciyar hankali da nutsuwa,ya rasa dalilin me yasa yake tsintar kansa a hakan.
Kodan son da yake yi mata ne yasa hakan take kasancewa oho.
"Ai na zata har kin kwanta??
"A'a ban kwanta ba idona biyu! na dai kusa na kwanta ɗin.
"Okay to yanzu me kike yi ne??
"Yanzu na gama cin abinci fa"
Ta faɗa tare da kai fruit salad ɗin bakin ta tana lumshe idon ta.
"Wai me kike ci haka ne my love?
"Fruit salad ne nake sha!"
"To ina nawa??
"Da gaske kana so?
"Eh mana! Ina son fruit salad sosai my love, idan muka yi aure ai zaki dinga yi min shi sosai ko??
"Eh mana zan dinga yi maka kullum ma".
MUKHTAR yace " yauwa tom shikenan thank you my love".
Murmushi HALIMATU tayi tare da rufe fuskar ta kamar yana gaban ta.
"Ya maganar koyan girki??
"Ae yanzu na iya girki sosai, yau ma kusan ni nayi girkin,kuma daddy yace girkina yana da daɗi".
"Very good my wife haka nake so, kinsan ni mutum ne mai son girke girke kala kala masu daɗi, shiyas nake so ki koya domin ki dinga cika mana dining da kalolin abinci".
Ya ƙarasa maganar yana Murmushi.
"Ki shirya duk ranar da nazo ke zakiyi min girki na musamman"
"Yaushe zaka zo??"
"Kina so nazo ne??
Ya faɗa cike da zumuɗi tare da tashi zaune.
"To me zaka zo kayi??
"Zuwa zan yi in ganki!!
ko ba kya so na zo??"
Cike da murmushi tace "ina so mana!"
"Okay tom shikenan zanzo my love".
Ɗan shiru ne ya gifta a tsakanin su kafin MUKHTAR yace mata
"Albishirin ki??
Tace "goro"
"Gaskiya bazan faɗa miki ba sai kin bani tukwi ci!!"
"To wanne Irin tukwi ci kake so??"
MUKTAR yace "duk abin da kika bani ina so my love " ya faɗa fuskar sa ɗauke da murmushin jin daɗi.
HALIMATU tace "ka faɗi duk abin da kake so in dai ina da shi zan baka!
"Soyayyar ki nake so!! soyayyar ki nake so zalla HALIMATU!!
"Ina fatan na samu??
Cike da kunya tace ni dai kunya nake ji! Ta faɗa tana rufe fuskar kamar tana gaban shi.
"Jamb ɗin ku ta fito, already na riga na duba miki,yanzu admission kawai ya rage,shima kuma ba matsala bane in sha Allahu".
Wani irin tsalle ta yi ta zabura ta miƙe tsaye saura kaɗan wayar hannu ta ta faɗi ƙasa sabo da tsananin murna da farin cikin da ta tsinci kanta a ciki.
Cikin sassanyar muryar ta take ta furta"
Alhmdllh, Alhmdllh, Alhmdllh".
Tsintar kansa yayi shima da miƙewa cike da farin ciki yana jin daɗi a cikin zuciyar sa da ruhin sa, sakamakon farin cikin da abar ƙaunar sa take ciki
Wayar ta kara a kunnen ta ta fara zuba masa godiya cikin nutsuwar da ta zame mata jiki.
Ido kawai ya lumshe yana jin kansa a sama,wai shi ne yau a ke zuba masa godiya da fatan Alkhairi haka, abin da bai saba ji ba shi ya sa ya ji kamar wani sarki.
"Ki shirya bani tukwici na idan na zo".
Amsa masa ta yi da "to"
Daga haka suka yi sallama tare da ajiye wayar.
Ku yi haƙuri da wannan pls............
Daga alƙalamin FATIMA BINTU ABDULLAHI (UMMU AYSHA)
Share fisabilillahi........
O81 62055134.
💝💞HALIMATU 💝💞
(Love, sacrifices, destiny
& betrayed)
💝💞💝💞💝💞💝💞
Story & Writing
By
FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)
Ƙarƙashin jagorancin
(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)
Golden pens...............✍🏻
💝💞💝💞💝💞💝💞
A 2024 novel
💝💞💝💞💝💞💝💞
Pages____________39&40
"ALHAJI USAMA"
A ɓangaren mahaifin RUFAIDA kuwa, lokacin da ya fita ya barsu a cikin wannan halin bai zame ko ina ba sai gidan aminin sa ALHAJI Garba.
