Sashe 6
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bata jirawo cewar sa ba ta kama hannun HALIMATU ta mi'ke suka nufi cikin d'akin.
Suna shiga ta bawa HALIMATU ɗaya daga cikin dogwayen rigunan da ta siyo mata,tare da takalmi da turare tace "maza kiyi sauri ki shirya driver yana jiran mu a waje"
Cikin sauri ta gama shiryawa . momy ta bata powder da lipstick ta shafa,nan take HALIMATU ta fito Kamar wata balarabiya, abinka da jinin fulani.
Momy tace "masha Allah doghter kinyi kyau" ta faɗa tana murmushi.
HALIMATU ta yi murmushi har dimple d'inta guda biyu suna lotsawa.
momyn ta miƙa mata jakar ta suka fito daga cikin d'akin.malam ummaru yace"har kun fito?? to Allah ubangiji ya kai Ku lafiya". ya saka hannu sa a cikin aljihu ya ɗakko wayar sa ya mi'ka wa hajiya Maryam yace mata ta saka masa number n wayar ta,ta karb'a ta saka masa.
ta miƙa masa wayarsa,yace "to ku muje in raka ku" har sun zo zasu fita Inna laure ta yi kukan kura tayi kan HALIMATU gadan gadan zata ruƙo ta,da sauri malam ummaru ya sha gaban ta ya riƙe ta tana ihu tana turjewa tana cewa bazata bari a tafi da HALIMATU ba......
ya dubi hajiya maryam yace "ku wuce ku tafi zamu yi waya idan kun kai gida, Allah ya kaiku lafiya" suka ce amin, tare da ficewa daga gidan........
Suna fitowa suka iske malam habu driver tsaye a baƙin mota,ga yara duk sun ke waye motar suna ta shafa ta.yace" Hajiya Barka da fitowa,da fatan na same ku lafiya!!" tace "lafiya k'alau malam habu"...
ya juya ya buɗe musu motar, momy ce ta fara shiga, sannan HALIMATU ta shiga.
Malam habu ya rufe motar, shima ya zagaya mazaunin sa ya shiga ya tada motar yayi horn yaran duk suka jaye daga jikin motar yaja motar suka ƙara gaba..
wannan ke nan................
*****************************************
A ɓangaren inna laure kuwa sai da suka kai ruwa rana ita da malam ummaru ,ta tara ma masa jama'a tana tayi masa tijara,tana ta cewa ya bada 'yarsa an tafi da ita birni za'a siyar ta ita saboda neman duniya.
Ae kuwa nan mutane suka dinga yi masa tofin alatsine....
Wasu sun yarda da zancen ta, wasu kuma basu yarda ba,saboda sun san halinta.duk wannan abin da akeyi akan idan hanne da haya niyar mutane da ihun inna laure ya tashe ta daga bacci,tana tsaye tana kallon rashin arzi'kin da inna take yiwa babansu .
Baƙin cikine ya sa ta koma cikin d'aki ta fashe da kuka.shi kuwa malam ummaru ya shiga cikin d'akin sa ya ɗakko jakar kayan sa ya fito daga cikin gidan ko ta kan inna laure bai bi ba yayi tafiyar sa.
Tana ganin haka ta fasa ihu tace "shikenan an rabani da mijina an shiga tsakanin mu,to wallahi banga ta zama ba"ta faɗa tana shigewa cikin d'akinta tare da ɗaukar mayafinta ta yafa akan ta ko ta kan hanne bata biba tayi fice warta daga ciki gidan..............
KANO STATE
(Ta dabo tun bin giwa)
Sun shafe tafiyar kusan awa biyu kafin su sigo cikin garin Kano,suna shigowa driver ya ɗauki hanyar rijiyar zaki........
Ko da suka shigo cikin unguwar HALIMATU ta d'aga kai tana ta kalle-kalle ,ganin gidaje manya manya ƙerarru gwanin ban sha'awa,bata san lokacin da murmushi ya sub'uce a kan kyakkyawar fuskarta ba....
