← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 80

Sashe 58

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali take sakkowa daga up stairs ɗin kamar bata son taka ƙasa ta nufi kitchen tare da ɗaukan babban try ta a jiye a gefe,wasu set ɗin food wamers ta ɗakko guda uku masu ɗan karan kyau ta ajiye , sannan ta janyo wata ƴar babbar food wamer ta buɗe cikin ta ta ɗebi wainar shinkafar da ta soya musu ɗazu tazuba a ɗaya daga cikin food wamers ɗin nan,ɗayar kuma ta zuba papper soup na naman rago da yaji kayan haɗin a ciki,ɗakko ɗayar ta yi tare da zuba pepper chicken a cikin.
Bayan ta gama zubawa ne ta jere su a kan babban try ɗin da ta ɗakko, sannan ta kawo plates da bowls da spoons ta ɗora a kai,wani haɗaɗen glass bowl ta ɗakko ta zuba samosa a ciki ta saka murfin sa ta rufe tare da ɗorawa a kan try ɗin.

Ɗaukar try ɗin ta yi ta fito daga cikin kitchen ɗin a hankali ta nufi parlon da su mukhtar suke ciki cikin nutsuwar da ta zame mata jiki tare da yin sallama ta shiga ciki, Nura da yake kusa da mukhtar yana bashi baki ne ya ɗago ya dube ta tare da amsa mata sallamar.

A hankali ta ƙaraso in da suke zaune ta ɗora try ɗin akan center table ɗin da yake gaban su, durƙusawa ta yi a gaban su ta gaishe da su , Nura ne kawai ya amsa mata gaisuwar ta ta yana ƙare mata kallo cike da mamaki,yanzu ya gasgata maganar abokin nasa da yace idan ya rasa ta komai yana iya faruwa da shi,domin ba ƙarya yarinyar muguwar kyakkyawa ce ta haɗu ta ko ina wallahi!bugu da ƙari ga zallar yarinta da ƙuruciya a tattare da ita! haba! dole ne hankalin mukhtar ya yi mugun tashi domin yana tsoron kar ya rasa ta,idan kuma ya yi sa'a ya mallake ta wallahi zai more sosai ta ko ina!.

Ya ƙarasa zancen zucin nasa tare da mai da hankalin sa kan mukhtar da yabi halimatu da ta miƙe tsaye ta nufi dining da jajayen idanuwan sa kamar ya cinye ta ɗanya saboda mugun son da yake mata.

Zungurin sa Nura ya yi,nan take ya sauke ajiyar zuciya mai sauti tare da kallon Nuran,cikin ƙasa-ƙasa da murya Nura yace masa,
"Ka dai-dai ta nutsuwar ka mana in sha Allah zamu yi mata wayo mu shawo kanta ka ji"
Girgiza kan sa ya yi ba tare da ya yi magana ba.
Dawowa ta yi hannun ta riƙe da bottle water guda biyu da kuma babban kwalin exotic ta ajiye a gaban su, juyawa ta ƙara yi ta je ta buɗe wardrobe ɗin kusa da dining ɗin ta ɗakko glass cup guda biyu ta kawo in da suke zaune ta ajiye a kan table ɗin.

Gyaran murya Nura ya yi tare da cewa,
"Muna godiya sosai amaryar mu da hidimar da a ke yi mana,nasan ba zaki kasa sani na ba a bakin abokina ba ko.? domin na san wani lokacin idan kuna hira yana sako miki labarin Nura abokin sa!"

Ya faɗa yana kallon ta da murmushi a fuskar sa.
Murmushin ta mai kyau ta yi masa tare da buɗe baki cikin daddaɗar muryar ta ta ce,
Ƙwarai kuwa sosai yana bani labarin ka,wani lokacin ma har da saƙon gaisuwa"
Ta faɗa tana murmushi.
Murmushi Nura ya yi tare da cewa,
"Ashe da gaske yana miƙo saƙona a gurin gimbiyar ta mu! ai na zata baya faɗa miki da yau naci shi tara!!"
Dariya ta ƙyalƙyale da ita mara sauti tare da saka hannu ta ta rufe fuskar ta, mukhtar dake zaune yana kallon ta yana jin wata iriyar nutsuwa na sakko masa,ga kuma wata iriyar madarar soyayyar ta mara algus tana tsatstsafo masa daga cikin jijiyoyin jikin sa da ɓargon sa.

Cike da mamaki yake kallon yadda suke hira da nura gwanin ban sha'awa, amma shi kuma gashi duk ta mugun ɗaga masa hankali.
Sai da Nura ya bari ta saki jikin ta sosai sannan ya kirawo ta a hankali tare da kafe ta da idanunsa, ɗagowa ta yi ta kalle shi tare da amsawa,ganin kallon da yake mata babu alamar wasa ga kuma wani mugun kwarjini da ya yi mata,nan take ta yi sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da ƴan yatsun hannunta.

Gyara zama Nura ya yi da kyau tare da cewa,
"Kin san abin da ya kawo mu gidan ku yanzu.??"
Girgiza masa kanta ta yi ba tare da ta yi magana ba.
"Good" Nura ya ce tare da cewa,
"HALIMATU me ya haɗa ki da MUKHTAR ne.??"
Shiru ta yi tare da sunkuyar da kanta ƙasa idanun ta suna tara ƙwalla.
"Kin yi shiru halimatu! baki cemin komai ba,ki gayamin idan wani abun ya yi miki sai na ɗauki mataki a kai kinji!"
A hankali ta saka hannun ta ta goge ƙwallar da ta gangaro mata daga cikin idanun ta,ɗago kanta ta yi tare da cewa,
"Ni babu abin da ya yi min,kawai dai ni bana son a yi min aure yanzu! Shi yasa nace masa a bar shi zuwa nan da shekara uku ko hudu idan yaso sai a yi auren namu!! to shi kuma ya ce min a'a baza'a ɗaga ba! shi yasa nace masa na fasa auren nashi gaba ɗaya wallahi!!"