Sallama ya yi a ƙofar gidan tare da bubbuga ƙofar gidan,in da Allah ya taimake shi ya yi Sa'a yana cikin gidan,domin bai daɗe da dawowa ba.
Daga cikin gidan ALHAJI Garba ya amsa masa sallamar tare da fitowa waje domin ya gane muryar sa,hannu ya miƙa masa suka yi musabaha tare da gaisawa.
Waje suka samu suka zauna a kan dakalin da yake ƙofar gidan domin su ji daɗin tattaunawar da za su yi,bayan sun zauna ne ALHAJI USAMA ya dubi aminin na sa yace
"Gurin ka nazo akan matsalar nan ta RUFAIDA da mijin ta,a gaskiya ba zan ɓoye maka ba wallahi abin ya fara damu na,tun ina ganin matsalar nan a matsayin ƙarama gashi yanzu tana nema ta zame mana babba.
Gashi yanzu har ta kai ga yaron nan ko kira na ma ya dena yi,ɗan Alkhairin da yake yi mana duk yanzu ya dena yi,kuma na san munafukin uban sa ne ya ɗaure masa gindi.
Shi yasa ban yi ƙasa a gwiwa ba na tako takanas domin in zo in gaya maka wannan matsalar,domin na san kai kaɗai ne zaka taimaka min mushawo kan al'amuran!!"
Ya ƙarasa maganar tare da sauke wata irin ajiyar zuciya.
Girgiza kai kawai ALHAJI Garba yake yi,daga bisani ya ɗago da kan sa ya dube shi tare da sauke ajiyar zuciya.
"Lallai ALHAJI USAMA ka yi babban sake! wa ya gaya maka ana wasa da irin waɗannan mutanan! Ka duba kaga ko ni da nake da suruki wanda bai kai arziƙin naka surukin ba na ruƙe abina gam gam kuma na iya taku na,amma kai da yake kaga ana zuba muku ruwan kuɗi shiyasa ka saki jikin ka ba tare da ka ɗauki wani matakin ba??"
Gumin da ya tsatsafo masa a goshin sa ya share tare da kallon Alhaji Garba yace
"Yanzu dai mai faruwa ta riga da ta faru sai dai mu kiya yi gaba,dan Allah ka taimaka min".
Numfashi ya sauke tare da duban ALHAJI USAMA yace
"Akwai wani boka da yake yi min aiki!! Aikin sa kamar yankan wuƙa yake,kuma muddin ya yi muku aiki zaku ji daɗin aikin sa,sai dai shara ɗin sa yana da matuƙar wahala, amma idan zaka jure tabbas zaka samu abin da kake so!!"
"Zan iya jure koma mene ne idan har akan cikar burina ne"
"Tom shike nan,ka shirya zamu je wajen sa, sannan kuma ka tana di kuɗi masu yawa,domin ba'a nan yankin namu yake ba! A yankin kudan cin nigeria yake! Sabo da haka duk lokacin da ka shirya zaka iya yi min magana!!"
Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke tare da miƙewa tsaye,ya miƙawa ALHAJI Garba hannu suka musabaha tare da cewa
"Zan je Mu yi magana da Madam,duk yanda ake ciki zan sanar da kai!".
Daga haka suka yi sallama ya shige cikin gida,shi kuma ya kamo hanyar dawo wa gida.
Wannan ke nan........
"INNA LAURE"
A ɓangaren su inna laure kuwa,sauƙi yana ta samuwa Alhmdllhi,domin zuwa yanzu tana ɗan ruƙe sandar da baba lado ya bata tana ɗan taka ƙafar a hankali.
Shi kan sa baba lado ya ga kyawun gyaran,domin inna laure tana da kyan jiki sosai shiyasa gyaran ya yi kyau sosai.
Zuwa yanzu altine ta koma gidan ta,yanzu daga ita sai Hanne,kuma Alhamdulillah tana samun kyakkyawar kulawa,domin HANNE tana iya bakin ƙoƙarin ta wajen kula da ita.
A gefe guda kuma ga Sama'ila saurayin HANNE shima yana taimakawa sosai,kusan kullum sai ya zo duba INNA LAURE! Kuma duk zai zo sai ya ruƙo wani abin,idan naman nan ne ko kaza haka zai kawo, wani lokacin ma har da zabi.
Wannan dalilin ne yasa ya ƙara shiga ran hanne da inna laure,sakamakon kyauta tawar da yake yi wa mahaifiyar ta.