Sashe 60
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A ɓangaren su HALIMATU kuwa,bayan tafiyar su mukhtar direct bedroom ɗin ta ta nufa cike da farin ciki cewa ba ita kaɗai za'a yi wa aure ba har da HANNE,cikin sauri ta buɗe wardrove ɗin ta ta ɗakko wani kyakkyawan trolly bag ta shiga haɗa duk wani abu da tasan zata buƙata,sai da ta haɗa komai tsaf sannan ta jingi ne trolly ɗin a gefe.
Toilet ta nufa ta ɗauro alwalar sallar azahar,tana fitowa ta saka ƙaton hijab ɗin ta har ƙasa ta tada sallar,tana idarwa ta yi addu'o'in da ta saba a duk lokacin da ta yi sallar farilla sannan ta miƙe tare da cire hijab ɗin ta ninke shi ta ajiye a kan sallayar.
Gado ta haye ta jawo wayar ta da ke kan bed side drower cike da farin ciki kamar ba itace ta gama kuka ɗazu ba,kunna wayar ta yi tare da ajiye ta gefen pillow ɗin ta ta kwanta,jim kaɗan bacci ya yi awon gaba da ita saboda kukan da ta daɗe tana yi.
Ba ita ta farka ba sai lokacin da aka kirawo sallar la'asar,bayan ta idar da sallar ne ta sauka ƙasa domin shiga kitchen ta taya baba ladi aiki,kusan tare suka shiga kitchen ɗin ita da baba ladin,gaishe ta ta yi ta amsa cike da fara'a sannan suka fara shirin haɗa dinner.
Suna gamawa HALIMATU ta wuce zuwa sama bayan sun jere komai a kan dining table ɗin.wanka ta yi tare da alwala ta saka kaya marasa nauyi a jikin ta domin lokacin an fara kiran sallar magrib,sallar ta gabatar tare da yin azkar ɗin ta na marai ce,ba ita ta tashi daga gurin ba sai da aka yi sallar isha'i sannan ta miƙe tare da ficewa daga cikin bedroom ɗin ta sauka ƙasa.
Gaba ɗayan su ta tarar a kan sofa zaune har da daddy suna hira,gaishe da su ta yi sannan suka ɗunguma zuwa dining table domin su yi dinner,suna gamawa ta kwashe plates da bowls da food wamers ɗin ta kai kitchen ta wanke su,sauran abin cin abincin da ya rage kuma ta zuba su a cikin freezer.
Ko da ta dawo ta tarar da su akan sofa suna hira,kusa da momy ta dawo ta zauna a gefen ƙafafuwan ta,kallon ta momy ta yi tare da cewa,
"Doughter ina fatan dai kin shirya kayan na ki ko.?"
A hankali ta buɗe baki kamar bata son yin magana ta ce,
"Eh momy na shirya kayan"
"To ko kefa"
Daddy ne ya yi gyaran murya tare da cewa,
"Doughter momyn ki ta gaya miki lokacin da aka tsayar da bikin ku ke da ƴar uwar ki HANNE ko.??"
Cikin san yi ta ce,
"Eh daddy ta gaya min"
"Toh Alhamdulillah, gobe idan Allah ya kaimu zaku yi tafiya zuwa Dubai da China zaku siyo kayan ɗakin ki,ki tabbatar kin zaɓi duk abin da kike so idan kun je kin ji doughter.?"
"Toh daddy"
"Sabo da haka daga nan zuwa safiya ku kammala duk wani shiri da za ku yi domin ƙarfe goma na safe jirgin ku zai ta shi".
"Tom in sha Allahu daddy".
Kallon momy ya yi tare da cewa,
"Ɗazu hafeez ya zo ya same ni a office yake gayamin cewa ya samo matar da zai aura har sun dai dai ta kan su,ba ƙaramin farin ciki na ji ba da jin wannan labarin na sa,sabo da dama kullum buri na naga hafiz ya ajiye iyali,toh da na tambaye shi a ina iyayen yarinyar suke sai ya ce min ai yarinyar Alhaji Auwal ce Amina! wallahi baki ji yadda na yi farin ciki sosai ba, sabo da yarin yar akwai nutsuwa da kamun kai, sannan ga ladabi da biyayya.toh ban yi ƙasa a gwiwa ba na je na sami Alhaji Auwal ɗin a company ɗin sa na yi masa bayanin abin da yake faruwa! wallahi ba kiga farin cikin da bawan Allahn nan ya yi ba,in da yake cemin kawai a haɗe auren da nasu MUKHTAR gaba ɗaya! toh yanzu dai a haka muka yanke hukun cin sabo da haka sai ki shirya haɗo lefe daga chan idan kun je".
Wani irin farin ciki ne da annuri a saman fuskar momy, babu abin da yake fitowa daga bakin ta sai
"Ma sha Allah, Alhmdllh!"
Yayin da wata iriyar kunya ta rufe Hafiz ɗin ya rasa in da zai sa kansa,miƙewa ya yi saɗaf saɗaf ya fice daga parlon gaba ɗayan su suka san ya masa dariya har da halimatu.
Cike da farin ciki Sadiq ya ce,
"Lallai zamu sha shagalin gagarumin biki a gidan nan!wallahi har na ƙosa ranar ta zo"
Daddy ya ce,
"Lallai kham, gwara ma tun yanzu ku fara shiri kar lokaci ya ƙure muku"
Miƙewa Sadiq ɗin ya yi tare da cewa,
"Bari ma tun yanzu naje na same shi na ji shirye-shiryen da ya kamata mu yi"
Ya faɗa yana fita daga cikin parlon.
