← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 80

Sashe 38

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dam Dam gaban HUMAIRA ya yi wani irin mummunar faɗuwa,nan take ta miƙe da sauri ta ɗauki wayar Hajiya RABI dake yashe a kan sofa ta kirawo wata new numbern da bata da suna,wadda take kyauta ta zaton itace numbern mutumin da ya kirawo MOMY.

Ba tare da ɓata lokaci ba ta danna Call ɗin wayar, ringing uku kawai wayar ta yi aka yi picking call ɗin,gaisawa suka yi da mutumin sannan ya ƙara koro mata dukkanin bayanin abin da yake faruwa.

Cikin matsanancin kuka take gaya masa ita ɗin ƴarsa ce,amma zata kirawo yayyin ta da ƴan uwan baban su ta gaya musu,ya amsa mata da toh tare da kashe wayar.

Durƙushewa ta yi a wajen ta saki wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro tare da karya zuciya,cikin kukan ta ɗauki wayar ta kirawo babban wansu KABIRU ta sanar da shi abin da yake faruwa,cikin tsananin tashin hankali ya umarce ta da ta tura masa numbern wayar mutumin.

Ba tare da ɓata lokaci ba ta tura masa numbern.

Ɗagowa Hajiya RABI ta yi ta kalle ta cikin kuka tare da cewa

"HUMAIRA kirawo Hajiya HAUWA muji gaskiyar lamarin nan! domin ni har yanzu ban yarda da zancen mutumin nan ba!!"

Hawayen da suke zuba a fuskar ta kamar famfo ta share tare da ƙara ɗaukar wayar a karo na uku ta danna numbern Hajiya HAUWA mahaifiyar RUFAIDA.

Lokacin HAJIYA HAUWA tana zaune a kan kujera ta rafka uban ta gumi sakamakon halin da suka tsinci kansu a ciki jiya ƙarfe biyu na dare,domin tana tsaka da bacci ta jiyo ihun RUFAIDA babu ƙaƙƙautawa,domin rabon da su yi waya da ALHAJI tun lokacin da ya ce mata za su taso daga ENUGU.

A firgice ta miƙe jikin ta na rawa ta nufi ɗakin RUFAIDA domin ganin abin da yake faruwa.

Lokacin da ta jefa ƙafar ta a cikin ɗakin tsaye ta yi turus sakamakon ganin abin da ya ɗaga mata hankali da ta yi.

"MALAM UMMARU"

Lokacin da su MALAM UMMARU suka ƙaraso garin HAƊEJA motar su bata tsaya a ko ina ba sai a dai dai ƙofar gidan sa drivern sa ya yi parking ɗin motar.

Fitowa drivern ya yi tare da buɗe musu ƙofar motar,a hankali MALAM UMMARU ya fito daga cikin motar bakin sa ɗauke da bismillah.

Zagayawa ya yi ya buɗe wa aunty AMINA ƙofa itama ta fito ɗauke da Ahmad a kafaɗar ta,hannu malam ummaru ya sa ya karɓi AHMAD ɗin da yake ta baccin sa hankali sa kwance,komawa ta yi cikin motar ta ɗakko hand bag ɗin ta ruƙe a hannun ta.

Jagora baba ya yi musu suka shiga cikin gidan bakin su ɗauke da sallama, Inna Laure da take zaune a kan tabarma tana shan kunun da HANNE ta dama mata ne ta zabura tare da dafe ƙirjin ta tace

"Wa nake gani kamar MALAM!! Ko dai gizau idanuwa na suke yi min??"

Murmushi baba ya yi tare da ƙarasowa cikin gidan ya tsaya tare da cewa

"Ba kama bace LAURE ni ɗin ne dai idanun ki suka gane Miki!!" ya ƙarasa maganar tare da gyara ruƙon da ya yi wa Ahmad.

Fashewa ta yi da kukan murna tare da cewa

"Alhamdulillah! Allah na gode maka da ka karɓi addu'a ta ka dawo min da miji na gida Cikin ƙoshin lafiya!"

