← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 80

Sashe 78

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaishe su mukhtar ya yi tare da miƙewa ya je gaban daddy ya ajiye robobin hannunsa ya ce,
"Daddy ga shi in ji ƴarka"
Ya ƙarasa maganar fuskarsa cike da fara'a.
Kallon halimatu momy ta yi tare da cewa,
"Haba doughter! Ke ko da yaushe bakya gajiya da hidima ne!!"
Murmushi kawai ta yi ta sunkuyar da kanta ƙasa ba tare da ta ce komai ba.

"Mun gode doughter, Allah ubangiji ya saka miki da Alkhairi ya baku zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba"
Momy ta amsa da,
"Ameen ameen"

Kallon momy mukhtar ya yi ya ce,
"Yauwa momy dan Allah ki duba ta,wallahi bata cin abinci sai fruits,shima sai na matsa mata take cin ɗan kaɗan.sannan cikin kwanakin nan jikin baya yi mata daɗi sosai".

Ƙura mata idanu momy ta yi tana nazarin maganar mukhtar,domin tabbas ita ɗin ma tun shigowarsu ta ga canji a jikin halimatun.tasowa ta yi ta ƙaraso gaban halimatu ta kama hannunta ta miƙar da ita tsaye ta ce,
"Ta shi mu yi tafiyar mu ɗaki kin ji doughter na"
Girgiza kai ta yi a hankali ta ce,
"Toh"
Sannan ta bi bayan momy suka wuce zuwa upstairs.

Suna wucewa daddy ya kalli mukhtar tare da cewa,
"Dawo nan kusa da ni ka zauna son!".
A hankali ya dawo kusa da shi ya zauna a saman sofa, kallonsa daddy ya yi ya ce,
"Ma sha Allah my boy,me yarinyar nan take baka haka ka fara yin irin wannan ƙibar lokaci guda!!"
Ya faɗa cike da mamaki fuskarsa ɗauke da yalwataccen farin ciki.
Wata iriyar kunya ce ta lulluɓe mukhtar ba tare da ya shirya ba!.
"Ka yi shiru my son baka ce min komai ba ko kunya ta kake ji ne.?"
Girgiza kai mukhtar ya yi tare da cewa,
"A a daddy!"
"Toh gaya min ya yanayin zaman naku yake! kar ka ji komai kaji.?
Girgiza kai ya yi tare da cewa,
"Wallahi daddy lafiya ƙalau Alhmdllhi muke"
Na take ya bashi labarin yanayin zaman su da halimatu da yanda ta riƙe masa yara tamkar ita ce ta haife su.
Girgiza kai daddy tare da cewa,
"Alhamdulillah! Alhamdulillahi! Alhamdulillahi! Allah mun gode maka, Allah ubangiji ya ƙaro muku zaman lafiya da kwanciyar hankali baki ɗayan ku"
"Ameen"
Mukhtar ya amsa, sannan suka ci gaba da hira kamar wasu abokai gwanin ban sha'awa.

