Sashe 4
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kee ya nuna inna laure yace"kina so ayi miki aiki a ƙara mallake miki mijin ki,sai yanda kikayi da shi,sannan kuma kina so ayi miki aiki kada mijin ki ya bada dama a tafi da 'yar kishiyar ki birni!!tabbas idan har aka samu nasarar tafiya da ita,to shine mafarin nasarar ta!!"....
Ke kuma, ya nuna hansai yace...............
"kina so yarinyar ki ta auri ɗan me gari da ya dawo daga birni karatu"
Dukkanin su suka haɗa baki suka ce"haka ne sarkin bokaye"boka ya tun tsure da wata iriyar mahaukaciyar dariya mai kama da kukan jaki, wacce ta jawo hatta kogon dutsen sai da ya amsa.....
Lokaci ɗaya kuma ya haɗe ransa,kamar bai taɓa dariya ba,ya kai duban sa ga inna laure yace......
"Aikin ki a kwai haɗari a cikin sa,idan kika yi kuskure wannan karon za'a iya samun matsala!!!"......
Inna laure ta ɗago da kai ta dubi boka gaban ta yana fad'uwa tace"zanyi yadda kace sarkin bokaye!!"....
Nan take boka ya ɗaga hannu sa sama sai ga ƙullin magani guda biyu sun bayyana,ya sauke hannun sa ƙasa,ya maida duban sa ga inna laure yace"wannan zaki barbad'a shi a ƙarƙashin shimfid'ar mijin ki,muddin ya riga ya kwanta to sai yadda kikayi da shi,wannan kuma ki zuba wa yarinyar cikin abincin ta,muddin ta riga taci to kome Za'a yi mata baza ta taba bari a tafi da ita wani wajen ba, kuma ba zata ƙara jin maganar kowa ba sai taki!!"
Ya ƙarasa maganar yana mi'ko mata ƙullukan maganin....
Inna laure jikinta na rawa tayi maza ta miƙa hannu ta karbi maganin, ta kwance ƙullin zaninta ta kwashe duka kuɗin da ta ƙulle ta ajiye a gaban boka......
Boka makau ya kuma ɗaga hannu sa sama yana wasu surutai marasa daɗin sauraro,sai ga wasu ƙullin maganin sun sake bayyana a gabjejen tafin hannu sa, ya juyo ya kalli hansai ya miƙa mata yace......
yace "wannan a barbad'a mata shi a cikin ruwan wankan ta, shikuma wannan kwalli ne,ta tabbatar idan ta saka shi to kada ta sake ta haɗa ido da kowa idan ba yaron ba"ya ƙarasa maganar yana miƙa mata ƙullukan maganin..........
Itama cikin sauri ta mi'ko hannu ta karb'a,saka hannu ta ciro kuɗi a ƙarƙashin zaninta ta ajiye a gaban boka.kafin wani daga cikin su ya ƙara faɗin wani abu suka ga boka ya buga sandar sa nan take suka b'ace daga cikin kogon.......
Basu tashi tsintar kansu a ko ina ba sai a tsakiyar daji sukaji an watsosu cikin duwatsu,ga guguwa kamar ta tashi dasu Sama....
Haka nan suka tashi suka karkad'e jikin su suka cigaba da tafiya.
Lokacin da suka fito daga cikin dajin anan bakin titi suka samu mashina suka hau aka maida su cikin ƙauyen su,suna isowa kowacce ta kama hanyar gidan ta....
lokaci da inna laure ta shigo cikin gidan ko sallama batayi ba ta faɗo cikin gidan wujiga wujiga da ita,ta iske hanne a tsakar gidan tana wankin uniform ɗin ta na makaranta.hanne ta ɗago da kanta ta dubi inna laure tace"haba inna ya zaki shigo mana cikin gida ko sallama babu,kamar ba gidan musulmai ba!!"....
Inna laure ta jiyo a fusa ce ta dubi hanne ta tace"don ubanki na shigo ɗin ko zaki dake ni ne!! nace ko zaki dake ni ne!! wallahi hanne ki kiyaye Ni,bana son fitsara,idan bahaka ba zanyi mummunan saba Miki".ta ƙarasa maganar
tana huci.
Hanne ta tab'e baki tace" Allah ya huci zuciyar ki Innar mu, wai ina kuka je ne nayi ta jiranki baki dawo ba,shiyasa ma nayi dawowa ta gida wallahi."....
