Sashe 59
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajiyar zuciya mukhtar ya sauke tare da kallon ta ya ce,
"My love taso ki dawo kusa da ni ki zauna!"
Ya faɗa yana nuna mata gefen sa da hannun sa.
A hankali ta ta tashi ta dawo kusa da shi ta zauna, hannayen sa biyu ya saka ya kamo na ta hannayen tare da damƙe su ciki tafin hannun sa,nan take ya ji wani irin mugun sanyi yana ratsa dukkanin hudar gashin da take cikin jikin sa, wata irin nutsuwa da ya daɗe bai ji irin ta ba yaji tana saukar masa a dukkanin ilahirin gaɓɓan jikinsa.
Numfashi ya sauke tare da kallon fuskar ta ya ce,
"My love! me ya sa kika yi min haka!! gaba ɗaga kin ɗaga min hankali na kasa suku ni kwata kwata,ko so kike yi zuciya ta ta buga na mutu ki huta ne!!"
Girgiza kai ta yi hawaye na gangarowa daga cikin idanun ta.
"Kin riga da kinsan ina matuƙar son ki sosai komai zai iya faruwa dani a kan ki!!"
Cikin raunin murya ta girgiza kanta tare da share hawayen fuskarta ta ce,
"Ka yi haƙuri ka yafe min habibi ba zan ƙara yi maka haka ba,yanzu ma tsoro ne ya sa ni yin haka!"
"is okay, ya isa dena kuka bana son ganin hawaye akan kyakkyawar fuskar nan ta ki kin ji"
Ya faɗa tare da ɗaukar ruwa ya zuba a glass cup ya Mika mata, karɓar ta yi ta ɗan sha kaɗan tare da miƙa masa cup ɗin.
Shanye ragowar ruwan ya yi tare da ajiye kofin a gefe.
Kallon sa ta yi tare da cewa,
"Habibi kaci abinci ka sha magani jikin ka akwai zafi sosai"
Murmushi ya yi tare da cewa,
"Ai kece maganin nawa tun da yanzu kin dena fushin da ni zan warke ai"
"Toh na ji nidai tashi kaci abinci kar yunwa ta kama ka! bari naje na ɗakko maka pain relief ka sha kaga nima ɗazu sai da momy ta sakani na sha!"
Ta yi maganar cike da shagwaɓa tana miƙewa ta fice daga cikin parlon.
Wani irin tafi Nura ya yi tare da yin ɗan ƙaramin ihu ya ce,
"Kaga romeo and Juliet,wallahi salon soyayyar ku tana burgeni aboki na"
Murmushi mukhtar ya yi tare da fara cin abincin sa,ta ɗauki ɗan lokaci kafin ta dawo sabo da lokacin da ta dawo har ya gama cin abincin sa.
Maganin ta ɓallo a hannu ta ta miƙa masa tare da tsiyaya masa ruwa a cikin glass cup ta miƙa masa,cike da wani irin shauƙi ya karɓa tare da zuba maganin a cikin bakin sa ya kora da ruwan da ta miƙo masa.
Miƙewa nura ya yi ya kalli halimatu tare da cewa,
"Toh mukam zamu wuce halimatu,sai kuma Allah ya sake dawo da ni"
"Toh ya ya Nura na gode sosai ka gaida min da aunty na da yarana"
Ta faɗa tare da durƙusawa ta miƙa masa ɗaya daga cikin ledodin da ta shigo da su a hannun ta tace ya kaiwa yaran.
Godiya ya yi tare da kallon mukhtar yace,
"Ka same ni a mota ina jiran ka, idan kuma ka daɗe wallahi na yi tafiya ta!"
Ya faɗa yana ficewa waje.
Ɗaya ledar ta ɗauka mai ɗauke da miet pie da cookies ta miƙa masa tare da cewa,
"Ga wannan habibi! ɗazu da safe muka yi su nida momy"
Karɓa ya yi tare da cewa,
"Thank you my love, Allah ya yi miki Albarka.
Amsawa ta yi da "ameen" a saman laɓɓan ta.