Tashi halimatu ta yi tare da cewa,
"Momy bari naje na duba naga ni ko akwai abin da ban saka ba sai na sa"
"Okay tom shikenan je ki duba"
Daga haka ta haye sama ita ma aka bar momy da daddy zaune a gurin,matsowa daddy ya yi kusa da momy ya jawo ta ya rungume ta sosai a jikin sa tare da cewa,
"Uwar gida sarautar mata,kuma amaryar Ibrahim,mamar amarya mamar ango! ya kamata a fara shirye shiryen bikin ko.??"
Hannun ta ta kai ta shafa sajen fuskar sa da gemun sa tare da cewa,
"Toh masoyi na! uban amaryar kuma uban ango mijin maram duk abinda ka ce a yi shi za'a yi"
Ta faɗa tana sakar masa wani irin French kiss a kumatu.
Gigicewa daddy ya yi ya kasa magana domin momy ta kashe masa jiki da salon ta gaba ɗaya,miƙewa tsaye ya yi ya cicciɓi momy da hannayen sa guda biyu ya haye sama da ita ya shige bedroom ɗin sa ya kulle ƙofa.
Washe gari tunda asuba da suka tashi basu koma bacci ba suna ta shirye-shiryen tafiya, ƙarfe takwas da rabi suka fito cikin shiri gaba ɗayan su har da su daddy,sabo da sune za su yi musu rakiya zuwa airport shi da Sadiq da hafiz.
Ba tare da ɓata lokaci ba suka shiga cikin motocin su suka ja tare da ficewa daga cikin gidan,suna zuwa airport ɗin suka tarar har an fara tan-tan ce mutane sabo da jirgin yana gab da tashi.
Nan take suma suka suka matsa aka tantan ce su ,ganin an fara shiga cikin jirgin ne ya sa suka yi sallama da su daddy tare da bin layin shiga cikin jirgin.
Suna shiga HALIMATU ta fara kalle kalle domin wannan shi ne farkon shiga jirgin ta,kama hannun ta momy ta yi suka nufi seat ɗin da numbers ɗin su suke,bayan kowa ya zauna ne aka umarci kowannen su ya sanya belt ɗin sa,da taimakon momy halimatu ta sanya na ta belt ɗin.
Ba a wani daɗe ba jirgin ya yi wata iriyar zabura ya tashi ya cilla zuwa sama,cike da tsananin tsoro halimatu ta ruƙunƙume momy tare da runtse idanun ta jikin ta yana rawa sosai,sai da jirgin ya yi dai-dai ta a sararin samaniya sannan ta zauke a jiyar zuciya tare da sakin hannun momy.......✍🏻✍🏻
Ina matuƙar godiya da addu'o'in ku a gare ni tare da fatan Alkhairi, ku ɗin na musamman ne a cikin zuciya,ina matuƙar alfahari da ku ƙwarai da gaske, Allah ubangiji ya saka muku da mafificin Alkhairin sa,ya biya muku buƙatun ku na Alkhairi🙏🏻🙏🏻
Daga alƙalamin
FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA).....✍🏻✍🏻
Game buƙatar littafin HALIMATU tun daga farko har zuwa in da aka tsaya ya tun tuɓe ni ta wannan numbern wayar👇🏻👇🏻
08162055134.
Share fisabilillahi.
💝💞HALIMATU💝💞
(Love, sacrifices, destiny & betrayed)
💝💞💝💞💝💞💝💞
Story & Writing
By
FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)....✍🏻✍🏻
Ƙarƙashin jagorancin
(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)
💝💞💝💞💝💞💝💞
Golden pens.....✍🏻✍🏻
A 2024 novel
💝💞💝💞💝💞💝💞
Pages__________ 77&88
____________lokacin da jirgin su ya sauka a Dubai international airport halimatu na ta sharar baccin ta sosai,ganin ba ta da niyyar tashi ne ya sa momy ta tashe ta domin lokacin mutane har sun fara fita daga cikin jirgin,kusan ma sune na ƙarshen fitowa daga cikin jirgin.buɗe idanu halimatu ta yi sakamakon tashin ta da momy ta yi ta shiga kalle-kalle kamar wata ba ƙauya,tana mamakin kyau da tsaruwar wannan gari sosai,ga mutanen garin nan suna ta shige da ficen su kowa yana ta harkokin sa babu ruwan wani da wani.
Taxi momy ta tare musu wadda zata kai su hotel ɗin da aka kama musu,dama tun kafin su zo daddy ya riga da ya yi musu booking hotel ɗin, suna ƙarasawa suka shiga cikin reception ɗin domin su yi musu bayani.bayan sun yi musu bayani ne wasu daga cikin ma'aikatan hotel ɗin ne suka ja trolly ɗin su tare da yi musu jagora har bakin room ɗin su suka buɗe musu tare da shiga da kayan su ciki suka ajiye musu suka juya suka fita.
Ɗakin room and parlo ne haɗaɗɗen gaske,babu abin da babu a cikin ɗakin,ga wani irin haɗaɗɗen ƙamshi da sanyin ac da yake tashi a cikin ɗakin.ba tare da ɓata lokaci ba momy ta wuce zuwa toilet domin ta watsa ruwa ta yi alwala ta rama sallolin da suke kanta,kwance ta bar halimatu a kan wata haɗaɗɗiyar sofa mai kama da gado ta yi ɗai-ɗai sabo da tsabar gajiya.
Lokacin da ta fito har baccin gajiya ya yi nasarar ɗauke halimatu,ta kowa ta yi har gaban sofar ta duƙa ta kirawo sunan ta a hankali,da yake ba tada irin nauyin bacci nan sai ta ware idanun ta da sauri akan momy,umartar ta momy ta yi da taje ta yi wanka tare da alwala ta zo ta yi sallah.