← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 80

Sashe 54

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin ɗakin da take kwance suka yi masa jagora gaba ɗayan su har malam salihu,kwance suka iske ta yan da suka barta tun ɗazu haka suka zo suka same ta tana ta rarraba idanun ta.
Idanun ta ta ɗago ta ƙurawa malam jazuli ido kamar me nazarin wani abu,shima malam ɗin ita yake kallo yana girgiza kansa a hankali.

Kallon sa ya mayar gurin su alhaji usama tare da cewa,
"A bani ruwa na yi alwala,kuma kowa yaje ya yi alwala!"
To suka ce tare da ficewa daga ɗakin gaba ɗayan su, alwala kowannen su ya ɗaura sannan suka ɗunguma gaba ɗayan su suka dawo cikin ɗakin kowa ya samu waje ya zauna.
Ƙur'ani malam ya ciro daga cikin jakar da ke riƙe a hannun sa ya yi bismillah ya fara karan tawa cikin babban sauti,gaba ɗaya kowa ya nutsu yana sauraron karatun damalam yake yi,sai da ya yi kimanin izu biyu! amma babu alamun rufaida za ta yi magana.

Gaba ɗaya zufa ce ta wanke wa malam fuska,hatta da rawanin sa sai da ya warware sabo da tsabar karatun da yake yi.chanja a kalar karatun ya yi tare da jero zafafan a yoyin Alƙur'ani mai girma, nan take rufaida ta kurma wani irin ihu mai firgitarwa wanda ya yi silar miƙewar hajiya Hauwa a zabure tana shirin rugawa a guje,da sauri Aminu ya kamo ta ya ruƙe ta sosai gudun kar a samu matsala.
Wata iriyar dariya mai firgitarwa rufaida ta kece da ita bayan ta gama ihun ta dubi sashin da malam jazuli yake zaune karon farko tun da larurar ta same ta bata yi magana ba sai yanzu tace,
"Malam jazuli karka jefa kan ka da zuri'ar ka cikin tashin hankali domin bazamu taɓa barin jikin ta ba, alƙawari ne muka ɗauka kuma mu bama saɓa alƙawari,sabo da haka ka ƙyale mu in da ka gan mu kawai"

Ta faɗa cike da wata iriyar murya mara daɗin sauraro.
Kuka hajiya Hauwa ta fashe da shi sabo da tsabar tsorata da ta yi,nan take ta saki fitsari nan in da take zaune a kusa da Aminu sabo da tsabar firgita da ruɗewar da ta yi.
Malam jazuli bai saurari maganar da aljanun suka ce masa ba,nan take ya buɗe jakar sa ya ɗakko wata gora da ruwan tofi yake ciki ya buɗe ya shiga yayya fawa rufaida a jikin ta.
Duk in da ya yayyafa sai aljanun su goce daga gurin,sabo da shi aljani babu in da baya yawo a cikin jikin ɗan adam. haka suka dinga yi suna wahalar da ita,bayan ya gama ne ya koma ya ci gaba da yin karatun.

Yana cikin karatun ne ya ji ta ƙara fashewa da wata iriyar dariya mai kama da kukan jaki,ta dube shi idon ta jawur karmar garwashin wuta tace,
"Wato baka jin magana ko! toh bari mu fita mu baka guri idan ka gama karatun naka zamu dawo tun da so kake ka ƙona mu,duk abin da ka gani ka yi kuka da kanka!!"
"Hhhhhhhhhhh"

Ta faɗa tare da yin atishawa,nan take ta langaɓe kan ta alamar bacci ya ɗauke ta.
Kallon su malam jazuli ya yi tare da sauke ajiyar zuciya yace,
"Gaskiya wannan babban al'amari ne ba ƙarami ba,idan muka yi duba da yadda take wannan dariyar abin ya girmama sosai! dole ne na yiwa malami na magana a kan wannan al'amarin ko zai iya yin wani abu akai!!"

Ya faɗa yana ciro man habbatussauda da man zaitun da man tafarnuwa ya miƙawa Alhaji USAMA yace a dinga shafa mata shi a jikin ta, sannan ya kuma ɗakko ruwan addu'a yace a dinga shafa mata shi a jikin ta gaba ɗaya tare da bata tana sha.

Yana gama faɗa ya miƙe tsaye tare da ficewa daga ɗakin malam salihu ya rufa masa baya,ko da alhaji usama ya dogaro sandar sa ya fito har sun fice daga cikin gidan.

Wannan kenan....✍🏻✍🏻

Ina matuƙar godiya da addu'o'in ku a gare ni tare da fatan Alkhairi,ku ɗin na musamman ne a cikin zuciya ta, ina matuƙar alfahari da ku ƙwarai da gaske, Allah ubangiji ya saka muku da mafificin alkhairin sa.🙏🏻🙏🏻🥰

Daga alƙalamin
FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA)...✍🏻✍🏻

Share fisabilillahi.

Ga waɗanda masu buƙatar littafin tun daga farko zuwa inda aka tsaya su tun tuɓeni ta wannan numbern wayar👇🏻👇🏻

08162055134.

