Sashe 50
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Daga haka suka wuce zuwa in da kayan mukhtar ɗin suke tare da kwaso su suka zuba su a cikin boot ɗin motar,ba tare da ɓata lokaci ba suka shiga cikin motar nura yaja suka tafi.
Direct gidan su mukhtar suka nufa lokacin har an shiga masallaci, fitowa suka yi cikin sauri suka yi alwala tare da shige wa cikin masallacin.
Bayan an idar da sallar ne daddy dake zaune cikin masallacin yana lazimi ya farga da su,matsawa suka yi in da yake zaune suka gaishe shi cikin girmamawa ya amsa cike da fara'a da nuna jin daɗin sa.
A tare da daddy suka fito daga cikin masallacin zuwa cikin gidan bayan gari ya yi haske,suna shiga parlon suka iske Hajiya zainab da masu aikin ta su biyu suna kimtsa dining table ɗin, durƙusa wa suka yi har ƙasar suka gaida MOMY cike da girmama wa.
Cikin matsanancin farin cikin ganin ɗan nata ta amsa tare da cewa:
"Ina fatan ka dawo gida lafiya my son.? ya hanya.?"
"Lafiya ƙalau Alhmdllhi momy hanya lafiya ƙalau sai dai gajiya"
"Ai dama wannan dole ne,gashi ka hana ɗana bacci ka taso shi cikin dare ya zo ɗaukar ka"
Ta ƙarasa maganar tana kallon Nura.
Murmushi Nura ya yi tare da cewa:
"Wallahi babu komai mommy,ai dama ni ya dace na ɗakko shi a wannan lokacin,bana so a takura muku sabo da dare".
"Allah ubangiji ya yi muku albarka,ya kare ku daga dukkan sharri"
"Ameen Ameen momy"
Daga haka momy ta ja su zuwa dining domin su yi break fast,da kanta ta zuba musu abin cin har da daddy sannan ita ma ta zubawa kan ta, MEENA da su sahal ne kawai basu fito ba,dama ta saba kullum tare da su sahal ɗin take cin abinci.
Bayan sun gama cin abincin ne Nura ya yi musu sallama akan zai je gida ya yi shirin zuwa office,godiya suka shiga yi masa tare da saka masa albarka,tare da mukhtar suka fito ya rako shi har parking space.
Buɗe boot ɗin motar nura ya yi tare fitar da akwatunan mukhtar ya ajiye a gefe, sallama suka yi nura ya ja motar sa ya tafi shi kuma mukhtar ya umar ci mai gadi da ya taya shi kwashe kayan zuwa part ɗin sa.
Dawo ya yi part ɗin su momy ya tarar har sun gama cin abincin suna zaune a kan sofa suna hira,waje ya samu ya zauna tare da cewa:
"Momy Ina su meena suke ne.? ban ji motsin su ba.?"
Suna sama ita da ƴaƴen ta yanzu zaka ga sun sakko cikin shirun su na tafiya school"
Murmushi ya yi yana jin jina irin soyayyar da meena take yiwa yaran nasa,ba ƙaramin ƙoƙari ta ke a kan su ba, komai ita take yi musu har tausayin ta yake ji idan ya tuna uwar da ta haife su ko janyo su a cikin jikin ta bata yi bare su saka ran za ta kula da su.
Sai ga shi ita meena da bata san zafin haihuwar su ba ita take ta ɗawainiya da su,hatta bacci tare suke yi kullum, haka abinci ma tare suke ci sannan ta yi musu wanka ta shirya su.
Tunanin sa ne ya katse lokacin da suka sakko ƙasa ita da yaran cikin shirin zuwa school,ba ƙaramin murna suka yi ba da ganin mahaifin na su ,nan take suka tafi da gudu suka rungume shi suna tsallen murna.
Rungume su ya yi fuskar sa cike da fara'a yana shafa kan su tare da tambayar su school,sahal ne yace:
"Daddy school lafiya ƙalau"
yasmin ta ce:
"Daddy ina tsarabar mu"
"Tsarabar ku tana nan na taho muku da ita kuda auntyn ku"
Murna suka kama yi har da tsallen su.
Meena ce tazo kusa da shi ta zauna tare da yi masa barka da zuwa,amsawa ya yi cike da fara'a tare da yi mata godiya game da hidimar da take yi da yaran na sa.
Ɓata rai ta yi tare da cewa:
"Haba yaya! me ye kuma abin godiya! yaran nan fa ƴaƴana ne halak malak! idan ban kula da su ba waye zai kula da su,dan Allah ka dena faɗin irin hakan wallahi bana jin daɗi"
Ta faɗa tana marairai ce murya kamar zata yi kuka, murmushi ya yi tare da cewa:
"Toh shikenan na bari auta,ta shi kije ku yi break fast ke da yaran naki ki kar ku yi late".
Miƙewa ta yi tare da kama hannun su suka nufi dining.
Duk abin da yake faruwa a kan idon momy da daddy,ba ƙaramin tausayin sa suke ji ba, miƙewa ya yi tare da cewa daddy da MOMY zai je ya ɗan kwanta ya huta.