A ɓangarensu halimatu kuwa, lokacin da suka ƙarasa cikin bedroom ɗin momy ta zaunar da ita a gefen bed ɗinta, sannan ta zauna a kusa da ita.
"Doughter kuna lafiya.?"
Cike da ladabi ta ce,
"Lafiya ƙalau momy"
"Babu wata matsala dai ko.?"
"Babu komai momy"
"Ki faɗa min idan akwai wani abu da son yake yi miki kin ji.?"
"Momy babu komai wallahi"
"Okay tom shikenan, Allah ubangiji ya ƙara muku zaman lafiya da kwanciyar hankali"
"Ameen momy"
"My son ya ce min bakya jin daɗi me yake damun ki.??"
Shiru ta yi ta sunkuyar da kanta ƙasa cike da kunya ba tare da ta ce komai ba.
"Kar ki ji komai my doughter,ki ɗauke ni a matsayin momyn ki kin ji.? Ki faɗa min duk wani yanayi da kike ji a jikin ki,ina so na duba ki na rubuta miki magani kin ji.??"
A hankali ta buɗe baki ta ce,
"Jikina ne yake yi min ciwo, kuma ba na iya cin abinci sai dai ruwan lipton da ɗan fruits,sai kuma ciwon kai da yake damuna!"
Kallonta momy ta yi cikin nazari sannan ta ce,
"Wannan watan kin yi period.??"
Da sauri halimatu ta ƙara yin ƙasa da kanta ta yi da shiru.
"Kar ki ji komai ki gayamin kin ji doughter"
"A'a ban yi ba"
"When last da yazo muku.??"
"Two months da suka wuce"
"Okay tom shikenan "
Ta faɗa tare da muƙewa tsaye.
First aid kit ta ɗakko ta buɗe ta ɗakko syringe da spirit da auduga ta zo kusa da halimatu ta zauna ta ce,
"Doughter bani hannuki!!"
Ta faɗa fuskarta babu alamar wasa, marairaice fuska halimatu ta yi kamar zata fashe da kuka Sabo da bata son allura.
A hankali ta miƙawa momy hannu tare da runtse idanunta, ɗaure hannu momy ta yi ta shafa spirit a wajen sannan ta buɗe syringe ta soka a hankali ta ja jinin ta cika syringe ɗin.ajiyar zuciya halimatu ta sauke ƙwalla na taruwa a cikin idanunta.
"Sorry my doughter kin ji"
Kanta kawai ta girgiza ba tare da ta ce komai ba.

Kallonta momy ta yi ta ce,
"Zan yi test ɗin jinin muga abin da yake damun ki idan ya so sai na rubuta miki magani ki.?"
A hankali ta ce,
"Toh momy,na gode Allah ubangiji ya saka da alkhairi ya ƙara girma"
Wani iri momy ta ji a cikin zuciyarta,nan take ta ju tausayin yarinyar ya kamata.
"Me kike so ki ci yanzu in kawo miki.?"
"Na ƙoshi momy bana jin yunwa ban daɗe da shan fruit salad ba"
"Okay tom ki kwanta ki huta kafin ku tashi tafiya kin ji!"
Ta faɗa tana buɗe first aid kit,wata sakko ƙaramar roba ta ɗakko ta zuba jinin da ta ɗiba a ciki ta a jiye a gefe guda sannan ta fito daga cikin ɗakin.

Direct ƙasa ta sakko ta samu guri kusa da daddy ta zauna,kallonta daddy ya yi ya ce,
"Ina kika baro ƴar taki.?"
"Tana ɗaki na ce ta kwanta ta huta"
"Amma kamar naga bata jin daɗin jikinta ko.??"
"Eh wallahi bata jin daɗi!"
"Ikon Allah!"
"Kin duba ta ne.?"
"Me ya sa Meta.??"
"Eh yanzun nan na gama dubata,ina tunanin kamar tanada juna biyu, amma na ɗebi sample ɗin jininta domin na ƙara tabbatarwa"
Da sauri mukhtar ya ɗago kansa ya dubi momy fuskarsa cike da mamaki,suna haɗa ido ya yi sauri ya sunkuyar da kansa ƙasa yana sosa ƙeyarsa kamar wanda ya yi abin kunya.
"Alhamdulillahi!! gaskiya idan hakan ta faru zan yi farin ciki sosai wallahi,domin ina son haɗa zuri'a da yarinyar nan! domin yarinyar tana da kirki ga ladabi da biyayya,uwa uba ga tarbiyya da girmama na gaba da ita.haƙiƙa samun irin su a yanzu saika tona,tabbas zan yi matuƙar farin ciki sosai idan naji tana ɗauke da jinina!!"
"In sha Allahu ba za'a rasa ciki a jikinta ba, bari ma na je na duba"
Ta faɗa tana miƙewa tsaye ta haye sama.