💝💞HALIMATU💞

(Love, sacrifices, destiny & betrayed)

💝💞💝💞💝💞💝💞

Story & Writing

By

FATIMA BINTU ABDULLAHI(UMMU AYSHA).....✍🏻✍🏻

Ƙarƙashin jagorancin

(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)

Golden pens.......✍🏻✍🏻

💝💞💝💞💝💞💝💞

A 2024 novel

💝💞💝💞💝💞💝💞

Pages ___________69&70

"MALAM JAZULI"

A ɓangaren su malam jazuli kuwa, lokacin da suka fita shi da malam salihu basu tsaya a ko ina ba sai bakin get ɗin gidan,a gaggauce malam jazuli ya yi masa sallama ya juya tare da hawa mashin ɗin sa ya tafi,domin gaba ɗaya hankalin sa ya koma gida yana jin tsoron kar shaiɗanun nan su taɓa masa iyalin sa,domin ya fuskanci kwata-kwata babu Allah a cikin ran su.
Cike da fargaba ya nufi gidan nasa,ko da ya ƙarasa gidan a tsakar gida ya taradda matarsa da yaran sa guda huɗu suna zaune a kan babbar tabarma suna bitar karatun su, suna ganin sa suka taso da gudu suka rungume shi cike da murnar ganin sa suna yi masa sannu da zuwa.

Rungume su ya yi tare da shafa kan su ya sauke wata iriyar ajiyar zuciya,guri ya samu ya zauna a kan tabarmar tare da umar tar yaran da suje su ci gaba da karatun su.

Ganin haka ne ya sa matarsa ta matso kusa da shi tare da cewa,
"Barka da zuwa malam! da fatan ka dawo gida lafiya!"
"Lafiya ƙalau hajara ya yaran.?"
"Yara kowa yana lafiya"
"To ma sha Allah Alhmdllh"
Daga haka ta fara jan shi da hira kaɗan- kaɗan duk da ta fuskanci a kwai damuwa a tattare da shi.
Wayar sa ya ɗakko a cikin aljihun sa ya yi dialling numbern malamin sa,bayan ya yi picking call ɗin ne suka gaisa sannan ya gabatar masa da maganar rashin lafiyar RUFAIDA! tare da yi masa bayani akan dukkan Abin da ya gani dan gane da ciwon nata.

Ajiyar zuciya malam muttaƙa ya sauke tare da cewa,
"Ka jirawo ni nan da kwana biyu zan dawo, domin na yi tafiya bana gari yanzu haka! amma idan na dawo in sha Allahu zamu san abinda za muyi!"
Amsawa ya yi da toh tare da yin sallama da junan su.

"MUKHTAR"

A ɓangaren mukhtar kuwa ba ƙaramin farin ciki yake ciki ba da wannan lokacin da aka saka na auren su,ji yake ya fi kowa farin ciki da zumuɗi game wannan al'amarin.
Zaune yake a cikin karafaren office ɗin sa yana duba wasu files, kallo ɗaya zaka yi masa ka san yana cikin nishaɗi,rufe files ɗin ya yi tare da janyo wayar da take gaban sa ya dadanna ya kara a kunnen sa,daga ɗaya ɓangaren aka ɗauka suka gaisa ya ce, "ka same ni a office yanzun nan!"
Ya faɗa tare da ajiye wayar.
Kimanin minti biyar tsakani Nura ya yi nocking ƙofar tare da yin sallama ya shigo cikin office ɗin,zama ya yi a ɗaya daga cikin kujerun da aka ƙawata office ɗin da su, tasowa mukhtar ya yi yazo kusa da shi ya zauna fuskarsa cike da fara'a.

Baki sake nura ya kalleshi tare da cewa,
"Aboki na ga dukkan alamu kana cikin tsantsar farin ciki wanda ka kasa ɓoyewa har sai da fuskar ka ta nuna, dama tunda na ga ka kirawo ni na san akwai babbar magana! bani labari in ji meye silar wannan farin cikin da kake ciki.?".
Ya ƙarasa maganar yana kallon mukhtar cike da mamaki.
"Hmm kai dai bari Nura! ai dole ne in yi farin ciki Sabo da burina ya kusa cika in sha Allah!"
"Tooo ina sauraren ka wanne buri ne wannan!!"
"Hmmm kai dai bari Nura! yanzu nan maganar da nake yi faɗa maka auren mu da halimatu saura wata huɗu masu zuwa! kaga kuwa dole in yi farin ciki!!"
Da tsantsar mamaki a kan fuskar Nura yake kallon mukhtar tare da cewa,
"Wai dan Allah da gaske kake yi abokina!"
"Hmmm nura kenan! ai kasan bana yi maka irin wannan wasan! shi yasa ban yi ƙasa a gwiwa ba na gaya maka wannan abin farin cikin! Sabo da haka ka fara shiri tun yanzu wallahi!!"

"Alhamdulillah! Alhmdllh! Alhmdllh!"
Nura ya ɗaga hannu yana faɗi fuskar sa cike da murmushi.
"Gaskiya na yi matuƙar farin ciki aboki na, Allah ubangiji ya nuna mana wannan lokacin da ran mu da lafiyar mu, Allah ya tabbatar da alkhairi a cikin auren nan da zaku yi! domin ina ji a jiki na zaka ji daɗin zama da yarinyar nan sosai da sosai! duk da cewa dai ban taɓa ganin ta ba,amma dai ina kyauta ta mata zato in sha Allahu!!"
Murmushi mai ƙayatarwa mukhtar ya yi tare da cewa,
"Ameen Ameen aboki na, ka shirya duk lokacin da zan koma wajen ta to tare da kai zamu je ka ganta ku gaisa!"
"Toh Allah ya kaimu lokacin,abin da ma ko a hoto baka taɓa nuna min ita ba! ai kawai na ma yi fushi!"
"Haba dai babban aminin ango! ka rufamin asiri! idan ka yi fushi da ni ya zan yi da rai na, wallahi bani da hoton halimatu a waya ta shi yasa ban taɓa nuna maka ba,sai ranar da na dawo ne ma da muka je gidan su har da su daddy da momy shine ta haɗa min ɗan ƙaramin party na murnar dawowa ta gida lafiya,to shi ne fa meena ta yi mana hotuna nida halimatu a ranar,bari ma ka gani!!"
Chapter 54 · 0% Book details