Sashe 10
Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƙarfe huɗu na asuba ya tashi,ya shiga toilet yayi wanka da alwala.yana fitowa jallabiya kawai ya zura ya ɗan fesa turare, dadduma ya ɗakko ya shimfida ya kabbarta sallah.bayan yayi nafila ya zauna yana ta addu'a yana kai kukan sa ga ubangiji sa.
Yana nan zaune aka kirawo sallar asuba, mi'kewa yayi tare da ninke sallayar ya fito daga cikin d'akin ya nufi d'akin rufaida.lokacin da ya shiga dakin kwance ya same ta tayi d'ai-d'ai a saman gadon,ko fitilar d'akin bata kashe ba haka ta kwana da abarta.
Ƙarasowa yayi bakin gadon tare da miƙa hannun sa ya bubbuga fillow ɗin da ta ɗora kanta tare da kiran sunan ta.cikin bacci taji ana tashin ta, nan take ta buɗe idanun ta tare da kallon shi,domin tasan babu mai yi mata haka sai shi.had'e fuskarta tayi tare da kallon shi tace"meye haka ina cikin bacci na zakazo kawani tashe ni"
Ya dube ta fuskar sa babu alamun wasa yace mata"malama tashi kije kiyi alwala kiyi raka'atanul fajir kafin a tayar da sallar asuba,kuma karki sake wallahi na dawo daga masallaci na tarar dake baki tashi kinyi sallah ba,idan ba haka ba sai nayi mummunan saɓa miki".bakinta ta zumburo tare da tashi daga kan gadon tayi hanyar toilet ɗin fuuuuuuu kamar mai shirin tashi sama.
Sai da yaga shigewar ta sannan ya fito daga cikin d'akin ya sakko ƙasa ya fita daga cikin gidan ya nufi masallaci.
Bata wani daɗe a toilet ɗin ba ko cikakkiyar alwala batayi ba ta fito daga ciki,ko sallaya bata shimfid'a ba a haka ta saka hijabi ta burbura sallar ta mi'ke.gadon takuma komawa ta haye tayi kwanciyar ta.d'akin yayi wani iri babu gyara amma ko ajinta babu abinda ya dameta.
Sai da gari yayi haske sosai sannan ya dawo daga masallaci.yana shigowa ya tarar da mai aikin su tana jere abinci a dining table. gaida shi tayi ya amsa sama sama tare da hayewa sama, ɗakin yaran ya nufa ya tashe su daga bacci sannan yayi musu wanka,brush ya mi'ka wa sahal ita kuma amal da kansa yayi mata, sannan ya shirya su cikin uniform ɗinsu na school.
Fitowa yayi daga d'akin bayan yace suyi sallah su jira shi a ƙasa.dakin sa ya shiga ya ƙara yin wanka ya shirya cikin suit royal blue,ba ƙaramin kyau kayan suka yi masa ba,muktar akwai iya ɗaukar wanka sabo da idan ka gan shi baza kace yayi aure har da yara biyu ba.muktar ba fari bane ba chocolate colour ne skin ɗin shi tana da matuƙar kyau da ɗaukar hankalin mutane.
Yana da tsaho kuma yana da faɗi,yana da murd'ad'd'en jiki da faɗin ƙirji,sannan yana da doguwar fuska da manyan idanu masu ɗauke da cikakken gashin gira.yana da madai dai cin hancin sa da ya ƙara ƙawata fuskar sa.sannan yana da small mouth pink colour, ga kuma wani lallausan saje da ya ƙara ƙawata kyakkyawar fuskar sa .ma sha Allah,muktar yana da kyau daidai gwar gwado.
Bayan ya gama shiryawa ne ya fesa tsadadden turaren sa mai matuƙar ƙamshi tare da ɗaura agogon rolex a hannun sa.sauri yake yi sabo da yana da mittig ɗin da zasu yi a company ɗin sa, sannan kuma akwai baƙin da suke son ganin sa.12 pm kuma zai shiga b.u.k sabo da yana da classes.
