← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 80

Sashe 33

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuwa yanzu maganar auren su taje gaban iyayen su,kuma dukkanin su sun yi amanna da al'amarin,yanzu haka inna laure ake jira ta ƙara jin sauƙin jikin ta ayi auren su.

A kullum INNA LAURE tana zuba ido akan dawowar baba,sai dai kuma shiru malam har yanzu babu wani labari kuma babu waya,idan ma an kirawo wayar sa ba samu ake yi ba, wannan lamari yana matuƙar ɗagawa inna laure hankali.

WAIWAYE

Lokacin da inna laure ta yiwa malam ummaru mahaifin HALIMATU tofin ala tsine ta tara masa jama'a,ji yayi gaba ɗaya duniyar ta yi masa zafi,me yayi wa laure da ta zaɓi yi masa irin wannan rashin mutun cin da tozarcin a idon mutane.

Wannan dalilin ne yasa ya tattara duk wani abu da ya san nashi ne ya zuba a bakko,bai bar gidan nan ba sai da ya rubuta mata saki uku ya linke takardar ya ajiye mata a kan window ɗin ɗakin.

Domin baya son wata alaƙa ta aura tayya ta ƙara shiga tsakanin su.

Cikin ɓacin rai ya bar garin ya koma inda ya fito ya ci-gaba da rayuwa,bayan kwana biyu ne ya zo garin ba tare da sanin inna laure ba ya sai da babbar gonar sa wadda ya gada a wajen mahaifin sa.

Sannan ya ƙara komawa garin kano kasuwar dawanau ya ci-gaba da kasuwancin kayan masarufi yana juya kuɗin sa,

Cikin hukuncin ubangiji Allah ya albarkaci sana'ar ta sa in da dukiyar sa ta ninku sosai da sosai,domin yanzu yana tura kayan abinci gari gari.

Wannan dalilin ne yasa ya sayi fili babba a cikin garin Kano ya gina gidan sa mai kyau da tsari, cikin haka Allah ya haɗa shi da wata bazawara mai suna Amina da mijin ta ya rasu ya bar mata yara guda biyu, ya nemi auren ta.

Bai wani sha wahala ba iyayen ta suka bashi ita,domin sun yaba da kyawawan halayen sa,cikin ikon Allah aka ɗaura musu aure ta tare a sabon gidan da ya gina,sannan kuma ya ɗakko marayun yaran ta ya ruƙe mata su tamkar shi ya haife su.

Amina tana da matuƙar kirki,ga ladabi ga biyayya, wannan dalilin ne yasa yaji daɗin zama da ita hankalin sa ya kwanta sosai har wata ƙiba ya yi ba shi da wata damuwa,domin ya damƙa HALIMATU a hannun da ya san baza ta taɓa yin kukan maraici ba, domin tamkar a hannun mahaifiyar ta take.

Abu ɗaya ne yake damun sa rashin jin muryar su sakamakon faɗuwa da wayar sa tayi,gashi yanzu ya chanja layi bashi da number su,kuma gidan da yasan su a da yanzu ba shine suke ciki ba.

Amma in sha Allahu zai cigaba da neman su tun da suna gari ɗaya,yasan wata rana za su haɗu in sha Allah.

Gashi yanzu Allah ya albarkace su da haihuwar ɗa namiji,dama bashi da ɗa namiji, in da aka raɗawa yaron suna Ahmad.

An yi shagali sosai, domin baba yana da rufin asiri sosai yanzu,ya riga da ya manta da wata inna laure,sai dai yana tuna ƴaƴansa a koda yaushe, wannan dalilin ne ma yasa yake son yaje garin domin ganin ƴaƴansa,duk da cewa yana da labarin abubuwan da suke faruwa a gurin wani maƙocin sa da suke yin waya.

Wannan kenan...........

"BUBA"

Lokacin da mutanan sa suka bazama cikin gari neman hansai da ƴarta Safara'u.

Haka suka dinga neman su saƙo da lungu amma Allah bai sa sun gansu ba.

