Sashe 53
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kayya kayya Alhaji Auwalu! ai baza'a daka ta ta taba,kasan su dama mata tunani su daban yake da namu,idan muka daka ta tasu sai a hankali,yanzu ka duba ka gani ƙanwarta fa za'a aurar nan da watanni biyu masu zuwa,kuma na tabbata da acan take da zama da tuni ta yi aure har ta yi haihuwa biyu!!"
Shiru ya yi na ɗan wani lokaci kafin ya ci gaba da cewa,
"Ina tunanin mai zai hana a haɗa auren nasu ita da ƙanwar ta ta idan har kun shirya! in yaso sai mu roƙi alfarma daga ɓangaren manemin ƙanwar ta ta a ƙara mana ko da wata biyu ne nan gaba!! ko ya kuka ce.? idan kuma baku shirya ba sai a bar shi nan da shekara biyun,amma dai na fi son ka aurar da ita tun da ƙuruciyar ta ba sai ta ƙosa ba!!"
Ai kafin ya kai ƙarshen zancen da yake yi daddyn mukhtar ya zabura tare da gyaran murya ya gyara babbar rigar sa yace...✍🏻✍🏻
Ku yi haƙuri da wannan yau waya ta babu chargi sosai.😢
Ina matuƙar godiya da addu'o'in ku a gare ni, ku ɗin na musamman ne a cikin zuciya ta, ina matuƙar alfahari da ku ƙwarai da gaske, Allah ubangiji ya saka muku da mafificin alkhairin sa ya biya muku buƙatun ku na Alkhairi.🙏🏻🙏🏻
Daga alƙalamin
FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)...✍🏻✍🏻
Share fisabilillahi.
Ga me buƙatar littafin HALIMATU tun daga farko zuwa in da aka tsaya ya tun tuɓe ni ta wannan numbern wayar👇🏻👇🏻
08162055134.
💝💞 HALIMATU💝💞
(Love, sacrifices, destiny & betrayed)
💝💞💝💞💝💞💝💞
Story & Writing
By

Ƙarƙashin jagorancin
(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)
Golden pens......✍🏻✍🏻
💝💞💝💞💝💞💝💞
A 2024 novel
💝💞💝💞💝💞💝💞
Pages____________67&68
______________gyara zaman sa ya yi tare da yin gyaran murya ya ce,
"A'a Alhaji! mukam a shirye muke ko gobe ne a ɗaura auren!"
Murmushi daddy da baba suka yi.
Gyara zama baba ya yi sannan ya ɗago ya kalle su a lokaci guda tare da cewa,
"Ni ba nida hannu a cikin wannan maganar,duk abin da uban yarinya yace shikenan,yanzu kuje ku sasan ta tsakanin ku idan ya so duk abin da kuka yanke shikenan"
Ɗago kai daddy ya yi tare da cewa,
"A'a ai ba komai,ina ga a barshi nan da wata huɗun kamar yadda ka ce ɗin"
"Toh kana ganin hakan be yi muku sauri ba! domin bana so a takura muku gaskiya!!"
"A'a malam ai babu maganar takurawa tun da shi alhaji Auwal yace a shirye suke ai ina ganin shikenan babu matsala muma ɗin a shirye muke"
Ya faɗa yana ƙara tabbatar wa.
"To ma sha Allah Alhmdllh,in sha Allahu zan sanarwa iyayen mane min ƙanwar ta ta da ƴan uwan ta, Allah ubangiji ya nuna mana lokacin da rai da lafiya ya hore mana,na bar maka komai a hannun ka Alhaji Ibrahim,duk abin da ka ga ya dace ka yi"
Gaba ɗayan su suka amsa da ameen.
Godiya suka yi masa tare da miƙewa suka yi sallama da shi ya raka su har bakin mota driver ya ja suka tafi.