Hajiya Maryam ta kalli yadda take farin ciki nan take itama ta tsinci kanta a cikin farin ciki,nan da nan taji wani abu ya tokare mata zuciya, sakamakon tunawa da tayi da mahaifiyar HALIMATU kasan cewar su biyu iyayen su suka haifa,shiyasa idan tana tare da HALIMATU sai taji kamar tana tare da 'yar uwarta ne......
tayi sauri ta maida ƙwallar da take shirin sakkowa daga cikin idanun ta.....
tsaya war da taji motar tayi shiya dawo da ita daga duniyar tunani da ta lula.ta d'ago kanta
Taga ashe har sun ƙaraso ma,ta juyo ta dubi HALIMATU da ke kallon katafaren gidan da taga driver ya faka a bakin get ɗin.batare da bata lokaci ba ya danna horn,nan take wani dattijo ya le'kowa ta ƙaramar ƙofar get ɗin.
Ganin motar gidan ce yasa shi ya koma da sauri ya buɗe musu get ɗin.malam habu ya danna hancin motar ya shiga ciki yayi parka motar a parking space ɗin gidan. ya fito da sauri ya buɗe motar. momy ce ta fara fitowa daga motar, sannan itama HALIMATU ta biyo bayan ta ɗauke da jaka a hannu ta...
Baba mai gadi yana ganin fitowar su ya taho da sauri yana wa hajiya barka da zuwa tace "barka dai baba fatan na same ku lafiya"
Yace lafiya 'kalau hajiya" HALIMATU ma ta gaishe shi ya amsa fuskarsa a sake.ya juya tare da komawa wajen zaman shi ya zauna ya cigaba da jin radion sa.
HALIMATU ta tsaya tana ƙarewa gidan kallo,gidan ya haɗu sosai an yi masa ginin zamani,ga shuke suke gwanin ban sha'awa.gidan part biyu ne sai boys quarters ,daga bayan parts ɗin kuma garden ne da aka ƙawata shi da shuke shuke kala kala ciki kuwa harda kayan marmari. part ɗin farko wanda shine ya fi girma shine nasu,na biyu kuma shine na yaran momy maza........
tunani takeyi a cikin zuciyar ta,shin yanzu itama a lirin wannan gidan zatayi rayuwa!! Kodai mafarki take yi ne!!..........
Duk wannan tunanin a cikin zuciyar ta take yinsa.tana cikin tunani ne ta jiyo muryar momy na 'kwala mata kira "tace tsayuwar me kike yi anan ne har na kusa shiga ciki baki taho ba"......
Cikkn sauri tabi bayan momy suka shiga ƙofar da zata sada su da babban falon gidan.
Suna shiga HALIMATU ta saki baki tana kallon haɗuwa da tsaruwar da falon yayi.
An zuba masa ƙayatattun royal chair ,ga dining table a gefe,ga katuwar plasma tana aiki.parlon ya haɗu sosai an an gyara shi tsaf tsaf gwanin sha'awa, ga ƙamshi sai tashi yake yi,ga kuma sanyin ac da ya mamaye falon gaba ɗaya......
Hajiya maryam ta samu waje ta zauna a kan ɗaya daga cikin kujerun falon,ta nuna wa HALIMATU kusa da ita tace tazo ta zauna ta huta...........
Tana zama ta lumshe idon ta, sakamakon jin taushi da laushin kujerar.nan take ta sauke ajiyar zuciya ta tsinci kanta a cikin tsananin farin ciki..
Zaman su keda wuya sai ga masu aikin gidan sun shigo su biyu suna yi musu sannu da zuwa, hajiya maryam ta amsa tana duban datti juyar cikin su tace "baba ladi ga 'yata HALIMATU da nake baki labarin ta, na ɗakko ta tadawo gurina zata zauna tare da mu".. baba ladi ta washe baki tace"barka da zuwa HALIMATU " itama tayi murmushi ta amsa mata da" yauwa baba,mun same ku lafiya??" "Baba tace lafiya k'alau".
Momy ta dubi ɗayar ta cewa da HALIMATU"wannan sunan ta uwani" uwani ta dubi HALIMATU tana murmushi tare da ƙare mata kallo,saboda ta ganta kyakkyawa sosai, gata yarinya ƙarama,gashi kuma Allah yayi mata diri duk da ƙanƙantar shekarun ta, a zuciyar ta tace wannan matar manya ce duk wanda ya aure ta wallahi ya more.............