Koda ya sakko ƙasa ya tarar da yaran sa suna jiran sa,be tsaya b'ata lokaci ba ya kama hannun su suka nufi dining table.indomie aka dafawa yaran,sai kuma fried irrish and egg da ya gani a cikin warmer.ba tare da b'ata lokaci ba ya saving ɗin yaran, shi kuma ya haɗa tea a cup tare da zuba irrish da kwai yai bismillah ya fara ci.
Ko kaɗan baya jin daɗin abincin,kawai dai yana ci dan babu yadda zai yi,idan ma ya tilasta rufaida ta dafa masa ma ba iya ci yake ba,har gwara ma na mai aikin nasu.shiyasa yake hak'uri yake ci kawai.suna tsaka da yin break fast ɗin ne suka jiyo alamun ana sakkowa daga sama.bai d'ago ba sabo da yasan ko wacece.ga dukkan alamu yunwa ce ta .tasheta
Kujera ta jawo ta zauna a kusa da shi tace"ashe baka tafi ba?"ta faɗa tana zuba irrish cikin plate,ya d'ago ya zuba mata manyan idanunsa yana ƙare mata kallo daga sama har ƙasa, kwata kwata babu alamun tayi wanka, kayan jiya ne a jikinta da su kuma ta kwana , yanzun ma dai sune a jikin na ta. Kansa kawai ya girgiza ya ci-gaba da cin abincin sa
Suna gamawa school bus ɗin yaran na ƙarasowa, hannun su ya kama suka fito suna d'agawa momyn tasu hannu, ita ma hannun ta d'aga musu alamar bye bye.bayan ya raka su ya dawo kai tsaye sama ya hau zuwa d'akinsa ya ɗakko briefcase ɗinsa ya sakko ƙasa.zaune ya same ta tana charting ta ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya.gefe guda kuma mai aiki ce take ta faman share share da goge goge.
Ya tako har zuwa gaban ta ya tsaya,cikin tsare gida da bada umarni yace mata "zan fita ki tabbatar kin gyara min d'aki na, sannan ki wanke min toilet dina,karki bari na dawo na tarar baki gyara ba ranki ne zai ɓaci.kuma kin dai san bana buƙatar mai aiki ta shigar min d'aki, Sabo da haka ke nake so ki gyara min" ya ƙarasa maganar tare da ficewa daga parlon ba tare da ya tsaya jin abin da zata ce masa ba.
HALIMATU
A ɓangaren su HALIMATU kuwa bayan sun yi sallar asuba suka sakko ƙasa ita da momy,ko da suka sakko sun iske uwani tana ta aikin share share da goge goge.uwani tana ganin su ta dur'kusa ta gaida momy,momy ta amsa tare da cewa "kun tashi lafiya ya aiki??" uwani tace "lafiya k'alau Hajiya". gaishe da uwani HALIMATU tayi tare da bin bayan momy suka shiga kitchen.
Koda suka shiga sun iske baba ladi tana ta faman feraye doya, nan suka gaisa suka ci-gaba da aikinsu.kasan cewar kitchen ɗin akwai time table na abin da ake girkawa shi yasa koda suka zo baba ladi ta fara rage aikin.cikin ƙan'kanin lokaci suka kammala aikin su.baba ladi da HALIMATU ne suka gyara kitchen ɗin tare da jere abinci a dining table.
Bayan sun gama ne baba ladi ta ɗauki nasu ta wuce ita kuma HALIMATU ta haye sama ta shiga d'akin yusra, ba tare da b'ata lokaci ba ta tashe ta tayi mata wanka tare da yi mata brush.cikin sauri ta shirya ta cikin uniform ɗin school ɗin su.kama hannun ta tayi suka sakko ƙasa,nan suka iske samarin gidan cikin shirin zuwa office .gaishe su HALIMATU tayi ita da auta,koda tazo kan faruq ta tsuguna har ƙasa ta gaishe shi.