Wannan dalilin ne yasa suka koma suka shaida wa BUBA cewa basu gansu ba, hankalin BUBA ya tashi sosai da jin wannan labarin,domin ya ƙwallafa ransa a kan Safara'u, ba ƙaramin buri yaci a kan ta ba,ya kuma ɗaukar wa kan sa alƙawarin duk lokacin da ya haɗu da hansai sai ya karai raya ta.

"HANSAI"

Lokacin da su HANSAI suka gudu daga cikin ƙauyen haɗeja basu zame ko ina ba sai tasha,in da ta nemi motar kano suka hau aka wuce da su cikin garin Kano.

Bata baro garin haɗeja ba sai da ta siyar da gidan ta da take ciki da gona,dama baban Safara'u ya rasu, kuma ita kaɗai ce ƴarsa.

Lokacin da aka raba gadon aka basu gidan da suke ciki da gona guda ɗaya,sauran kuma aka rabawa iyaye da ƴan uwan sa.

Kuɗin gidan da gonar ta ƙulle su a ƙugun ta suka gudu daga garin,bayan sun zo garin Kano ne suka sauka a wata unguwa da ake kira Gwamna ja.

In da HANSAI ta samu gida ɗan madai dai ci mai ɗaki uku ta siya,ragowar kuɗin kuma ta ja jarin sai da kunu da ƙosai a ƙofar gidan,da daddare kuma suna yin awara da dankali soyayye.

Da wannan sana'ar suke samu suke ci su sha kuma suyi larurorin rayuwa,har makaranta ta saka Safara'u ta boko da islamiyya, wannan dalilin ne yasa ta samu nutsuwa,duk da cewar tana kewar ƴan uwan ta da ta baro a ƙauye.

To amma bata da yadda za ta yi,tasan muddin ta koma garin nan kila sai BUBA ya kusa kashe ta,shiyasa duk lokacin da ta tuna dangin ta da ta baro silar BUBA a ranar wuni take yi tana tsine wa BUBA,domin a cewar ta shi ne silar rabuwar ta da dangin ta.

"HALIMATU"

Bayan sun gama waya da mukhtar ne ta miƙe ta je ta kaiwa MOMY wayar ta,wanka ta shiga tare da ɗauro alwala tazo ta saka night dress tayi addu'a ta kwanta.

Washe gari tunda asuba ta tashi ta yi salla tare da yin azkar,bayan ta idar ta sakko ƙasa ta shiga cikin kitchen ta fara ƙoƙarin haɗa break fast.

Sai da ta kusan gamawa sannan baba ladi ta zo suka ci gaba da yin aikin,ƙarfe takwas suka gama yin komai suka jere a kan dining Baba ladi kuma ta ɗauki nasu ta wuce ɓangarensu,ita kuma ta yaye up stairs domin ta yi wanka ta yi shirin zuwa makaranta.

Ƙarfe tara ta sakko ta yi break fast a gurguje Sabo da farouq da yake zaune yana jiran ta domin ya kaita makaranta.

Sallama ta yi wa MOMY Sannan suka kama hanya suka fice daga gidan.

Wannan kenan...

"Ina matuƙar godiya da addu'o'in ku a gare ni, ku ɗin na musamman ne kuma ina alfahari da samun Ku, Allah ubangiji ya saka muku da Alkhairin sa ya biya muku buƙatun ku na Alkhairi.......

Daga alƙalamin FATIMA BINTU ABDULLAHI (UMMU AYSHA)........✍🏻

Share fisabilillahi......

08162055134..

💝💞HALIMATU💝💞

(Love, sacrifices, destiny & betrayed)

💝💞💝💞💝💞💝💞

Story & Writing

By

FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)

Ƙarƙashin jagorancin

(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)

Golden pens...........✍🏻

💝💞💝💞💝💞💝💞

A 2024 novel

💝💞💝💞💝💞💝💞

Pages ___________41&42

"ALHAJI USAMA"

A ɓangaren ALHAJI USAMA kuwa, lokacin da ya ƙaraso gida a zaune ya tadda umma tayi nisa wajen tuna Ni.

Ta ƙulla wannan ta kwan ce wancan.

