← Book details Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 80

Sashe 63

Halimatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Okay tom shikenan,pls ki gaya musu su yi sauri"
"To momy"
Daga haka suka yi sallama ta sauke wayar daga kunnen ta tare da kallon aunty amina ta ce,
"Aunty momy ta ce ku yi sauri ku fito drivern da ya kawo ni zai koma da ku"
Mikewa aunty Amina ta yi tare da cewa,
"Altine da rahine da sabuwa ku tashi mu tafi ana jiran mu a waje"
Miƙewa su ka yi gaba ɗayan su tare da ɗaukar mayafan su suka yafa,tun da dama a shirye suke,ba tare da ɓata lokaci ba suka fita zuwa bakin get ɗin in da habu driver ya ke ta faman jiran su,buɗe musu motar ya yi suka shiga ya ja motar ya tafi....✍🏻✍🏻

Please a yi haƙuri da wannan wallahi ai kine ya yi min yawa cikin kwana kin nan🙏🏻🙏🏻

Ina matuƙar godiya da addu'o'in ku a gare ni tare da fatan Alkhairi, ku ɗin na musamman ne a cikin zuciya ta, ina matuƙar alfahari da ku ƙwarai da gaske, Allah ubangiji ya saka muku da mafificin Alkhairin sa ya biya muku buƙatun ku na Alkhairi.🙏🏻🙏🏻

Daga alƙalamin

FATIMA BINTU ABDALLAHI(UMMU AYSHA)....✍🏻✍🏻

Share fisabilillahi.

Ga masu buƙatar littafin HALIMATU tun daga farko zuwa in da aka tsaya su tun tuɓeni ta wannan numbern wayar 👇🏻👇🏻

08162055134

💝💞 Halimatu💝💞

(Love, sacrifices, destiny & betrayed)

💝💞💝💞💝💞💝💞

Story & writing

By

FATIMA BINTU ABDALLAHI(UMMU AYSHA)..✍🏻✍🏻

Ƙarƙashin jagorancin

(MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION)

Golden pens....✍🏻✍🏻

💝💞💝💞💝💞💝💞

A 2024 novel

💝💞💝💞💝💞💝💞

Pages___________81&82

_____________haɗaɗɗen lefe ne aka kawo na ji da gani sosai da sosai,lefe ne wanda ya amsa sunan sa lefe,domin mukhtar ya yi rawar gani sosai ya ƙara ɗaga daraja da kimar halimatun sa,an zuba kaya iri-iri daban-daban abin dai sai wanda ya gani.
Babu kalar kayan da ba'a saka mata ba,akwati set takwas kamar an buɗe babban shago,babu kayan da suka siya anan gaba ɗaya kayan daga waje suka yi oder ɗin su babu na nan gida Nigeria,sarƙoƙin gwal kuwa ba a magana har dana ƙafa da na kai ,abin ku da masu abin da kan su.

Gaba ɗayan su sun girgiza da ganin yawan kayan musamman ma ƴan uwan ta na ƙauye sai abin ya ba su mutukar mamaki sabo da basu saba da ganin ko kwatan su ba,se yaba kayan ake yi ma sha Allah.
Babu kalar kayan da mukhtar bai saka mata ba,hatta dogwayen riguna tsadaddu na alfarma an zuba su dayawa sosai sabo da ya san tana son su sosai,a ɓangaren gwala-gwalai kuwa sai da aka saka mata set huɗu da kuma fashion fashion masu tsadar gaske,abin ku da masu harkar siyar da gwala-gwalan.
Kyakkyawan tukwici aka basu na alfarma da ban girma ga kuma snacks da lemuka masu yawa da aka basu,domin harka ce a ka yi ta ta ban girma sosai, kowanne ɓangare sun yaba ma ɗan uwan sa,haka taro ya tashi kowa yana sam barka.