Bayan tafiyar su baba ya kirawo aunty Amina suka zauna suna tattauna wa a kan yanda abubuwan za su kasan ce da kuma shirye-shiryen da ya kamata a fara yi tun yanzu,in da baba ya yanke shawarar idan bikin ya rage saura wata ɗaya hanne sai ta dawo nan ɗin da zama tun da halimatu tana gurin momy.
A ɓangaren su daddy kuwa bayan sun koma ya zayyana wa momy dukkan abin da ya faru game da tattaunawar da suka yi da baban HALIMATU,ba ƙaramin shock ta ji ba da ta ji an sa nan da wata huɗu masu zuwa za'a yi bikin, nan take hankalin ta ya tashi duk ta bi ta birki cewa daddy tana ta sumbatu a kan ita gaskiya yarinyar ta ta yi ƙarama da yawa bata isa aure ba, dole ne ta je ta samu mahaifin HALIMATU ta yi masa magana a ɗaga bikin gaskiya.
Da ƙyar da siɗin goshi daddy ya shawo kanta ta yarda,in da ya ce mata su shirya nan da wata biyu za su tafi Dubai ita da halimatu ta zaɓi dukkanin abin da take so.
Ba dan taso ba ta yadda da zancen sabo da babu yanda zata yi biyayya ce kawai ta yiwa mijin ta.
Duk wannan budurin da ake yi halimatu bata san me ake ciki ba, karatun ta kawai ta saka a gaba.
"MUKHTAR"
Shigowa cikin parlon ya yi da sallama ɗauke a bakin sa sakamakon kiran da daddy ya yi masa,zaune ya tarar da daddy da momy a kan sofa suna hira,tsugunawa ya yi har ƙasa ya gaishe su cike da tsantsar ladabi,amsawa suka yi fuskar su a sake.
Guri ya samu ya zauna a gefe tare da cewa,
"Daddy gani"
Ya faɗa yana sunkuyar da kansa ƙasa.
Ɗago kai daddy ya yi ya kalle shi tare da cewa,
"Abin da ya sa na kirawo ka dama magana ce zamu yi da kai a kan batun auren ka da halimatu"
Da sauri ya ɗago ya kalli daddy na wasu ƴan daƙiƙu sannan ya kuma mai da kansa kasa.
"Ɗazu munje har gidan mahaifin halimatun ni da Alhaji Ibrahim kamar yadda dama jiya na yi maka bayani a kan zamu je,toh Alhamdulillahi mun je mun same shi mun tattauna game da maganar auren ku,in da ya ce in dai mun shirya nan da wata huɗu masu zuwa za'a yi bikin! domin yana so ya haɗa su ita da ƙanwarta ya aurar da su lokaci guda!! idan kuma bamu shirya ba sai a yi na ƙanwar nan da wata biyu masu zuwa! dama sabo da a haɗa da halumatun ne ya ce zai roƙi iyayen manemin ƙanwar ta ta su ƙara mana wata biyu akai sabo da mu fara shiri,amma in dai bamu shirya ba karmu ta kurawa kanmu a bar shi nan da shekara biyun a yi na halimatu!!".
Da sauri MUKHTAR ya ɗago kai ya dubi daddy cikin suɓutar baki ya ce,
"A'a wallahi daddy ko yaushe aka ce za'a yi a shirye nake!!"
Kallon sa daddy ya yi cikin ɗaure fuska tare da cewa,
"To gaskiya sai dai ka yi haƙuri! domin na riga na gaya musu a bar shi nan da shekara biyun zai fi! tun da naga alamar baka shirya ba, sannan kuma ko zancen bana ji kana yi!!"
Cike da tsananin tashin hankali mukhtar ya ɗago ya kalli daddy bakin sa yana rawa kamar zai fashe da kuka yace,
"Wallahi daddy ko yanzu aka ce za'a ɗaura auren a shirye nake! dan girman Allah ka taimaka ka gaya musu wallahi na shirya"
Ya ƙarasa maganar muryar sa na rawa kamar zai fashe da kuka.
