← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 80

Sashe 73

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

ki saka mu tafi gida dare yana yi" Ya faɗa yana tsare ta da idanunsa da suka fara chanja colour. A hankali ta miƙa hannu ta karɓa ta ɗaura gabanta yana ta dukan uku-uku, dama duk abinda take yi dauriya ce take yi,domin mai gyaran jiki ce duk ta koya mata kissa da kuma yanda zata kula da mijinta da tarai rayar shi! amma ita har ga Allah tsoron mukhtar take ji ƙarfin hali ne kawai take yi. Miƙewa yayi tsaye ya ɗau mayafinta ya yafa mata sannan ya miƙar da ita tsaye,wayar ta ya ɗauka ya riƙe mata sannan ya kama hannu ta suka fita daga cikin ɗakin zuwa ƙasa. Durƙusawa suka yi a gaban su momy da daddy suka yi musu sallama, sannan daddy ya yi musu nasiha mai ratsa jiki tare da ƙara tuna tar musu da haƙƙin auren da yake kan junansu,daga ƙarshe ya yi musu addu'a da fatan Alkhairi. Kallon mukhtar momy ta yi tare da cewa, "Tashi kaje cikin bedroom ɗina akwai wani kwali ka ɗakko ka kawo min. Miƙewa ya yi da sauri ya haura sama. Shima daddy miƙewa ya yi ya haye sama domin ya gaji zaije ya yi wanka, juyowa momy ta yi ta kalli halimatu tare da cewa, "Doughter kiyi haƙuri da mukhtar kinji ko.? Idan ya yi miki wani abun kar ki gayawa momyn ki kizo ki gayamin zan ɗauki mataki a kai ƙunci.?? Ki riƙe mijin ki da kyau ki kula da shi sosai kiyi masa ladabi da biyayya kinga auren da ya yi na farko bai ji daɗin komai ba! bai samu nutsuwa da farin ciki ba ko kaɗan! Ina riƙon ki dan Allah kiyi min alfarma ki bashi dukkan kulawa ki yi haƙuri da buƙatar sa! nasan keɗin yarinya ce baki saba ba,amma kiyi haƙuri zaki saba a hankali, mukhtar bashi da matsala ina da yaƙinin zai ruƙe ki da amana, sannan ki kula da sirrin mijinki kinji doughter.??" Gingina kai ta yi tare da share hawayen da suka zubo mata. "Allah ya yi muku albarka ya baku zuri'a ɗayyiba" Ta ƙarasa maganar tana kallon mukhtar da ya ƙaraso riƙe da kwali a hannunsa. Karɓan kwalin ta yi ta buɗe tayi mata bayanin turarukan da suke ciki na gida dana jiki da yanda zata yi amfani da su.godiya halimatu ta yi mata, sannan suka yi sallama mukhtar ya ruƙe kwalin suka tafi,ajiyar zuciya momy ta sauke tare da bin su da addu'ar fatan Alkhairi.
Chapter 73 · 0% Book details