← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 80

Sashe 11

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da yake akwai ma'aikata da yawa a saloon ɗin,nan da nan aka fara tsefe musu kansu aka wanke shi tas aka gyara, matar tana ta mama kin irin yawan gashin HALIMATU,ga yawa ga tsawo.ta dubi momy tace "hajiya wannan kyakkyawar yarinyar 'yarki ce??" ta faɗa da murmushi a fuskar ta.momy tace "ae 'yata ce". matar ta ce"ma sha Allah".

Daga nan aka yi musu ƙunshi ja da baƙi wanda yayi mutuƙar haɗuwa, kuma ya haska farar fatar su musamman ma HALIMATU.bayan an gama ne aka yi musu gyaran jiki.halumatu tayi matuƙar kyau,ta ƙara haske fatar ta sai she'ki takeyi,idan ka gan ta sai ka ƙara kallon ta.

Bayan an gama musu ne momy ta biya kuɗin suka fito suka kama hanyar gida.suna shiga ana yin sallar azuhur,basu zauna ba sai da suka gabatar da sallah.bayan sun idar ne suka ɗun guma zuwa cikin kitchen dan gabatar da girkin tarbar dady.

**********************************************

INNA LAURE ..................

Bayan ta gama koke koken da jimamin abin da buba yayi mata ne cikin sauri ta tashi ta fara gyara d'akin tana yi tana tsinewa momy,domin a cewar ta itace ta jawo mata wannan masifa.sai da ta gama gyaran d'akin sannan ta fito ta fara gyara tsakar gidan,tana yi tana haki abinka da mai 'kiba.

Tana gamawa ta saka mayafinta tare da ɗaukar makulli ta fito ta kulle gidan,domin a cewar ta bazata zauna ita kaɗai ba cikin dare buba yazo yayi mata yankan rago ba,gwara ta gudu ta bar gidan,idan ta samo kudin ta dawo.yanzu ma wajen wanta zata tafi taje ta karb'o awakin ta da ake yi mata kiwo,sai takai su kasuwa ta siyar ta biya buba kudinsa, abin da ya rage kuma sai su ƙara sabon shiri.daga haka ta kama hanya ta tafi .

MUKTAR............

Bayan ya isa Company ɗin ne babu daɗewa suka shiga mitting,sai da suka shafe two hours sannan suka gama mitting ɗin.suna fitowa ya zo ya taradda baƙi na jiransa,batare da b'ata lokaci ba ya zauna da su suka tattauna akan kasuwancin da suke son su ƙulla a tsakanin su.

Bayan ya sallame su ne ya bar company ɗin ya tafi b.u.k, yana zuwa office ɗin sa ya nufa ya zauna ya rage ayyuka kafin lokacin da yake da class yayi,level one yake ɗauka da two da three da kuma four.shabiyu daidai ya fito daga office ɗin ,ya na tafiya cike da ƙasaita, fuskar nan tasa a ɗin ke babu alamar wasa.

'Yan mata da samari na hango shi suka mi'ke da sauri suka fara shiga aji, saboda sun san dokar sa,indai ya riga ka shiga aji to ba zai bar kowa ya shiga ba.yana ƙarasowa ya shige cikin ajin,nan take ajin yayi tsit kamar babu abu mai rai a cikin sa..............

Ina matuƙar godiya da addu'o'in ku a gare Ni, kuɗin na musamman ne a cikin zuciyata.sannan ina yi muku fatan alkhairi🙏🏻.a cigaba da yimin ruwan comments, domin shine zai bani ƙwarin gwiwar yi muku update 🥰🥰🥰💝🙏🏻..........

FATIMA BINTU (ABDULLAHI UMMU AYSHA)..................✍🏻

08162055134.