Hakan da tayi ba ƙaramin basu dariya yayi ba,shi kuwa gogan ji yayi kansa ya ƙara girma sosai shi a dole yayanta.ba tare da b'ata lokaci ba suka d'un guma gaba ɗayan su zuwa kan dining table, ɗaya bayan ɗaya HALIMATU tayi saving ɗinsu.bayan sun gama ne momy ta dubi sadiq tace"ya maganar da muka yi da kai??" yace "momy na karb'o form ɗin harma na riga na cike,yanzu passport ɗin ta za'a bayar a saka ajin form ɗin "
Tace "to ma sha Allah, gaskiya naji daɗi sosai,maganar hoto ba matsala bace ba idan muka fita anjima sai ayi mata".yace okay tom shikenan, bara mu wuce ofice".daga haka suka tashi suka yi musu sallama suka fita,shima farouq mi'kewa yayi ya ɗauki lunch box ɗin auta ya kama hannun ta suka fita,dama shine yake kaita school,yace",momy bari naje na kai auta daga nan zan d'anje unguwa" .
Momy tace "okay tom shikenan sai ka dawo". daga haka suka fice daga gidan.bayan fitar sune momy ta kalli HALIMATU tace "daughter tashi muje muyi wanka mu shirya mu fita da wuri,kinga yau dadyn ku zai dawo gwara mu fita muje mu dawo da wuri". HALIMATU tace "to".daga haka suka tashi suka wuce sama kowa ya nufi d'akin sa.
Cikin shigar Black abaya ƙirar dubai momy ta fito,tayi rolling da mayafin abayar tana baza ƙamshi,shigar tayi mata mutuƙar kyau abin ka da farar mace.nan ta iske HALIMATU zaune a parlon ita ma ta shirya cikin doguwar riga tayi matuƙar kyau abinta.karb'ar mayafin momy tayi ta naɗa mata.tace "ma sha Allah daughter kinyi kyau".
Daga haka suka fito daga parlon suka nufi parking space, momy ta buɗe mota suka shiga taja suka fice daga gidan.sun ɗan yi tafiya mai nisa sannan suka iso wani ƙaton super market,guri momy ta samu tayi parking.suna shiga ba tare da lokaci ba momy ta rinƙa judo mata kaya,tun daga kan dogayen riguna da ƙana nan kayane,kayan bacci ne atamfofi ,leses ,shaddodi da kuma materials.
Daga nan kuma suka nufi ɓangaren braziers,panties, under wears da best.bayan sun gama da nan suka nufi ɓangaren kayan cosmetics da takalma.haka momy tayi ta jido mata kaya kamar bata san ciwon kuɗi ba.halimatu bin momy kawai take yi da kallo,saboda tsabar murna da farin cikin da take ciki ne yasa ta zubar da ƙwalla.momy ta rungume ta tana lallashin ta ce"ba kuka zakiyi ba, gode wa Allah zakiyi a bisa ni'imar da yayi miki"girgiza kai tayi alamar to .
Bayan sun gama suka tattara kayan suka nufi gurin biyan kuɗin,nan akayi total ɗin kuɗin aka faɗa musu, HALIMATU ta girgiza da jin yawan kuɗin.batare da b'ata lokaci ba momy ta bada a. t. m card ɗin ta aka cire kuɗin.daga nan ma'aikatan super market ɗin suka kwaso musu kayan zuwa wajen mota suka loda musu a cikin boot.
Bayan sun fito daga super market ɗin sai da suka tsaya a wani gidan hoto aka yiwa HALIMATU passport.sannan suka nufi wajen tailor ɗin da yake yiwa su momy da auta ɗinki,nan yasa aka auna HALIMATU momy ta biya kuɗin ɗinkin.daga nan kuma wani babban saloon suka nufa,suna shiga mai saloon ɗin tana ganin momy tace mata"hajiya barka da zuwa"ta faɗa fuskar ta ɗauke da murmushi,da yake momy nan take zuwa shiyasa suka santa.momy ta amsa fuskar ta a sake.
Matar ta ƙara duban momy a karo na biyu tace "hajiya me za'a yi muku"ta faɗa tare da kai duban ta ga HALIMATU.momy ta ce mata"gyaran gashi za'ayi mana tare da gyaran jiki da kuma ƙunshi ja da baƙi"matar tace"okay hajiya".