Ƙare masa kallo daddy ya yi cike da mamakin yana yin da ya shiga yanzu yanzu nan sabo da kawai an ce an bar bikin nan da shekara biyu! tab ɗi jam! wannan wanne irin so yake yiwa yarinyar nan!! abun ya matuƙar ɗaure masa kai sosai,sabo da mukhtar ba ƙaramar kunya ce da shi ba , amma yanzu a kan halimatu ya bur kice musu nan da nan kamar ya yi musu kuka.
Maganar momy ce ta katse masa tunanin da yake yi in da take cewa,
"Ikon Allah! ashe ka shirya mu bamu sani ba! ai da sai ka faɗa mana!!"
Murmushi daddy ya yi tare da cewa,
"Ai nima naga alama ɗan naki a shirye yake!"
Ya faɗa yana kallon momy fuskar sa ɗauke da murmushi.
Duban sa ya kai ga mukhtar wanda duk ya yi wani iri dashi lokaci guda kamar wani maraya ya ce,
"Kwantar da hankalin ka na yi magana an bar shi nan da wata huɗun! sabo da haka daga yau sai kaje ka fara shiri!!"
Zunɓur mukhtar ya miƙe tare da ƙarasa wa in da daddy yake zaune ya durƙusa har ƙasa tare da ɗora kan sa a kan cinyar daddy yana ta zuba masa godiya har sai da abin ya ƙara basu mamaki.
A hankali daddy ya ɗora hannun sa a kan mukhtar ɗin yana shafawa tare da cewa,
"Kar ka damu my lovely son,ai farin cikin ka shine na mu,shi yasa na dage a kan a bar shi nan da wata huɗun,sabo da na san zaka yi farin ciki sosai"
Ƙwallace ta ziraro masa a kan fuskarsa,a hankali ya saka hannun sa ya share gudun kar daddy ya gani,sabo da ya rasa ma wanne irin farin ciki zai yi,gaba ɗaya ya susu ce wani iri yake jin kan sa kamar mai shawagi a cikin sararin samaniya sabo da farin cikin da yake ciki,babu abin da yake sauke wa sai a jiyar zuciya akai-akai.
Maganar daddy ce ta dawo da shi daga cikin hayyacin sa in yake cewa,
"Baba na dan Allah ka riƙe yarin yar nan amana kaga yarinya ce ƙarama, sannan iyayen ta suna da matuƙar mutunci, Allah ubangiji ya yi muku albarka ya nuna mana lokacin da rai da lafiya"
A hankali ya amsa da ameen tare da miƙewa ya gyara zaman sa a ƙasa fuskar nan cike da farin ciki.
"Gobe idan Allah ya kaimu zamu je dubiyar kakan yaran nan tun da Allah bai nufa mun je yau ɗin ba,sai ka same ni goben da la'asar a office sai mu tafi".
"To daddy in sha Allah, Allah ya kaimu goben lafiya"
Ya faɗa yana miƙa wa tsaya tare da ficewa.
Yana fita daddy da momy suka kalli juna tare da yin murmushi,domin idan ka kalle su zaka ga tsan-tsan farin ciki a tattare da su,su kan su suna mutuƙar ƙaunar halimatun,sabo da ta kwanta musu a cikin ran su sosai,shi yasa kullum suke yiwa ɗan su addu'a Allah ya ba shi mata ta gari da za su yi alfahari da ita dukkanin su,yanzu kuwa suna hasashen Allah ya amshi addu'ar su.
***************************************************************************
"RUFAIDA"
A ɓangaren rufaida kuwa, lokacin da malam SALIHU ya zo da malamin da zai duba ta ba ƙaramin farin ciki suka yi ba da zuwan na sa, nan take suka karɓe shi hannu bibbiyu cike da girmama wa,sabo da suna ganin cewa zai yi ƙoƙari a kan samun lafiyar ƴarsu.
Ba tare da ɓata lokaci ba ya buƙaci ganin rufaidan domin ya ga ta inda zai fuskanci lamarin nata.