← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 80

Sashe 39

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shirun da malam musa ya yi tare da sunkuyar da kanshi ƙasa shine ya tabbatar masa da cewa bai sanar mata da saƙon ba.
Ajiyar zuciya malam musa ya sauke tare da cewa
"A gaskiya ban faɗa mata saƙon ka ba, sabo da bansan yanda zata ɗauki abin ba, musamman ma da abubuwa suka dinga faruwa kala kala shi yasa ban faɗa mata ba,amma yanzu tunda Allah ya kawo ka sai ka faɗa mata komai,domin waƙa a bakin mai ita tafi daɗi".

Har ya buɗe baki da nufin yin magana kwatsam suka jiyo sallamar altine da rahinatu suna shigowa cikin gidan HANNE na biye da su a baya,cikin tsananin farin ciki kowaccen su ta nufi in da mahaifin na su yake zaune a kan tabarma shida abokin sa kuma maƙocin sa.

Zama suka yi a gefe tare da gaishe shi cike da so da ƙaunar mahaifin na su, amsawa ya yi cike da tsantsan son su da kewar su da ya yi,in da yake tambar su jikokin sa da mazajen su,gaba ɗaya suka amsa masa da kowa yana lafiya.

Juyawa ya yi ya kalli INNA LAURE dake tsaye har yanzu yace
"Idan kinga dama ki zauna muyi magana,idan kuma Ba zaki zauna ba shikenan!"

Badan ta so ba ta samu guri ta zauna tana botsare botsare.

Cikin nutsuwa baba ya soma magana

"Alhamdulillah, dama ina so sai kowa ya zo sannan in yi bayani a gaban kowa,duk da cewa malam musa ya san komai"
Ya faɗa yana nuna malam musa da hannun sa.
Ya ci gaba da cewa
"Lokacin da ƙanwar mahaifiyar HALIMATU ta zo zata tafi da ita sakamakon muzgunawa da duka da rashin jin daɗin zaman da HALIMATU take yi a wajen mahaifiyar ku,ga talla da take ɗora mata safe da yamma,abinci ma sai ta ga dama zata bata"
Shiru ya yi tare da sunkuyar da kansa alamar yaji ciwon abin,daga bisani ya ɗago da kansa ya ci gaba da cewa

"Hakan yasa na bata goyon baya na ɗauki amanar HALIMATU na damƙa mata na bata ita halak malak........"

Labarin abin da ya faru ya basu tun daga farko har ƙarshe da kuma cin mutuncin da inna laure ta yi masa tare da tijara da tofin alatsine.
Ya ci gaba da cewa
"Ban bar garin nan ba sai da na datse ragowar igiyar aure na ɗaya da take kanta,na rubuta mata takardar sakin ta na ninke ta na ɗora mata akan windon ɗakina, Sabo da bazan iya tafiya da igiyar auren ta a kaina ba,na yi haƙurin zama da ita shekara da shekaru tana muzguna min,kwata kwata bata gani na da kima da daraja"
Ya ci gaba da cewa......

"Hatta mahaifiyar HALIMATU da na auro haka ta rayu cikin wahala da ƙunci na uƙubar mahaifiyar ku har ta koma ga Allah,yanzu kuwa babu sauran igiyar aure tsakani na da ita.

"Bayan na rabu da mahaifiyar ku Allah ya kuma haɗa ni da matar kirki na aura,kuma cikin hukuncin ubangiji Allah ya albarkace mu da samun ɗa namiji in da aka saka masa suna Ahmad,yanzu haka tare da ita mukazo nan tana gidan malam musa, sakamakon afkamata da mahaifiyar ku ta yi yunƙurin yi,shi yasa nace mata ta koma can ɗin '".