Miƙewa ya yi tare da cewa,
"My love bari na tafi kar Nura ya gudu ya barni na san ba ƙaramin ai kinsa bane ba".
"Toh habibi ka gaida su momy,gobe idan Allah ya kaimu zamu wuce Dubai daga nan kuma zamu je China,idan muka gama siyayyar sai mu wuce saudia mu yi umara"
Cike da mamaki ya ce,
"Tafiya gobe goben nan amma baki faɗa min ba!!"
"Nima wallahi ɗazu momy ta ke gaya min wai siyayya zamu je mu yi"
Wani irin ƙayataccen murmushi ya saki domin yanzu ya gano dalilin tafiyar ta su.
"Okay tom shikenan, Allah ubangiji ya kai ku lafiya ya dawo da ku gida lafiya"
Cike da jin daɗin adduar sa ta amsa da "ameen"
"Ki kunna wayar ki zamu yi waya anjima"
"Toh" tace.daga haka suka yi sallama ya juya ya tafi....✍🏻✍🏻
Ina matuƙar godiya da addu'o'in ku a gare ni tare da fatan Alkhairi, ku ɗin na musamman ne a cikin zuciya ta, ina matuƙar alfahari da ku ƙwarai da gaske , Allah ubangiji ya saka muku da mafificin Alkhairin sa,ya biya muku buƙatun ku na Alkhairi🙏🏻🙏🏻
Daga alƙalamin
FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)...✍🏻✍🏻
Share fisabilillahi.
Ga masu buƙatar littafin tun daga farko zuwa in da aka tsaya su tun tuɓeni ta wannan numbern wayar👇🏻👇🏻
08162055134.
💝💞 HALIMATU 💝💞
(Love, sacrifices, destiny & betrayed)
💝💞💝💞💝💞💝💞
Story & Writing
By
FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA).....✍🏻✍🏻
Ƙarƙashin jagorancin
(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)
💝💞💝💞💝💞💝💞
Golden pens.......✍🏻✍🏻
A 2024 novel
💝💞💝💞💝💞💝💞
Pages____________75&76
___________direct mota ya nufa sabo da uban horn ɗin da Nura yake danna masa,buɗe motar ya yi ya shiga Nura na ta zazzaga masa masifa,shiru ya yi yana ta sakin wani irin murmushi a kan fuskarsa ba tare da ya tanka wa Nuran ba.
Suna ƙarasowa bakin get ɗin gidan baba maigadi ya buɗe musu ƙofar get ɗin tare da ɗaga musu hannu,hannu mukhtar ya sa a cikin aljihun sa ya ɗakko duka kuɗin da yake ciki ya miƙa wa baba maigadi.
Hannu na rawa baba maigadi ya miƙo ya karɓa tare da yi musu godiya, sallama su ka yi da shi sannan Nura ya ja motar da gudu suka fice daga gidan, suna hawa kan titi mukhtar ya sauke wata iriyar ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya fuskarsa cike da annuri.
Kallon sa Nura da ke tuƙi ya yi tare da cewa,
"Wallahi da ka ƙara minti biyar da sai dai ka zo ka tarar na yi tafiya ta in ya so ka taho da ƙafafun ka"
Hannun sa ya kai yana shafa kwantaccen sajen fuskar sa da gemun sa fuskarsa cike da murmushi ya ce,
"Kai ka isa ka tafi ka bar ni ba tare da ka tsaya ni ba".
Cike da mamaki Nura ya ɗan juyo ya kalle shi tare da cewa,
"Au hakama zaka ce! to wallahi ka kori gaba gobe ma rana ce! da ni kake zancen, tun da na gama yi maka komai ka samu kanka ai dole ka yi min rashin mutunci"
Ya ƙarasa maganar yana yin ƙwafa.
Fashewa da dariya mukhtar ya yi tare da cewa,
"Afuwan a bokin na,baka ga ina cikin shauƙin soyayya bane.?"