Inna laure tace"inda kika aikemu nan muka je"ta ƙarasa maganar tana shigewa cikin d'akinta, batare da ta ta karbi takan hanne ba......
****************************************
tana shiga ɗaki ta ajiye mayafinta, ta kwance ƙullin zaninta ta ciro ma ganin wajen boka makau ta fice daga cikin d'akin, ta buɗe d'akin malam ummaru ta shiga ciki,ta ɗaga ƙarƙashin shimfid'ar sa ta barbad'a maganin,tayi maza ta maida shimfid'ar ta fito daga cikin d'akin.....
A ɓangaren su HALIMATU kuwa suna nan zaune suna hira suka jiyo sallamar hanne suka amsa mata,ta shigo cikin d'akin nasu ta samu waje ta zauna...
Hajiya Maryam ta dube ta tace "hanne har kun dawo??"....
hanne tace"wallahi momy ta howa ta nayi, saboda tun da mukaje gidan suka tafi unguwa ita da inna hansai har yanzu basu dawo ba,shiyasa na gaji da jira nayi dawowa ta".
ta ƙarasa maganar ranta a b'ace.hajiya maryam tace ai da kinyi haƙuri kin jirata ta dawo ɗin in yaso sai ku taho tare,a dinga hak'uri hanne,mahaifiyar kice ki dinga jin maganar ta, tace mata to.daga nan ta tashi tace zataje ta wanke uniform ɗin ta na makaranta .to tana cikin wankin ne inna laure ta dawo.
Su HALIMATU suna cikin ɗaki basu san inna laure ta dawo ba,kawai sai jin sallamar ta suka yi a ƙofar d'akin da suke ciki.cike da mamaki hajiya maryam ta amsa sallamar inna tana kallon ƙofar d'akin, ganin inna ta shigo cikin d'akin ta samu waje ta zauna da kwano riƙe a hannun ta.....
Inna ta washe baki ta kalli hajiya maryam tace "maryam an wuni lafiya, wallahi tun safe nake ta son in shigo mu gaisa ban samu dama ba,saboda na ɗan fita unguwa,ban daɗe da shigowa gidan ba"....
ta ƙarasa maganar fuskarta ɗauke da makirin murmushi .hajiya maryam ta dube ta fuskarta ɗauke da murmushi tace"wallahi babu komai laure na gode da kulawa" inna ta ƙara sakin murmushi a karo na biyu ta dubi HALIMATU da ta sha jinin jikin ta cike da kissa tace HALIMATU ga abinci na kawo miki maza ɗauki kici kinji kwad'on zogale ne yanzu nayi shi saboda ke!!"......
ta ƙarasa maganar tana mi'ko mata kwanon.HaLIMATU ta saka hannu ta karb'a tace"na gode Inna".inna laure tace "to maza ki saka hannu ki cinye shi yanzu"
Hajiya Maryam tace "wallahi laure mun ƙoshi,bamu daɗe da gama cin abinci ba" nan take inna laure ta canja fuska zuwa damuwa,hajiya maryam tace"karki damu Laure,in anjima zataci".
Badan inna laure ta soba ta fito daga cikin d'akin,tana ta addu'a acikin ranta Allah yasa HALIMATU taci abincin.
Bayan fitar ta ba bu dad'ewa hajiya Maryam ta d'akko kwanon ta samu leda ta juye kwad'on zogalen,ta boye a bayan kofa dan kwata kwata bata yadda da inna laure ba..........
**************************************
Bayan ta juye ta ce da HALIMATU ta tashi ta zuba mata ruwa ta yi alwala,saboda lokacin sallar magriba yayi
HALIMATU tace toh,ta na fitowa ta ji sallamar malam ummaru yana shigowa cikin gidan,cike da zumud'i ta nufi inda yake tsaye taje ta dur'kusa fuskarta ɗauke da matsanancin farin ciki tace"baba sannu da zuwa,an dawo lafiya ya hanya??" duk ta jera masa tambayoyin a lokaci guda......!!
Ya dago ya dube ta fuskarsa ɗauke da farin cikin ganin ta yace"lafiya k'alau HALIMATU na ya gida,da fatan na sameku lafiya,ina 'yar uwarki hanne??"