Ya cigaba da cewa

"Yanzu haka wannan zuwan da na yi nazo ne domin na ganku na duba ku sosai,duk wanda yake da wata buƙata ya faɗa min,duk abin da kuke so zan yi muku shi,dan yanzu Allah ya hore min ina samu sosai"

Nan ya basu labarin irin gwagwarmayar da ya sha bayan tafiyar shi da kuma yanda Allah ya yi masa arziƙi.

Kallon altine ya yi da take kukan jin ciwon abin da mahaifiyar su ta aikata yace

"Tashi ki shiga cikin ɗaki na takar da na nan akan window nannaɗe ki ɗakko min ita!"
Cike da mutuwar jiki ta miƙe tare da shigewa ɗakin da yake matsayin nashi a da.
Bata wani ɗauki lokaci ba ta fito hannun ta ɗauke da wata farar takarda da aka nannaɗe ta duk ta yi ƙura sosai tazo gaban baba ta tsuguna tare da miƙa masa takardar.

Hannu yasa ya karɓa tare da buɗe wa ya miƙa wa malam musa yace
"Gashi nan kowa ya duba ya gani domin ya zama shaida, dubawa ya yi tare da girgiza kansa ya ɗago ya dubi malam ummaru yace

"Tabbas haka ne wannan, Allah ubangiji yasa hakan shi yafi zama alkhairi"

Ya faɗa tare da miƙa masa takardar.karɓa ya yi tare da miƙa wa yaran ɗaya bayan ɗaya kowa sai da ya gani daga bisani kuma aka miƙa wa Inna Laure.

Wani irin karkarwa jikin ta ya kama yi kamar wadda aka jonawa shocking a jikin ta, ɗagowa ta yi da rinannun idanun ta ta kalli baba tare da cewa

"Ni zaka wulaƙanta ummaru Sabo da ka yi arziƙi shine zaka sake ni ka auro karuwa!! Tun kana matsiyacin ka nake tare da kai amma yanzu ka kuma kwaso wata sabuwar karuwar ka kawo mana kana liƙirarin wai matarka ce har kana saki na akan ta toh.......
Ɗaga mata hannu ya yi ba tare da ya bari ta ƙarasa abin da ta yi niyyar cewa ba yace

"Dakata Laure!! Yanzu ba irin da bane wallahi! domin ummarun da ki ka sani a da yanzu ba shi ne ba,dan haka karki ƙara kiran mata ta da karuwa idan kuma ba haka ba hukuma ce zata rabamu da ke!!"wani irin mugun ashar ta lailayo ta ƙunduma masa tare da cewa

"Wallahi sai dai ka yi duk abin da zaka yi, amfaɗa ance karuwa! kayi abin da zaka yi nace!"

Wani irin runtse ido baba ya yi kamar wanda aka watsa wa garwashin wuta, idanun sa sun kaɗa sun yi jawur sabo da ɓacin rai.

Kallon ta malam musa ya yi tare da cewa

"Haba LAURE me yake damun ki ne! Ke wacce irin mace ce da bata san kima da mutuncin mutane ba!har yanzu dai kina nan da halin ki bazaki taɓa canja wa ba ne?? Ai ko dan abubuwan da suka yi ta faruwa yakamata su zame miki Babban darasi a rayuwar ki!!"

Cikin tsanani fusata ta yo kan malam musa tare da cewa

"To baƙin munafiki algungumi! Ai dukkan wani abu da aka shirya tare da kai aka yi shi,kuma wallahi,wallahi,sai ka yi nadamar sani na da ka yi a rayuwar ka!!"

Tahowa altine ta yi da sauri ta kama hannun ta tajata da ƙarfi tana turjewa ta turata cikin ɗaki ta kulle ƙofar.

Tsugunawa suka yi a gaban baba suna bashi haƙuri akan abin da mahaifiyar su ta yi masa, Murmushi ya yi musu tare da cewa

"Babu komai ku rabu da ita,gida kuma dama naku ne na bar muku shi halak malak,zata iya ci gaba da zama a cikin sa albarkacin ku,idan kun gama ku shiga gidan malam musa ku gaida auntyn ku,zata bawa kowannen ku tsarabar da nayo masa, Sabo da da anyi la'asar zamu koma,bana son masu kawo kayan saka ranar bikin HANNE su iske Ni.