Gyaran murya daddy ya yi tare da cewa:
"Zauna zamu yi magana"
Babu musu ya koma ya zauna.
Kallon sa daddy ya yi tare da cewa:
"Idan ka huta ko zuwa gobe ne idan Allah ya kaimu zamu je mu duba Alhaji USAMA kakan yaran nan,domin sun samu tsau-tsayi a kan hanyar su ta dawo wa daga ENUGU shi da abokin nan nasa Alhaji Garba ɓarayi suka tare su,yanzu zancen da nake yi maka shi Alhaji Garban sun kashe shi, shi kuma Alhaji USAMA sun raunata masa ƙafafun sa da harsashi wanda sakamakon hakan ya sa aka yanke masa ƙafarsa guda ɗaya,dan haka ka yi ƙoƙari ka samu lokaci muje mu dubo shi!".
Ba ƙaramin girgiza mukhtar ya yi da jin wannan labarin ba,nan take ya ce wa daddy:
""Toh daddy in sha Allah"
Ya faɗa tare da miƙewa ya fice daga parlon zuwa part ɗin sa domin ya kwanta ya huta.
***-----------****-----------****
***-----------****-----------****
A ɓangaren su HALIMATU kuwa yau shima daddy zai dawo da marai ce,shi yasa tun da suka tashi da asuba suke ta shirye-shiryen karɓar baƙin.
Tun jiya momy ta kirawo me saloon ɗin da take musu ta sanar da ita za su zo yau da sassafe,hakan ne ya sa mai saloon ɗin ta fito da wuri ta buɗe shagon.
suna isowa ba tare da ɓata lokaci ba aka fara gyara musu jikin su tare da gyaran jiki da lalle ja da baƙi,zuwa ƙarfe 12 na rana aka kammala duk wani abu da za'a yi musu,ba ƙaramin kyau suka yi ba musanman ma HALIMATU, wannan dalilin ne ya sa momy ta yiwa mai saloon ɗin kyau ta mai tsoka sannan suka baro wajen.
Direct kasuwa suka nufa domin siyen abubuwan da ba suda shi,nan halimatu ta sayi kayan haɗin cake decorations domin haɗawa MUKHTAR ɗan ƙaramin party, kasancewar momy ta iya harkar baking sosai shi yasa halimatu itama ta iya sosai.
Ƙarfe biyu suka ƙaraso gida a mutuƙar gajiye,sallah kawai suka yi suka shiga kitchen suka fara aiki su uku har da baba ladi,dama tun kafin su iso ta fara rage wasu ayyukan,ita kuma HALIMATU ta shiga haɗa kayan haɗin cake decorations,dama tun jiya ta yi baking ɗin cake ɗin.
Ƙarfe huɗu suka gama dukkanin abin da zasu yi suka shirya dining table ɗin ya yin da su Hafiz da Sadiq suka tafi ɗakko daddy domin ƙarfe huɗu jirgin su zai sauka,ita kuma HALIMATU ta shirya wa MUKHTAR nashi daban a parlon baƙi wanda ta yiwa dining area ɗin decorations ya yi kyau sosai har da su balloons.
Wanka suka je suka yi yayin da mai make up ɗin da momy ta kirawo ta tsan tsara musu kwalliya mai kyau da burgewa, shigar wani haɗaɗɗen lesss suka yi mai tsada kalar maroon da golden su uku har da auta, ba ƙaramin kyau suka yi ba abin ka da fararen mata sai less ɗin ya ƙara fito da tsantsar kyawun da suka yi.
Su daddy basu ƙaraso gidan ba sai kusan ƙarfe biyar, zo kaga murna wajen family ɗin nan ba ƙaramar tarba daddy ya samu ba,ba tare da ɓata lokaci ba aka haɗu gaba ɗaya akan dining aka yi ƴar ƙaramar walima.
Daddy sai satar kallon momy yake ya gaza yin haƙuri sabo da ba ƙaramin kyau ta yi masa ba sosai sai kace an chanja masa ita kamar wata ƙaramar yarinya, kasancewar tana da jiki mai kyau shi ya sa idan mutum ya ganta sai ya yi zaton ba ita ta haifi yaran nan ba.
A koda yaushe godiya yake yiwa Allah da ya mallaka masa ita a matsayin matar auren sa kuma uwar ƴaƴen sa,tana matuƙar girmama shi da yi masa biyayya da kuma faran ta masa ransa,hatta da iyayen sa alfahari suke yi da samun ta a matsayin surukar su,domin ta ɗauke su tamkar iyayen da suka haife ta, wannan dalilin ne ya ƙara mata daraja da kima a idon mijin ta da dangin sa.
Basarwa momy ta yi da kallon da yake yi mata kamar bata gani ba, sabo da bata son ta biye masa su ji kunya a gaban ƴaƴen su,fahimtar hakan da Hafiz ya yi ne ya sa yana kammala cin abincin ya miƙe tare da cewa:
"Daddy bari naje part ɗin mu akwai aikin da zan yi Allah ya hutar da gajiya".
Ganin haka ya sa Sadiq shima ya miƙe ya bi bayan sa, ita ma halimatu miƙewa ta yi tare da kama hannun auta suka haye sama aka bar daga momy sai daddy.