💝💞HALIMATU💝💞

(Love, sacrifices, destiny& betrayed)

💝💞💞💝💞💝💞💝

Story & writing

By

FATIMA BINTU ABDULLAHI (UMMU AYSHA)

Ƙarƙashin jagorancin

(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)

Golden pens...............✍🏻

💝💞💝💞💝💞💝💞

2024 novel

💝💞💝💞💞💝💝💞

Page_____________15&16

Tsit kake ji kamar babu ɗan adam a cikin class ɗin,kowa ya shiga taitayin sa gudun kar yayi laifi ya jishi a waje, cikin ƙasa ƙasa da murya wasu 'yan mata suke magana suna satar kallon sa.d'aya daga cikin su tace"gaskiya gayen nan ƙarshe ne wajen haɗuwa komai nasa da aji yake yinsa,ga kwarjini ga haiba,uwa uba kuma ga nera.gaskiya ya haɗu ta ko ina,ki duba kiga yana shigowa ajin yayi tsit kamar ruwa ya cinya mutane ,gashi Allah yayi masa ƙwaƙwalwa kamar me,duk rashin gane karatun mutum indai Dr muktar ya koyar da shi zai gane, wallahi ina matuƙar san gayan nan".

Ta ƙarasa maganar fuskar ta ɗauke da murmushi.d'ayar da take kusa da ita ce ta dube ta tace "lallai sumayya kina da aiki babba,kin ɗakko wa kanki dala ba gammo,nima nan da kike gani ina matuƙar san sa wallahi,amma abin da na fahimta shine kwata kwata bamu ishe shi kallo ba,ki duba fa ki gani ranar nan da muka je capteria a gaban idanun mu ya kun yata wasu manyan mata,sun fimu haɗuwa ta ko ina amma a haka yayi musu wulak'anci".

Sumayya tace "haka ne zulaiha, Allah ya karkato da hankalin sa garemu ko mun samu damar shiga gidan sa,duk da naji ance yana da mata, amma wallahi indai na samu na shiga gidan sai ta raina kanta,domin ruƙo zanyi masa bana wasa ba".ta ƙarasa maganar tana duban kyakkyawar fuskar sa.ganin ya nufo inda suke ne yasa suka shiga taitayin su, sabo da sun san halin sa sarai zai iya korar su.

Yana ƙarasowa dai-dai inda suke ya ɗora hannun sa akan table ɗin su ya buga shi da ƙarfi tare da cewa"get out of my class" ya faɗa fuskar sa babu alamun wasa. ganin basu da alamar motsawa ne ya sake buga hannun sa a karo na biyu yace"i say get out of my class!!".

Cikin sauri suka mi'ke jikin su yana rawa suka fita daga cikin ajin.bayan fitar su ne ya fara gabatar da lesson ɗin cikin ƙwarewa da gogewa,sai da ya dauki kusan awa ɗaya da rabi yana yi musu lecture kafin ya fita daga ajin.bayan ya fito wani ajin ya nufa,bashi ya bar makarantar ba sai wuraren ƙarfe shida na maraice, tu'ki yake yi cikin sauri saboda sun yi waya da dadyn sa yana kan hanya,kuma ya gaya masa ƙarfe shida jirgin su zai sauka, shi yasa yake sauri ya ƙarasa airport ɗin kafin ƙarfe shidan ta yi.

HALIMATU

A ɓangaren su HALIMATU kuwa girki suke babu kama hannun yaro, babu abin da yake tashi sai ƙamshin girke girke kala-kala, HALIMATU anyi bussy anata hidima.momy ce ta kalli HALIMATU tace "daughter bari naje nayi wanka na shirya, tunda naga mun kusa kammala wa,idan yaso sai ku ƙarasa keda baba ladi,kinga ƙarfe shida jirgin su dady zai sauka, saboda haka kuyi sauri ku ƙarasa kema kije kiyi wanka ku shirya ke da auta".

HALIMATU tace "to momy"daga haka ta fice ta barsu a cikin kitchen ɗin suna cigaba da yin aikin.suna gamawa suka jere komai a kan dining table, batare da b'ata lokaci ba suka gyara kitchen ɗin tsaf kamar ba'ayi girki a cikin sa ba.bayan sun gama ne HALIMATU ta kama hannun auta suka haye sama .

'Dakin auta suka nufa, ba tare da b'ata lokaci ba tayi mata wanka ta shirya ta cikin Black abaya mai matuƙar kyau da tsada,ta feshe mata jikin ta da turare mai ƙamshi,ba ƙaramin kyau yusra tayi ba ma sha Allah.ta na gama shirya ta tace mata"woww gaskiya kinyi kyau sosai my yusra,maza jeki ƙasa ki jirawo ni yanzu nan nima zan shirya".