Koke_koken da INNA LAURE take yi ne ya fito da HANNE da gudu daga cikin ɗaki,turus ta yi sakamakon ganin baba da ta yi ɗauke da wani kyakkyawan yaro ruƙe a hannun shi,bayan sa kuma wata kyakkyawar mata ce ƴar gayu fuskar ta ɗauke da murmushi.

Tahowa ta yi da gudu ta rungume Baba tare da fashewa da wani irin kukan murna.

Ganin haka ne ya sa aunty AMINA karɓar Ahmad daga hannun baban,domin su ji da ɗin gaisawa da kyau.

Shafa kan HANNE ya yi tare da cewa

"Toh kuma meye na kuka HANNE?? Me makon kiyi murnar gani na kuma sai naga saɓanin hakan...?"

"Ɗago fuskarta ta yi ta kalli baban hawaye na zuba tace

"Ai kukan na murnar ganin ka ne Baba,kullum sai mun yi kukan rashin ka a tare da mu,amma muna ji a jikin mu wata rana zaka dawo"

Hannu sa ya sa ya share mata hawayen da yake zuba a fuskar ta tare da cewa

"Kwantar da hankalin ki auta ta,ai gashi yanzu Allah ya nufa na dawo,ko da yake bake ce auta ba ga ƙanin ki nan Ahmad!!"

Ya faɗa yana nuna Ahmad da yake hannun aunty AMINA.

Jin kalmar Ahmad yasa INNA LAURE miƙewa ruƙe da sanda a hannun ta,ta ƙaraso in da suke tare da tsayawa a gaban aunty AMINA ta tsura mata idanun ta mamaki cike da fuskar ta.

Cike da ruɗani ta juwo ta kalli malam ummaru tare da cewa

"Wacece wannan kuma malam...?"
"Meye haɗin ka da ita har kake kiran yaron hannun ta da ƙanin HANNE..?"

Murmushi mai ƙayatarwa baba ya yi tare da cewa

"Kwantar da hankalin ki Laure! Saurin me kike yi ne..? Ai idan ki ka kwantar da hankalin ki zan miki bayanin matsayin ta a guri na!!".

Wani ƙululun baƙin ciki ne ya taso wa Inna Laure,nan take ta ɗin ke fuskar ta daga fara'ar da take yi ta kama saƙe-saƙe a cikin zuciyar ta.

Juyowa ya yi ya kalli HANNE tare da cewa

"ɗakko tabarma mana ki shimfiɗa mana kun barmu a tsaye!!"

Murmushi HANNE ta yi tare da juya wa ta buɗe ɗakin Baba ta ɗakko babbar taɓara,sai da ta kaɗe tabarmar sosai sannan ta shimfiɗa musu ita.

Zama suka yi gaba ɗayan su a kan tabarmar ban da INNA LAURE da ta yi tsaye ƙerere a kan su tana huci.

Ɗago da kansa ya yi ya kalli inna laure tare da cewa

"Haba LAURE!! Ya zaki tsaya a kan mutane ƙerere haka!! ya kamata ki samu guri ki zauna kema!!".

"Wallahi ba zan zauna ba har sai ka gayamin wacce wannan matar da take tare da kai!!" ta faɗa tana huci.

Girgiza kansa ya yi fuskar sa ɗauke da ɓacin rai,wato me hali dai ba zai taɓa canja halin sa ba.

Ya faɗa a cikin
zuciyar sa.

"To tun da kin ƙi zama in yi miki bayani a nutse yadda zaki fahimta ai shikenan!!"

"Wannan matar da kike gani ba kowa bace face mata ta! Shi kuma wannan yaron ɗana ne wanda ta haifa min!! dan haka in zaki zauna ki zauna idan kuma ba zaki zauna ba sai kiyi ta tsayuwar!!"

Suman wucin gadi INNA LAURE ta yi sabo da tsanani kaɗuwar da ta yi sakamakon jin wannan mummunan labarin.wani irin ƙololon abu mai ɗaci taji ya tokare mata zuciyar ta ,nan take ta ɗago fuskar ta ta kalli baba da jajayen idanuwan ta tace

"Wallahi tallahi ƙarya kake yi baka isa ka yi min kishiya ba,idan ma kayi wallahi sai ka sake ta yanzu yanzun nan,ko kuma kayi nadamar da baka taɓa yi ba!! Muna fikin banza muna fikin wofi!!".