Gaisuwar da HALIMATU take yi mata ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da take,ta amsa mata da "lafya 'kalau,fatan kunzo lafiya"ta ce mata lafiya lau"...
Bayan sun gama gaisawa ne suka shirya musu lafiyayyen abinci a saman dining table daga nan suka fita suka koma inda d'akin kwanan su yake.........
Bayan fitar su hajiya maryam ta kama hannun ta suka nufi kan dining table ɗin suka zauna,ta shiga buɗe food wamers ɗin da aka jere a gurin.
Kular farko fried rice ce da taji kayan lambu da zallar tsokar kaza,ta biyu kuma alkubus ne da akayi shi da miyar ganye wadda taji naman rago,ta uku kuma pepper chicken ne da yaji had'i sai ƙamshi yake yi,sai kuma coleslaw da yaji da faffen ƙawai.......
Momy ta juyo ta kalle ta tace "daughter mai zan zuba miki"HALIMATU tace "ki zauna ni zan zuba miki momy". tace "to"tare da komawa ta zauna HALIMATU ta ɗauki plate ta zubuwa momy alkubus saboda ta ga shi take son taci, sanan ta ɗauki bowl ta zuba mata miya,ta kuma jawo wani plates ɗin ta zuba mata pepper chicken ta tura gaban ta........
Momy tace "thank you daughter,kamar kin san abin da nake son ci kenan,kema zauna ki zuba kici".
HALIMATU ta jawo plate ta zuba fried rice da papper chicken,har zata zauna momy tace "aa ya baki zuba coleslaw ɗin ba??"......
HALIMATU ta sake jawo coleslaw ɗin ta zuba, sannan ta zauna tayi bismillah ta fara ci,tana ci tana lumshe ido saboda abincin yayi mata mutuƙar daɗi sosai.
Bayan sun gama cin abincin ta tattare kayan da suka b'ata momy ta nuna mata kitchen taje ta kai ta ajiye,har zata wanke taji momy ta ƙwala mata kira.ta amsa tare da fitowa daga cikin kitchen ɗin.
"tace"momy gani"momy ta kama hannun ta tana cewa"muje in nuna miki d'akin ki kiyi wanka ki kwanta ki huta kafin auta ta dawo daga school ta hana ki runtsawa"......
Suna hawa sama ta buɗe wani d'aki kusa da d'akin auta, d'akin ya haɗu sosai an zuba masa furnitures masu kyau ƙirar itali.ga kujeru guda biyu da ɗan ƙaramin table........
A gefe guda kuma ga table ɗin karatu.d'akin ya haɗu babu laifi kuma babu tarkace a cikinsa.halimatu sai kallon ikon Allah take.momy ta kama hannun ta ta kaita har cikin toilet ta nuna mata yanda zatayi amfani da toilet ɗin ta fito ta barta a ciki....
Bayan ta fito ta buɗe jakarta ta ɗakko wa HALIMATU ɗaya doguwar rigar da suka siyo da turare ta ajiye mata a kan gado, tajawo ƙofar d'akin ta rufe mata,ta nufi ita ma nata d'akin sabo da a gajiye take sosai tana buƙatar tayi wanka ta kwanta ta huta........
Tana fitowa daga toilet ɗin ta goge jikin ta da towel ɗin da momy ta nuna mata tun a cikin toilet ɗin.bayan ta gama ta ɗauki lotion ɗin da ta gani akan mirror ta shafa.ta ɗauki rigar ta saka ta d'an fesa turare kaɗan ta haye gado ta kwanta.
Nan take wani bacci mai mugun daɗi ya ɗauke ta......
To jama'a ga fa HALIMATU a birni,yanzu labarin zai fara!!
Kudai ku cigaba da bina,domin jin yadda labarin zai kasance............
Ina godiya da addu'ar ku gareni.
Kuma nima ina muku fatan alkhairi....
FATIMA BINTU ABDALLAHI (UMMU AYSHA)..................✍🏻