Tana tsaka da tunanin ne ta jiyo sallamar Alhaji USAMA,miƙewa ta yi tsaye tare da cewa:

"Sannu da zuwa Alhaji"
"Yauwa sannu! Ya gida!"
"Hmmm gida gashi nan babu wani daɗi ko kaɗan! Allah ya sa an dace"

"To muna dai saka ran dacewar"

Ya faɗa tare da neman guri ya zauna a kan sofa,kallon sa ya mayar kan hajiya Hauwa mahaifiyar RUFAIDA tare da cewa:

"Daga wajen ALHAJI Garba nake yanzu! Mun yi magana ne sannan na yi masa bayanin komai,nan dai ya kwashe yadda suka yi ya gaya wa umma.

Ɗagowa ya yi ya dube ta tare da cewa: "yanzu mene ne abin yi?"

Numfashi ta sauke tare da cewa:
"Wannan ba matsala bace ba, tun da rufaida tana da sarƙoƙi kaga sai a ɗauki guda ɗaya a siyar a yi abin da ya dace! domin biyan buƙata ai ya fi dogon buri!!"

"Haka ne! Nima na yi wannan tunanin! hakan ya dace a yi! "to yanzu yaushe ya kamata mu yi wannan tafiyar??

"Kawai ka sanar da shi cewa a shirye muke! Ya saka muku ranar da zaku tafi,idan ya so kafin lokacin sai mu ƙara sa shirya wa"

"Gobe zan shiga kasuwa na siyar da sarƙar,tun da kaga yanzu yamma ta riga da ta yi dole mu bari zuwa goben".

Waya ya ɗakko ya buga wa ALHAJI Garba in da yake sanar da shi yadda suka yi da hajiya Hauwa,daga ɗaya ɓangaren yace masa ya shirya gobe da ƙarfe sha biyu na rana za su tafi,amsa masa yayi da to.

Washe gari da misalin ƙarfe tara na safe umma ta ɗauki sarƙa ta tafi kasuwa domin ta siyar da ita,bata wani sha wahalar siyar wa ba sakamakon akwai recipt ɗin sarƙar,domin cikin irin waɗan da MUKHTAR yake kawo mata ne daga kamfanin su.

Kusan million biyu da wani abu aka sai da sarƙar,ba tare da ɓata lokaci ba umma ta kamo hanyar dawo wa gida,koda ta ƙaraso ta tadda ALHAJI USAMA da abokin sa ALHAJI Garba a ƙofar gidan suna jiran ta.

Gaisawa suka yi da ALHAJI Garba in da suka ƙara tattau nawa a kan yanda tafiyar zata kasance musu,ALHAJI Garba ya ba da shawarar su ruƙe kamar dubu ɗari biyar a hannun su Sabo da kuɗin mota da abincin su da kuma abin da za su kai wa boka.

Hakan kuwa aka yi, in da ALHAJI USAMA ya bi hajiya Hauwa cikin gidan ya karɓi kuɗin suka yi sallama da iyalin sa Hajiya Hauwa ta yi musu fatan nasara.

Fitowa yayi ya iske ALHAJI Garba yana jiran sa,ba tare da ɓata lokaci ba suka hau adaidaita sahu ya kai su tashar sabon Gari,daga nan suka yanki ticket ɗin motar da zata kai su garin ENUGU.

Fita suka yi suka je super market mafi kusa da tashar suka sayi biscuits da ruwa da lemo,sannan suka biya restaurant suka sa a kayi musu packaging ɗin abin cin da za su ci a hanya.

Kasan cewar motar sai ƙarfe shida na yamma za ta tashi,shi yasa suka samu space ɗin kimtsa wa sosai,ƙarfe shida dai dai passingers suka fara shiga cikin lexserious ɗin,ƙarfe bakwai mota ta tashi suka kama hanyar zuwa garin ENUGU, to! Sai dai mu ce Allah ya kyau ta.

"MALAM UMMARU"

A ɓangaren malam ummaru kuwa, shirye shirye yake yi domin zuwa garin HAƊEJA ya gano gida da kuma yaran sa, shirya wa suka yi shida matar sa AMINA suka shiga kasuwa suka yi siyayya mai yawa sosai,kowacce a cikin yaran sa sai da ya yi mata siyayya.
Chapter 33 · 0% Book details