Na bar komai a hannun malam musa,ku karɓi numbern waya na da ta auntyn ku a wajen ta Sabo da mudinga gaisawa akai akai,sannan dukkan wani abu da kuke buƙata ku dinga sanar min a waya,idan na kuma samun lokaci zanzo na ɗauke ku na kaiku har gida na kunji, Allah ubangiji ya yi muku albarka baki ɗayan ku"

Hawayen da yake fuskar su suka share da hannayen su,domin su kansu sheda ne mahaifin su ya sha baƙar wahala a zamantakewar su da inna laure,wanda ba kowane namiji bane zai iya wannan wahalar.

Juyawa suka yi suka fita daga gidan shida malam musa.

Wannan kenan....

***************************************

"HAJIYA HAUWA"

A ɓangaren Hajiya Hauwa kuwa, lokacin da ta jefa ƙafarta a cikin ɗakin RUFAIDA, tsaye ta yi turus! Sakamakon ganin abin da ya ɗaga mata hankali da ta yi.

Domin RUFAIDA ta gani kwace a ƙasa idanun ta a kakkafe babu alamar numfashi a tattare da ita,cikin sauri ta afka cikin ɗakin bakin ta na kiran sunan RUFAIDA babu ƙaƙƙautawa,hannunta ta sa ta ɗago da ita zuwa jikin ta tare da jijjigata tana ƙara kiran sunan ta,amma shiru kake ji babu alamar motsi a tattare da ita.

Ganin haka yasa ta buɗe toilet ɗin ɗakin ta ɗebo ruwa ta shafa mata a fuskar ta,amma duk da haka bata motsa ba.

Ganin haka yasa ta ɗora hannu a kanta tare da cewa

"Na shiga uku!! Me ya same ki RUFAIDA? ko wani ne yazo ya yi miki wani abu ne...? Tell me my baby what is happening..?"

Ta faɗa tana ƙara girgiza ta tana kuka,ganin hakan da take yi babu wani ci gaba da aka samu yasa ta miƙe tsaye da sauri ta fice daga cikin ɗakin.

Ɗakin Aminu ta nufa wan RUFAIDA ta bubbuga masa ƙofar da ƙarfi sosai,cikin baccin sa mai daɗi yaji wani irin bugu da ake yi masa wanda ba na hankali ne ba.

A firgice ya miƙe ya ɗauki jallabiyar sa ya ɗora akan boxer ɗin sa ya buɗe ɗakin ya fito,umma ya gani tsaye a bakin ƙofar tana kuka,cike da tashin hankali ya ƙarasa fitowa daga cikin ɗakin ya kama hannun umma yace

"Umma mai ya faru...?
cikin kuka tace masa

"RUFAIDA!" RUFAIDA!" RUFAIDA!".

Ta faɗa tana yarfe hannayen ta.

Cike da tashin hankali yace

"Umma wai me ya samu RUFAIDA ne.....? Ki gayamin dan Allah....?"

Hannun sa taja tare da yi masa alamar su tafi, Bin bayanta ya yi suka nufi cikin ɗakin,yanda ta barta haka suka same ta ma a yanzun.

Cikin tashin hankali ya zuba mata idanu tare da jijjigata,jin bata motsi ya sa ya ciccibeta ya ɗora a kafaɗar sa ya fita da ita,buɗe mota ya yi yasata a ciki.
Juyowa ya yi ya kalli umma da take tahowa ɗauke da mayafi a hannun ta da takalmin ta a hannu,kana ganin ta kasan bata cikin hankalin ta.ɗaga muryarsa ya yi tare da cewa
Chapter 39 · 0% Book details