Cike da murna yusra ta washe baki ta tafi da gudu ta sauka ƙasa.ita kuma HALIMATU ta juya da sauri ta nufi d'akin ta .tana shiga batare da b'ata lokaci ba ta faɗa wanka, mintuna kaɗan ta ɗauka a toilet ɗin ta fito d'aure da towel a ƙugun ta.cikin sauri ta buɗe ledar shopping ɗin da suka yi ta ɗauki new bra da pant underwear d best.

Sannan ta kuma buɗe ledar kayan cosmetics, ta ɗakko tsadadden set ɗin mayukan shafawa tare da turaruka ta ajiye akan bed d'inta,ta ƙara buɗe ledar dogayen riguna ta ɗakko wata had'ad'd'iyar abaya maroon colour,wadda aka yi mata ado da golden ɗin stone.

Cikin sauri ta fara shiryawa murmushi ɗauke a kan fuskar ta, kana ganin ta kasan tana cikin farin ciki.powder ta shafa tare da red lipstick, sannan ta ƙara gyara gashin girar ta, wowww nan take tayi wani irin masifar kyau.cikin sauri ta zura doguwar rigar a jikin ta,rigar ta zauna mata ɗas gwanin ban sha'awa kamar dan ita aka ƙera ta.cikin sauri ta ƙara gyara gashin kanta, wanda tsayin sa ya sakko har kusan ƙugun ta. rolling ɗin mayafin rigar tayi tare da feshe jikin ta da turare mai sanyin ƙamshi.ledar takalma ta buɗe tare da zaɓo wani had'ad'd'en hill shoe ta ajiye a ƙasa.

Tana shirin sakawa ne auta yusra ta shigo da gudu tare da cewa"aunty kiyi sauri ki fito mu tafi inji momy".tana gama fad'ar sa'kon ta juya da gudu ta tafi.halimatu tayi sauri ta saka takalmin ta tare da tattare kayan gefe guda da niyyar idan suka dawo ta shiya su.

Ƙwas ƙwas ƙwas kake jin takunta cike da nutsuwa take tafiya,gaba ɗaya ido suka zuba mata lokacin da take sakkowa daga sama,suna mamakin irin kyan da tayi kamar ba ita ba.tana ƙarasowa momy ta kamata ta rungume ta tare da cewa"ma sha Allah daughter na,wallahi kinyi kyau sosai kamar ba keba, Allah ubangiji yai miki albarka ya baki miji na gari wanda zai kulamin da ke".

Cike da kunya tace"amin"tare da rufe fuskar ta da tafin hannayen ta.farouq yace "lallai ma yarinyar nan baki da kunya,in banda abin ki wazai kwashi zabiya irin ki??ai sai dai a taimaka miki a aure ki".ya ƙarasa maganar yana mata dariya.halimatu ta kwab'e fuska kamar zata yi kuka tace"momy kinga shi ko".

Kafin momy tayi magana sadiq ya rigata tare da cewa "rabu dashi my sweet syster kishi kawai yake yi dan ya ga kin fishi kyau"ya faɗa yana yiwa farouq gwalo.murmushin jin daɗi HALIMATU tayi,shi kuwa gogan ya haɗe fuska alamar anb'ata masa rai ,momy kuwa mai zatayi in ba dariya ba.

Shigowar hafiz ce ta katse musu drama ɗin da suke yi,ya dubi momy yace "ku tashi mu tafi jirgin su ya kusa sauka"cikin sauri dukkanin su suka mi'ke suka fito zuwa parking space ɗin,mota biyu ce za suyi momy da HALIMATU da auta farouq ne yaja su, shi kuma sadiq ya shiga motar hafiz suka fice a jere suka hau kan titi.

Suna isa suka samu waje suka yi parking motocin su,momy da HALIMATU a cikin mota suka zauna basu fito ba,yayin da sauran su kayi ficewar su daga cikin motar.

MUKHTAR

Go slow ne ya tare shi a kan hanya yana ƙarasowa cikin airport ɗin yaji gabansa yana fad'uwa,nan take ya kama ambaton innalillahi wainna ilaehi raji'un a cikin zuciyar sa.bud'e motar yayi ya fito tare da tsayawa a bakin motan.tsayuwar sa babu daɗewa yaji ana sanar war jirgi zai sauka.
Chapter 11 · 0% Book details