Bayan tafiyar masu kawo kayan lefen ne mutane suka zauna suka ƙara kallon kayan da kyau,bayan sun gama ne momy ta umarci su rahine da su kwashe kayan gaba ɗaya sukai wani haɗaɗen bedroom dake a ƙasa,haka kuwa aka yi suka kwashe kayan gaba ɗayan su suka jere su a cikin bedroom ɗin suka rufe.
Kasancewar magariba ta gabato ya sa aunty AMINA ta ce musu su ta shi su tafe kar dare ya yi musu a hanya,waya momy ɗauka ta kirawo malam habu driver ta ce ya fito da mota ya mai da su gida.sallama suka yi wa momy ta raka su har bakin mota tare da yi musu godiya.

Har bakin get ɗin gidan baba malam habu driver ya kai su sannan ya juya ya tafi,suna shiga gidan basu zauna ba kowaccen su ta tafi ta je ta yi alwala ta gabatar da sallah,basu tashi a gurin ba sai da suka yi sallar isha'i sannan aka dasa sabuwar hira ana bada labarin lefen halimatu.
Kayan snacks ɗin da suka zo da su ne da drinks da su fried rice da kaji sune suka ɗakko su ka baje aka hauci ana hira,ita dai halimatu kasa cin komai ta yi gaba ɗaya ma kasa sakewa ta yi a gurin sai ta shi ta yi ta koma bedroom ɗin aunty Amina ta yi kwanciyar ta,da kallon tausayi aunty amina ta bita da shi domin ta san duk alhinin auren ne yake damun ta.

Altine ce ta bita da kallo tare da cewa,
"Halimatu kenan,ga dukkan alamu bata son yin auren nan yanzu,domin naga ko irin ɗokin nan da amare suke yi ita bata yi,in banda shirme Allah ya baki mai kuɗi sosai da sosai in da za ki je ki huta meye kuma na damuwa"
Ta ƙarasa maganar tare da tura ƙaton cake cikin bakin ta.
Rahine ce ta karɓe zancen da cewa,
"Ai ko tana so ko bata so dan ƙaniyar ta dole ne mu wanke ta mukai wa mijin ta ita,ban da abin ta ga sa'anninta can sun hayayyafa,daga masu haihuwar yara biyu sai masu haihuwar yara uku,yo ko sa'anin su HANNE sun yi haihuwa ɗaya ko biyu bare ita"
Ta ƙarasa maganar tana kai naman kaza cikin bakin ta.

Kallon su aunty Amina ta yi tare da cewa,
"Ni dai kar ku birki ta min ɗiya ta wallahi,dama momyn ta ta ce min da ƙyar ta lallaɓa ta ta yadda da auren"
Murmushi sabuwa ta yi tare da kallon aunty amina ta ce,
"Ai ni abin da na fuskanta bata son rabuwa da maman ta Sabo da ta shaƙu da ita sosai, ba ƙaramin tattalin ta take yi ba, Allah ya sa mijin da zata aura ya so ta sosai da sosai"
Gaba ɗayan su suka amsa da ameen.
Kallon aunty amina sabuwa ta yi tare da cewa,
"Tashi muje ki kunna min wuta akwai wani tsumin magani da zan dafawa halimatu ta fara sha tun yanzun nan,domin ina ga ma idan zata tafi tare da ita zamu tafi in ci gaba da yi mata gyaran mu na gargajiya kamar yadda na yiwa ƴar uwar ta Hanne"

Dariya aynty amina ta yi tare da miƙewa tsaye ta ce,
"Oh!, lallai amaren nan ana ji da su sosai ba kaɗan ba Inna,taso mu je kitchen ɗin"
Miƙewa sabuwa ta yi tare da shiga ɗakin da suka sauka ta ɗakko wani ɗan ƙaramin buhu ta bi bayan aunty amina zuwa cikin kitchen ɗin.
Wani irin tsumi sabuwa ta dafa mata mai bala'in kyau,domin yana da amfani sosai a jikin mace,yana gyara mace sosai ya saukar mata da ni'ima,sannan ta haɗa mata ingantacciyar zumar mata gangariya mai bala'in kyau irin tamu ta ƴan sokoto.
Tun a daren ta tilasta halimatu shan tsumin da zumar,da safe da ta yi break fast ta kuma sha,ai kuwa nan da nan jikin ta ya fara chanjawa.
Wanka ta yi ta shirya domin malam habu yana kan hanyar zuwa ɗakko ta,tana gama shirya wa ya iso suka wuce ita da inna sabuwa.