Kafin ta bashi amsa sai ga hanne ta fito daga cikin d'akin sakamakon jin muryar baban nasu da tayi.itama tazo gaban sa ta dur'kusa cike da farin ciki tayi masa sannu zuwa ya amsa fuskarsa sa a sake,yace musu "to ku tashi mu shiga ciki "
Suka ce tom........
HALIMATU ta amshi ɗan buhun da yake hannun sa suka nufi cikin d'akin sa,ta ajiye buhun a ƙasan d'akin.malam ummaru ko zama beyi ba yace da HALIMATU ta zuba masa ruwa yayi alwala,sai a lokacin HALIMATU ta tuna bata zubawa hajiya maryam ruwan alwalar ba,gaba ɗaya murnar dawowar baba ta mantar da ita....
Cikin sauri ta zuba ruwa acikin butoci guda biyu jin har ana gab da tada sallar magriba,ta mi'kawa baba buta ɗaya ɗaya kuma ta ajiye a gurin ta nufi ɗaki ta samu momy tsaye tana shirin fitowa,saboda taji HALIMATU shiru,tace"momy kiyi haƙuri, wallahi ina fitowa daga ɗaki baba ya shigo cikin gidan, murnar dawowar sa ta saka na mance shaf wallahi!! amma ga ruwan can na zuba miki"
Hajiya Maryam tace ba komai daughter,ashe malam ummaru ya dawo?ma sha Allah!!gobe da yardar Allah zamu tafi"ta ƙarasa maganar cike da murmushi.
HALIMATU tace......
"Ae momy yanzu ya dawo,amma ya tafi masallaci yayi Sallah!!".....
Tace okay tom shikenan,bari naje nayi alwala nayi sallah kafin ya dawo.ta faɗa tana fita daga d'akin......
Itama HALIMATU fitowa tayi daga ɗakin ta ɗauki tsintsiya ta nufi ɗakin babban nasu domin ta gyara masa,saboda d'akin yayi ƙura sosai,kuma tasan inna laure ba gyarawa zatayi ba.
Tana shiga ta hau gyaran d'akin tana karkad'e ƙura,ta kwashe shimfid'ar gaba ɗaya ta karkad'e sosai ta share ɗakin tas ta kwashe, sannan tayi masa shimfida ta fito daga cikin d'akin taje tayi alwala ta shiga ɗaki domin gabatar da Sallah.
A ɓangaren inna laure kuwa tun lokacin da ta koma ɗaki cike da waswasin ko HALIMATU taci abincin ko bata ciba,tana cikin wannan tunanin malam ummaru ya dawo amma sam bataji shigowar sa ba,saboda ta faɗa duniyar tunani.
tana a cikin wannan halin ne hanne tayi sallama ta shigo cikin d'akin,ta sameta ta ƙura ido a waje ɗaya tana tunani,bama ta san ta shigo dakin ba.hanne taje ta tab'ata tace innar mu baba ya dawo!!ai daga ji tayi maza ta dawo daga duniyar tunani,nan take ta mi'ke tsaye,bata tsaya ta ƙarasa jin maganar da hanne take faɗa mata ba tayi maza ta fito waje.
Tana fitowa shikuma baba na shigowa,ya dawo daga masallaci kenan ta ɗago ta lalle shi tace "malam ashe kana tafe!!ai bansan yau zaka dawo ba,da ko fura ce na dama maka!!".....
Yace"hanne kenan yau Allah ya nufa na dawo, kinsan komai nufi ne na ubangiji.ina fatan na sameku lafiya!!"
Inna ta keb'e baki tace"ƙalau muke"yace Alhmdllhi"......
nan ya bar ta tsaye a wajen ta bishi da harara cikin yin ƙasa da murya tace "ai yau zanyi maganin ku, daga kai har 'yar taka da kuma waccen muna fukar matar wallahi,tayi ƙwafa ta bi bayan sa.
Lokacin da ta iso ɗakin a zaune ta same shi kan shimfid'ar sa yana waya ,bayan ya ajiye wayar sa keypad ƙirar tecno ya kai duba gare ta yace "lafiya dai ko??"
Tace........
"Hmm lafiyar ce ta kawo haka,wai babu wata taraba da kazo mana da ita ne? badai haka ka shigo mana gidan fanko da kai ba" ta ƙarasa maganar tana tab'e baki...