"Hmm ai ni kuwa naga alama tun da ka kusa mace mana a kan yarinya ƙarama! ko da yake ba lafin ka bane ba yarinyar ce duk in da mutum yake zaton ta ta wuce nan!ga shinan cikin lokaci ƙanƙani na yi mata wayo na shawo kanta,kai ma haka zaka din ga yi mata sai kaga cikin sauƙi ka janyo hankalin ta".
Ya faɗa yana kallon mukhtar da ke murmushi.
"Hmmm ai yanzu na gano kan karatun aboki na, wallahi gaba ɗaya kaina ƙullewa ya yi domin ina jin tsoron in rasa ta! shi ya sa kaga duk na rasa nutsuwa ta".
"Toh yanzu dai sai ka dawo da nutsuwar ka mu fara shirye-shirye kafin lokaci ya ƙure mana!"
"Kai dai bari aboki na,ai dole ne mu yi shirye-shirye masu ƙayatarwa wallahi! shi ya sa ma na damƙa komai a hannun ka".
"Babu matsala in sha Allah,bari na koma gida na samu natsuwa sai in san tunanin da zan yi a kai!"
"Yauwa toh ka fara sauke ni a gida domin bazan koma office ɗin nan ba wallahi!!"
Dariya suka yi gaba ɗaya har da tafa wa.
A bakin get ɗin gidan ya sauke mukhtar, sallama su ka yi ya juyar da kan motar ya wuce, ajiyar zuciya ya sauke tare da bin motar da kallo har ta ɓace masa da gani,wata iriyar ƙaunar Nura ce ta ƙaru ninkin ba ninkin a cikin zuciyar sa, domin Nura mutum ne mai mutuƙar kirki da ruƙon amana.
Tun suna yara suke tare har girman su, ruƙon sada amanarsa ne ya sa ya bashi babban matsayi na managern Company ɗin sa,izuwa yanzu alaƙar su ta tashi daga abokai ta koma musu tamkar ƴan uwan juna,domin da yawan cin mutane kallon shaƙiƙin ɗan uwan sa suke masa.
A hankali ya juya ya shiga cikin gidan ta ƙaramar ƙofa,part din sa ya shiga tare da shiga toilet ya ɗauro alwalar sallar azahar domin jin kiran sallar da ake yi,a gurguje ya canja kayan sa zuwa milk ɗin jallabiya ya fesa turare kaɗan sannan ya fice daga gidan zuwa masallacin.
Ana idarwa ya fito daga masallacin ya shigo cikin gidan,part ɗin su momy ya nufa da sallama ɗauke a bakin sa,momy dake zaune a kan sofa ita da wata mai kama da ita suka amsa masa sallamar,cike da murmushi matar ta ce,
"Welcome my son,kamar kasan zancen ka muke yi yanzu!!"
Murmushi ya yi tare da durƙusawa ya gaishe su cike da ladabi ya ce,
"Nima wallahi kaina ne yake ɗan yi min ciwo shi ya sa na dawo yanzu ashe da rabon zamu mu haɗu"
"Ayya sorry my son,hope dai ka sha magani ko.??"
"Eh mamy na sha,yanzu ma daga masallaci nake"
"To ma sha Allahu son Allah ya ƙara sauƙi"
A hankali ya amsa da"ameen".
Kallon sa momy ta yi tare da cewa,
"Yauwwa son dama yanzu muke magana da mamyn ku akan zancen haɗo lefen ka,sabo da kar lokaci ya zo ya ƙure mana!".
A hankali ya ce,
"Toh momy duk abin da kuka ga ya dace a yi,sai ku yi list ɗin komai idan ya so sai ku je duk in da zaku je ku haɗo kayan,idan kun gama lissafi sai ku sanar da ni"
"To shikenan son,ka nema mana visan tafiya dubai nan da kwana biyu,idan ya so sai muje mu sayi komai a can ɗin ina ga hakan zai fi mana ko.?"
"Toh shikenan mamy bari na je na fara yi muku shirye shiryen!!"
Ya faɗa yana miƙa wa tsaye tare da ficewa daga cikin parlon.
****************************************************************************************************