Kalmar na fasa auren da ta furta ce ta yi nasarar dukan ƙirjin mukhtar nan take jikin sa ya kama rawa kamar mazari,cikin ƙanƙanin lokaci idanunsa suka kaɗa su ka yi jajur da su kamar an watsa masa barkono a fuskar sa.
Kallon ta Nura yake yi cike da mamakin furucin ta,daga bisani ya sauke a jiyar zuciya tare da cewa,
"Me ya sa ba kya so a yi auren ku yanzu.??"
Kamar baza ta yi magana ba sai kuma can ta ce,

"Bana so na yi aure yanzu sabo da na yi ƙarama da yawa ina jin tsoro!!"
Girgiza kai Nura ya yi ya kafe ta da idanunsa tare da cewa,
"Tsoron me kike ji ne! gaya min kar ki ji tsoron faɗa min kin ji??"
Ya yi maganar cike da lallashi.
Cikin san yin murya cike da yarin ta ta ce,
"Ina jin tsoron a yi min aure yanzu in zo gurin haihuwa na mutu! kaga mama na ma kafin ta haifeni ta yi ta rashin lafiya, tana haihuwa ta bata daɗe ba ta rasu! shi yasa nima nake jin tsoro!!"

Ta ƙaras maganar tana fashewa da kuka mai cin rai.
Ajiyar zuciya Nura ya sake sauke wa a karo na wajen uku yana kallon ta cike da zallar yarin ta da ƙuruciyar da ke tattare da ita,gaba ɗaya mukhtar ya rasa sukuni saboda kukan ta ba ƙaramin ɗaga masa hankali yake yi ba.

Cike da lallashi Nura ya ce mata,
"Yi shiru dena kuka kin ji, Allah ubangiji ya jiƙan mama da rahama ya sa ta huta kin ji!"
Girgiza kanta ta yi tare da cewa "ameen"
"Ɗago kan ki ki kalle ni mu yi magana kin ji!"
Ɗagowa ta yi ta ɗora idanun ta akan nasa, gyaran murya Nura ya kuma yi tare da cewa,
"Kin ganni nan lokacin da na auri mata ta shekarar ta sha bakwai,tana gama secondary school muka yi aure,ni na saka ta a University har ta gama,yanzu haka result ɗin ta yana gurina na ajiye mata shi sabo da wata rana, watan mu tara cif cif da yin aure ta haihu,yanzu haka muna da yara guda huɗu! biyu maza biyu mata,kuma babu abin da ya same ta,ita ma mama da kika ga ta rasu lokacin ta ne ya yi,ko da haihuwa ko babu haihuwa idan lokacin mutum ya yi dole ne ya amsa kiran ubangijin sa, Sabo da haka ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru sai alkhairi kin ji??"

Girgiza masa kanta ta yi domin maganar sa tayi matuƙar tasiri a cikin zuciyar ta.
Murmushi ya yi mata tare da ci gaba da cewa,
"Kuma kinga mahaifin ki shi ne da kansa ya tsai da lokacin auren na ku,kinga idan muka ce masa mun ɗaga ba zai ji daɗi ba saboda ya ce so yake ya haɗa bikin ku ke da ƙanwar ki HANNE domin ku kaɗai ne ya rage masa bai aurar ba,yana so ya ga auren ku kafin ya mutu!!"

Da sauri ta ɗago ta kalle shi jin har da HANNE za a haɗa a yi musu aure, girgiza mata kansa ya yi tare da cewa,
"Ƙwarai kuwa da gaske ku biyu ke da HANNE za a aurar da ku duk lokaci ɗaya!domin su dangin mijin hannen ma wata biyu suka saka masu zuwa,baba ne ya nemi alfarma daga wajen su ya ce musu su ƙara masa wata biyu domin yana so ya haɗa bikin ku gaba ɗaya!!"
Jikin ta ne ya yi wani irin sanyi kamar wadda zazzaɓi ke shirin kamawa,nan take ta ji duk wata fargaba ta kau a cikin zuciyar ta.
Maganar Nura ce ta dawo da ita cikin hankalin ta in da yake cewa,
"To yanzu gayamin kin haƙura??"
Ya faɗa yana tsare da idanun sa masu kaifi.

Hannu ta ta ɗora a kan fuskar ta ta jin jina masa kanta cike da kunya,murmushi ya yi tare da cewa,
"Alhmdllh,amma fa sai na ci tarar ki tunda kika ɗagawa abokina hankali kika hana shi sukuni har kin sa zazzaɓi mai zafi ya kama shi!"
Da sauri ta kai kallon ta kan mukhtar karon farko tun zuwan su cikin gidan,wani irin rama taga ya yi idanunsa sun yi zuru-zuru kamar wanda ya yi sati kwance.
Gaban ta ne ya faɗi lokacin da suka haɗa idanu da shi,nan take ta ji wani irin tausayin sa ya kamata.

Maganar Nura suka jiyo yana cewa,
"Ni dai abani abinci naci domin yunwa nake ji!!"
Cikin sauri ta tashi taje ta tsuguna a gaban center table ɗin ta shiga saving ɗin su,sai da ta zuzzubawa kowane su kalolin abinci da yake gurin sannan ta tashi ta koma wajen zaman ta.
Tashi Nura ya yi ya kwashi abincin sa ya wuce kan dining table domin ya basu waje ya zauna ya fara ci,domin babu ƙarya yunwa yake ji.
Chapter 58 · 0% Book details