Kallon mukhtar daddy ya yi ya 3,
"My son dama yarinyar nan tana da juna biyu shine baka faɗa mana ba"
"Wallahi daddy ban sani ba,na dai san kwana biyu bata jin daɗin jikinta"
"Tom Allah ya sa fatan mu ya zama gaskiya"
A hankali ya ce,
"Ameen daddy"

Sakkowar momy ce ta katse musu maganar da suke yi, ƙarasowa ta yi kusa da daddy ta zauna ta kalle shi tare da cewa,
"Abani albishir kafin na faɗa muku.?"
Cikin sauri daddy fara faɗa min tukunna naji"
Cike da tsananin farin ciki ta ce,
"Surkarka tana ɗauke da jininka har tsawon na wata uku!!"
"Alhmdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah"
"Allah ubangiji ya inganta ya raba su lafiya ya bada rayayye mai albarka"
"Ameen ameen daddy"
Mukhtar ya faɗa tare da tasowa ya rungume daddy cike da tsananin farin ciki.
"Yauwa yanzu sai ku bani goron albishir ɗina"
Da sauri mukhtar ya ce,
"Momy zan baki sarƙa da ɗankunne har da awarwaro"
Cike da tsananin farin ciki momy ta ce,
"Lallai ana ji da wannan ɗan tun kafin yazo duniya"
"Ai wani abin ma sai yazo! Akwai motocin da na yi ordern su,idan sun zo zaki zaɓi ɗaya daga cikin su"
"Ma sha Allah,duk ni kaɗai haka! To ina godiya sosai, Allah ubangiji ya inganta ya raba su lafiya"
Gaba ɗayan su suka amsa da,
"Ameen"

Miƙewa tsaye mukhtar ya yi tare da cewa,
"Momy bari naje na kirawota mu tafi gida dare na yi"
"A'a son!! Kabarta anan tayi ko wata biyu ne, kaga sannan jikinta ya ƙara yin ƙarfi!"
Da sauri ya durƙusa a gaban momy ya ce,
"Dan Allah dan Annabi momy kiyi haƙuri kar ki rabani da matata, wallahi ita ce farin cikina ina jin daɗin zama da ita ina samun farin ciki da kwanciyar hankali sosai daga gare ta,idan kika raba mu wallahi zan iya shiga cikin wani hali!!"

Ya ƙarasa maganar hawaye na taruwa a cikin idanunsa.
"Kayi haƙuri anan ɗin zatafi samun kulawa sosai!"
Juyowa ya yi ya kalli daddy ya ce,
"Dan Allah daddy ka bawa momy haƙuri ta bani matata mu tafi!"
"Ya isa haka!! tashi kaje ka ɗauki iyalinka ku tafi gaba ɗaya, Allah ubangiji ya yi muku albarka ya ƙara baku zaman lafiya da kwanciyar hankali,dan Allah ka kula da ita sosai kaga yarinya ce ƙarama ga kuma shigar ƙaramin ciki!!"
"Tom in sha Allahu daddy,na gode sosai Allah ubangiji ya ƙara lafiya da nisan kwana masu albarka"

Yana gama faɗin haka ya haye sama,jim kaɗan sai ga su sun sakko ƙasa tare yana ruƙe da hannunta.sallama suka yiwa su momy sannan suka kama hannun yaran za su tafi,har sun kai bakin ƙofar fita momy ta kirawo sunansa tare da cewa,
"Zan yi maka test ɗin magungunan da zaka siyamata,za su taimaka mata in sha Allah"
"Toh momy mun gode sosai sai da safe!"
Daga haka suka fice daga ɗaya daga parlon.

Haka mukhtar ya yi ta kula da halimatu sosai,duk wani abu da take so tana samun shi awajen su iyayen mukhtar,a gefe guda kuma momynta tana kula da ita sosai.ɓangaren babanta ma ba'a bar su a baya ba,domin yana yawan tura aunty ameena taje ta gano masa ita.

Suna waya da altine da rahinatu, sannan lokaci zuwa lokaci hanne da Meena suna kawo mata ziyara,duk cewar suma suna fama da na su ruwan cikin,amma hakan bai hanasu ziyartar junansu ba.duk cikinsu ita ce cikin yake bata wahala sosai,domin makaranta ma da ƙyar take iya zuwanta,a gefe guda kuma ga mukhtar da baya ɗaga mata ƙafa.dan ma wani lokacin idan ya ga tana jin jiki yana haƙura ya ƙyaketa.

BAYAN WATA SHIDA
Chapter 78 · 0% Book details