Ko da suka isa gidan sun iske masu gyara ana ta gyare-gyaren gidan,gaba ɗaya furniture's ɗin gidan an chanja su an saka sababbi sosai,ga wani irin fenti mai mugun kyau da ake yi a gidan gaba ɗaya, hatta da kitchen ɗin gidan an chanja masa abubuwa da dama na amfanin cikin sa,gida fa ya yi kyau sosai ma sha Allah.
Momy ta yi farin ciki sosai da zuwan inna sabuwa,domin ko ba komai zata taimaka musu da abubuwa da dama,ba tare da ɓata lokaci ba inna sabuwa ta yiwa momy bayanin abubuwan da ta haɗawa halimatu, sannan ta ƙara da cewa tana so ta haɗa mata kaza mai kyau da ƴan shila da zakara.

Ba ƙaramin daɗi momy ta ji ba da wannan karamcin na inna sabuwa,dama tana tunanin wacce zata kawo ta yi musu wannan aikin,nan take ta bawa inna sabuwa haɗin kai tafara shiryawa halimatu haɗaɗɗun magunguna, a cewar momy ai dole a gyara halimatu kodan ta ƙara shiga zuciyar mukhtar sosai.a gefe guda kuma mai gyaran jiki nata aikin ta babu wasa, haka suka saka ta a gaba kullum suna yi mata wani irin gyara ciki da waje.

∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆

A ɓangaren su mukhtar kuwa,shirye shirye ne suke yi sosai da sosai,ya gama gyaran gidan sa ko wanne part ɗin duka,gaba ɗaya furniture's ɗin gidan an fitar da su an chanja sababbi,part ɗin halimatu ne kawai ba a saka komai ba,hatta kitchen a ƙara gyara shi tare da chanja komai na ckin sa.
Domin a cewar sa amaryar sa sabuwa ce dal shi yasa komai zata yi amfani da shi dole ya kasance sabo ne shima.wani irin farin ciki yake ciki mara misaltuwa idan ya tuna saura sati ɗaya bikin su da halimatu,sun riga sun gama tsare tsaren su na ɓangaren su shi da babban aminin sa Nura,har sun bugo invitation sun rabawa abokanan su.

Sun shirya bayan ɗaurin aure za su yi walima su da abokan su,sai kuma wata gagarumar dinner da suka haɗa ranar ɗaurin aure da daddare har da su Hafiz da Meena,gaba ɗaya mukhtar ne ya ɗauki nauyin komai da za'a yi a wajen dinner ɗin.
Momy ta shirya musu gagarumar waleema ita da HANNE bayan ɗaurin aure,in da aka gayyaci malami da dama domin su faɗakar su kuma wa'zantar da mutane.

An shirya gift ɗin da za'a rabawa mutane wajen walimar kamar irin su,turmin atamfa,jakunkuna,daddumai,hijabai,dinner set,jugs,cups,plates, tissues,da dai sauran abubuwa da dama.akwati biyu manya mukhtar ya yi wa halimatu na kayan da zata saka na fitar biki tun daga ranar kamu har zuwa ranar da za a kaita ɗakin mijin ta,itama MEENA haka Hafiz ya aika mata da nata kayan fitar bikin,ya yin da aunty AMINA ta karɓi kuɗi gurin baba ta yiwa HANNE kala biyar na fitar biki,domin ta san kayan lefen ta baza su sawu anan ba gaskiya,duk da kasancewar shima Sama'ilan ya yi iya bakin ƙoƙarin sa wajen haɗa mata lefe, domin a can ƙauyen haɗejan har cewa a ka yi Sama'ila ya yi riya sosai,sabo da a cewar su wai kayan sun yi yawa.
Chapter 63 · 0% Book details