Miƙe wa HANNE ta yi da sauri ta shige cikin ɗakin ta wanda a da shine a matsayin na HALIMATU,wayar ta ta ɗauka cikin hanzari ta kurawo altine da rahinatu ta basu labarin abin da yake faruwa,nan take suka ce mata gasunan tafe yanzu nan!!"

Ina matuƙar godiya a gareku masoya na masu Albarka abin alfharina,ku ɗin na musamman ne a cikin zuciya ta, Allah ubangiji ya saka muku da mafificin alkhairin sa,ya biya muku buƙatun ku na Alkhairi.....

Daga alƙalamin......

FATIMA BINTU ABDALLAHI (UMMU AYSHA).................✍🏻✍🏻

Share fisabilillahi..

O81 62055134.........

💝💞HALIMATU💝💞

(Love, sacrifices, destiny & betrayed)

💝💞💝💞💝💞💝💞

Story & Writing

By

FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)

Ƙarƙashin jagorancin

(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)

Golden pens.........✍🏻✍🏻

💝💞💝💞💝💞💝💞

A 2024 novel

💝💞💝💞💝💞💝💞

Pages____________47&48

"INNA LAURE"

Fitowa HANNE ta yi daga cikin ɗakin da sauri sakamakon jiyo muryar inna laure da ta yi tana ta zage-zage,turus ta yi ganin yanda INNA LAURE ta miƙe da sauri ta yi kan aunty AMINA tana huci.

Tahowa ta yi da gudu ta ruƙe hannun INNA LAURE tare da cewa

"Haba inna? mai ki ke shirin yi ne haka!!".

Ɗago da jajayen idanuwan ta ta yi tare da watsawa HANNE wani mugun kallo zuciyar ta na mata wani irin tuƙuƙi tace

"Sake ni dan uban ki ko in mangareki anan wajen wallahi! Sha-sha-shar yarinya kawai!!.

Buɗe baki HANNE ta yi da nufin yin magana kwatsam suka ji sallamar malam musa maƙobcin su yana neman izinin shigowa,amsa masa sallamar baba ya yi tare da bashi damar shigowa cikin gidan.

Shigowa ya yi tare da nufar in da Baba yake tsaye yace

"Subhanallahi! Me ya ke faruwa ne malam ummaru! tun ɗazu nake jiyo hayaniya na tashi daga cikin gidan nan! Ina fatan dai lafiya dai ko!!"

Ya ƙarasa maganar yana kallon Malam Umaru.

Kallon HANNE baba ya yi tare da cewa

"Ki raka Auntyn ki gidan malam musa ta huta ta yi sallah"
Buɗe baki ta yi da ƙyar kamar mai ciwon baki tace "to"

Juyowa ya yi ya kalli aunty AMINA da ta yi wani iri da ita ga Ahmad yafara yi mata kuka sakamakon hayaniyar da yaji tana jiggigashi ya ce

"AMINA ki bita kuje zata kai ki in da zaki huta,kuma ki kulamin da Ahmad sosai,sannan akwai take away a mota ki ɗauka ki ci"

Kai ta girgiza tare da juyawa ta bi bayan HANNE suka fice daga cikin gidan.gidan malam musa suka nufa in da suka samu kyakkyawar karɓa a wajen sabuwa matar malam musa.

Shigar su babu wuya drivern su ya yi sallama ya fara shigo da kayan da suka yi tsaraba da su,sai da ya kwashe komai ya kawo tsakar gidan malam musa sannan ya koma waje ya zauna yana daddana wayar hannun sa.

Bayan fitar su HANNE daga cikin gidan ne malam ummaru ya dubi malam musa yace

"Ga dukkan alamu baka gaya mata saƙona da na bar mata shi a cikin ɗaki na ba kafin na tafi ba ko?"
Chapter 38 · 0% Book details